DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

“hjyr ka da muka yi waya da ita a beach itace ta rasu”kallon mamaki ya binki da shi
“baki sani ba” girgiza masa kai nayi da alamar tausayi a fuskata, nan ya shiga bani labarin mutuwar ta da ɗaurin auren mu da guduwar da yayi, ta tausaya masa sosai wai ace mijina ne ya shiga wannan halin amma ban sani ba, koda yake ba laifi na bane duk rashin sani ne ya kawo haka, amma in sha Allah na sha alwashin sai na zama mace me shayar da mijin ta daɗina faɗa araina

ƙara tausar shi nayi tare da bashi haƙuri akan rashin hjyrsa
“haba ba komai ai yanzu ya zama tsohon zance” ya faɗa, shiru ne ya biyo baya, ganin shirun na naiman yin yawa ya sani na ce
“kace zaka ban tukwicin girkin” na faɗa ina karyar da kaina
“nawa kike so faɗi” rufe ido na nayi na ɗora hannuna akan lips ɗina tare da cewa
“guda goma” shiru naji kmar ba mutum a kusa da ni hakan ne ya sani buɗe ido na, yana zaune bai motsa yana kallona,
“baka ce komai ba ko bazaka bada tukwicin ba” murmushi yayi ya jamin hancin na taer da miƙe wa ya kama tafiya, binshi nayi ina shagwaɓar kaifa kace zaka bani tukwici har muka shige ɗakinsa ina yi masa mita shi kuwa ko ƙala baice ba sai ma ban ɗaki da ya shiga wanda ni kuma na samu wuri a gadonsa na kwanta

     da daddare bayan na gama komai na koma ɗakin nasa don in kwanta, a kwance na same shi inda nima naje na kwanta kusa da shi, ban daɗe da kwanciya ba ya tashi ya shiga banɗaki, da alwalar sa ya fito ya tada sallah, tun yana yi ina ƙirga raka'a nawa yayi har bacci ya kwashe ni be idar ba, sai ji nayi ana cemin ki tashi an kira assalatu


 tashi nayi ina yin magagi don zuwa toilet nan naci tuntuɓe da shinfiɗar sa wato kenan ma a ƙasa ya kwana kenan ko na faɗa araina, raina bai min daɗi ba me yasa yake min haka na faɗa araina, toilet na faɗa nayo alwala ta na fito na tada sallah, har na idar nayi lazimi na tare da azkar bai dawo ba don haka kawai sai na ɗan gyara gadon tare da kwashe shinfiɗar tasa nai part ɗina don haɗa mana breakfast



      *************

wasan saurayi da budurwa muka koma yi nida aliyu inda sam baya wani sakan min fuska sosai ba kasa fai ba ma ya fiya magana sai dai in nayi abu yayi murmushin nan nasa, babu wani irin technich da ban bi ba don ganin na jawo hankalinsa kaina a banza wai an shuka dusa, kai da ƙarshe ma daya ga abin nawa ba na ƙare bane sai ya tsiri azimi da sallah dare, ina shigowa ɗakin in ya tsiri sallah har sai na yi bacci yake dainawa ga idon nawa da shegen son bacci kamar na kasa, azimi kwa kullum kusan yana cikisa wai irin azimin annabi dauda yake son yi

   Yau ta kama monday an tashi da sanyi sosai kasancewan ruwan saman saman da aka kwana ana tafkawa, kuma har yanzu anayi don aliyu ko masallaci baije ba don ruwa a ɗakin sa mukayi tare, ko da muka idar na yi lazimina tare da azkar na idar sai nazo gaban sa yana jan carbi 

“yallaɓai me zaka karya da shine yau inje in haɗa maka da wuri”
“jekiyi kwanciyar ki yau azimi nake yi”ƙwalalo ido nayi yau monday fa”
“to menene ba a ai ranar monday, azimi me falala ma da ma’aiki (saw) da kansa yace muyi, ai banga me zai sani ƙinyin azimin yau ba” girgiza kaina nayi lallai ma mutumin nan na faɗa araina, jiya fa yayi lahadi amma shine yau ma ya tsiri shi

tashi nayi naje na ɗibo ruwa afrigde na zo zan wuce kenan nayi tintiɓe ruwa ya ɓare tas a kan shinfiɗar malam aliyu sarkin azimi da ƙiyamul layli, baice min komai ba ganin haka ne ya sani kwasar shinfiɗar nayi tafi don in shan ya masa

haushin daya bani yasani shanya masa kayan shinfiɗar tasa aruwa, nima garin mugunta ƴar nightie ɗin da ke jika na ta jiƙe, cire ta nayi na ɗaura zani na kwanta, ko daya tashi kwanciya yaje yaga a inda na shanya masa kayan sai ya dawo
“matsa can ƙarshen gadon zan kwanta” naji yace, bance komai ba na matsa sosai har ina ɗan takure kaina da jikin bangon don kar jikin mu ya haɗu, lallai ma wannan mutumin in kasan wata ai baka san wata ba na faɗa rai na

    kwanciya yai tare da jan bargo ya rufe kanshi, bai daɗe da kwanciya ba aka doka wata irin tsawa wacce tasani wurgi da zanin da ke jikina na shige cikin bargon nasa tare da maƙalƙale shi

“lfy” naji yace
“tsoro nake ji” na bashi ansa
“tsawa ce ba komai koma wuri ki” ƙara maƙalƙale shi nayi tare da sa masa kuka
“ni tsoro nake ji” kuma wallahi ba qani tsoron tsawa da nake ji
“shhhhhhh its ok” ya faɗa yana ɗan shafamin bayana alamar lallashi
“wait tsaya ba kaya a jikin ki” ya faɗa, ƙara rushe mai nayi da kuka tare da kara shige masa jiki

“sshhhhh nace ya isa haka ko ai gani akusa da ke ba inda zanje” ya faɗa tare da cigaba da shafe min jikina wannan karan bada sigar lallashi bane

 nidai bansan hawa ba ban san sauka ba sai dai kawai jinayk minkna ya maida ni cikakkiyar mace thank u thank u thank u shukran shukran kawai yake faɗi duk kunyar shi sai ta kama ni, ko da muka ɗan nitsa sai naji ya jaa min hancina

“auch, da zafi fa”
“naughty girl kin karya min azimina” kunya ce ta kamani na ƙara shige wa jikin sa, shi kuma ya ƙara rungumeni tare da zuba min ruwan kisses????????????????????
[7:43PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

ya muka ji da alamar shigowar sanyi Allah ya sa mu wuce lfy, mata sai a tanadi kayan harka???????? don kuwa maza in akace sanyi yayi abin sai a slow da fatan zamu dinga kula da tsaftar jiki Allah yasa mu wanye ƙalau

  Page:21????



   Rayuwa ta sauya mana dani da ɗan mijina, nida tun ran da ya mayar dani matar sa ban kuma ganin shi yayi ƙiyamul layli ko azimin na shi ba a zuciyata nakan ce daman ba don Allah ake yi ba, sosai na matsa wa aliyu akan muje china ya ƙara ganin dr. ɗin nasa, daga ƙarshe ya yarda in da yai mana visa tare muka luluƙa birnin sin, 

Mun sauka Beijing daka birnin china inda muka sauka ana suburda sanyi, don haka kullum muma manne da aliyu na???? love one tin tin, yaje ya ga dr. ɗin nasa inda ya shaida masa ba wani matsala amma ya dinga gujewa da abinda zai dinga ɓata mata rai, kasancewar da turanciyayi bayanin nasa ya sa na ɗan fahimci wani abin, amma ba duka kasancewar accent ɗin chinese ya fita daga cikin maganar sa don haka ganewa sai ka nutsu sosai

sai yanzu na fahimci dalilin da zakuga sanyi na wucewa sai kiga mata suna laulayi, ashe su maza kasuwar su ce take buɗewa in ana sanyi, ko ya ka ɗan taba namiji sai kaji ka a ƙasan sa, ba damar kana cikin murna kace zaka rungume mijinka abi na gaba da zaka fuskanta shine fuskar ka tana kallon ceiling ???????? wayyo gani sabon shiga amma hakan bai sa aliyu tausaya min ba



watan mu biyu a china kasancewar nan ma wani wurin aiki wa mijina kuma ayadda naji anan ya fara samun arziƙin sa, nakan bishi deport ɗin in har jirgin shi daya ɗauko kaya ya iso, ina mamakin ganin irin maka makan jiragen ruwan da mijina ya mallaka at his age, aiki ne sosai ba ƙarami baya faɗa




 sai da muka shafe wata biyu sannan muka kama hanya inda muka sauka ƙasa mai tsarki, nai murna nai kuka wai yau nice a ƙasa mai tsarki, mun yi ziyarar mu sosai a madina, ba inda bamu je na tahiri, inda da muka je dutsen uhud na siya dabinon ajwa don gashi nan baja baja kamar basa so, akwai ɗanye akwai busash she ni dai busashen na siya don tsaraba zanyi




satin mu biyu a madina mukai makka sai da muka tsaya a zul hulayfa inda ake ɗaukar niyyar ummara in ka taho daga madina masallaci ne babba sosai da banɗaku na saboda wankan ɗaukar niyya umma,


   mu ka ɗau niyyar umara, mukai wanka muka sa haramin tare da yin sallah raka'a biyu kamar yadda yake a sunnan sannan muka shiga mota muka kama hanyar makka



   tafiyace miƙaƙƙiya daga madina zuwa makka inda nai ta mamakin wai wannan doguwar tafiyar ma'aiki (saw) da sayyidina abubakar suka yi daga makka zuwa madina don tabbatar da addinin islama, wanda mu muka zo muka same shi a cikin ruwan sanyi gaskiya dole ne ajinjina musu



        sai ƙarfe biyun dare sannan muka ƙarasa makka , wai nice yau a garin makka abin kamar a mafarki, direct hotel muka nufa wanda yake a unguwar bin laden, bashi da nisa sosai da haramin,



sai gab da asuba sannan muka je haramin don yin umara, tafkeken masallaci na ci karo da shi, nai godiya ga  ubangijin talikai, nayi addu'ar shiga masallaci na shiga, muka shiga har can ciki inda haramin yake, ɗawafi muka kama yi sannan bayan mun gama aliyu ya jani har jikin ka'aba don in sunbace ta tare da yi adda'a nayi kuwa sosai da sosai har mahaifiyata da bata duniyar nan sai da tasan na zo ɗaki mai tsarki yau sannan daga ƙarshe na haɗa da dukkan ƴen uwa musulmai duk na addu'e mu da fatan mai duka zai karɓa. 

V

Mm

      ko da muka gama ummara, mu ka koma masaukin mu don hutawa, kwanan mu takwas a makka sannan muka wuce jidda inda daga nan muka wuce dubai don aliyu yana da aikin da zai yi anan, kwanan mu huɗu a dubai ya gama abinda ya kawo shi daga nan sai ya tsiri cewar muyi yawo don ganin gari, ni kuma a lkcn ba abinda nake so da wuce bacci, da na ɗan zauna sai gyangyaɗi sai bacci, na ɗauka ko na gajiya ne har aliyu yana tsokana ta wai bazan iya yaƙi ba tunda daga yin ummara na tsiri bacci ba ji ba gani




ganin baccin nawa kamar harda rashin lfy yasa aliyu matsa min muka je asibiti, ko da muka je asibiti bayan dogon bincike ya nuna cewar ina da shigar ciki har na sati takwas da kwana biyar, inda alamu suka nuna a china na samu wannan cikin



  farin ciki waken aliyu kamar ya zuba a ƙasa ya sha yai farin ciki sosai har kyauta yayi wa dr ɗin daya dubani mai tsoka,  a hanyar mu ta zuwa gida ne ya dameni 

“wai nine nayi cikin nan, da gaske, don Allah ya akayi nayi cikin nan, kamar mafarki fa haka nake gani wai nima daga ƙarshe dai zan ga wanda zan ki ra nawa na kaina” ya dinga sunbatun sa shi kaɗai ni daya ishe ni ma kwanciyata nayi nayi kamar ina bacci har na gasken ya zo yayi awon gaba dani

  sama kawai naji anyi dani ashe har mun zo hotel ɗin namu bansani ba, da muka shiga ya dire ni akan gado 

“wannan cikin naki calls 4 celebration, dole ne muyi celebrating samun ciki ya faɗa cire rigar sa dana ga yana yi yasani na fahimci irin celebration ɗin da zamuyi kai namiji dai sai dai abarshi na faɗa araina

  haka aliyu yai ta nan nan da ni akan cikin nan dana samu har tambaya yake yi wai ina ji motsi don Allah kunji wani zance, ko da muka koma nigeria ma haka kulawar tashi bata ragi ba nan ina samun kulawa sosai daga gare shi ko yana office ne yai ta doka min kira mu wuni muna abu ɗaya yana tambayata ya nake ji ko ya fara motsi ni sai dai in bishi da a a har yanzu, da abinya ishe ahi wai babyn be fara motsi ba ya kwashe ni sai asibiti inda yai musu compain na cewar babyn bai fara motsi ba




    an duba ni inda aka tabbatar da lafiyar babyn sannan aka ce mana motsi sai nan da wata uku a lkcn yana da wata biyar kenan sannan hankalin aliyu ya kwanta muka dawo gida, bana laulayi ko kaɗan kuma duk abin da na samu ina ci ina ci ƙamshin turare ne kawai bana so don haka dole aliyu ya hakura da sawa



 yau tj ya kawo mana ziyara, ya shigo har part ɗina don mu gaisa, inda naji ƙamshin turaren sa yai min daɗi har wani lumshe ido nake don daɗin sa da nake ji, suka ƙaraci hirar su ba abinda na fahimta tunda yawancin maganar tasun akan harkokin su ne don haka ne ma yasa ban samu baki ba ni dai kawai shaƙar ƙamshin turaren nake yi ina lumshe ido na kamar mai jin bacci



 ko da tj ya tashi tafiya sai na ɗan bata raina,

“lfy kuwa madam” Inji tj
“ƙamshin turaren ka yayi min” na amsa, aliyu ne ya doka masa harara
“sai ka cire rigar taka ka ajiye mata kusa da ita muje in baka wasu kayan daga nan ka raka ni nima in siyo irin shi, ba dole ta so turaren ba ka sako turaren mata sai kace wani ɗan daudu”

sai da suka je part ɗin sa ya bashi kaya ya saka sannan suka kawo min wadanda ya cire har wani kai fuskata nake yi kusa da rigar in shaƙa ina jin daɗi

ko da suka daso daga siyan turaren aliyu ya baje jikin sa da turaren ko daya zauna kusa da ni har wani ƙara shishi shige masa nake yi ina shaƙa wannan ne ya bashi damar sauke min nauyin da ke marar sa a sauƙaƙe ba tare da nayi complain ɗin banaso

 mijina ya samu dama ta don haka cin karensa yake yi babu babbaka akaina ba dare ba rana da ya bushi iska abinsa sai yaje ya bazo turaren sa ya matso kusa dani yasan cewar ina jin ƙamshin nan zan dinga shishi shige shi kuwa dama abinda yake so kenan sai yaci karen sa babu babbaka



 to kunsan abin me ciki ba tabbas don haka Allah ya taimake ni na daina son ƙamshin turare nan, ranar kuwa ya bazo shi ya tinkari gadon da nake kwance zai kwanta da amai ya taso min da gudu nayi banɗaki sai da na amayar da duk wani abinda yake cikina sannan naji daɗi ko da ya tambaye ni ma ya samin amai sai nace masa warin turaren sa ne bana so aikuwa wanka ya je yayi sosai ya fito amma duk da haka bai daina ƙamshin bahi daman sawars mugunta yayi shiyasa Allah ya kama,  don haka dole yau angulu ta koma gidan ta tsamiya don kuwa shinfiɗa yayi a ƙasa ya kwanta don bana son warin tj yau ya sha zagi yau sosai wai bai gaya mai ba cewar abin nawa ba permanent bane shi duk ya sakankance, ina jinshi bance komai ba sai ma dai bacci daya dauke ni me daɗin gaske

[7:44PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

Page :22????



   sai da na wahalar da aliyu sosai sannan na haƙura na cemasa ya daina warin turaren ba ƙaramar kewata yayi ba na gane hakan ne ta yadda ya dinga rawar jiki a kaina hmmm 



 Cikina ya fara fitowa, nan rawar kan aliyu ya kuma ƙaruwa sai ya zauna yai ta hira da cikin, siyayya kuwa yi yake yi ba kama hannun yaro hatta kayan funitures sai da ya canza min ni kuma na aikawa  khadija nawa


 Gyaran gidan ya shiga yi da yaga lkcn haihuwa ya kara matsowa, ko kaɗan baya jin kuɗin sa in dai aka zo maganar cikin  jikina ne kuɗi kawai yake fitar wa kamar baisan zafin su ba, ko na yi masa magana sai yace bazaki gane bane, yanzu zanga wanda kullum zan dinga tunawa cewar nima yanzu ga jinina a kusa da ni, yakan ƙulle min kai da maganganun sa tare da soki burutsu don haka nake ɗaukar zancen nasa




       Lahadi da daddare muka shirya domin zuwa asibiti awo, na ci kwalliyata sosai kamar ba me ciki ba , muka ɗau hanya, ko da muka je asibitin da nake awo sai aka ce likitan bata nan don haka sai dai muga wani, shi kuwa aliyu ba abinda ya tsana da ya wuce ace namiji ne zai ganni don haka tun farko ya nemi likita mace ta zam dr ɗina,



ko da na faɗawa aliyu ceqar bata nan si dai namiji, sai yace shi bai yadda ba bari kawai ya kirata, ko da aka kira ta sai tace mu same ta general hospital



nan muka je don ta duba mu, labour room ta sa na je don tayi min awon a can, ko da naje da mutane don hka sai tace inɗan jira kaɗan, tana cikin duba aka zo aka kira ta emergency don haka sai ta fita, sai ta sa wata dr ɗin ta ci gaba da duba mu,





         ko da zo sai ta kalle mu tace

“duk naƙuda kuke yi” dukaan su suka ansa banda ni, ta kalle ni tayi murmushi
“daga gani har yanzu bata matse ki sosai ba shiyas kika ci wannan kwalliyar”

  sai da ta gama duba su tsab snnan tace min in zo, kamar zan mata musu sai dai na tafi, ta sani na kwanta ta duba ni 

“kina 2cm,nan da 4hrs zaki iya haihuwa, kije kiyi ta zaga yawa” saukowa nayijikina yai sanyi wai zan haihu

 ko da na fito na tarar da aliyu yana jira na 

“me suka ce”
“nan da 4hrs zan haihu”
“wattttt kina nufin nan da awa 4 ƙwarara ina nan da baby na a hannu” ya tambaye ni gyaɗa mas kai nayi

  nan ya rikiɗe sai sunbatu yake duk ya bi ya ɗaga hankalinsa wai ance haihuwa da wuya, shi bai shirya ba kawai mu tafi gida ma dawo nan gaba idan ya shirya, ya kalle ni 

“zainab bana son ki wahala wajen fito da babyn nan mu gudu gida kawai kinga dole haihuwar ta haƙura har sai lkcn da muka shirya ko” ya faɗa yana ja min hannu alamar mu bar wurin

   ni da nake shirin fito da babyn hankalina ya fi nashi kwanciya

“hubbi, ba komai am alright, we can do together, baby yace yau yake son yazo ku haɗu pls lets grant our babys first wish” na faɗa masa ina mai tallafar fudkarshi don mu haɗa ido, wannan abinda nai masa ba karamin kwantar masa da hankali yayi ba har ya fara rakani takawar

  sai ƙarfe 1:30 na dare sannan na shiga cikin labour room din lkcn wahalar haihuwa ta fara damƙata, na sha wahala sosai bini bini naga call ɗin aliyi kon haihu sai ince masa da saura



 ba ni na haihu ba sai da asuba, byan ma anshiga masallaci sallah asuba sannan Allah ya suke ni lfy na haifi ɗana namiji kyakkyawa fari tas da shi




    ya na idar da sllah y kirani na faɗa masa na sauka, kashe wayar kawai naji yayi, inda daga baya ya kirani yai ta min godiya tare da addua, aka shirya baby nima akai min duk abinda  ya dace ai min da karfe 6:00 aliyu ya kira ni 

“ga abinci nan na sa an miki za a shigo miki da shi ki ci, naji ance me jego ta dinha cin abinci sosai ko ruwan nono ya zo ko” to kawai nace

      na ɗauka abinci ne irin baifi food flask biyu ba, ba sai naga sai shigo da abinci ake yi, dariya abin ya bani ohh aliyu komai naka daban ne na faɗa arai na, bismillah naƴi wa nurses ɗin da kowa da kowa har ƴen uwana masu naƙuda da waɗanda suka haihu sai da suka sa albarka atakaice da ɗan karamar liyafa akai da safen nan 





   Sai ƙarfe takwasa sannan aka sallame ko da aliyu ya ga babyn har ƴar ƙwalla yayi tare da kissing ɗin babyn, San nan muka kama hanyar gida,muna komawa gida naga duk ma'aikatan gidan sun fito domin tarar mu, naji daɗin hakan da suka yi mana 



ɗakina na wuce direct aliyu ɗauke da babyn ko da muka je zama nayi don bansan abin da zanyi ba, kallona yayi yace 

“madam lfy ko” ya tambaye ni yana kashe min ido
“ba komai, kawai dai ban iya wankan baby bane”
“oh na ɗauka ma ko har kin fara missing ɗine ne, kar ki damu akwai wacce zata zo”

   murmushi nayi masa nayi masa godiya nasan cikin *dangin sa* zai sa wata ta zo min, wataya ta na ɗauka na fara kira ina faɗawa mutane ga mamaki su khadija ma sun sani wai baba ne ya faɗa mu, na kira number mama ban samu ba nasan zata ce zata zo suna mama kenan na faɗa 


  aliyu ne ya ƙara shigowa ɗakin ɗauke da babyn kasancewar dama ya fita da shi don masu aiki su ganshi

“madam kin ga yaron nan kowa sai cewa yake yi kamar mu ɗaya” ya faɗa ya kallon babyn
“hmmm kawai suna faɗa ne amma ba abinda ya ɗauko naka,sai haske” saboda babyn fari ne sosai
“kina dai baƙin ciki, kin ga yaro jinin larabawa”
“yauwa hubbi, pls ka koya wa babyn nan namu larabci kaji”
“ce miki akayi na iya”
“ba balarabe bane kai”
“mahaifiyata ce balarabiyar saudiya, mahaifina baƙi ne kamar ki” ya faɗa yana lakuta min hanci
“baka girma da ita bane” na kuma jeho masa tambaya, don a gaskiya babu wanda na sani a dangin sa tunda muka yi aure sai tj kawai

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Leave a Reply

Back to top button