DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

itace ta wanke min ɗana tas ta shirya shi nima ta samin ruwan wanka na yi naji daɗi sai bacci daga ni har ɗan jaririn 

abu haidar ne ya faffaɗi haihiwar tawa don ni ko ta kan waya ma ban bi ba ina ta kaina, da daddare daya dawo directly ɗakina ya shigo ya ganmu kwance reras ni da ƴaƴa na sai ga hawaye again a idon sa

tooo wannan kukan sa na biyu kenan a yau lfy na faɗa ina jawo shi zuwa jikina tareda shafa masa baya alamar lallashi
” idan na ganki da ƴaƴan nan nawa sai in godewa Allah wai yau ni aliyun dana rayu cikin ƙyama da kyara daga dangi na wai yau nine da ƴaƴa har biyu sai inji zuciyata ta karye”

kara shafa masa baya nayi tare da cewa
“duk abinda ka gani ya samu bawa muqaddari ne daga Allah haka Allah ya ƙaddaro masa don haka duk abinda ya same mu bama cewar ba zamu yafe ba sai dai mu yafe hakan zai kara kusan tamu da ubangiji” gyaɗa kai yayi

“zainab kenan wasu abubuwan sun wuce mutum ya yafe sai dai kawai ya ɗauke kansa daga wurin gaba ɗaya”
“kamar me fa”
“kar ki damu bari inje in watsa ruwa a jikina yau duk zan feɗe miki daga biri har wutsiyar sa na abinda ya haɗa ni da dangi na har na watsar da su”

to kawai nace ya manna min kiss tare da faɗin i love u with all my heart sannan ya wuce toilet don wanka, komawa nayi na kwanta ina tunanin yau me zanji ya haɗa aliyu da dangin sa Allah dai yasa matsalar da zan iya warware wace da sauki na faɗa a raina
[7:44PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

Page :29????

 *Asalin labarin*

 jakara ta kasance unguwace tsohowa zaka gane hakan ne idan kayi la'akkari da irin gine gine da ke cikin unguwar wanda yawancin su ginin ƙasa ne, inda a ɗaya  daga cikin gine ginen ƙasa ya kasance na mlm musa me icce ne,


  sana'ar icce yake ko an san shi sosai kasancewar iccen shi akwai sauƙi sosai, yana da mata ɗaya tare da yara 10 maza 5 mata ma 5, 


 acikin ƴaƴan sa sani shine na biyar, yaro ne zuciya tun yana ƙarami, yake neman nasa na kansa, mlm musa yana da mata ɗaya wadda ƴaƴan ta suke kiran ta iya, 

markaɗe shine sana’ar, inda in ta kunna injinmarkaɗen ta tun safe sai ya kai 1:00 na rana a kashe ba saboda tsabar markaɗe

   mlm musa beyi ilimin boko ba don haka be sa ƴaƴan sa, ya kan de jasu zuwa wajen sana'ar sai da itacen sa su taimaka mishi, sani shi kaɗai ne yake makarantar boko a gidan shima da kanshi ya sa kanshi kuma yake ɗaukar nauyin kansa don daga malam ɗin har iyar babu wanda ya damu da boko


 abokin sani wanda gidan su yake jikin su sanin shine kaɗai yake ƙarfafa wa sanin akan karatun boko wanda tare da shi suke yi, kuma da taimakon Allah Allah bai hana sani wani abin na biya wa kai buƙatar mkrt

sai ya wuni yana taimakawa iya markaɗe inda in ta bashi ladan aikin sa sai ya adana yayi hidimar mkrt da shi a haka yake karatun nashi, ana ta gurgurawa da daɗi ba daɗi haka suka dinga karatun su inda duk lkcn da abu ya kakare wa sani abokin nan nasa me suna buhari shine dai me taimaka masa don bai isa ya tinkari iyayen sa ba sai suce ai ba su suka aike shi ba

 ko da suka gama secondary school, sai suka fara fafutukar neman jami'a, inda Allah ya taimake su suka samu abu zaria, inda suke karantar ɓangaren  lab science duk da dai sani likota ya so zama amma hakan bai samu ba


    suna cikin shekarar su ta biyu a jami'a gwammatin kano ta raba scholarship, da taimakon malamin secondary ɗin su wanda ya shige musu gaba suka samu scholarship ɗin inda zasu india karatu


 murna a wajen waɗannan bayin Allahn ba a cewa komai ba, ba su ba har iyayen su, gwanda mahaifiyar buhari wadda ake cewa hjy da gumin ta ɗan ta yake karatu, 

amma mlm musa da iya waɗanda basu san ta yadda ɗan nasun ya samu ilimin ba ma suna ba a barsu a bayan wajen murnar ɗan su zashi india karatu, duk wani wanda yake mu’amala da iya ko mlm musa ya san da wannan zancen

a kazo aka fara shirye shiryen tafiya duk wannan ɗokin da iyayen da sani suke ko da aka zo batun kuɗi duk sai suka noƙe, sani shi yayi fafutukar shi shi kaɗai ba tareda taimakon kowa ba har Allah yasa suka ɗaga zuwa kasar india lfy don karatu


  sun sauka india lfy sun fara karatun su lfy lau ba kama hannun yaro duk inda kaga ɗaya sai kaga ɗayan haka suke, sun maida hankalin su sosai akan abinda ya kawo, a haka har suka ƙare shekarar su ta farko lfy ba matsala, ba su dawo gida ba acan suka zauna sukayi hutun to in sun dawo ma wa zai basu kuɗin jigin komawa

a shekarar su ta biyu a mkrt ne Allah ya haɗa sani da matashiya ƴar saudiyya, me suna salma, da farko ƙawance ne ya ɗa su, amma daga baya sai ƙawance su ya koma soyayya

 Tun suna yi a rufe har suka fito da shi kowa ya sani, salma riga sani shiga mkrt  don ita a 3rd year ɗin ta take, ina take karantar medicine,


Soyayya su ce ta kaisu ga ɗaura aure don gudun gujewa ruɗun shaiɗan, buhari ya so ya hana sani yin auren nan, amma sani ƙiri ƙiri ya ƙi ya biyewa salma suka ɗaura aure, inda suke tare a sabon gidan su


soyayya suka dinga zubawa sannan ga karatun suna yi hankalin su kwance duk wanda ya gansu saisun bashi sha'awa ganin yadda suke son juna tare da tattalin junan su




 Suna cikin shekara ta biyu da aure Allah ya sa salma ta samu ciki, murna sosai sani da matar  sa salma suka dinga yi, suka shiga tattalin cikin,



  tun buhari na kau da kai daga lamarin su har ya koma shima yayi tsamo tsamo cikin hidimar cikin siyayya sukayi sosai har Allah ya kaisu lkcn haihuwa

lami lafiya ta haihu amma ƴar ta zo ba lfy, inda bayan kwana biyu tace ga garinku nan baƙin ciki a wajen salma da sani kamar ba gobe har kuka sai da suka yi, sannan daga baya suka dangana

pls kuyi haƙuri da wannan yau uziri yai min yawa salam ????????

[7:44PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

Page :30????

   Sai da ta ɗan huta na shekara ɗaya sannan suka kuma trying, kuma Allah ya basu sa a ta sami cikin, wannan karon ba karamin kula sosai suka ba wa salmar ba, sannan suna karatun su lfy, inda ahalin yanzu salmar tayi graduating shi kawai take jira ya gama su koma gida



 Sun gama yanke shawarar cewa baza su zauna a nigeria ba sannan bazasu zauna a saudiyya ba zasu samu wani garin su zauna ne, ganin haka yasa suka yanke hukuncin zuwa nigeria salmar ta haihu daga nan sai su wuce saudiyya don dangin salmar suga babyn kafin nan sun gama shawarar inda zasu zauna 



 Duk wani siyayya na haihuwa sun gama, lkcn da sani ya gama course ɗin sa a lkcn cikin salma yana wata tara haihuwa ko yau ko gobe don haka sai suka shirya tafiya nigeria inda suka bar buhari zai yi musu lodin kayan su ta cargo kafin ya biyo bayan su



  Sun sauka lfy a nigeria inda suka wuce jakara directly sani yaga yadda unguwar ta ƙara lalacewa, wato a nigeria in ba unguwannin masu kuɗi ba to vaza ka taɓa ganin cigaba ko, ya faɗa a ransa 



  A farkon layin su taxi ɗin da suka ɗauko ta faka, suka tako a ƙafa, salma tana ta mamakin irin wannan rayuwar amma bata kushe masa ba ganin shi take so kuma ba anan zasu yi rayuwa ba,



     har suka cikin gidan yana mata bayanin yadda halin rayuwa yake a nan nigeria mu ita kuma tana gyaɗa kai cike da tausayawa, a tsakar gida suka ci karo da iya inda da sairi sani ya je ya rungume ta



 waigowa iya tayi cike da tsoro waye wannan, ganin ɗan ta da ta daɗe bata gani ba yasa yin saurin ƙara ruƙunƙume shi, tare da sakin kuka, sai daya rarrashe  tayi shiru, sannan ya nuna mata salma wacce tun shigowar su tana tsaye tana kallon su

“iya ga matata dana aura a india, amma ƴar saudiyyace” ya faɗa yama miƙa salma hannu wanda ita kuma ta ƙaraso tare da riƙe hannun nasa

  wani shegen kallo iyar ta bita da shi daga sama har ƙasa, ganin salmar da tsohon ciki ya sa iyar ƙara murtuke fuskar ta 

“abinda kaje ka koyo kenan a indiar, kazo da mace da tsohon ciki kace matar kace, uban waye ya ɗaura maka aure da ita, ko an gaya maka saboda bamu da ilimi yasa kake tunani cewar bamusan sai da aure ake kiran ɗa ɗan halak ba” ta faɗa tana miƙa wa salmar harara, wanda hakan ne yasa salmar sunkuyar da kanta tare da ƙara shigewa jikin mijin nata

wannan abun da salmar tayi ƙara tunzurawa iyar rai yayi"au karuwancin da kuke yi zaku zo ku ƙara nuna min a gaba na, ai ba sai kun kwatan ta ba cikin da ke jikin ki ya isa ya nuna sheƙe ayar da kike yi da wasu mazan"

“iya ba fa haka bane wallahi matata ce, sai da na aure ta fa sannan, wannan ma ba shine na farko ba ta farkon ta rasu”
“kawai cewa zakayi ta gama zuzzubar da cikin mutane shine wannan ta ƙi zubar da shi ta maƙala maka, ta wai ma waye shaidar cewa ka aure tan”

“iya buhari mana shima yana nan tahowa cikin satin nan”
“ni zaka rufe a bai bai, to wallahi ban yadda cikkn nan ba naka bane shege ne, kuma bazan yadda ka zauna da karuwa ba sai dai ka ƙyale ta ta koma can gari su taje taci gaba da watsewar ta, haka kurum bazan haɗa zuri’a da kuruwai ba”

“iya don Allah kidaina faɗin hakan wallahi matata ce”
“wai baka ji me nace bane ban yadda ba, me kake in cewa mutane sani ya je turai ya dawomin da karuwa a matsayin matar sa harda cikin shege, wallahi ƙarya kake ban tonawa kaina asiri ba babu ɗan da ya isa ya tona min” ta faɗa tana gyara kallabin wanda sauran ƙiris ya faɗi saboda tsabar masifa

 babu yadda sani baiyi ba don ya fahimtar da iya amma ta rufe idon ta tai ta tafka bala'in tun suna yi su kaɗai har ƴaƴanta suka fara shigowa suna taruwa


duk wanda ya shigo yaga sani ya dawo sai ya fara murna amma da yaji faɗan da iya take yi sai su koma bayan ta suna goyan bayan ta na bai isa ya haɗa su da shege ba, a cikin faɗan nasu ne ma yaji rasuwar mahaifinsu shekara uku da suka wuce abu goma da ashirin suka haɗu suka haɗar masa ya rasa acikin ƴen uwan nasa wanda zai ɗan fahimce ahi koda so ɗaya ne su dai burin su kawai ya kori salma da cikin da ke jikin ta, su tsaya ma suji abinda zai ce su ƙi kawai haniya suke yi tsakanin su tare da rantsuwar baza su zauna da karuwa ba



 kasancewar gidan su buhari katangar su ɗaya da su sani yasa hjyr su buharin jin hayaniyar tasu, tasan tsakanin iya ne da ƴaƴanta kamar karta shiga sai kuma wata zuciyar tace ki shiga haƙƙin maƙotaka ce tasa, hijabin ta dake jikin ƙyaure ta ɗauko ta saka tayi gidan iya  


ko da shiga taga sani tayi mamaki amma sai ta danne don sulhu ta zo yi  daga baya taji lbrn ɗan natan, tambayar abinda ya faru tayi inda wata matar wan sanin tayi wa hjy bayanin abinda ya faru, to ita hjy bata ga abin tada jijiyoyin wuya ba menene don yaro ya auro farar mace ta faɗa



   har wajen iyar tajee tayi mata nasiha akan tabi abin a sannu don a samu a shawo kan maganar amma iyar ko sauraran ta batayi ba inda daga ƙarshe ta ƙare wa hjyr tanadi tas har da cewa ita taga ɗan ta ita ma ta jira taga da wace tsararbar ɗan natan zai zo mata dashi 



ba haka hjy ta so ba ta so iyar ta kwantar da hankalin ta har a samu bakin zaren amma daga dukkan alamu iyar ta riga tayi nisa kuma harda laifin ƴaƴanta don kuwa su suke ƙara zugata, can ta hango sanin idon shi ya kaɗa yayi jajir sai lallaɓa matar da yazo da ita yake yi wacce ita kuma take a tsugunne tana kuka, su kuma ƴen uwan nasa suna gurin iyar suna ta zigata 

har kusa da shi hjyr ta ƙarasa tayi masa nasiha sosai akan darajar uwa sannan ta kama hanyar gida don bata ga alamar iyar tana da niyyar sauraren wani a wannan lkcn ba

haka aka wuni ana abu ɗaya babu sassau a cikin lamarin ta tubure sosai sai salmar ta  bar gida, inda maƙarraban ta ke zigata 


sani hankalin shi ya kasu biyu ga faɗan da iya take tayi ta ƙi shiru duk tabi ta tara mutanen unguwa ta sheganta masa ɗa tun kafin ya zo duniya, ga ita kuma salmar ta tada hankalinta baza iya zama ba tafiya zata yi, ga wani azababben ciwon kai da yake damun sa wanda ya sashi yaka ganin dishi dishi, matsawa yayi kusa da salmar wadda har yanzu take kuka domin ya lallashe ta amma ga mamakin sa jikin ta zafi rau da shi 

“subhanallahi salma zazzaɓi kike yi ne” ya faɗa yana ƙara taɓa jikin ta tabbaa zazzaɓi ne, tausayin ta ne ƙara rufe
“isbiri la tabki habibti” ya faɗa tare da share mata hawayen da suke gangariwa daga idon ta
“saufa ashtari lakkid dawa” gyaɗa kanta kawai tayi, tare da gyara zaman ta

tashi yayi ya miƙe don ya je ya samo mata magani, dole ne ya bar salma ta tafi saudiyya, dole ne ya haƙura salma har sai Allah ya daidaita su da mahaifiyar sa dole ne salma ta tafi in ya so idan ya fahimtar da iyar cewar salmar halak malak ɗin sa ce in yaso daga baya sai su kuma tsara yadda zasu ci gaba da rayuwar su, amma bazai iya rayuwa ba salma ba taya ma zai iya rayuwa babu salma a cikin ta dole yasan yadda zai yi salma ta riga ta zama komai na shi na rayuwar zai san yadda yayi ya shawo hankalin iyar bayan ya mayar da salmar yasa ganin salmar anan ne yasa iyar tayar da hankalin ta amma da zarar salmar bata anan idan hankalin iyar ya kwanta in shaa Allah zai san yadda zai shawo kanta ta yadda da auren nasu da salma hakan zaiyi ya faɗa yana gyaɗa kansa

gabaki ɗaya tafiya yake yi amma sam bai san inda yake jefa ƙafarsa ba don yayi zurfi a cikin tunani, baya iya ganin komai kawai tafiya yake yi ƙugin mota kawai yaji tare da sunkuce shi da motar tayi ta maka shi da ƙasa wani azababben zafine yaji ya ziyarci kansa wanda bai taɓa ji ba, ƙoƙari yayi don ya motsa amma sai ya kasa, idon shi a buɗe suke amma baya gani komai sai duhu haniyar mutane yaji suna ƙarasowa inda yake
“kar ku taɓa shi kanshi ne ya fashe yake zubar da jini” tun yana iya fahintar abinda suke cewa har ya koma ya daina

inna lillahi wa inna ilaihir raji’un ai ya mutu inji wani daga gefe
[7:45PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

Page :31????



 Salma tana zaune ainda ya tafi ya barta, gaskiya dole ne in bar musu gidan su, ta faɗa a ranta, yau ɗinnan kuwa gwanda ko hotel ne ya kama min, kuma da na samu jirgin saudiyya in gudu ta faɗa tana ƙara gyara zaman ta a saman ƴar tabarmar da take zaune 

duk ta gaji hankali gabaɗaya a tashe yake sai kace sun ga wani kashi yadda sukai treating ɗin ta kamar ba musulmai, gaban ta ne ya yanke ya faɗi, 

“subhanallah” ta faɗa tare da dafe ƙirjin ta, cigaba yayi da faɗuwa inda ita kuma ta ci gaba da kwararo addu’o’i tana mai neman tsari da duk wani sharri da zai zo gareta

Gafara gafara gafara kawai taji ana cewa duk da dai bata san abinda yake faruwa ba amma ta ɗago kanta don taga menene


  Mutum taga an shigo da shi an shige da shi ɗakin iya, tsayawa tayi tana tunanin lfy, kukan iya taji tare da kururuwa tana ƙwalawa sani kira, bata san lkcn da ta zabura tayi ɗakin iyar ba, bangaje mutane tayi ta yi har sai da taje kan sa, 

“innalillahi wa inna ilaihi raji’un” shine kawai abinda bakin ta yake faɗi

Durƙusawa tayi kjsa da shi ta fara kuka cikkn nutsuwa, iya da ke kansa tana kururuwa ta ɗago don jin mutum a kusa da ita, tana ganin salma tayi kanta da duka da zagi
“mayya daga zuwan ɗana kin lashe masa kurwa” ta dinga dukan ta tana zagin ta

ko kaɗan salma batai yunƙurin hana ta ba don ita raɗaɗin da yake damunta a zuciyar ta ya fi ƙarfin dukan da iyar take mata, kuka kawai take yi tare da yin istigfari ga Allah ubangiji (swt)

   hjy tana gidan ta ta kuma jiyo hananiya da kururuwa tare da ƴen koke koke, hijabin ta kawai ta kuma ɗauko wa tayo waje, tana zuwa gidan ta tarar da mutuwar sani da kuma irin jibgar da iyar take yi salmar wanda babu wanda yai yunƙurin hana iyar


 da sauri taje ta janye salmar, 

“idan kika kashe fa” inji hjy
“na kashe banza na kashe wofi ai nima kashe min ɗana tayi Allah ya isa tsakanina da ke shegiya” ta dinga bin salmar da zagi, ragiwar ƴaƴan iyar suma suka yooo chaaa wai sai sun dake ta ikon Allah

ba shiri hjyr ta janye salmar zuwa gidan ta don taga alamar zasu iya yiwa salmar lahani in aka bar musu ita, gida ta wuce da ita direct, ta ɗauko panadol da ruwa ta ba don taji jikin nata zafi rau da shi oohhh Allah haka yake ikon sa

ko da tasha sai tayi mata shimfiɗa don ta ɗan kwanta don a gaskiya tana buƙatar hutu don sai ta iya shiga wani  hali ga halin da take ciki, 




 har akayi wa sani sutura aka fita da shi salma tana kwance ita ba bacci take yi ba komai ba, hjy ta so ƴen uwan sanin su bar salmar tayi masa kallo na ƙarshe amma ƙiri ƙiri suka ce idan ta zo sai sun lahanta ta me yayi zafi inji hjy 



Salma ranar taga baƙin ciki ido da ido ta rasa abinda yake mata daɗi burin ta kawai gari ya waye ta kama hanyar garin su, ko da dai tana tunanin me zata cewa iyayen ta idan sun ganta da ciki amma hakan ita a ganin ta sai ya fi mata kwanciyar akan irin wulaƙan cin da take fuskanta a nan 



 cikin dare nakuɗa ta kama salma, ta sha wahala sosai, hankalin hjy ba ƙaramin tashi yayi yadda taga salmar tana nunfashi sama sama gashi ta kasa nishin, ita hjy ba turanci balle larabci ita salma ba hausa ba, don haka sai communication yai wuya sosai a tsakanin su ga naƙuda ta zo da matsala sosai, ga dare babu abin hawa, addua kawai hjyr ta dinga tofawa tana ba salmar tana sha wuya sosai kafin daga bisani Allah ya sauke ta lfy gab da asuba, ta samu ɗanta namiji


Shi kanshi ɗan a wahale ya zo don sai da aka watsa masa ruwa sannan yai kuka, hamdala hjy ta dinga yi, inda salma ba abinda take yi sai kuka,


 hjy ta haɗa mata ruwan wanka don ta ɗauraye jikin ta, hjy ta kama ta ta kai ta har banɗaki ta ɗauraye mata jikin ta sannan ta haɗa mata ruwan lipton me zafi tace mata ta sha,


   ta kuma haɗa ruwa ta wnke ɗan tsaf da shi ta ɗauko sabon zanin goyo ta naɗe shi a ciki ba abinda salmar take yi har yanzu illa shash sheƙar kuka barin ma idan ta kalli yaron, hjy sai ta ɗauka ko tausayin sa take ji



 shimfiɗa ta ƙara gyarawa  salmar sannan tai mata umar nin ta kwanta, ita kuma ta ci gaba da kimtsa komai, salma kwanciya tayi ta tasa ɗan ta a gaban ta tana kallon sa wasu zafafa hawaye ne suke ta sintiri a idon ta, tausayin sa ne taf zuciyarta, 

ko ya rayuwar sa zata kasance ta tuna irin tattalin da sani yake yiwa cikin tun kafin ya zo amma wai yau ga shi ya zo amma kuma ba sani, ya za ayi ta iya tafiya da ɗan da babu uban sa, inda ma ace sanin yana da rai ne da ta tafi da shi, amma yanzu taje tace wa iyayen ta ɗan waye, waye zai yadda cewar ba shege bane

zargin ta za a dinga yi, kuma yaron ya tashi a dinga yi masa kallon shege tunda babu wanda ya san uban sa, kuka ta kuma fashe w da shi, ta rasa mafita, ita baza ta iya zama a nan ba don ƙiri ƙiri mmn sani ta nuna mata ƙiyayya wanda har hakan yai sanadiyyar mutuwar mijinta, idan na tafi da kai bazan taɓa mantawa da wannan baƙin ciki ba, idan na tafi da kai shari’ar garin mu bazavta bari in rayu da kai ba, idan na tafi da kai har abada da tabo zaka tashi, rayuwarkar anan itace rufin asirin mu ni da kai, idan da rabon mu ƙara haɗuwa Alƙah ya sada mu da alkhairinsa ta faɗa idon ta taf da hawaye

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Leave a Reply

Back to top button