WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 1

????WATA TAFIYAR????       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

????????????????????????????????

*????✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????✨*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“????`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~????????~~~~~~~

PAID BOOK

                  Free Page    

               01

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank, 

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

       Babban gida ne irin na matsakaita ƙarfi,wanda ake ma laƙabi da GIDAN ƊAN NANNE,gida ne mai ɗauke da Shiyoyi biyar,wanda huɗu daga ciki,ya’yan Nanne ne a ciki da iyalansu,sai shiya ɗaya wanda tsohuwa Nanne ne a ciki.

 

Babban abin da zai ba mai karatu mamaki,shine yanda duk girman wannan gidan da zaran ƙarfe bakwai na yamma ta yi,to zaka ga ko wani shiya su na shigewa daki suna kullo ƙofofi da winduna,duk zafi duk sanyi.

Magana na ke ji kasa-kasa a ɗayan shiyar,wanda hakan yasa na leka dan ganin me ke faruwa, 

“Karima wai ba dake nake magana ba! 

” Mama dan Allah ki yi haƙuri,ina jira ne talgen ya ɗan ƙara nuna sai in tuƙa tuwan”

“Amma dai baki da hankali,kina ganin sauran mintina biyar ƙarfe bakwai ta yi,shine zaki ce sauran kaɗan,sauran kaɗan ɗin ƙaniyar ki! Tuwon banza tuwon wofi,da in sha dukan Aljannu ai gara mu bar tuwon a nan,in yaso mu kwana da yunwa! Maza sauke talgen ki shiga da murhun daki”

Ɓata fuska ta yi “Mama yanzun fa lokacin zafi ne,kuma shine za a shigar da murhu daki,bancin za a kulle ƙofa da windo,ta ina iska zai fita,Mama ai sai zafi ya kashe mu”

Dundu ta tika mata a baya”amma dai ke kam Karima an yi yar banzan ƴa, da dukan Aljannu ai gwara zafi ya kashe mu, na san yanzun za ki ji ta fara tunda ita yanzun garin ta ke wayewa”

Ba tabi ta kan Karima ba,ta hau shigar da murhu daki, da duk wani kayan amfanin su,harta da kwanun da suke fitsari a ciki, dan a cewar su,ba za su fito ba haka kawai kai ba kasha dukan ƙato ba kasha na Aljannu,shi yasa in ma ya kama su shiga da Fon kashi ne, to gwara su yi kashin a daki su kwana da warin in yaso da Asuba sa fito su zubar, lokacin daren ta yayi.

Ƙarfe bakwai dai-dai na bugawa,na fara jin wani irin ihu wanda da farko a hankali ya ke fitowa haɗe da magana,zuwa can sai kuma ihun ya fara ƙara ƙarfi,

A hankali nake takawa domin son zuwa ganin me ke faruwa,jin kamar ta shiyar tsakiya ne yasa na shiga,wani daki ne kaɗai wanda ƙofar shi yake a buɗe,

 Zaune take ƙafarta a tankwashe,yayin da suman kanta ya sauko ya rufe mata fuska ya sauko har gadon bayan ta,hakan yasa bana iya ganin fuskarta,riƙe take da ƙatuwar sanda a hannun ta,tana bugawa a gefen ta,idan ta buga a gabanta sai kuma ta juya gefen ta da sauri ta buga sandar da ƙarfi,can kuma sai ta shiga karkade jikin ta, yanda kasan dai wance ke dukan wani abu,haka kuma kamar wacce cinnaku ke bi a jiki, 

Ihu ta yi tana ƙara buga tsandar da karfi”ku mutu! Ku mutu!yauwa na kashe na shiga,saura kai, saura kai”nan ta shiga karkade jiki”ku sake ne, ku sauka a jiki na,ba inda zan je! ni wallahi ba zan bi ku ba “wani irin ihu mai razanarwa ta yi,wanda idan har ka  natsu ka saurara zaka fahimci irin rauni da gajiyawa dake tattare da me wannan muryar,can kuma kamar wacce aka kwato maganar da ƙarfi sai gashi ta fara karanta Ayatul Kursiyu,yi take da ƙarfin ta, tana ƙara mai-maitawa, 

Zuwa ƙarfe biyu na dare sai gashi ta fito, dai dai ƙaton bishiyar dake tsakar gidan ta tsaya tana sauraron kukan Mujiya,wanda ya karaɗe gaba ɗaya gidan, sam bashi da daɗin ji da sauraro,, domin idan kaji wannan kukan dole tsigar jikin ka ya tashi, 

Tsince-tsince ta keyi a tsakar gidan, sai da ta gama tara iya adadin da zata iya sannan ta shiga ɗaukar ɗai-ɗai tana jefa dutsen da ƙarfe saman bishiyar,tana jefa ma Mujiyar, kuma tana ci gaba da karatun da ƙarfi, wani lokaci kuma tayi ihu, harma ta ce”ba zan je ba,kuta kirana ba zan biku ba”wannan shi ne asalin abin da take yi, a kowace dare,wanda ya kasance yanzun tsayin watanni takwas kenan da wannan laluran ya same a halin gidan NANNE,wanda idan ta fara tun bakwai na marece sai ƙarfe biyar na asuba suke samun salama.

Washegari da safe,ɗakin Inna ta shiga da sallama,zaune suke suna ƙaryawa,

“Inna ina ƙwana”

“Lafiya klau ASMA’U, da fatan kin tashi lafiya”

“Na tashi lafiya Inna” Shigowar Baba ɗakin ne ya katse su,ni man wuri ya yi ya zauna, 

“Baba ina kwana”

“Da ban kwana ba zaki ganni? 

Shiru ta yi tana dukar da kai, 

” Saude,ba yarinyar nan abin karinta ta bar nan “duk yaran dake wurin kusan su biyar ba wanda ya ce komai,ita ma Inna ba ta ce komai ba sai miƙa mata wani kofin sulba da tayi, wanda ke dauke da koko,sai kosai data ɗibar mata” Na gode”ta na faɗar haka ta ɗauki abin karin ta ta fita,

Ɗaki ta koma ta ajiye sannan ta ƙara fita tana shiga ko wani shiya tana gaida su,wasu su amsa wasu su bita da harara,shiyan Baba Auwalu ne na ƙarshe da ta shiga, daga nan sai shiyar Nanne, a ƙofar shiga ne suka kusa cin karo da Hafiza,

Da sauri ta matsa baya”A’a Anty Asma’u zo ki shiga ”

Murmushi ta yi “mun tashi lafiya Hafiza”

“Lafiya klau Anty Asma’u”

“Naga kwana biyu ba ki zo kin ta yani hira ba,ko dai ke ma kin fara tsoro na ne Hafiza? 

“Inaa wallahi ba haka bane Anty na,kwana biyunga ina tsayawa karatu ne shi yasa, kuma kinsan mun kusa fara jarrabawa ƙarshen zango shi yasa,amma ai nasan kin san ko da kowa zai guje ki dan lalura ni ba zan taba gudun ki ba,saboda kin nuna mana gatan da ko waɗanda muke ciki daya basu nuna mana ba,yanzun dan lalura ya same ki sai kowa ya manta baya ya guje ki,to ni ban manta baya ba Anty na,insha Allah zuwa anjima zan zo musha hira”

Murmushi ta yi, wanda ke ƙara ma fuskar ta kyau da kwarjini,tana mai jin sanyi a zuciyar ta,dan kaf yaran gidan gudun ta suke, haka ma iyayen su,ba ma su  bari yaran su mata magana in ba ita Hafizan ba,kai Allah sarki duniya,ba ka sanin masoyin ka sai yau an wayi gari kana tare da wani lalura,a lokacin zaka gane masoyin ka ko maƙiyinka”shi kenan Hafiza sai na ganki”

“To Anty, zaki gaida Nanne ne”

“Eh,in ce dai idonta biyu”

“Idonta biyu,tana ma zaune ne”

Daganan sallamah suka yi,yayin da ita ta shiga dakin Nanne,tsohuwa mai ran ƙarfe,gaisawa suka yi, sannan ta ni me gefe ta zauna a rakube,

Kallon ta Nanne ta yi,tana murmushi ganin irin zaman da ta yi “Fettel”

Dago kai ta yi ta na kallon Kakar ta su, wacce duk duniya ita kaɗai ke kiranta da wannan sunan,Fettel yana nufin ƙarama. 

“Zo mana”

Tasowa ta yi a hankali ta tsugunna gaban ta. 

Riƙe mata hannu ta yi “me ne ne”

Hawaye ne ya zubo mata a kan kyakkyawan zagayayyen fuskanta,yayin data kara lumshe matsakaitan idanun ta,hakan ne ya ba ma zara-zaran gashin idonta damar kwantawa yayin da wasu hawayen suka ƙara saukowa, madai-daicin bakin ta mai dan faɗi ta buɗe “Nanne kowa goduna ya ke saboda lalura na,ba bu mai son zama kusa da ni,gashi saboda ni kuna ta kashe kuɗin ku ke da Baba Mudansir akai na,Nanne bazan warke ba ko? gashi ma har wasu suna kirana mahaukaciya”

Ita ma Nanne kuka ta ke”zaki warke Fettel in sha Allahu, ita kuma SHU’UMAR data miki wannan danyan aikin ba dan ta wulakanta ki ba,sai dan ta kashe ki ta raba ki da rayuwar ki gaba daya,Allah ba zai bata sa a ba Insha Allah,tunda gashi duk inda mu kaje ita ake cewa,kai Allah ya isar mana tsakanin mu da wannan shaidaniyar matar,za taga abin ta da yardan Allah “

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button