
nayi mamaki sosai dana ga alamar tsoro ko ince mamaki a fuskar tj
“jakara zaki je”
“eeeh nan nake son in fara zuwa ko akwai wani abinne”
“no no no no ba komai” ya faɗa yana girgiza kansa kamar ba a cikin hayyacin sa yake magana ba
“sai muje anji ma in kin shirya”
“ba abinda zanyi ni a shirye nake” na faɗ ina gya hijabin da ke jikina
“ok bari in watsa ruwa sai in fito, tashi yayi ya shige ni kuma na koma ɗaki ɗauke da haidar a hannuna, ban kawo komai a raina ba illa murnar da nakeyi yau ɗana zai ga dangin sa na ɓangaren uban sa, nasan ƴen gayu ne ƙila ma farare ne kamar abu haidar ɗin
ƙara duba kaina nayi a mudubi na tabbatar ko shugaban ƙasa zan iya gani a haka sannan hankalina ya kwanta bana son inje gidan ƴen gayu a raina ni, na zauna ina tunani na na yadda ƴen uwan abu haidar zasu karɓe ni ko da fara'a ko a wulaƙance ni dai sai saƙe saƙe na nake tayi, salma ce ta shigo ta ce min yana jirana, ɗan ƙara kimtsawa nayi tare da sa mayafin da zai shiga da kayan, sannan na ɗauko haidar na fito
A mota na same shi ya buɗe min sit ɗin baya na shiga ni da ɗana, na zauna sannan muka fara tafiya, kasancewar bansan garin kano ba yasa bansan ina muke daso ba, bayan mu ɗan yi ƴar doguwar tafiya muka zo wata unguwa wacce layikanta suke a tsuke sai da dabara ma sannan muke iya wucewa,
ƴar tafiya muka yi kaɗan sannan tj yayi parking, muka fito ya karɓi haidar ya fara tafiya, mun yi tafiya da ɗan dama kafin mu zo wani ɗan durƙusash shen gida wanda yake ginin ƙasa ne, duk gefen soron wajen gidan ɗan pilastar da akayi masa ya zazzage ana gani jar ƙasa muraran,
Soro biyu muka shige waɗanda duk sun dafe kamar ana girki a cikin su, sannan muka shiga, tsakar gidan na ƙasa ne ko arziƙin siminti bai samu ba, yara ne a baje a tsakar gidan suna ta wasansu a cikin ƙasa ba tare da iyayen sun damu ba, sallamr mu ce ta katsewa iyayen hirar su da suka yi dandazo sunayi ba tare da sun kula da halin da ƴaƴan su suke ciki ba, gabaɗayan su suka juyo tare da ansa mana
“wa ‘alaikumus salam, a a awata sabon gani tijjani ne yau agidan namu, lallai yau za ayi ruwa da ƙanƙara” inji wata wacce daga ganin ta zata haifi tj ɗin,
“mmn habu wallahi uzuri ne yayi min yawa kiyi haƙuri”
“kayya ba komai ku ƙaraso ai iyar tana ciki”
ƙarasa shiga ciki muka yi inda kwata tayi wa gidan kwalliya, sai da muka tsallaka wata yar ƙaramar kwata sannan muka shiga wani ɗaki wanda saka durƙusa sannan zaka shiga,
babu abinda ke ɗakin sai wata ƴar tsuhuwar kujera guda ɗaya a gefen ɗakin wanda cushion ɗin kujerar duk sun patattake kana ganin soson cikin kujerar wanda shima yayibaƙi ya yayyage, ƙasan ɗakin an simince shi amma duk ya fargashe ramuka ne aoaai a ɗakin kamar ba mutun ne a ciki ba, bangon ɗakon yai baƙiƙƙirin da shi kamar ana girki da murhu a ɗakin, sai iayayen calandu na mutane duk an zagaye ɗakin da shi
Wata ƴar tsohuwace ta fito daga cikin uwar ɗakan ɗakin,
” wa nake ji kamar ahmadu, lallai yau nayi gamo da alheri” ta faɗa tana fitowa tare da ƙoƙarin gyaran ɗan kwalinta tsohuwa ce amma daga gani harda rashi ya sa ta ƙara lalacewar tata
tabarma ta ɗauko ta shinfiɗa mana muka zauna, bayan mu gaisa ne take cewa
“wannan dai ba sirikar tawa bace ba koo, ko kuma idon nawa ne”
” iya idonki ras yake ba ita bace matar ali ce, ta haihu shine tazo gaishe ku” tsayawa tayi tana kallo na
“ali dai ali alin hjyr” ta faɗa, murmushi yaya tare da gyaɗa kansa
“shi kuwa” hannun ta na rawa ta matso ta ɗauki haidar da ke hannun tj, sai ga hawaye a idon ta, ni dai ina zaune ina kallon ikon Allah don har yanzu bansan inda muka zo ba, amma koma ina ne daga gani talauci ya zuba ƴaƴa har da jikokin sa a gidan nan, don babu wacce zaka gani kace bata fama da babu har ita tsohuwar da ke gaban mu tana fama da babu, zanin jikin ta kawai zaka kalla kasan cewar talauci yai mata damƙar kuku
tashi tayi ta fita sai gata da mutanen gidan sai shigowa suke yi ana gaisawa da ni suna ɗaukar haidar, da yake ɗakin ba wani girma gare shi don haka sai wasu sun fita sannan wasu suke shigowa ko da aka gama gaisuwar sai gashi an kawo mana ruwa a wani kwanon silba, ni bin kwanon nayi kawai da kallo amma gaskiya bazan iya shan ruwa cikin sa ba, ganin cewar kamar bazamu sha ruwan bane yasa iyan tace wa wata yarinya da bazata wuce shekara shida ba
“humaira zo kije gidan ummi kice nace ta bani pure water guda huɗu nayi baƙi” a guje yarinyar ta tafi can zuwa jimawa sai gata ta dawo duk tayi duƙun duƙun da ita
“iya kinga ina cikin gudu na faɗa kwata”
“ina aiken da na miki” iyar ta tambaye ta
“au tace wai shekaran jiya da kikayi baƙi kika karɓi na 15 baki aiko mata da kuɗin ba” yarinyar ta faɗa batare da damuwa ba
fuskar iyar ta nuna damuwa sosai tj ne ya ce
“iya karki samu damuwa bama jin ƙishi ma” ya zaro 1000 ya ba yarinyar gashi nan jeki ce ta ɗauki kuɗin ta, yarinyar ce ta kuma kallon iya inusa me shago ɗazu yayi min maganar bashin sabulun wankan da kika karɓa”
“kije shima ya ɗauka aciki” inji tj wallahi matar duk sai ta bani tausayi don ƙiri ƙiri kana gani kasan cewar tana buƙatar taimako, tj ne ya katse shirun da mukayi tare da tambayar iyar ragowar ƴaƴan nata inda ita kuma take bashi ansa dai dai sanin ta
Wata mata ce ta shigo ɗaki kamar an jeho ta
“lfy bilki sai tace wacce aka koro”
“wallahi iya yara ne suka je gidana suka ce matar ali tazo shine wanki ma nakeyi na ajiye na fito don inganta”
“ina kwana sirika ta” ta juyo gare ni muka gaisa
Suka gaisa da tj har tana mai ƙorafin ya yada daita shi kuma ya dinga kawo mata uzirin sa na baya zama ne
hannun ta da ke jike ta goge tare da miƙowa iyar hannu kawo jikan nawa inganshi, ta karɓi haidar tare yi masa addua, sannan ta juyo gareni
“ashe a abuja kika tare” gyaɗa mata kai nayi
nan ta zauna suka dinga hira da tj itama iyar takan ɗan tanka musu ni dai ina zaune idan anyi abin dariya in dara, mun ɗan jima ni dai buri na in fita daga gidan don haƙurin zama kawai nakeyi, tare muka miƙe da bilkin muka fito har soro mutan gidan suka rako mu inda bilkin ta karɓi number wayata wai don mu dinga gaisawa da kuma wai inta haihu zata kira ni ta faɗa min kasancewar ciki ne da ita ya fito sosai, tj yai ta musu rabon kuɗi hatta yara ƴen ƙanana sai da suka samu suna ta shi masa albarka muka fito har muka ƙule daga lokon gidan suna kallon mu wata ajiyar zuciya na saki dana ga mun bar layin nan kai Allah mun gode ma amma talauci baiyi ba ko kaɗan
[7:44PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: L????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Paga :25????
Har muka ƙaraso inda mukai parking ina tananin bayin Allah nan Allah ya gani ina tausaya musu, kamar suna rayuwa a ƙauye kamar ba civilization, jikina duk yai sanyi na rasa yadda zan kwatanta bayin Allah nan, muryar tj ce ta katse
“madam daga nan sai ina”
“tj nace ma gurin kakar aliyu zanje in gaishe ta” na faɗa jiki na duk yai sanyi har yanzu ina tunanin bayin Allah nan, na ɗauka wani abin yake yi amma ga mamakina in ɗagowa sai naga ya kallona,
“kima nufin baki san gurin wacce kika je ba yanzu” girgiza masa kai nayi
“itace kakar aliyu, iyar da muka ke ɗakinta muka zauna ta ɗauki haidar itace ta haifi mahaifin aliyu” rasa bakin magana nayi
“kana nufin iyar da muka fito daga gidan nan yanzu ita ta haifi baban mijina”
“ƙwarai kuwa, duk waɗannan da kike gani daga matan ƙanin baban sa sai ƙannan baban sa a gidan babu bare, itama wannan bilkin da kika ga ta shigo daga ƙarshe itacw autar iyar, uwarsu ɗaya uban su ɗaya d bbn ɗan uwa”
shiru nayi jikina duk yayi sanyi mekenan yake shirin faruwa aliyu ne *dangin sa* suke rayuwa kamar almajirai, kamar akansu aka yanke wa talauci cibiya abin ma wallahi da ɗaure kai
“tj kana nufin waɗan nan sune dangin aliyu, waɗanda zai kalla yace sune dangin sa
gyaɗa kamsa kawai yayi tare da ƙoƙarin buɗe ƙofar don in shiga, shiga nayi amma gabaɗaya hankalima yana tashe, ya za ayi ace wai waɗannan su ne *dangin sa* mutumin da ya mallaki dukiyoyi bila adadin ko jirgin ruwa ɗaya gare aliyu zai iya ciyar da kusan rabin kano amma mutumin daya mallaki jiragen ruwa wai shine *dangin sa* suke cikin wannan baƙin talaucin
"tj kana ganin abu haidar ya san halin da ƴen uwan sa suke ciki" na tambaye shi a ƙage
“gwanda dai ki tambaye shi kinsan ance waƙa a bakin me ita tafi daɗi” ba yadda ban yiba don inji wani abin a bakin tj amma ƙiri ƙiri duk abinda na tambaye shi sai yace in dai tambayi mijina, haka na haƙura nai shiru
“akwai inda kike son zuwa ne kuma”ya kuma jeho min tambaya, bazan iya zuwa ko ina ba don gabaɗaya jikina yayi sanyi ganin irin yanayin da na samu ƴen uwan mijina
“tj kai ni gida kawai gobe nayi yawon amma gaskiya yau ina buƙatar inyi nazari sosai akan halin da bayin Allah nan suke ciki” shiru yayi bai tanka min ba
ko da ya ajiye ni bai shiga gidan ba wai yana sauri, na shiga ni kaɗai salma tai mamakin gani na, na dawo da wuri, nan na rattabo mata abinda na gani a gidan dana je ko zanji wani bayani daga gare ta amma ga mamakina sai ta nuna min bata san komai ba, ba irin tambayar da ban mata ba amma ƙiri ƙiri tace min wallahi bata san komai ba amma dai tasan akwai wata mai tsami sosai tsakanin miji na da *dangin sa*
“to waɗanda suka zo suna fa ba dangin sa bane”
“ƙannan baban islam ne”
“meye dangatakar mijinki da nawa” na tambayeta a ƙagare, dafa ni tayi
“in kina son ansar da zata gamsar da ke ki tambayi mijiki” tana faɗar haka ta juya tayi shigewar ta ɗaki ta barni da baki a buɗe
kasancewar hausa ba wani isa ta tayi ba sosai ya sa na tsaya ina nazarin abinda salmar tace amma har na gama bincika dictionary ɗin ƙwaƙwalwata ban ga ne me take nufi ba, haka na shige ɗaki na kwanta don ina buƙatar kaɗaicewa ko nayi ɗan nazari
me ya haɗa mijina da *dangin sa*haka da har yayi tsami har ya iya kallon su cikin halin da suke ya ƙyale su ba tare da ko ɗan kula su ba, me yayi zafi, ko dai sun wahalar da shine lkcn da iyayen sa suka rasu, haka naita saƙa ina warwarewa babu me kama min ni kaɗai nake ta saƙe saƙe na babu me gyara min ko kuma me faɗa min abinda ya faru sai dai injira dawowar shi wanda abin ya faru da shi, ƙila shi ya faɗa min abinda ya faru kai doe ne ma ya faɗa min tunda yanzu ai mun zama ɗaya na faɗa ina mai juyi akan gado don inji daɗin kwanciyata
sai bayan sallah magariba sannan abu haidar ya kira ni, muka gaisa da wasa da dariya,
“mutan kano ya kanon an fara yawon, Allah yasa dai ba a wahalar min da ɗana” ya faɗa a zolaye
“ni ko ka tambayeni ta ɗan ka kake ko” na faɗa tare da zunɓuro baki kamar yana wajen
“yi haƙuri habibti ya kike”
“lfy” na ansa a taƙaice
“an fara yawon ne” ya tambaya
“eewh yau munje jakarah” shiruuuuuu naji yayi har na ɗauka ko wayar ce ta katse sai da nace hello sannan naji yace min
"wa ya saki kije"
“ai naga ƴen uwankane”
“shut up, dont provoke me now young lady, da izinin wa kika je,na ce miki ki je can ne” ina iya jiyo nunfashin da yake fitar wa saboda tsabar fushi da yake ciki
“ki shirya kayan ki yanzu ki bar kano kin gama yawon”
“ban je ko ina baa” ɗitttttttttttt naji ya kashe wayar, me kenan hakan yake nufi na faɗa, raina ya baci sosai da sosai komawa nayi na kwanta abin abu haidar ya fara sha min kai yanzu
*************
sun fito kenan daga meeting zasu cin abinci a wani sea food da ke kusa da deport ɗin da suke yace bari ya kira wannan me yawon yaji ta fara yawon nata amma abin mamaki yana kiran ta sai yaji wani zance da ya fi muni gareshi wai taje wurin waɗan da a aduniyar nan bashida maƙiya kamar su me zai kaita jakarah, ya maimaita tj ka cuceni don me zaka ɗauki mamata da ɗana ka kai wa mutanen da tun ina cikin uwata suke kirana da shege, don me zaka kai min iyalaina wurin mutanen da tunda nake basu taɓa so na ba don me zaka kaimin iyalaina wurin mutanen da basa so na ko kaɗan
lallai yau dole ne ta bar garin nan, don naga almar tj baya son ta zauna agidan sa ne, ɗaukar wayar sa yayi ya kira tj ɗin, ringing biyu tj ɗin ya ɗauka
“ɗan uwa ya birnin sin ɗin” tj ya tambaya ba tare da kawo komai a ransa ba
“tj na gode da abinda kayi min kuma na gano ka baka son matata ta zauna a gidan ka ne shiyasa har ka kaita gidan da kasan na fi tsana, don haka ka tattara min ita ka kai min ita airport ta kama hanyar gidan ta”
shiru tj ɗin yayi yasan cewar aliyun ya faɗi abinda ya faɗa ne cikin ɓacin rai,
“ko baka jine ka mayar min da matata” ya daka masa tsawa
“sai da safe don yanzu dare yayi”
“ban damu ba ni dai kawai matata ta bar min gidan ka yanzu”
“kamar yadda nace sai da safe kawai ka haƙura sai da safe”
“idan bazaka sa ta a jirgin ba zan aiko a ɗauke ta da kaina”
“ince dai tana cikin gidana zanga wanda zai shigo min gida wai da nufin ɗaukar ta ayau, in kuma ka isa ka baro inda kake ka zo ka ɗauke ta” yana gama faɗin haka ya kashe wayar don yasan idan ya ci gaba da biye masa sai suyi ɓatacciya don ya san halin aliyu sarai in dai ta kan dangin sa ne sai ya rufe idonsa ya ci maka mutunci
to inba aliyu ba waya faɗa wa zainab maganar jakara, salma salma ce zata faɗa mata ya faɗa aransa amma zata gane kurenta duk jan kunnen da yayi mata akan duk abinda zainab ɗin zata tambaya tace mata bata sani ba amma sai da ta saki baki tayi magana, gaskiya salma baki kyauta min ba ya faɗa tare da shiga motar sa domin zuwa gida dole ne ya nuna wa salmar kuren ta
[7:44PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :26????
Tunda muka gama waya da aliyu na kashe wayar gaba ki ɗaya don kar ya dame ni don me bangama yawona ba zaice wai in koma don kawai na je gidan su mtsss na ja dogon tsaki wasu mazan ma sai su, kwanciya nayi ina shirin bacci na ji tj yana ƙwalawa matar sa kira tun daga ƙofar falo, tooo Allah dai yasa ƙalau na faɗa tare da jan bargo na ina mai yin addua ta yin bacci
Tun daga bakin ƙogar falo yake ƙwala mata kira
“salma salma salma” gaskiya yau salma ta ƙular da ni don me zata faɗa wa zainab cewar dangin mijinta suna jakara, har cikin ɗakin nata ya shiga ya tarar tana salla dole ya samu wuri ya zauna don gaskiya baiji daɗi ba