
ko da aka shige get ɗin gidan ya ganshi fes kamar yadda ya sa ran samun shi da kewar iyalen shi ya dawo amma sai ya dake ya kama hanyar part ɗin sa, ba tare da ya kalli part ɗin natan ba don shi a tsarin shi mace bata isa ya bita ba, don shine gaba da ita
a gaskiya yai tsammanin ganinta amma ga mamakin sa sai taƙi zuwa har dare yayi babu ita balle yaga ƴaƴan sa me kenan zainab take nufi
ita ma dai zainab a nata ɓangaren tana jiran shi ya shigo don taga dawowar sa harda ɗan shirinta don tasan yadda ya kwashe kwanakin nan bai gansu ta san zai shigo ya biɗa haƙƙin sa amma abin mamaki shiru bashi ba labarin sa har bacci ya kwashe ta
duk kowannen su ya kwana tare da bacin ran ɗan uwan sa, abinda bai taka kara ya karya ba ya kai ga masoyan nan cikin tashin hankali kowannen su yana ji haushin ɗan uwansa yana gani ɗan uwan bai ɗauke shi da daraja ba
haka suka tashi kowannen su yana cike da ɗan uwan sa gaba ce sosai ta shiga taakanin su inda a kowane ɓangaren suke cutuwa kuma suna begen juna tare da fatan faɗan nan zai zo ƙarshe amma da yake sun bar shaiɗan ya na yi musu huɗuba sai kowanne ya ɗau fishi tare da ɗorawa ɗan uwan sa laifi
har aliyu sai kwashe wata da wani abun gabar nan tasu babu sauƙi, ya gaji don haka sai ya nufe ta don ya na son sanin me take taƙama da shi da har zata dinga yi masa wannan abun kamar ba mijinta, wannan karon ba zai juri rashin mutunci ta ba inda tayi taga taci riba wannan karon bata isa ba ya faɗa tare da dosar part din natan
itama zainab a nata ɓangaren abin yana damun ta mutumin nan me yake nufi kenan bata wata daraja kenan ya tafi kusan wata huɗu be taɓa neman su ba yanzu kuma ya dawo ko ta kansu be bi ba hidimar sa kawai yake yi, wasu hawaye na takaici suka zubo mata bata bi ta kan hawayen ba sai ta ƙyale su suna zuba da kansu ko taji sanyi zuciyarta
banko ƙofar ɗakin natan taji anyi kamar ana yaƙi da sauri ta goge hawayen da ke zuba tare da juyowa taga waye, gogan ne ranshi a bace yana tsaye tare da riƙe ƙofar da hannun sa fuskar nan tasa kamar me don ya bala'in haɗe rai
“ke wai me kike taƙama da shi ne ki faɗa min, ko an gaya miki bazan iya rayuwa bake bane ko kuma don kin haifa min ƴaƴa guda biyu shine kike tunanin zakiyi min rashin mutuncin da ranki yake so, bazan zauna da matar da bata da mutunci ba wacce bata san mitinci mijinta ba kina ƙarƙashina amma baki san komai na kula da miji ba so kike yi kullum ya kasance ni zan dinga binki, ki kalle ni kyau banyi kama da namiji me bin mace ba ita kuma tana yin rashin mutuncin ta ni ban ɗauki mace a bakin komai ba face abara ajiye wa agida
ko kina tunanin ni da ƴaƴa na bazamu iya rayuwa ba sai da ke ki kalle ni nan tun uwata ta haifeni ta gudu ta barni kuma gani nan daram har nafi wasu mada suka rayu da iyayen su don haka bazan juri wannan rashin mutuncin naki ba tare rashin tarbiyya
ki shirya kayan ki ki koma gidan ku idan kinje kin koyo yadda ake kula da miji kya dawo don bazan iya zama da macen da bata san darajar mijinta ba, har ya fita ya dawo
kuma da fatan bazaki tafin min da ƴaƴa ba ko ɗaya har mohd ɗin ma ki ajiye min abina don bazan bari suje su koyo rashin tarbiyyar da kike taƙama da ita ba
ya fita daga ɗakin tare da banko ƙofar kamar zai balla ta kuka kawai na saki tare da tausayawa kaina, rashin mutunci aliyu ya isheni haka duk abinda yayi min be ishe shi sai daya biyo ni har ɗaki yai in rashi mutunci gaskiya dole ne in bar masa gidan sa na faɗa ina fara haɗa kayana
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:39????
Haɗa kayana na fara yi tare da sa na mohd ni ba mahaukaciya bace idan shi bashi da tausayi to ni ina da shi haidar de zan bar masa amma bazan bar masa ɗana me shan nono ba na faɗa araina
Bayan na gama haɗa kayana na fito da su tare da kiran masu aiki su taimaka min su fitar min da akwati na har bakin get naje da mohd a goye a baya na ga akwati na ina ja, amma sai me gadin ya hanani,
“hjy yallaɓai yace kar in barki ki tafi da yaro ko ɗaya” kaina ne ya ɗaure au har faɗawa ma’aikatan sa yayi cewar kar in tafi da yaro ko me
Na kai duba ga mohd wanda yanzu na sauko shi sai baccin sa yake tayi, hawaye naji sun cika min ido ya za ayi in tafi ba tare da wannan yaron ba me yayi, in ni yana ganin nayiasa laifi ɗana fa me yayi yaron da babu abinda yake ci daga nono sai ɗan ruwa in yaga dama
Komawa nayi cikin gidan indai kuwa bazai bari in tafi da ɗana ba to kuwa babu inda zani na faɗa, bai dawo ba sai dare, ya shigowa part ɗina ya nufa fuskar shi amurtuke
“ke da yake bai da mutunci nace ki tafi shine kika ƙi tafiya ko”
“ce maka akai gidan ka aljannah ne da zaka ce na ƙi tafiya, na so tafiya me gadinka ya hanani”
" au da kina nufin da ƴaƴa na zaki tafi"
“ai kai da yake baka da imani shine zaka raba ni da wannan ɗan jaririn” na faɗa ido na taf da hawaye
“rashin imani kike son gani, yau zaki san kin zo ƙarshe”
Ƙwace mohd yayi daga hannun na, bazan iya cewar zan hana shi ba don in muka ce zamuyi kokawa akan yaron shi yaron ne zai cutu,
nanny ɗin sa ya kira me suna hannatu don yanzu na sallami kafiran nan nannies ɗin yara duk musulmai ne, yace ta karɓi mohd ina kallo aka fitar min da yaro na kuka kawai nake yi ban taɓa ganin wulaƙanci irin wannan ba a raba ka da ɗan ka
dawowa yayi kaina yana jana har sai daya kaini waje sannan ya sani a mota tare da driver ɗin yasa lock a motar sai ga kayana an biyo ni da shi har da yar jakar hannun na
window ɗin ya buɗe tare da wullo min purse ɗin a fuskata "duk randa kika san darajar miji kya dawo" kuka na saki me sauti in Allah ya yadda ni aliyu har abada bazan kuma zama da mutumin da be san darajar ɗan adam ba na faɗa
driver ya ja muka fara tafiya sai lagos ina jin shi yana ja wa driver ɗin kunne ya tabbatar da ya ajiye ni a ƙofar gidan mu, sai kace wata yarinya, ranar naci kuka irin wanda ba taɓa yi ba
wai dama haka mutum yake ji idan wanda yake so ya ƙona masa rai don Allah ya za ayi in iya yafewa aliyu irin wannan cin kashin da yayi min, sai asuba sannan muka ƙarasa lagos aikuwa har ƙofar gidan namu ya kaini lkcn gari ya waye ma sosai kasancewar go slow ɗin da muka tarar a hanya
adaidai ƙofar gidan mu yayi parking tare da fita ya ƙwanƙwasa gidan ina zaune cikin motar ina jiran shi don gabaɗaya motar a kulle take har yanzu be buɗe ba
wata yarinya ce tazo ta buɗe, sai shi kuma ya juyo ya zo ya ɗaukar min akwatina tare da miƙawa yarinyar sannan ya buɗe min ƙofar na fita
tooo faaaa yau ake yin ta me zancewa baba kenan, na faɗa araina, ohhh ko ya ɗana mohd ya kwana shi kaɗai ya faɗo min araina naji wasu hawaye, goge hawayen nawa nayi sannan na saka kai na cikin gidan namu yau dai sai yadda akayi da ni
nayi mamakin dana ga falon gidan babu kowa sai yarinyar nan da ta buɗe min daka gani ƴar takwa ce ( ```irin yaran nan da ake ɗauko su daga niger suna yin aikatau```)
"ina maman" na tambaya ina neman wajen zama
“ta tafi shagamu da asuba ita da baba”
“me akeyi a shagamun”
“ɗan ƙanwarta ne ya rasu jiya da daddare shine sukayi sammako don su samu jana’iza” ta faɗa
Allah yayi mama da ƙanne sosai a shagamu don haka sai ban damu da sanin ko wacce bace na dai bishi da addu'ar Allah ya jikan rai
“to ina su amina da su bashir” na kuma tambayar ta ƙannena, wato ƴaƴan mama
“duk tare suka tafi”
“ke kaɗai ce a gidan” gyaɗa min kai tayi, daga gani ta ɗan jima a gidan amma da bata daɗe ba mama bazabta taɓa barin ta ita kaɗai ba
miƙewa nayi aikuwa banga ta zama ba da su mama na nan ne da sai in zauna amma tunda ba wanda ya san na zo gwanda in ƙara gaba don yanzu da sun dawo ni zasu ba rashin gaskiya tare da mai dani wurin wancan mara mutuncin da be san darajar ɗan adam.ba na faɗa tare yin waje da ɗan akwati na
"aunty zaki tafi ne in ta dawo wa za ace mata tazo" shiru nayi ina tunanin wa zance ni yanzu duk na manta ƙawayen maman ma balle in anbaci sunan ɗaya koma zan iya anbata ƙila yarinyar ta san su sai nace mata
“kice mata ƙanwarta ce ta zo su tafi shagamun tare, ko da yake barshi ba sai kin gaya mata ba idan muka haɗu acan zan cemata na biyo ta nan” to kawai tace min nai mata sallama na kama hanyar waje
purse ɗin da ke hannuna na duba naga tabbas kuɗin ciki zasu kai ni kano daga nan tashar mota dake agege na nufa domin kama hanyar kano
*************
duk da dai yasan badace ba abinda yayi mata amma hakan a ganin shi shine dai dai ƙila idan taje ayi mata faɗa, gaskiya yana son zainab sosai amma wani lkc dole ya rufe ido ya taka mata burki idan tanas wani abun nata
madara yaje ya siyo wa mohd, kan a dinga bashi shima sai yanzu yaga kuskuren shi ƙwace yaron da ya bar mata shi ƙiri ƙiri yaro ya ƙi shan madara tunda be saba da feeder ba, don haka sai ya ƙi karɓa yana ta kuka
haidar ganin ɗan uwansa na kuka ya sa shi fara kuka tare da kiran ```ammi na```kuka kawai suka dinga yi daga shi har mohd ɗin, nannies ɗin nasu rasa yadda zasuyi sai suka kira aliyu don ya san a halin da ake ciki
yana zaune a office aiki ne gare shi sosai a gaban sa, amma kusan rabin hankalin sa ya kan wayar sa yasan iyayen zasu iya kiran any moment shi ma so yake yi ta dawo ko don ƴaƴan sa ya faɗa,
“taurin kai gare ki baki iya bada haƙuri ba duk da kin san ke me laifi instead sai ki ka so yi min rashin kunya”
gabaɗaya ya rasa abinda yake masa daɗi, yana cikin wannan tashin hankalin ne ya samu waya daga gida inda aka gaya masa halin da yaran suke ciki
wannan shine tashin hankali akan tashin tashin, haɗe kayan sa yayi ya kama hanyar gida, yana zuwa gida ya ga halin da yaran suke ciki duk sai yaji ya ƙara shiga ruɗani, ya rasa abinda yake masa daɗi, wai me yasa iyayen zainab har yanzu basu kira shi bane ko kuma ƙarya taje tayi masa, ya tambayi kansa
ɗaukar yaran yayi ya sasu a mota ya fita dasu ƙila in sun ga waje sayi shiru, ga haidar wannan abin ya ɗanyi yi masa aiki amma mohd ko a jikin sa yunwa kawai yaron yake ji don haka kuka kawai yake yi babu ƙaƙƙautawa
hankalin shi fa ya tashi sosai da sosai, asibiti ya nufa direct don kar yaron ya kamu da wani ciwon saboda kukan da yake yi, babu abinda aka ba mohd face da aka cewa aliyu yunwa kawai yake ji a bashi abinci, ya roƙi dr. cewar mmn shi ba lfy ta tafi jinya kuma ya ƙi cin abinci
sai da dr. ɗin ta gama yi masa faɗan ta sannan ta sa ya kawo mata abincin babyn ta haɗa masa da ɗan dumi ta bashi da yake yaron yaji yunwa sosai sai kawai ya karɓa ya fara sha, aliyu har wani ajiyar zuciya yayi da gode wa Allah daya ga mohd ɗin ya karɓa, sai daya sha ya ƙoshi dr. ta lallashe yayi bacci sannan ta ba aliyu shi tare da ce masa akai shi wajen mahaifiyar sa
shidai be tanka mata ba don shi a ganin shi babu abinda zai sa ya nemi zainab bayan ita bata ne me shi ba, kai inta neme shi ma sai ya wana ta sosai ya ja mata aji don tasan cewar shi ba kanwar lasa bane (``` ni dai mmn walid nace zamu ga me jan ajin kai da kake fama da ƴaƴa da ita da take ita kaɗai```)
be koma gida ba sai daya biya ta wani pediatric hospital ya sa suka yo masa hayar nanny wacce tasan kan yara sosai, sannan ya haɗa da ita da yaran ya kai gida shi a tunanin sa ya gama da wannan
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :40????
Bamu muka iso kano ba sai ƙarfe takwas na safe kasancewar sai yamma muka taso, ina sauka na kama hanyar jakara gidan su aliyu, ko da naje na ga sauka kyakkyawa kuma yanzu iyar ba laifi don gaskiya ina turo mata ɗan abin inna samu
Tea ta haɗa min da egg ɗina har da bread, sai da naci na ƙoshi har na manta rabon da inci abinci, sannan nai mata bayanin zuwa na, tai mamaki sosai sai tace min ina ƴaƴan na faɗa mata duk yadda mukai da shi,
Ita kanta sai da naga jikinta yayi sanyi ƙila ta tuno da rayuwar aliyun ne
“haƙuri zakiyi abuu ki koma ɗakin ki ki riƙe ƴaƴan ki”
“iya ƙyale shi jikan nan naki be san darajar ɗan adam ba ya ɗauka kuɗi sune komai, idan yaji a jikin sa ya fahinci daraja ta na koma, amma yanzu nan nika zama” na faɗa tare da gyara zama na
"to shi sanin fa kin yaye shi ne"
“ina fa ya kwace shi, amma ai ina matse nonon idan ya ciko don haka zan cigaba da matse wa kar yayi tsamin har Allah yasa ya dawo da shi”
“ohhh ni saude wannan hali naku na yaran zamani”
“iya wallahi ba laifina bane” Iya de bata yadda ba babu yadda bata yi da ni ba akna in koma naƙi, haka ta haƙura ta zubawa sarautar Allah ido don ba yadda zatayi dani
da daddre da ƴaƴan ta suka dawo sai ta gabatar musu dani amatsayin na zo zan ɗan zauna ne amma bata faɗa musu daliin zuwan nawa ba, nima kuma sai naji daɗin hakan
kashegai iya ta kaini na zazzaga cikin gidan daga waje gidan yake ƙarami amma idan ka shiga ashe da girma sa waje waje ne kamar gidan ƙauye sai dai kowa ya ɗan gyara nasa dai dai ƙarfin sa
daga can ƙarshen gidan ne wani part shi kuma amma ya rushe ina jin ko rashin samun gyara, har gurin rusashen ginin muka je
“kinga nan nan ne gadon mijin ki”
“iya da gaske na faɗa fuskata da fara’a”
“sosai ai marigayi sani yana da gadon baban su, don haka kinga ai doe a ba mijinki gadon uban sa kuwa ko”
tsayawa nayi ina kallon gurin a taƙaice zai iya yin ɗaki biyu da ɗan banɗaki da kitchen harda ɗan tsakar gida, sai na juyo ga iya
“za a samu masu gini a unguwar nan”
” me ze hana ai ɗana lawan ma magini ne me zakiyi”
“ginawa zanyi in zauna a cikin sa”
mamaki ne taf fuskar iya
“kinsan kuwa gini da cin kuɗi” ta faɗa
“ba komai ai nima na zo da su”
“shi ke nan zanyi wa lawan ɗin magana sai a fara”
“yauwa iya” na faɗa
ko da ɗan iyar ya dawo oyar ta faɗa masa ra'ayin zainab ɗin na son gina part ɗin ijina sai yaji daɗi ko ba komai ɗan ɗan uwan su zai dawo gare su, tayi masa baya non ɗakin biyu take so da ɗan banɗaki inda hali da kitchen da tsakar gida
dariya yayi yace "kina rena wurin nan idan nace miki zeyi ɗaki uku da banɗakin babba da tsakar gidan kuma fa, ai shi fili kina ganin shi haka idan an gina shi kuma abinda za afitar a ginin yana da yawa"
nai masa godiya tare da cewa yayi min ɗaki biyu kowanne da banɗakin sa da kitchen da tsakar gida
muka rabu da shi akan zai je ya ga nawa ginin zai ci kuma nawa zan fara bayar wadon a samu a fara a sa, nai masa godiya sosai, bayan kwana biyu kuwa sai gashi ya kawo min list,
aunty bilki na kwasa muka je banki nayi using atm card ɗin da aliyu ya bani tun ina gidan nayi withdrawing kuɗin da zasu ishe ni sannan daga nan nayo iya cefa ne, ko da na kawo masa kuɗin a ranar yasa yaran sa suka fara ƙarasa ruguza ragowar ginin da bai zube ba tare fara haƙa
**************
aliyu dai rayuwa ta juya masa abaibai, don kuwa yaran gabaɗaya basa jin daɗin canjin da suka samu, ya rasa abinda yake masa
mohd baya cikakken kwana biyu da lfy bini bini ya kama gudawa ko amai, kuma indai ya kama yin su baya denawa har sai in an sa masa ruwa don gudawar tsululu haka yake yin ta
shima kanshi haidar zazzaɓin dare yake ta fama da shi ga yawan kiran ```ammi naa```kullum dare haka ake fama da shi, anke asibitin amma ina har nanny ya sha canza musu ko nannies ɗin ne amma ina
shi kanshi ba daɗin yake ji ba yana fama da zuciyarsa wanda ayanzu takan tayar masa akai akai ya sha zuwa asibiti sai likita yace masa ya daina damun zuciyarsa da bakin ciki ya dinga barinta tana huta wa saboda he has a weak heart very weak one,zata iya bugawa at any moment idan ya cika damun ta kuma zai iya rasa rayuwar sa saboda hakan, tayaya zai iya wai controling ɗin ta bayan zainab ta tafi kuma wai ƴen gidan su sun ƙi neman sa don sulhu
abubuwa ne suka haɗu suka chakuɗe masa, rasa yadda zaiyi yayi ga yaran kusan kullum basu da lfy barina mohd har yanzu ya kasa sabawa da madarar da yake sha, ba irin madarar da ba ai masa trying ba amma duk a banza be dena gudawar nan ba duk ya lalace da shi
shi kanshi haidar kusan kullum da zazzaɓi yake kwana tare da kiran sunan zainab ɗin, wayar sa ya ɗauko ya kira tj yai masa bayanin duk halin da yake ciki, don bashi da wanda zai gaya wa da ya wuce shi
faɗa sosai tj ɗin yayi masa kamar wani ɗan yaro sannan yace zai zo abujar suje lagos don dawo da ita, ba abinda aliyu yake yi sai godiya sai kace qanda tj ɗin yayi masa kyauta
tj ma be ji daɗi ba ko kaɗan ɗauko wayar sa yayi ya kira zainab ɗin amma wayar ta a kashe take don haka sai ya ajiye, ya fara haɗa kayan sa domin zuwa abujan, aliyu yana da matsala menene na korar da mace har da kwace mata ƴaƴa, daga gani zanab ɗin ba ƙaramin haƙuri take yi da ɗan uwan nasa ba
sarai ya san halin aliyu ba haƙuri gare shi sosai, ko ma dai menene idan Allah ya kaimu muka je maa jo ko menene, su ma iyayen zainab ɗin basu hankali ba ya fɗa a ransa, ai da sai su kira shi suji me ya haɗa su ko basuyi don komai ba sayi hakan dan ƴaƴan zainab ɗin
kashegari da safe tj ya bi jirgin safe daga kano zuwa abuja daga nan suka bi private plane ɗin aliyu zuwa lagos ƙarfe 11:00 dai dai na safe sun sauka agarin lagos daga nan suka kama hanyar gidan su, fisabillahi aliyu farin ciki ne taf zuciyar sa ganin yau zai ganta amma a fiskar sa sai ya wani haɗe rai kar ace ya kasa
amma abin mamaki da takaici sai mutan gidan su zainab suka ce ai bata zo ba, aliyu yai musu bayanin cewar shi da kanshi yasa ta amota drivern sa ya kawo ta lagos amma inaa suka dage bata zo ba
a bayanin da yake musu ne mama ta gano ai ranar da zainab ɗin ta gano cewar ranar da zainab ɗin tazo suna shagamu, don hka sai ta kira me aikin ta tare da tambayar ta ko tayi bakuwa ranar da ta tafi shagamu,
me aikin ta tabbatar mata da ƙanwar ta tazo a kwatancen da me aikin tayi na baƙuwar anan suka gano cewar zainab ɗin ce, to amma ina ta tafi daga nan shine babu wanda ya sani, nan aka shiga neman ta amma inaa duk inda ake tunanin za ta je amma abin mamaki bata nan
ko da su aliyu suka ga babu wani nasara sai suka kama hanyar abuja tare da yaran don yace ba zai iya barin yaran nan lagos ɗin ba duk da dai mama ta o ya barsu, amma ƙiri ƙiri ya ƙi haka suka koma jiki duk babu ƙwari
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:41????
Zainab tana zaune duk abin duniya ya ishe ta bata taɓa ɗaukar cewar zata daɗe haka ba ba tare da ƴaƴan ta ba amma gashi yanzu kusan watan ta ɗaya har da sati, kullum ta tashi matse nonon ta takanyi kukan yaushe Allah zai haɗa ta da ɗan ta,
Ita shap tama manta cewar ita ce ta ɓoye kan ta duk laifin ɗorashi take yi akan aliyu, kuka ne ya kwace mata tana me tausaya wa kanta, Allah ya taimake ta ma iya bata nan ta tafi biki ita kaɗai ce aɗakin
ganin shirun yayi yawa yasa ta ɗauko wayar ta da tun ran da ta bar gidan aliyu ta kashe ta bata kuma kunna ba ta kunna don ta shiga watsapp ko zata ga abinda zai ɗebe mata kewa ta daina tunanin don kar ta haifar wa kanta wani ciwon
Saƙon ni ne sosai suka dinga shigo min waya kamar zasu tsaga wayar yawanci na grps ne sai kuma na ƴen uwa da suke ta tambayata ina na shiga, ashe aliyu ya je gidan mu ke tunda gashi ance mijina na nemana
banda lkcn sa na faɗa, saƙin mimma ne ya ɗauke min hankali sosai tambataya take ƙfy ta kuwa kwana biyu saƙon sun fi ɗari duk na tambayar ina na shiga ne
ɗaukar wayar nayi na danna number ta don inkira ta, don gaskiya ina neman wanda zanyi magana da shi in ji daɗi, ni ƴar adam ce don haka dole at stage ɗin da nake i really a shoulder to lean on an cried ma heart out,
kun san wani lkcn baka san mutum ba amma zaka ga u can talk to him musamman ma yanzu social media freinds some will love u honestly kuma zasu iya baka shawarar da zata fidda ka cikin tashin hankali don haka mimma na ɗauke ta kamar irin mutanen da ban sani ba amma zata iya bani shawarar da zata kwantar min da hankali
ringing biyu ta ɗauka tare da cewa
“ma za hadatha laki, ma hadatha li jawwala tiki, ai na dakalti,”
kuka kawai na sakar mata don gaskiya i really need to cry ina bala'in son yi kuka sannan in samu me rarrashina, bata hanani kukan ba sai da nayi me isa ta sannan na yi tare da cewa
“good day mimma”
“how dy, habibti”
“fine” Na ansa shiru ne ya biyo baya daga ni har ita
“habibti will u like to talk about wats rong wit u” ta tambaya
na shiga rattabo mata yadda mijina yake da matsala da da *dangin sa* da yadda matsala ta juye kaina, na faɗa mata komai bata katse ni ba har sai da taji na yi shiru alamar na gama sannan ta fara
Mimma ji tayi kamar zainab ɗin ta fama mata wani mugun ciwo da har yanzu yaƙi warkewa acikin rayuwarta, har gobe idan ta tuno da ɗanta daya rasu, sai tayi kuka duk rashin hankali da ƙuruciya da yasa ta tafiya ta bar ɗanta a hannu wanda bata sani har yayi sanadiyyar rashin ɗan, har gobe gani take yi da bata bar ɗan ta ba da ƙila yana nan yana rayuwar shi kamar kowa, hawaye ne taf idon ta zuciyarta tai mata ɗaci kamar zainab ɗin tana tariyo mata tarihinta ne da labarin da take bata sai da ta ɗan nutsa sannan ta fara magana don gaskiya bazata bari yarinyar nan ta tafka kuskuren da ita ta tafka ba wanda hanyanzu yake bibiyarta, ya ƙi kyale ta har gobe tana mafarkin ɗan ta
"habibti da farko dai baki kyauta, tayaya ɗan ki zai shiga tsakanin faɗan ki da mijinki" faɗa sosai mimma tayi min kamar ta ari baki tana yi kuma muryata na rawa kamar wacce zata yi kuka
mimma tayi faɗan ta dosai wanda ba abinda nake yi sai shesheƙar kuka inda itama kaga jin yadda take maganr kamar kuka take yi
“kuma abu na ƙarshe da zan faɗa miki shine ko ki koma gidan mijinki ko kuma ki sa aɗauko miki ƴaƴanki ki riƙe kayan ki, don banga zaman me kike yi ba babu ƴaƴan ki a kusa da kesalam” ta faɗa tare da kashe wayar
jikina ne duk yayi sanyi duk kalmar da mimma ta faɗa gaskiya ne uwa da tausayi aka santa, to yanzu ya zata yi, zata koma ne ko kuma zata sa aɗauko mata ƴaƴan ne
kai komawa gidan aliyu ba option bane bani da niyyar komawa zaman gidan sa har sai ya sauko daga fushin da yake yi da *dangin sa* sannan zan saurare shi ta faɗa a ranta
To yanzu wa zansa ya ɗaukƙ min ƴaƴan nawa, na tambayi kaina, su linda da rebecca ba zasu taɓa kwaso min ƴaƴan nan ba don kuwa tsoron aliyu suke ji, na fi son in samu wanda baya shakkar aliyu ko kaɗan
tj ne ya faɗo min a raina ina rawar hannu na ɗauko wayata na danna number sa lallai tj ne kawai zai iya taimaka min a wannan harkar don shine kawai baya tsoron aliyun kuma aliyun be isa yace zeyi masa barazanar sa ba na faɗa
tj yana zaune a falon gidan aliyu tun da suka dawo daga lagos ya kasa tfy don ya fahimci aliyun yana cikin tashin hankalin rashinganin zainab ya san daurewa kawai yake yi yana nuna bai damu ba, ko kuma yace don ƴaƴan sa amma daga ganin sa ba acikin kwanciyar hankali yake ba
Kusan kullum yaran basu da lfy barin ma haidar kusan kullum da zazzabi yake kwana mohd de nashi da ɗan sauki sosai tunda yanzu gudawar da sauƙi sai dai amai da yake akai akai wanda kuma ba laifi be wani ji jiki ba kasancewar yana shan ruwan gishiri da sugar, ya tausaya wa yaran sosai faɗan iyayen yaran ya shafe sun bashi tausayi sosai
wannan ne dalilin daya sa shi kasa komawa kanoya ɗan zauna ko dan yaran, wayar shi ta fara ringing, kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya kai hannu ya ɗauko ta
ganin harafin *yayata* akan screen ɗin ya sa sji daga wayar jikin shi na rawa
“ina kika shiga” shine kawai abinda tj ya iya faɗa
kuka na saka masa tare da yi masa bayanin halin da nake cikinsa na son ganin ƴaƴa na