JIDDATUL KHAIRJIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

JIDDATUL KHAIR 58

Parking yayi ya sauka yana kallon mai gadi dake xaune a waje, wanda har ya mike xai bude gate a tunaninsa Ahmad ne sai ya ga akasin haka, suka gaisa Abuturrab ya shafa kansa yace “Suna ciki?” Yace “Aa gaskiya basu jima da fita ba” Yace “Ba kowa a ciki yanxu?” Mai gadin yace “Babu kowa, ko awa daya basu yi da fita ba Yallabai” Abuturrab ya tsaya kallonsa, Mai gadin na washe baki yace “Da na ga motar

ma na xata su ne ai” Abuturrab yace “Ohk, shkkn ba ma sai kace masu na xo ba… Sai anjima” Daga haka ya koma motarsa ya shiga, a hankali yake driving din… Parking yayi ya jinginar da kansa da kujera, bayan few seconds ya dau jotter a cikin motarsa da biro, ya cire pieces daya a ciki, kan steering ya ajiye takardan ya fara rubutu a jiki, bayan some minutes ya gama rubuta abinda xai rubuta ya maida biron

sannan ya linke takardan gently, ya kashe motar ya sauka ya shiga cikin gidan, knocking yyi jin kofar a kulle, cikin minti kadan Maimoon ta bude kofar, matsawa tayi tana kallonsa daga sama har kasa, lkci daya ya daure fuska, ta xaro ido tace “Au, sannu da xuwa yaya” Da sauri ta juya ta koma parlon, Umma dake xaune Jiddah ma na xaune kasa daga kusa da ita ta daga kai tana kallonsa, tunda Jiddah ta kallesa

sau daya ta sunkuyar da kanta, Ya karasa parlon ya xauna yana kallon Umma yace “Ina yini Umma” Tace “Lafiya lau, aka ce yau xaka yi tafiyar?” Yace “Ehh in sha Allah…” Sai kuma ya shafa kansa yace “Naga ban xo mun yi sallama bane” Umma tace “Bayan wanda mu ka yi a gidan Yaya?” Ya sunkuyar da kansa, Maimoon dai na tsaye sai kallonsa take, idan ta kallesa sai ta kalli Jiddah da taki dago kanta sai wasa da

fingers dinta take, Umma tace “Toh ki kawo masa ruwa Maimoon” Maimoon tace “To Umma…” Har ta kai bakin kofar kitchen din ta tsaya tana kallon Jiddah tace “Jiddoh xan xuba moringa din yanxu, ki xo ki gani” Jiddah ta d’an kalleta, Umma tace “Ba kince kina son koya ba, ki tashi ki je” Mikewa Jiddah tayi ta wuce kitchen din, da gefen ido ya bi ta da kallo a sace yanda Umma ma baxata sani ba, Umma tace

“Amma daxu mun yi waya da Ahmad yace xai je kai ka airport…” yace “Ehh Umma, xan koma yanxu.. nan da awa daya da rabi ne flight din” Umma tace “Toh Allah ubangiji ya tsare, ya kai ku lafiya ya dawo da ku lfya” Yace “Ameen” Jiddah na shigowa kitchen Maimoon ta kulle tana kallonta tace “Kawai sai

naga yaya Aliyu, alhalin for almost 2 weeks bai xo gidan nan ba” Jiddah ta hade rai tace “Toh me yasa kike gaya min?” Dariya Maimoon tayi har da tafe hannu tace “Aa ni fa kawai hira nake maki wllh…” Jiddah ta juya xata fita Maimoon ta rikota tana dariya tace “Ke wllh ni kawai jajantawa nake son mu yi da

ke” Jiddah tace “Ki sakeni fita xan yi” Maimoon tace “Dallah ki tsaya in hada miyan tukunna, to meye don nace kawai sai ga yaya Aliyu, au ni na ma xata Safiyya ce nake maki wannan maganan, abinda mun saba gulman mu haka, amma ke kina so ki min wata fassara” Jiddah dai bata ce komai ba sai kallon

miyan dake saman gas take, Maimoon ta tafi ta dau ruwa da coke ta daura kan tray ta dawo tana kallon Jiddah ta mika mata tace “Don Allah ki kai masa kar miyan ya kone” Da sauri Jiddah ta matsa ta tafi gun miyan tace “Bar min miyan xan dinga dubawa kije ki dawo” Maimoon ta hade rai tace “Kika san me xan

ma miyan to?? Ni wllh wani lokacin kina bani mamaki, meye a ciki kawai dai kije ki dungurar masa da tray din a gabansa ki taho, wllh ba don miyan ba ni da kaina xan kai, ai ni aka sa ba ke ba” Maimoon ta d’an yi tsaki ta ajiye tray din tace “Haba, sai kace warce nace ki kai ma wani dodo ruwan sha” Gun miyan ta tafi tana juyawa, sai kuma ta nufi kofa a tunanin Jiddah daukan ruwan xata yi ta kai masa, sai taga

bata dauka ba, Maimoon na fita parlor ta kullo kofar kitchen din tana kallon Umma tace “Umma wai Aunty Malika na ta kiranki, kamar wayarki na daki koh?” Umma tace “Ta kira ki ne?” Maimoon na d’an rawan baki tace “Haka dai tace min” Mikewa Umma tayi ta nufi hanyar dakinta tana cewa “To ai wayar na daki” Maimoon ta koma kitchen da sauri tana ci gaba da juye juyen miya bayan gas din ma a kashe

yake tace “Kawai minti nawa kin kai ruwa kin dawo, idan ba dai da akwai wani abu a ranki da kike boye ma mutane ba” Jiddah dai bata ce komai ba sai kallon tray din take, Maimoon banda satan kallonta babu abinda take, daukan tray din Jiddah tayi daga karshe ta nufi kofa tana tafiya kamar bata son yi, ta bude

ta fita, sai da ta shigo parlor taga Umma bata nan, ta fara kalle kalle, yana ganin haka ya mike, ta dungurar da ruwan kamar yanda Maimoon tace, xata juya yyi saurin kamo hannunta, ta juya ta

marairaice masa murya kasa kasa tace “Wllh xan maka ihu ka sakeni, ka daina min abun nn da kake yi bana so” jan hancinta yayi har sai da ta ji xafi sannan ya saka mata takardan hannunsa a tafin hannunta yana kallon kwayar idonta, fixge hannunta tayi daga rikon da yayi mata kusan a guje tayi hanyar dakin

amma takardan da ya bata na hannunta har sannan, ya bi ta da kallo kafin ya juya, ido hudu suka yi da Maimoon da ta d’an bude kofar kitchen din tana lekosu, ai da sauri ta yi jamming kofar bayan sun hada ido, yayi hanyar kitchen din, saura kadan ta tunkude miyan kan gas din bayan ya shigo kitchen din, sai

xare katon idonta take tace “Xa a xubo maka abincin ne Yaya?” Janyo hannunta yayi yace “Ba dai kin iya munafurci ba??” a gigice tace “Don girman Allah kayi hakuri yaya, naje kulle kofa ne sai ka gan ni…” Bai saurareta ba ya bude kofar kitchen din ya fita yana rike da hannunta…. Umma ce ta fito parlor tace “Au,

tafiya yayi shashashan?” Babu kowa parlon balle a bata amsa, Ta wuce dakinsu Jiddah taga Jiddah kadai a dakin tace “Aliyun ya tafi ne?” Jiddah tace “Ina daki ban sani ba” Umma tace “Toh ga shi ki amso min kati na dubu daya a waje” Jiddah ta d’an xaro ido amma bata ce komai ba ta amshi kudin gabanta na

faduwa, Umma na fita dakin ta saka hijab dinta ta fita ita ma, duk jikinta a sanyaye ta fita compound, tana isa gate ta leka waje ta ga motar Ahmad instead, amma Abuturrab ne a ciki Maimoon na tsaye daga window din kusa da shi ta daddage tana cewa “Ni dai wllh ka tura yanxu kafin ka tafi yaya, haka kawai

idan ka je ka manta bayan na sanka da mantuwa, kawai bari in kira maka account number din ai yana kai na” Ko kallonsu Jiddah bata sake yi ba ta nufi kantin da xata amso kati, Abuturrab na danna wayarsa yace “Call the account number” tana washe baki ta shiga kira masa account number dinta har ta gama,

snn ta fara kallon wayarta dake hannunta tana murmushi, cikin few seconds sai ga alert, ta duba da sauri taga dubu hamsin, wani tsalle ta doka tana tafe hannu sannan tayi masa blow din kisses tace “Nagode sosai yayana, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara maka budi, Allah ya kai mana kai lafiya ya dawo da kai lafiya” Komawa baya tayi ganin ya tada motarsa tana daga masa hannu har ya bar layin, baki har

kunne ta shige cikin gida, Jiddah ma ta shiga gidan don duk tana kallon abinda Maimoon take a titi…. Dakin Umma jiddah ta tafi ta kai mata katin sannan ta fito ta shiga nasu dakin, gaban madubi ta tafi ta dau takardan da ta ajiye bayan ta shigo dakin daxu, daukan takardan tayi ta shiga warwarewa, haka kawai ta ji gabanta na faduwa, ganin ta kusa gama budesa ta rufe idonta, sai da ta warware gaba daya

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button