
Kissing lips ɗina yayi sannan yace
“ga lips ɗin nan naki da kyau gashi da tambaya, bari inje inga me akeyi a wajen nan” ya juya ya fice, aliyu ya iya waskewa idan baya son ansa tambaya
ban damu ba saboda yanzu nasan na haihu dole ƴen uwansa su zo suna, na faɗa a raina, daga dukkan alamu baya son magana akan *dangin sa* har ya kai ƙofar fita ya juyo
“wai yaushe zaki gama wannan abin naki ne”
“wane abu” na tambaye shi da mamaki
“ina nufin yaushe zaki warke, don insan kwana nawa zanyi ban same ki ba” ya faɗa yana kashe min ido
oh Allah ni abu yau Allah ya haɗa ni da miji ɗan world nafaɗa araina
“ko da yake ai akwai ƴen dabaru da zamu dinga yi ko,akwai darussa sosai da ya kamata ace kinyi degree akan su a harkar nan, amma ba komai tunda har lkcn yazo zamu fara darasin mu daga yau ba ɗaga kafa” fahinta yayi cewar duk kunya ce ta rufe ni yasa shi fita yana dariyar mugunta tare da cewa
“ki shirya darasin na yau na musammam ne”
Mama ce ta shigo tare da amina ƴar autar mu, mamaki ne ya kamani ganin ta kwatsam a gida na
“mama” na faɗa ina zare ido
“na’am me jego, kinyi mamakin ganin mu ko, ai mijinki yana kira da asuba yace kin haihu baban ku yace min in shirya, shine mijinki ya sa aka samu a jirgi”
murna ce ta kamani na kamo amina da naga tana noƙewa kamar bata saki jikin ta ba, na zaunar da ita kusa dani tare da ɗora mata babyn akan cinyar ta
“ga ɗanki” na faɗa
“au abin ma ɗan wariya ne” mama ta faɗa tana dariya
“mama bari ta ganshi sai ta baki, kin san abin jini” na mayar mata nima da raha
“to ai shike nan”
“bari insa a haɗa muku breakfast” Na faɗa ina fita don bada umarnin na a haɗa musu breakfast
naji daɗi zuwan mama sosai don gaskiya bata da son jiki ko kaɗan duk da dai ina da masu aiki baja baja amma hakan bai sa mamabata zama ko kaɗan, kwanana uku da haihuwa su khadija suka zo da maryam harda ƴaƴan mama wato su iyami da ƴen uwanta da yaran su, na fa gidan ya kuma cika, da daddare sai ga tj ne nan da matar sa ashe baya gari ne shiyasa bai zo ba ni kuwa nayi mamakon rashin ganin sa
ana jibi suna mama ta faɗwa wa aliyu cewar tana son kwatancen gidan don akwai masu tahowa saboda suna, sai yace duk su haɗu a gidan mu gobe da safe zai sa aɗauko su, ai kuwa haka akayi har gida ya sa aka kawo su
da daddare *dangin sa* suka ƙaraso na ɗauka zanga farar fata ko ɗaya ne amma ga mamakina duk baƙaƙe ne yen uwana, a zuciyata nace ko dangin uban sa ne
Sauka ta musammam akai musu inda aka basu ɗaki biyu don su sakata su wala, sai shirye shiryen suna akeyi ba kama hannun yaro, ƴen uwana da abokan arziƙi sin min kara sosai har mutan gezawa sai da na aika musu da kuɗin mota suka zo har ƴen uwan mahaifiyata sai da suka zo kasancewar duk ƴen gezawa ne, gida ya cika danƙam ba masaka tsinke sai shirye shiryen suna akeyi idan na kalli waɗannan ayawan mutanen na gano ceqar duk don ni suka zo sai inji wani daɗi ya lulluɓe ni nakan godewa Allah da ya bani ƴen uwa masu ƙaunata
kashegari muka tashi da sunan aliyu aliyu sani sunan mahaifin shi jariri yaci inda zamu dinga ce masa haidar, ansha hidima, ga ciye ciye ba kama hannun yaro munyi hotuna sosai don tarihi sai dai muce Allah ya raya mana haidar aliyu
kashegarin suna aka fara watsewa inda duk wacce zata tafi da tsarabar sunan ta a leda sannan a biki da kuɗin mota wanda aliyu ne wanda yanzu ya koma abu haidar ya ba mama cewa adinga sallamar baƙi da kuɗin mota kuma za a baka wanda zai kaika gida har da ɗan wanda zai rage
ranar labara mutan kano suka shirya tafiya wato *dangin sa* basu shirya da wuri ba don haka lkcn suka shigo ina banɗaki ina jin khadija tana ce musu ina banɗaki to bari miuj inda aka sauke mu mu jira ta
suna fita na fito daga wankan, zan shirya mama tace min insa hijabi na inje in sallame su ba daɗi jira, na ɗauko zunbululen hijabi na na saka sannan na kama hanyar ɗakin su don muyi sallama, ina shirin tura ƙofar ɗakin naji suna magana tare da kama sunan mijina don haka sai na dakata don in ɗan ji
“ke dai bari hauwa wallahi ko kaɗan baya kyautawa, dubi yadda ya bar dangin sa cikin ƙunci da talauci kamar ba abinda ya haɗa su, sai ma kinga ƙannen mahaifinsa da ke unguwar mu su da ƴaƴan su yadda kika san almajirai, wallahi babu wani abinda yake musu” ɗaya ta faɗa, wata ka ta kama
“rannan da naje jakarar gidan mu na shiga dan gaisawa da inna kakar tasa wallahi zanin jikin ta bazakiyi tsimma da shi ba saboda tsabar lalacewar da yayi, tsayawa kawai nayi ina kallon ikon Allah, nace a zuciyata wai jikan matar nan ne yake da maƙudan kuɗin da baisan iya adadin su ba amma jibi kayan da ke jikin ta don Allah”
“ke dai bari zulai nima abinshi yana bani mamaki kome sukayi maka ba sai ka haƙura ba, tunda ko ba komai yanzu ka fisu, Allah kinsan hauwa ko banɗaki basu da shi a gidan nan nasu, langa langa ce aka sa arufe wai shine bayi”
suka ci gaba da tattaunawa akan talaucin da ke tattare da *dangin sa* wanda sukw mamakin rashin kula sun da bayayi, jikina ne yayi sanyi na shiga ɗakin a sukwane, duk sai suka sha jinin jikin su
tsugunnawa nayi muka gaisa
“lfy naga me jego jiki ba ƙwari sai kace bakya shiga ruwan zafi” Inji ɗaya daga cikinsu kasancewar ba sanin su nayi ba yasa na kasa tantance waɗanda sukayi maganar da naji
“da zazzaɓi na tashi yau” na amsa ahankali don duk maganar da sukayi ta gama kashe min duk wani kuzari na jikina
“ayya dahuwar ƙashi ce, Allah ya sauwaƙe” amin na kuma ansawa a sanyaye duk sukai min Allah ya sauwaƙe sannan mukai sallama da su na tafi zuciyata cike da tunanin ta me kenan ya ke faruwa tsakanin mijina da DANGIN SA
[7:44PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :23????
Ko da na koma ɗakina kasa shiryawa nayi duk zancen su sai nake jin sa kamar yanzu akayi shi sai dawo min yake yi yana min yawo a ƙwaƙwalwata, ga shi bana son faɗawa kowa saboda wannan kamar sirri ne day kamata in ɓoye tunda ya shafi mijina kuma ba abin alkhairi bane, khadija ce ta shigo ta ganni zaune ba tare da nasa kaya ba
“tooo me jego a zaune yai ba kaya a jikin ta” ta faɗa tana kama bakin ta
“kodai jikin ne” girgiza mata kai nayi
“ai kuwa ya kamata ki sa kaya a jikin ki don kar sanyi ya kama ki, muje in taya ki zaɓar kayan don yau naga gaba ɗayan ki bakya jin daɗi” closet ɗin muka tashi muka nufa, nidai tafiya kawai nake yi amma jikina gabaɗaya a mace yake na rasa abinda yake min daɗi
Wata jar shadda ta ɗauko min ɗinkin bubu sabuwa dal
“karɓi saka wannan” ta faɗa tana miƙo min,
“khadija ina mama” na tambaye ta
“tana can wajen rabon kayan suna kinsan duk yau za a watse, itama wannan ƴar iskar tana can, sun tasa kaya a gaba suna ta rabo, sukan duk waɗanda take mutunci da su da basu samu daman zuwa ba ta ɗiban musu, har da maƙotan ta, kinji ƴar iska” murmushi nayi maryam ai yadda kasan mama ce ta haifa ta wajen shishshigi da rawar kai haka take
"wani abu naji daga bakon ƴen uwan aliyu da suka zo ya tsaya min a rai" dawowa tayi kusa dani ta zauna tare da zare min ido menene
tas na kwashe abin da naji na faɗa mata ba tare da na ɓoye komai ba,
“haba biri yayi kama da mutum, nan mama take cewa ita fa bata ga wani abinda ya nuna alamar cewa waɗannan da suka zo suna sun haɗa wani abun da mijinki ba, shi fari tas kana ganin shi ka ga balarabe su kuwa ko ni nan na fi su haske” ta faɗa tana kallon hannun ta
“mahaifin shi baƙi ne kamar ki, na ɗauka dangin mahaifinsa ne tunda yace mmn shi basaudiyace”
“to ina iyayensa suke” shiru nayi don tunda nake ban taɓa tanbayar sa ba hasalima daga gani baya son a dinga yi masa zancen dangin sa
“ina tunanin sun rasu koo don tunda nake da shi bai taɓa cewa ga inda suke ba, to kinga ƙila sun rasun” na faɗa ina kallon ta
“ba shakka ƙila sun, sannan shi kuma ya tashi a wurin dangin sa inda suka yi masa ƙila ruƙon sakaynar kashi ina jin shi yasa shima daya girma ya watsar da su” khadija ta faɗa tana mai jinjina kanta alamar gaskata abinda ta faɗa
haka muka zauna muna ta tattaunawa akan abinda yasa aliyu ya daina kula da *dangin sa* amma har muka ƙare zancen namu bamu samu wani ƙwaƙƙwaran dalili ba
“kinga ance waƙa a bakin me ita tafi daɗi, ki bari idan aka watse si tambaye shi hankali akwance ƙila yai miki bayani ya fi wannan shaci faɗin da muke tayi” khadija ta faɗa tana me ƙoƙarin kauda mana da zargin da muke, don kar muje mu zargi bayin Allah waɗanda basuji ba basu gani ba,
“hakan zanyi ya na iya, amma ya zama dole in san me yasaijina ya ke wulaƙanta dangin sa baya taimaka musu ya barsu suke rayuwa kamar almajirai”
“hmmm Allah dai ya kyauta kar kiyi saurin yanke hukunci baki san me ya faru ba”
“haka ne Allah dai ya kyauta” na faɗa ina miƙe wa
ko da muka je sallama da su kawai kallon su nakeyi gashi ina son tambayar su dalilin daya sa suke wannan maganar amma ba dama tambayar su don sai suce nayi musu laɓe ina kallon su haka suka kama hanya suka tafi ciki na cike da tambaya amma ba daman yi
su khadija sai da suka ƙara kwana biyar sannan suma sukayi haramar tafiya, bayan na cika su da goma ta arziki kai ɗan uwa da daɗi yake, haka suka tafi ina kewar su ya rage daga ni sai mama, don ita tace sai anyi arba'in haka sukayi da baban mu wato ita mama babu ruwanta da yiwa kanta baƙin ciki inda wata ce cewa zatayi bazata zauna ba saboda ƴar kishiya ce amma mama ko a jikin ta zaman ta tayi
na so mu keɓe da mijina watoa abu haidar don in samu in amayar masa da tambayoyin da ke ciki na amma hakan ya gagara don kuwa aiki yake yi tuƙuru ba kama hannun yaro, idan ya shigo wurin mu kusan a tsats tsaye yake ganin mu ya ƙara gaba, ga kuma mama bana son inyi masa tambayar tana nan
sai da mukayi arba'in da kwana biyu sannan mama ta fara haɗa ya nata ya nata don tafiya ita ma, abu haidar ya kaita siyayya hmmm naga hidima wurin mama ta kwaso kaya kamar ba gobe haka ta dawo dasu niƙi niƙi, sai shi wa mijina albarka take yi, ni dai kawai riƙe baki nayi ina kallon iyayen kayan da mama ta kwaso Allah ya kyauta na ce a raina
ranar da mama ta kama hanyar lagos ranar shima abu haidar ya kama hanyar china wurin wani project da suke yi shi da wani ɗan china, bayan ya yarde min inje kano yawon arba'in, har airport na raka shi sannan na dawo da zummar kashegari zan tafi kano wayyo daɗi yaushe rabona da birnin dabo Allah ne kaɗai ya sani na faɗa a raina
kashegari da wuri na kama hanyar kano a mota kasancewar ina son ganin gari sosai, tafiyace miƙaƙƙiya daga abuja zuwa kano, a gajiye liƙis na sauka don na manta rabona da irin wannan tafiyar, directly gidan tj na nufa don nan zan sauka, ɗakine guda aka haɗamin da ban ɗaki a cikin sa, watsa ruwa nayi kawai na kwanta don na gaji sosai, bacci kawai nake so don jiya kawana nayi ido na biyu
[7:44PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :24????
Bani na fito daga ɗakin ba sai da safe sannan na fito saboda gajiyar da nayi ko abincin dare banci ba, ina jin salma ta shigo ɗakin ko motsawa kasa yi nayi
Sai da nayi wanka nayi wa haidar na shirya sannan na fito falon gidan sanye cikin shadda ta brown ɗinkin bubu kasancewar ni akwai son buba sannan na ɗauko hijabi na ɗora tunda gida ba naka bane
Tj na tarar a falon da salmar suna karya wa, ina fitowa salma ta karɓi haidar inda tj ya karɓe shi daga hannun ta"yaron nan kullum kamar shi baban sa ƙara fitowa takeyi" ya faɗa yana kallon haidar
“da baban sa ko dai mamansa, ai wannan kamar su ɗaya da zainab kudai kun fiya son kai ne, haka da haifi Islam kace kamar ku ɗaya”
“ai ku bakusan kama bane shi yasa, me ya haɗa wannan da mamansa ai wannan kamar ɗan uwa yayi kaki haka yake bari kiga ya ƙara girma…………..”
“a lkcn ma zaka ga kamar tasa da uwarsa ta ƙara fitowa” salma ta ƙarashe masa zancen nasa, sakin baki yayi yana kallan ta
“to ai shike nan zamu gani” ina dai ban tanka musu ina dai zaune ina jiran su gama musun su mu gaisa
“sannu wannan baƙuwa Allah ya zuba miki bacci, tun da kika zo gidan nan kike bacci sai kace wata kasa” tj ya faɗa yana dariya, murmushi nayi tare da cewa
“ina kwanan mu” duk nayi musu jam’i
“lfy kin iso ƙalau tun jiya nake sa idon ganin ki salma tace kina bacci, bayan kafin kizo ba irin jan kunnen da ba ayi min ba akan in kula da ke da haidar sosai” ya faɗa a zolaye, murmushi nayi kaɗan daga aikin abu haidar ne zai aikata na faɗa araina
“bari a kawo miki abinci” inji salma
“no bazan sha shayi ba indai da cheery noodles ita nake son ci, bari ma kiga in shiga kitchen ɗin in dafa” tashi nayi tsam na shige kitchen ɗin don gabaɗaya ban sake ba
Biyo ni tayi
“ya baƙuwa da girki, ko kina son aliyu yace bamu riƙe masa amanar da aka bamu bane”
“ko kaɗan akwai yadda nake son dafa noodles ɗina ne, karki damu” na mayar mata da martani tare da murmushi
“to bari in taya ki”
“ba komai kije ki sallami mijinki tukunna”
“yace ya ɗau hutu daga wajen aiki har sai kin tafi don zai dinga kaiki unguwa” shiru nayi ina sauraren ta sai banji daɗi ba
“laaa dama kince ya ci gaba da aiki ai da driver na zo saboda yawon”
“wannan kuma ki gaya mai da kanki ƴar amanar mu” ta faɗa tare da dafa min bayana, murmushi na cigaba da yi ita kuma ta fice
ko da nagama dafa abata na juyo ta plate da niyyar in wuce ɗaki amma salma sai ta hanani tace sai dai in zauna a falo inci tj ya fita, ba yadda na iya haka na zauna a falon nan ba dan na so ba, sai dana kammala sannan ya shigo ɗauke da haidar ga islam a hannusa, tana gani na ta taho a guje ashe bata manta dani ba
“lallai islam ashe bakya manta mutane” na faɗa
“ai wannan kusan kullum sai tayi hirar abj” salma ta ansa min, tj ne ya zauna sannan ya ce
“yayat yaushe za a fara zaga dangin ne, kuma ina zaki fara zuwa” shiru nayi don ni ban san kowa ba acikin dangin sa ba tunda muka yi aure ba wanda na sani, gashi waɗanda nake tunanin sune dangin sa ɗin sunce ya kasa kulawa da dangin sa
“jakara, jakara zan fara zuwa” na faɗa tabbas jakara naji sunce a nan kakarsa take,