DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

 ta gama yanke shawarar abinda zatayi, ta kalli yaron ta kallo na ƙarshe ta sinbace shi a kai tare da yi masa addua, sannan ta tashi saɗaf saɗaf tayi waje ba tare da hjy taji ba 


   ko da hjy ta tashi da asuba kasancewar ta ɗan kwanta bayan ta gama kafin asuba tayi, tai mamaki ganin ɗan jariri shi kaɗai sai ta ɗauka ko salmar ta shiga banɗaki ne, tai jiran har ta gaji don haka sai ta wuce ta duba ta, ba inda bata duba ba ba ita babu alamar ta 


 har gari ya waye ana neman salma bata ba dalilin ta a haka suka sadauƙar da ta gudu, haka mutan gidan hjy suka haƙura da neman nata suka zubawa sarautar Allah ido


     hjy ce ta ɗauki ɗan jariri domin sada shi da *dangin sa* gidan iya ta shiga da ɗan jariri, iya tana zaune a falon ta ana ta cin naman salmar tana sha zagi wai dama shege ne ahi yasa ta gudu ta bar shi, shigowar hjy bai sa sunyi shiru, suka gaisa amma da ƙyar iyar take ansawa


  hjy ta ɗauki ɗan ta ɗora shi a cinyar iya, "ga abinda aka samu nan" wani wulli da iyar tayi da jaririn daba dan hjyr tayi sauri ta sa hannun ta ba da tuni jaririn ya sha ƙasa, 

“ya zaki ɗauki kazantar nan ta najasa ki ɗaura min kan tsabta taccen hannuna” ta faɗa tana goge hannun ta a ƙasa kamar ta taɓa kashi
“haba iya me yayi miki idan iyayen shi kina ganin sun ɓata miki shi me yayi miki, ko ba komai kya tausaya masa mana ta yadda ya rasa iyayen sa lkc guda”

Wata ƙanwar iyar ce tayi carab tace 

“ai mummunar ƙaddara gare shi duk wanda ya ɗauki yaron nan yai ta gamo da mummunar ƙaddara kenan tunda shi haka aka hallice shi da ita tun randa zaizo duniya ƙaddarar tasa ta fara nunawa” nan suka ɗauka haka ne kam babu shakka

  hjy tsayawa tayi tana kallon jahilci tsabarsa, tqna mamaki dama hannun ka yana ruɓewa ka yanke ka yar, shiru tayi sannan tace 

“to nidai ayi haƙuri atunda ita mahaifiyar shi ta gudu kinga ruƙon yaron nan ya dawo hannun ki a matsayinki na kakarsa”

“uwar shi ma ta gudu saboda ƙaddarar da ke tattare da shi sai ki ɗauko shi ki ce uwar mu ce zata riƙe shi ke me yasa baki riƙe shi ba” inji wata ƴar iyar
“rabu da ita bata san cewar haushin ta neke jiba, don sai yanzu na fahimta cewar babu munafiki sai buhari, don ba gashi ya turo marigayi da wannan karuwar ba, shi ya zauna ya lafe so yake yi idan ƙura ta lafa ya lallaɓo ya dawo ya tunkuɗa ɗana ga halaka ya haɗa shi da ajalin sa, Allah ya isa tsakanina da shi munafiki kawai annamimi, maci amana kawai” ta faɗa tana kuka

abin nan da iyar tayi ba ƙaramin ɓata wa hjyr rai yayi ba tshi tayi tare da sauke ɗan a gefe tayi hanyar waje,

“zo ki ɗauke dawo ki ɗauke don babu wanda zai ɗauki wannan mummunar ƙaddarar a cikin zuri’a ta” tana jin ban bamin iyar da muƙarraban ta na ta dawo ta ɗauki ɗan amma tayi burus da su

   bayan ta koma gida ta shige ɗakin ta tafara hidimar ta ,can zuwa anjima ta fara jin kukan jaririn tausayin sa ne ya kama ta ya fara jin yunwa kenan ta faɗa a ranta, ta ɗauka abin wasa ne amma ga mamakin ta sai taji har yaro ya doshi kusan minti talatin yana kuka normal kukan jarirai har yazo yana kuka kamar ana cutar da shi ne 

ba shiri hjy ta yayimo hijabin ta ta fice abin mamaki da takaici a tsakar rana a dandamar ƙasa ta ga karirin sabuwar haihuwa, guje taje ta ɗauko shi tana kuka wannan wane irin rashin imani ne dama zafin rana yake kuka, rungume shi tayi ta kara sakin wani sabon kukan tausaya wa yaron, ta juyo ta kalle su kowacce tana sha’anin ta
“in Allah ya yarda sai yaron nan da kuka wulaƙanta ya zame muku inuwa” ta faɗa tana ficewa

baƙaƙen maganganu ne suka raka hjy tana jin su tayi tafiyar ta sune basusan Allah ba amma ita tana da imani kuma tasan Allah koda ace yaron nan shege ne ai bai cancanci ayi masa haka ba amma dubi yadda mutanen nan suka wulaƙanta ta ɗan jaririn  da bai ji ba bai gani ba, ta duba fuskar ɗan jaririn da tayi ja jajir saboda tsabar dukan da rana tayi masa

“Allah ya raya min kai ka zama inuwa ga waɗanda suka wulaƙanta ka randa aka haife ka” ta faɗa tana goge ƴar ƙwallar da take fito mata saboda tausayin sa
[7:45PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

 page :32????


  haka hjy ta ci gaba kula da ɗan jaririn wanda ranar suna ta sama masa sunan ɗan autan ta daya rasu wato Aliyu, har gidan iya taje ta kaimata shi tare da faɗa mata sunan da ta sa masa, amma iyar sai ta bita da baƙaƙen maganganu, haka ta taso ta bar gidan zuciyarta duk ba daɗi 



   satin aliyu uku da haihuwa buhari ya dawo, yai takaici tare da baƙin cikin abinya samu abokin sa, yai kuka kamar ba gobe, sannan ya tausaya wa aliyun ganin irin halin daya shiga tun randa zai zo duniya 


har gidan iyar ya shiga don yayi mata bayanin yadda abin yake amma iyar ta toshe kunne ta, ta rufe idon ta ta wanke shi soso da sabulu tai masa tas, ba shiri ya bar gidan ,ko da hjy taga yanayin da ya dawo tasan cewar bai samu yadda yake so ba don haka sai tayi shiru



 ko da kayan su sani su ka zo buhari sai daya kwashe duk wani kayan da ba na sanin bane sannan ya kaiwa iyar, amma iyar si ta zo tace wai sai dai abata kayan da buhari ya zo da su gabaɗaya, duk hjy ta nuna mata waɗanda suka ɗauka, kayan jarirai ne kawai, sai hotunan sanin da salmar waɗan da suka ɗauka tare don a ajiye wa yaron ko da nan gaba zai tashi sai ya ga iyayen sa



 Ganin irin kayan jariran da suke wajen ba ƙanana bane ga uban yawa ya sa iyar nan fa ta hau bala'i ai ɗan ta ne ya siya kuma basu da gadon don haka sai an bata, buhari ne ya rufe ido yai mata tas hjy bata tanka masa ba don ita ma iyar ta kaita bango


me zatayi da kayan jarirai ba mamaki so take yi ta karɓa ta siyar, hatta kayan salmar an ba iyar amma wai kayan da za a sawa ɗan jaririn shine tazo tana tada jijiyoyin wuya sai an bata, ran hjy ya ɓaci sosai, sai ta ƙyale buhari yai maganin ta, da iyar taga baza ta samu ba sai ta haƙura ta fice tana Allah ya isa wai sun ci haram 




  haka hjy ta ci gaba da kula da ɗan marayan ɗan ta wanda buhari yai rawar gani sosai wajen tallafawa yaron har ragon sun sai da ya siyo aka yanka masa, duk da dai ragowar ƴaƴan hjyr musammam ma matan basu so hjyr ta ɗauki aliyu ba amma babu yadda suka iya tun da hjyr ta dage 





  aliyu ya taso da kuzarin sa idan ka ganshi, sai ka rantse nonon uwarsa yake sha yai shar da shi ga kyau kullum ƙara fitowa yake kamar su ɗaya da mahaifiyar sa, kamar tayi kaki ta tofar, wannan abun ne yake ƙara tunzura iyar take cewa yaron ya gado maitar uwar sa


  aliyu yana shekara ɗaya da rabi, baba wato buhari kenan yai aure  ya auro mama halima daga bauchi, Allah ya haɗa shi da mace ta gari, tana taimakawa hjy kula da aliyu sosai, ta so ɗan sosai da sosai, bata daɗe ba ta samu ciki, ko da lkcn haihuwa tayi Allah ya sauke ta lfy ta haifi ɗan ta namiji wanda yaci sunan bbn buhari wato ahmad amma ance masa tijjani


Rayuwa me daɗi suke ciki da buhari da iyalen sa babu abinda yake rabawa tsakanin aliyu da tijjanin komai ɗaya yake mu babu bambanci wannan abun yana farantawa hjy rai sosai don duk wanda ya kula da ɗan wani Allah zai kular masa da nasa


 lkcn da tijjani ya isa yaye sai hjy ta haɗa su da aliyu ta riƙe ita kuma haleema a lkcn tana laulayin cikin ta na biyu don haka sai kawai ta ji da kanta, ko da lkcn haihuwa yayi sai halima ta roƙi alfarma awajen baba buhari na taje bauchi ta haihu be musa ba amma yace mata bazata tafi da su aliyu ba, ba haka ta so ba amma ba yadda ta iya 


 ranar wata jumma'a suka kama hanyar bauchi tare da buharin don ya kaita, tafiyar da badu kuma dawowa ba, don kuwa a hanya suka haɗu da haɗarin da yayi sakamakon rasa rayuwar su



   sai da suka kwana biyar sannan hjy ta samu lbr ba shiri ta kama hanyar bauchin hankali a tashe, ta je ta tarar da wannan tashin hankalin, tun ran da suka rasu aka so faɗa mata amma kasancewar ba ɗan aike ya sa bata ji da wuri ba



   haka hjy ta ci gaba da kula da ƴen marayun ƴaƴan ta har guda biyu, gwanda tj shi yakan samu taimako daga ɓangaren mmn sa ko ƴen uwan uban sa, shi kuwa aliyu sai abinda hjy ta samu tayi masa


rayuwa taci gaba da tafiya, Hjy tana kula da ƴen marayin ƴaƴan ta, don ta samu rufun asirin ta sai ta fara sai da alala da manja don kawai ta smu ɗan abun da zasu dinga kau da matsalolin yau da kullum 


tj da aliyu suka taso tare tun suna ƙanana suke kiran junan su da ɗan uwa, da wuya kaji sun ambaci sunayen su, shaƙuwa ce aosai tsakanin su, baka taɓa jin tsakanin su ko hjy haka take ganin su ta bar su


aliyu ya taso mara son magana, in kaga hirar sa da dariya to ka tabbatar da hjyr sa ce ko kuma ɗan uwan sa, wannan dalilin ne yasa baya shiga mutane sosai babu yadda hjy batai ba na ya dinga zuwa yana gaida iya amma da kyar yake zuwa tabbas tasan iyar ce take zagin amma kuma ya zata yi jikan ta ne ta zama dolen sa 


 ganin hakan ne yasa idan hjy zatayi alala aliyu ne me kai markaɗe gidan iya, kuma kullum yaje da zagin da zai sha wajen iyar kafin tayi masa markaɗe


 takan zage masa uwa tas, wai ta yada shi ta tafi yawon karuwanci, yakanyi mamaki wacece wannan uwar tasa kuma meye ya haɗa ta da iyar haka da har ta tsane ta kuma tsanar ta shafe haka 



 kamar kullum yau ma hjy ta aiki aliyu ya kai markaɗe yana fitowa daga gidan sai yaci karo da wani ɗan maƙocinsu bala da ƙanin sa

“alin hjy ina zaka” bala ya tambaya
“zan shiga gidan iya in kai markaɗe ne”
“iya bala’i zaka ce, kai baka gajiya kullum ka shiga gidan matar na sai ta zage ka, kuma ka kasa faɗawa hjy ta dai na aiken ka”

murmushi aliyun yayi be ce komai ba
“kawo ina habu ƙanina ya kai yau ka huta da zagi” kamar aliyu ya ƙi amma sai ya ba habun ganin cewar ai markaɗe ne kawai

"zo muje ka raka ni wani wuri" inji bala ya faɗa yana jan hannun aliyu

“zan taya hjy aikin alalan ta”
“ai ba daɗewa zamuyi ba zan koya wa wani yaro hankali ne” ya faɗa yana jan hannu aliyu wanda shi kuma ya bishi zingwi zingwi ba tare da ya sake yi masa musu ba

  sun ɗan yi tafiya sai ya ga balan ya tsaya ya laɓe a ƙofar wani gida shima sai ya biye masa, wani yaro ne ya fito daga wani gida dake ƙasan layin, ko da yaron ya matso kusa da su sai bala ya ɗauko wani dutse ya jefi yaron da shi sannan ya ruga a guje, shi kuma aliyu sai ya tsaya yana kallon ikon Allah 


ko da ya ga jini a goshi yaron ga kuma mutane sun fara taruwa sai shima ya ruga a gujen, yana jin wani yana cewa alin hjy ne ya jefe shi gashi can yana gudu


 shidai tun daya samu ya tsere kawai sai yayi filin ƙwallo don yasan dole za a je gidan su neman shi, to idan suka je basu ganshi ba ai dole su haƙura ya faɗa, sai bayan la'asar sannan ya kama hanyar gida yasan yanzu ƙurar ta lafa ya faɗa aranshi yasan yau sai hjy tayi masa faɗan zuwa yawo ya faɗa yana kama hanya


yana shawo kwanar gidan nasu yaga ƙofar gidan cike daƙam da mata da yara sai zage zage suke yi, ko da ya lura sosai sai yaga ƴaƴan hjy ne sai mutan gidan iya da ita kanta iyar to me ya faru ya faɗa 


ko da idon su ya kai kanshi da gudu aka je aka kamo shi kamar wanda yayi sata kowa yana masa tofin Allah tsine, babbar ƴar hjy wato hauwa itace taiyi masa mari a dukkan kumatun sa guda huɗu ƙwarara


nan suka hau dukan sa wai duk abinda uwarsu tayi masa sakayyar da zai mata kenan, gaba ki ɗaya duk cikon taron wurin nan daga me dukan shi sai me zagin sa, shi ko kaɗan be ma san abin da yayi ba



zagin sa da suka dingayi na tsintacciyar mage itace ta fi ƙona masa rai, duk cikin gurin nan babu me ƙaunar sa, to me yayi musu tabbas tun taso war sa yasan shi ba irin su don shi kana ganin sa kaga balaraben asali fari ne kyakkyawan gaske ga gashi irin na larabawa, ga baƙi ga kyau da sheƙi don ma baya samun kulawar da ta dace shi



  tun tasowar sa yake fuskantar kyara da tsangwama su kansu ƴaƴan hjyr a gaban idon ta ne suke nuna suna sonsa amma da babu ita a wuri shike nan shi tashi ta kaɗe, ya rasa me yayi musu me mahaifiyar shi tayi musu me yasa suka tsane shi haka, shi bama sanin mahaifiyar tashin yayi ba amma kullum sai ya sha zagi da tsinuwa sabida ita wai me mahaifiyar shi tayi ne haka da muni da har abin yanzu ya dawo kansa

duk wannan dukan da suke yi masa da zagin nan idon ƙamas yake ba hawaye, sai dai zuciyar sa da ke bugawa tana wani karta masa kamar ana soka masa allura acikin ta, ƙirjin sa kawai ya kama tare da tsugunnawa ƙasa ganin halin da yake ciki be sa sun fasa zagin sa ba sai ci gaba da yi masa gorin hjyr su tayi masa shi kuma da yake tsintacciyar mage ne bata mage sai ya saka mata da wannan

  Iya ce ta ɗauka kun manta yadda uwar sa ta kashe min ɗan ran da ya dawo, haka ne iya uwar sa ta lashe kurwar sani don kince ba ki yadda da auren su ba, nan suka fara caccakar mahaifiyata tare da bin ta da munanan addua

kun san ai munmunar ƙaddara ce take bibiyar sa tun haihuwar sa me zai hana duk wanda yake tare da ta shafe shi, inji iya

to wallahi ƙaryar ka mummunar ƙaddara ka baza ta faɗa akan uwar mu shekara goma sha uku hjyr mu tana ta ɗawainiya da kai uwar da ta haifeka ma tun da ta yar da kai ta gudu bata kuma waiwayar ka ba saboda ƙaddarar ka to wallahi tun wuri ka kama gabanka kasan inda dare yi ma don babu abinda ya haɗa mu da kai taimako ne sai ka jefa mana uwa cikin bala’i

to wai wacece mahaifiyata me ya haɗa ta iya da har ta kashe mata ɗa ina kuma hjy tayi me yasame ta ya faɗa a ransa gaskiya doƙe ya bar gidan nan ya bar mutanen tun da sun fito ƙiri ƙiri sun nuna masa basa ƙaunar sa kuma yana gudun kar munmunar ƙaddarar sa ta shafi hjyrsa macen da tafi kowa son sa da tausaya masa hjy ina kika shige nedon yasan inda tana nan basu isa suyi masa wannan cin kashin ba
[7:45PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

wannan page ɗin naku readers ɗin DANGIN SA na sadaukar da shi kacokam ɗinsa gare ku ????????????????

  page :33????



  Gajiya sukayi da zazzaga masa bala'in sannan suka kama hanya ko ina zasu oh, na dai ji hauwa tana cewa ku zo muje muga uwar tamu mu ƙyale wannan tsintacciyar magen, 

Kafin kace me duk an watse an barni a durƙushe riƙe da ƙirjina wanda zuciyata take bugawa kamar zata tsaga ƙashin ribs ɗina ta fito

tashi nayi don dole ne inje inji me ya samu hjyr, yana shiga gidan a tsakar gida ya tarar da tj yana ta sharɓar kukan sada sauri ya ƙaras kusa da ɗan uwan nasa

“ɗan uwa me ya same ka” ya tambaya yana dafa shi, jin muryar aliyu yasa tj ɗago da kansa tare da kallon aliyun

"ɗan uwa me su aunty hauwa suka yi maka" ya tambaye ni 

“babu abinda suka yi min, ina hjyr take”
“ƴen sanda sunzo sun tafi da ita wai ka fasa wa wani kai”

aliyu be sain lkcn da yayi baya yai zaman daɓaro ba, oho sai yanzu ya fahimci dalilin daya sa su aunty hauwa yi masa haka, wai an kama hjy, to ai shi yayi ba 



 ya kalli tj wanda har yanzu yake shash sheƙar kukan sa 

“wane police station aka kai ta”
“nima ban sani ba, amma tace idan ka dawo ka jira ta kar ka fita” gyaɗa kai kawai nayi

  wato koda da tana cikin wannan halin amma ta damu da shi wayyo hjy wallahi bani nayi ba, kuka nake son yi sosai amma na kasa don idona a soye yake, sai zuciyata da ke ta bugawa da ƙarfi da kuma sauri kamar nayi gudu 




  haka muka zauna zaman jiran gawon shanu, hjy sai da akayi magariba sannan sai gata da ƴaƴan ta, tana ganina ta yo kaina tare da tambayar "kaci abinci kuwa"   gyaɗa mata kai kawai nayi duk da dai banci komai ba amma ko kaɗan bana ji yunwa



      "ya naji jikin ka zafi baka da lfy ne" ta kuma tambaya

“wallahi hjy bani na jefe shi bala ne”
“haba alina ko ba wanda zai shede ka ni zan shaide ka nasan ba kai kayi, ka kwantar da hankalin ka ba abinda akai min asibiti kawai na kai yaron” ta faɗa tana ƙara jawo ni jikin ta, wanda ni kƴma na lefe nayi luf da ni, gaskiya ina ƙaunar matar nan har cikin rai na

ƙiri ƙiri ƴaƴan ta suka nuna ya kamata tayi min faɗa nan ta hau su da faɗan babu ruwan su, ba yadda suka iya haka suka haƙura sai dai saƙon harara da suka dinga aiko min da shi

 Sai da na kwanta jinya har na kwana uku kasancewar ƙirjin nawa ya saukar min da zazzaɓi me zafi, tare da ciwon kai hjy ta ɗauka zazzaɓin ne kawai don haka sai tayi ta dura min maganin malaria



    aikuwa cikin ikon Allah na ɗan samu sauƙi don ita ma zuciyar ta ɗan rage dukan da take min, ko da naga na ɗan warwaresai na shirya barin gidan, don gwanda in bar gidan nan kar mummunar ƙaddara ta ta shafi hjy da tj mutanen da suke ƙaunata 


  da safe bayan na gama komai nayi sallama da hjy akan na tafi in gaida iya, hjy tai murna har tana samin albarka, ina kallon hjy ina jin zuciya ba daɗi idan na tune cewar baza ta kuma ganina ba


naira hamsin ce kawai a aljihuna, tun da na fita nake gararan ba na in shiga nan in fita nan har dare yayi min sannan na samu mkrt almajirai na lafe a cikin su nai bacci na




 duk da ba wani baccin kirki nayi ba ni da saba bacci a lafiyayyar katifa amma wai yau nine kwance a dandamaryar ƙasa, hana kaina kuka nayi gwanda inyi wannan rayuwar da inyi rayuwar jin daɗi bayan hjy kullum zata dinga fuskantar ƙalu bale saboda ƙaddara ta haka har bacci ya kwashe ni ina tunanina 



kashegari da sassafe na tashi na kama gabana tun kafin su fahinci cewar ni ba a cikin su nake ba, haka na dinga yawo kwararo kwararo inna gaji in samu inuwa in lafe inna huta in ci gaba da tafiya inna ji yunwa in tsaya inyi bara har sai na ƙoshi sannan in ci gaba 



   haka na ci gaba da rayuwa ta har na kwashe wata shida ni ba almajiri ba ni ba ɗa ba in kin ganni a lkcn baza kice nine alin hjy ba don na canza sosai, acikin yawace yawacen nawa ne na haɗu da wani almajiri me suna shapiu, ɗan katsina ne bbn shi ya kawo shi almajiranci amma da malam ya ishe shi da duka sai shima ya tsere, shine muke gararan bar tare

shapiu ya girme ni sosai don haka ya fini wayo nine me barar shi kuma yana zaune sai dai in samo in kawo mana sannan muci tare

rannan yawon mu ya kaimu ƴen kaba kasuwar kayan miya, ana ta loda kayan miya cikin motoci suna fita da shi zuwa garuruwa, abin yabi sha'awa nan nan nima na shiga loda kaya cikin mota, ko da muka gama sai aka bani naira 100


wannan kuɗin da aka bani ba ƙaramin daɗin su naji ba, sai na fara loda kaya a duk motar da tazo domin lodi ina samun kuɗi shi kuma shapiu ba abinda yake daga yaje wacce inuwar ya zauna sai ya je ya nemi wannan majalisar ya zauna ayi hira da shi nine me neman kuɗin



  in kaga ya nemi ni to yaki yunwa haka zaizo yana min ƴar murya ni kuma bana iya hana shi ganin kamar shi kaɗai ne ya sanni don haka ina yi masa kallon ɗan uwana, idan kuwa na bashi bana kuma ganin shi sai ya ƙara jin wata yunwar


 watan mu uku a kasuwar ƴen kaba shapiu ya kawo shawarar mu tafi lagos wai anfi samun kuɗi a can banyi wata wata ba muka kama hanyar lagos a cikin wata motar kayan miya, tafiyar da ta canza min rayuwata tafiyar da ta maidani abinda nake yanzu. 


ayi hakuri da wannan yau na tashi ɗan jariri na walid ba lfy don Allah ku sa a addua ????????

[7:45PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

  *ga gode sosai da adduar ku gare ɗana ya ku masoyan dangin sa Allah ya barmu tare ya samu sauki Allah ya saka* 



Page:34????

Hjy ce zaune a fali ta zuba uban tagumi tana tunanin rayuwa, yanzu aliyu a doshi shekara da ɓata ba shi babu lbrn sa, ta tuna lkcn da ya ɓata da taga har dare be dawo ba kuma tasan be saba yawo ta shiga neman sa

Babu inda basu ba shi ba ita da tj, inda tj ɗin ba abinda yake yi in banda kukan ɗan uwansa itama hjyr daurewa kawai take yi 

daga ƙarshe suka biya gidan iyacigiyar sa duk da hjyr tasan bazai taɓa zama a gidan ba amma dai ance in kana neman raƙumin ka ko cikin tandu sai ka duba

nan iya ta kwashe lbrn abinda ƴƴan hjyr sukayi wa aliyun randa aka kulle ta police station tas ta faɗa wa hjyr, wai hjyr tana riƙe da shege bayan ƴaƴan da ta haifa basa son sa 


Hjy rasa bakin magana tayi haka ta dawo gida jikin ta a sanyaye, a daren har kuka tayi tai sallah sosai ta roƙo Allah ya kare mata shi duk inda yake, kashegari ta kira ƴaƴan nata bayan sun zo ta wankesu tas da soso da sabulu sannan tai musu albishirin aliyun ya gudu don haka sai kawaccen su hankalin ta ya kwanta


haƙuri suka fara bawa hjyr nasiha tai musu sannan tace su kuma san da cewar duk wani abinda ya samu yaronnan mara kyau su san da cewar da kamashon su a ciki


kowacce sai jikinta yai sanyi bayan hjyr ta gama yi musu kuma ta patattake su, haka ta zauna ta dinga bin aliyu da addua kullum bata fasawa kuma bata mantawa,


 ****************

 mun sauka lfy a garin *yanki* inji mazauna can, directly kasuwar idi yaraba muka wuce acan muka sauka na fara harkar dako, to rayuwar a lagos ba kamar kano bane, komai da sauƙi, don haka ni da shapiu kowa tasa ta fish she shi mukeyi 


 Wasu ƴen area boys yake bi babu yadda banyi da shi akan mu nemi abinda ya kawo mu wato bugun abuja amma ƙiri ƙiri sai ya nuna min shi ba sune a gaban sa ba babu yadda na iya shi haka na ƙyale shi, tun yana ɗan zuwa harbya koma ma sai in shafe qata bangan shi ba, a haka tarayyar mu da shapiu ta watse

Aikin da nakeyi na ɗaukar kaya sai kai kaya wurare ba ƙaramin samun kuɗi nake yiba kuma bayan abinci ba abinda nake siya tarawa kawai nakeyi don inyi wa hjyta siyayya

   yau kusan watana bakwai a lagos kuma ba laifi na waye sosai na san gari kuma na san harka kama kuɗi nake yi dai dai aikina, akwai wani wai shi umar tare muke aikin mu da shi shima ɗan kano ne amma ɗan kurna da iyalen sa akano


 ina son zama da umar sosai ko ba komai idan yana hirar iyalin sa sai inji kamar ina gida, rannan katsaham sai gashi wai gida zashi yayi kewar iyalinsa, kawai nima sai naji hjy ta faɗo min rai, gaskiya ban kyauta yau kusan shekara ɗaya kenan da wani abin da guduwata amma ban taɓa leƙa ta ba kuma nasan tabbas hankalinta ba a kwance yake ba


duk dani ma kullum suna raina ita da tj wanda wani lkcn tsabar tunanin su take sawa inji zuciyata na buga min tare da min wani azababben ciwo gaskiya dole ne inje inga hjyta na faɗa araina


Umar na samu na faɗa masa nima ina da ra'ayin zuwa kanon yai murna tare da min nasihar in dinga kula da iyayena barin idan basu da hali sosai



 kuɗin da hannuna na haɗa muka tafi kasuwa nida umar, siyayya sosai mukayi, buhun taliyar nan irin ta damage na campany guda biyu, sai jan wake na san hjy ta na son sa, akwai wata madara da ake siyar wa daɗi gare ta, da bourntiva ɗinta a haɗe kawai sugar zaka sa sai ka haɗa shayi,botikin penti biyu na siyo sannan na samu gwangwani manya manya na madara na juye su a ciki, su hjy su sha shayi mu more, 



sai kayan gwanjo masu kyau da sai wa tj, ita kuma hjy na sai masa lesis masu kyau guda uku marasa nauyi



  muka kamo hanyar kano, a hanya ne na dinga ba umar lbrin abinda na sani game da rayuwata da dalilin guduwata, ya tausaya min sosai daga nan bai kuma cewa komai ba



 mun tsaya a hanya muka sai doya da manja, tj kawai na hango don masoyin doya ne, a kura muka tsaya muka sai shinkafa ƴar hausa me kyau, ta dafawa da ta tuwo sai gero, sannan muka ƙaraso cikin garin kano



munyi siyayya kamar ba gobe barin ma niduk abinda na gani sai na siya, don haka muna sauka kano muka ɗau akori kura sai kurna gidan umar muka sauka don nace masa bazan je gidan hjy ba sai dai in masa kwatance


  kasancewar da safe muka sauka sai da muka huta sannan da yamma muka kama hanyar gidan hjy don so nakeyi a ranar in koma lagos ɗin



 taxi muka ɗauka aka loda mana kayan nawa har layin da za a shiga gidan hjy sannan muka sauka muka samu almajirai suka ɗau kayan, nai masa kwatancen gidan sosai sannan nabi bayan shi don in laɓe don ina son ganin hjyta sosai

dubu biyar na bashi tare da wasiƙar kwantar mata da hankali tare da nuna mata inanan lfy wacce na rubutata tun a lagos, sai hotunana guda biya, a ƙofar gidan ya tsaya ya doka sallama

 hjyr ce da kanta ta fito sanye da hijabin ta tana nan yadda na barta Allah sarki hjyta na faɗa araina, sun daɗe suna magana tare da hjyr inda daga baya ya miƙa mata envelope ɗin da wasiƙar tawa da pics ɗin wa suke ciki



  Hjy tana karantawa tana hawaye ni kaina sai ta bani tausayii amma dole ne inyi haka in tashi don in gina kaina don kuwa bani da gata bani da me yi min don haka dole in san in da dare yayi min, sukayi sallama bayan ya sa an kwashe mata kayan an shigar mata da su ciki


koda muka haɗu sai dinga min faɗan in koma hjy tayi kewa ta sosai tooo kawai nace masa mukayi sallama sanna na kama hanyar tashar sabon gari don komawa neman kuɗina


na koma lagos na ci gaba da neman na kaina, duk wani burina yanzu akan hjy yake da tj, duk wani abu idan na samu sai in tura kano umar sai ya tura ƙaninsa ya kai musu, bama waya amma muna musayar wasiƙu musamman ma tj, duk abinda yake so in dai ya faɗa min sai na siya na aika masa ita kuma hjy babu komai a wasiƙar ta sai nasiha da adduar kullum in zama me gaskiya tare da neman halal kawai


***************


hjy tana zaune tana girki taliya take dafa wa wacce taji kayan miya tare da nama, zuƙu zuƙu tana tunanin rayuwa yanzu komai sun fi ƙarfin sa in dai ta ɓangaren sutura ne da abinci to sai dai ta bawa wani, sallamar da aka doka ce ta katse mata tunanin ta, tashi tayi ta ɗan leƙa sai ta ci karo da nasiru ƙanin umar, ga kayan abincin nan buhu buhu a kusa da shi



bayan sun gaisa ya bata kayan ya kama hanyar sa har kuɗi ta bashi amma ƙiri ƙiri ya ƙi karɓa, haka ta sa aka shigo mata da kayan nan ko waɗan da ya aiko musu da shi wancen watan bai ƙare ba ko rabi basu ci ba amma wai yau gashi yanzu ya kuma aiko musu da wani kamar bai san ciwon kuɗin sa ba


shawara ce ta faɗo mata sai ta raba kayan biyu tasa yara suka ɗaukar mata rabi sai gidan iyababu abinda ba ta ɗibarwa iyar ba harda kuɗi dubu uku


 iya ganin ana ta shigo da kaya ɗakin ta yasa ta sakin bakin tana mamakin waye, ganin hjy ya sata ƙara mamaki har da ƴar fara'ar ta rabon da hjy taga fara'ar iya har ta manta

bayan sun gaisa hjy tai wa iyar bayanin irin hidimar da aliyun yake musu sannan tace mata gashinan na raba kayan biyu na kawo miki rabi kema kici arziƙin jikan ki duk da dai kince ba jininki jininki bane amma kowa ya san jinin ki, don haka gashi kema kici arziƙin jikan ki

 hjy ta ɗauka iyar zatai bala'in ta da ta saba amma ga mamakin ta sai taji iyar tana bin aliyun da adduar Allah ya kare shi duk inda yake , hjyr sai ta ɓoye mamakin ta tare da ansawa iyar da amin sukayi sallama a mutunce hjyr ta kama hanyar gida cike da mamakin canzawar da iyar tayi

[7:45PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺U☺☺☺☺☺☺☺

 page:36????


   Haka na ci gaba da neman kuɗi tare da turawa hjy duk wani kuɗin daya zo hannuna, ban damu ba idan na zauna banni da ko sisi in dai na tabbatar da cewar gidan hjy akwai abinci to bazan damu ba 


 Shekara ta biyu a  idi yaraba sannan Allah ya haɗa ni da wani bayarabe wai shi balogun, yakan zo kasuwar mu, a haka shaƙuwa ta shiga tsakanin mu, ko da muka shaku sosai sai ya yi min tayin wai in zo in fara aiki da shi a deport, ban wani dogon tunanin ba na bishi a lkcn umar yana kano don haka babu wanda inda na koma


 Aiki a deport yana wuya amma kuma samun kuɗin da ake yi a can bama za a haɗa da idi yaraba ba, don haka kan a ce wannan na tara kuɗi ba kaɗan ba 



  Watana uku a deport na tara kuɗin da ni kaina ban san cewar zan same su ba, kuma har yanzu ban kuma neman umar ba, ranar wata talata ana saura sati biyu a fara azimi na shirya zuwa ganin umar don in aikawa da hjy kayan azimi, don in shaa Allah azimin bana hjy sai ta shana 


 bayan mun gama aikin mu na shirya sai idi yaraba, umar yai murna sosai da ganina tare da faɗa min yadda hankalin hjy ya tashi da taji lbrin ya bar idi yaraban, nan ya faɗawa umar sana'ar da ya koma yi a deport, ɗin 

Umar ya jinjina wa aliyun yaro ne ɗan ƙarami amma Allah ya bashi zuciyar nema, komai wahala yanzu me ya kai aikin deport wahala, akwai samun kuɗi amma akwai wahala kuma, da kaya sun zo daga waje ko cikin dare ne dole ku fito ku kwashe tare da loda su a cikin motacin da zasu kai garuruwa, haka in kaya suka tashi a fitar da su daga nan, nan masai sun kwashe sun loda

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Leave a Reply

Back to top button