
lallashina yayi tare da neman sanin inda nake, sai da na sashi yai min alƙawarin ba zai faɗawa aliyu ba kumabtare da min alƙawarin zai kawo min ƴaƴana sai na faɗa masa ina gidan iya
tj yayi mamaki sosai sannan yace mata yana abujan ya faɗa mata irin halin da yaran suke ciki ya kuma roƙe ta tadawo, kuka sosai na sakawa tj tare da roƙar sa ni dai kawai ya kawo min ƴaƴana, babu irin rarrashin da tk be yi min ba amma naƙi daga ƙarshe dole ya haƙura akan zai kawo su mukai sallama da niyyar zai taho kano yau da su
daɗi naji sosai tare da godewa Allah da kuma tj ɗin da zai kawo min ƴaƴana bayan na ɗauke tsammanin ganin su kusa
tj ya sa su hannatu haɗa masa kayan yaran sannan ya kama hanyar kano a jirgi shi kanshi hankalin sa zai fi kwanciya idan yaga ya sada ƴaƴan dabuwar su, don ta aliyu me saƙi ne duk lkcn daya sauko ya so su shirya ya kai kansa
magariba ce ta kawo tj kano, direct jakara ya wuce ya samu zainab ɗin tare da bata ƴaƴan ta, yai mamakin yadda yaga haidar ya wani kwanta a jikin na ni kuma ina shafa shi yadda nake idan zaibyi bacci kan ace meye wannan kuwa tuni bacci ya kwashe shi, shi kanshi mohd ɗin da yake ɗan ƙarami lub yayi ajikina kamar yasan abinda yake yi
na tausayawa ƴaƴa na daga gani ba ƙaramar rashi na sukai ba, tj faɗa ya dinga yi min akan in dinga haƙuri da ɗan uwan sa jin sa kawai nake yi amma aliyu yana buƙatar me koya masa hankali
yanzu hankali na akwance yake yake ganin gani ga ƴaƴa na babu abinda yake gabana yanzu daya wuce a ƙarasa min ginina in tare, kun san ance inda kuɗi kasha kallo to lallai tabbas na yarda da wannan kari maganar don kuwa mutanen nan ginin suke yi kamar ba mutum ne yake yi ba
ba abinda nake yi sai jiran a gama mu tare da bin dare ina gaya wa Allah buƙatata ta ya karkato da hankalin mijina gare ni tare da kawo ƙarshen wannan gabar da ya ke yi da *dangin sa*
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
*wannan abu na kishi da mata muka ɗauka muka ɗorawa kanmu don Allah don annabi mu rage, kishi halak ne amma kuma ba irin wannan kishin matan ƙwarai suka yi*
sannan na biyu masu yaɗawa kuma kuji tsoron Allah a kodayaushe an fi son mutum ya yaɗa alkhairi ba sharri ba, hadisi ne ingantacce ma’aiki (saw) yace “fal yakul khairan auli yas mut“` to kuwa in haka ne don me za a dinga yaɗa abin yake ba alkhairi, don Allah mu daina, don tun ana yaɗa gaskiya har a zo ana yaɗa abinda yake ƙarya, mutane sun manta shap cewar idan ka yaɗa abinda yake ba dai dai akan ɗan uwan ka musulmi ka ɗau haƙƙin sa
*don haka don Allah abar zancen nan ya wuce abar ita wacce tayi abin taji da abinda yake gaban ta ba mutane sun ƙara mata stress ba, Allah yasa mufi ƙarfin zuƙatan mu*
*wallahi abin nan ya kashe min jiki don haka yau typing ɗin sai kunyi haƙuri da abin da ya samu na shiga vibration, duniya tazo ƙarshe, Allah yasa mu wanye ƙalau*
page 42????
ko da aliyu ya dawo gida ya tamabayi yaran sai aka gaya masa tj ya ɗauke su, sai yaji sanyi aransa, amfanin ɗan uwa kenan in bashi ba wa zai masa haka, ko ba komai yaran zasu fi sakewa gidan shi don ita ma salmar uwa ce zata san abinda yaran suke so
Aliyu yana kwance tun da safe ya kasa yin komai, yau yaran sa kusan watan yaran sa ɗaya da tafiya amma tj be taba kiran sa ba wai ko don ya gaya masa ya suke, shi kuma hidima sun masa yawa
ya san yaran sunanan lfy tunda ance inka ji shiri to lfy ce amma ai ya kamata a ce tj ya kira shi ko so ɗaya, shi fa tj ba wani hankali gare shi sosai ba be san abinda ya dace ba da wanda bai dace ba,
ɗaukar wayar sa yayi ya kira tj ɗin don yaji ya yaran suke, ringing ɗaya tj ɗin ya ɗauka
“ɗan uwa ka manta ni” inji tj
“kai fa ba hankali gare ka ba ace mutum kwana nawa da ka kwashe min ƴaƴa amma baka taɓa kira ba” ya faɗa da ɗan faɗa
“ban gane ba, ai ni ƴaƴan ka basa hannu na” Ran aliyu ne ya ɓaci
“ban ga ne me kake nufi ba, na ɗauka tun randa ka tafi akace kai ka tafi da su yanzu kuma kace basa hannu na”
“yayata ce ya kira ni tana kuka wai don Allah in kawo mata ƴaƴan ta ni kuma gani yanda yaran suke ciki yasani kai mata su”
“kana nufin zainab ta kira ka ka kai mata ƴaƴan tashine ka kwashe min ƴaƴa ka kai mata ba tare da shawara ta, me ye haɗin ka da zainab ɗin ba ni bane ɗan uwanka ba amma sai ka koma ka bi bayanta bayan ta guje mu”
aliyu ya ci gaba da faɗan sa wai tj ya ci amanar sa ya kwashe masa ƴaƴa bayan yasan sune kaɗai makamin sa na sawa zainab ɗin ta dawo ko bata so, yai faɗa sosai kamar zai ari baki daga ƙarshe yace
“sai kaje ka dawo da ita kuma wallahi baka dawo da ita ba sai na saɓa maka ba kaɗan ba”.
tj dariya ce kawai take cin sa don daga dukkan alama ɗan uwan nasa ya fara missing zainab ɗin in shaa Allah burin su shi da zainab zai biya don zasu yi amfani da wannan damar na ganin sun shirya aliyu da *dangin sa*
zainab tana zaune a tsakar gidan iya ana ta hira da mutan gidan yanzu ko babu komai hankalinta ya ɗan kwanta don gata ga ƴaƴan ta kuma mutan gidan ba ƙaramin so suke nunawa yaran natan ba
kafin ta tashi tayi musu wani abin har an riga anyi musu don haka hutawar ta kawai takeyi sai kuma ginin ta da take jira a ƙarasa, tj garesu ya zama ɗan halak don duk abinda suke buƙata kafin ta fidda kuɗi ta siya ya fitar ya siyo musu don haka hankalin ta akeance shi kan shi aliyun tana ɗan jin labarinsa awajen linda kuma yana nan ƙalau don haka itama sai ta kwantar da hankalinta
pls kuyi haƙuri da wannan hankalina gabaɗaya yau ba ajikina yake ba
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
*na gode sosai da tambayar da kuka dinga yi min na ko lfy, wallahi lfy ƙalau jiki da jini ne kawai, da masu yi magana ta prvt da ta grps tanks sosai, ni nayi mamakin ma yadda aka san number ta????*
Page :43????
A yanzu an gama min gini na, shirin tashi kawai muke yi mu koma, in da ragowar kayan aikin na ce ayi wa iya gyaran ɓangaren ta, iya na bawa jari tana saro icce da gawayin coal, ana sama mata su a ɗakin soro
Ciniki take yi sosai babu kama hannun yaro, don duk mutan gidan nan da maƙota a wurin iya ake siyan icce da coal, sana'ar ta amshi iya sosai har tana kurin ita ba hayen sana'ar sai da icce tayi ba daga wajen mijinta ta gada, idan tana faɗin hakan takan bani dariya???? dama agado ne awajen miji
ko da na gama haɗa part ɗin nawa rana ɗaya na saka muka koma, ɗan tsakar gida ne, sai falo da kitchen a ciki sai ɗakuna biyu, kowanne da banɗakin sa
aunty bilki cevta rakani na sissiyo kayan da na saka na gyara part ɗin nawa sosai, ganin unguwar babu wuta ya sa na haɗa mana solar inverter, a gidan don mu rinƙa samun wuta tunda gaskiya ni bana son ƙaran inji, ban san solar haka take tsada ba gaskiya nayi barnar kuɗi sosai wajen haɗa solar amma kuma daga ƙarshe sao gashi ko ima a gidan sun samu wuta
duk zama na agidan babu wanda yasan cewar guduwa nayi sai iya kaɗai kuma ta kwaɓe kar in faɗa wa kowa sai muka barshi da cewar aliyun yayi tafiya ne, a haka nake zaune ba tare da kowa ya san dalilin zama na ba
ganin wuta available ya sani nima na fa siyar da kunun aya duk da dai ina da kuɗi sosai a account ɗina amma ina neman abinda zai ɗebe min kewa sosai wannan ne ya sani fara sana'ar sai da kunnun ayan
Hankalin aliyu yanzu a kwance yake ganin cewar ƴaƴan shi suna wajen zainab amma duk da haka yana son ganin su, don haka sai ya kira tj
“kai ɗan iska sai yaushe zaka kawo min iyalina ne, kana zaune lfy da iyalin ka ni kuma ka kwashe min nawa” shiru tj ɗin yayi don bashi da ansar da zaiba aliyun
” wai baka ji bane yaushe zaka dawo da ita”
“yayata fa tace sai dai ka tako da ƙafar ka kazo biko sannan zata saurare ka”
“bangane ba ba nace ta dawo ba”
“to ai in mace ta bar gidan mijinta dole sai mihin yaje biko, don haka sai ka shirya ka taho kano biko”
Allah tj ka mayar dani sa'an ka, in zaka kaɗo min ita ka kaɗo ta in kuma raina min hankali zaku tsaya kuna yi da kai da itan Allah ya baku sa a" ya faɗa yana kashe wayar sa
tj yana son raina masa wayo yasan zainab tana gidan sa shi yasa aliyun be damu ba don yasan ba inda zata je da ya wuce gidan tj ɗin, to amma yai mamaki da tj ɗin ya baro kano suka je lagos neman zainab ɗin kokuma sai daga baya ta koma gidan tj kai wannan munafuncin nasu ya fara isar sa
wayar sa ya kuma ɗauka ya tura wa da tj da saƙon cewar ya dawo masa da matar sa in ba haka ba sai yayi mugun ɓata masa rai ya tura masa tare komawa ya kwanta
ko da tj ɗin ya ga text ɗin be yi ƙasa a gwiwa ba sai ya kama hnayar jakara, yaje ya faɗa wa zainab ɗin mijinta fa ya dame shi da ya dawo da ita harda nuna mata saƙon da aliyun ya turo
“tj kace masa idan yana son ganina sai dai ya tako ya zo inda nake” tj ne ya ɗauki wayar ki kuma kiran aliyun
“ɗan uwa gani ga yayata tace sai dai kazo da kanka”
“ban gane ba nace mata ka dawo da ita shine zaka zo min da wani zancen banza, kawai ka ce mata ta dawo in ba haka ba zan kwashe ƴaƴa na”
tj ya faɗawa zainaba abinda aliyu yace, ita zainabɗin ta maida nata martanin
“kace masa yanzu ba da bane yanzu na waye” tj ya isar da saƙon zainab
haka suka dinga musayar magana da zance tun ana yin me ɗan dama dama har kowannen su zuciya tayi zafi shidai tj da yaga abin na neman zama faɗa sai ya cewa aliyu
“kasan number zainab ɗin”
“wannan wane irin zancen banza ne”
“to ka kira ta ku tattauna don na gaji naga alamar daga kai har ita ɗin babu me niyyar ɗaga wa ɗan uwan sa ƙafa ka kira ta sai ku shirya”
"zan maka rashin mutunci tj ba kai kazo ka ɗauke min ƴaƴa na ka kai mata ba, da ba ka kai mata ba zata dinga min abinda take min ne na faɗa maka ka kawo min matata, tun kafin mu raba hanya da kai don duk randa nazo da kaina kanon nan Allah sai ka gane baka da wayo"
“to ni ya zan yi ne tunda ban isa ince ta koma ba tunda tace sai kazo ba sai kazo ba kawai, ai ba a kanka aka fara zuwa biko ba ko”
“bikon yaci uwatar bazan zo ba kuma wallahi ka dawo min da ita”ya faɗa yana kashe wayar sa
tj yau yaga ikon Allah shi fa lkcn da akayi faɗan nan be sani ba amma yanzu ya zama shine ma me lefin, ɗaukar yaran yayi a hoto tare da turawa aliyu ta whatsapp, sannan ya shiga tausar zainab ɗin ko zata haƙura ta koma abujar
Zainab ƙiri ƙiri tace fafur ba zata koma ba sai dai aliyun ya tako ya zo da kansa sannan zata saurare shi ta faɗa kanta tsaye da tj yaga itama babu wani abinda zai mata da zai canza mata ra'ayin ta sai ya kama hanyar gida shi abun su ya fara isar sa kowa yana ji da girman kai kai Allah ya kyauta
ko da aliyu ya buɗe whatsapp yaga pics ɗin da tj ya turo masa ya ga yadda ƴaƴan sa suka koma gwanin ban sha'awa sai yaji duk hankalin sa ya tashi burin sa kawai ya ganshi da ƴen ƴaƴan sa ƙagu sosai ya ganshi cikin iyalin sa amma a gaskiya ba zai iya bin zainab ba ai ya yada girman sa na namiji wai biko to shi tarihi zai fara kafa sunan shi akan namijin da baya biko ya faɗa a ransa
wayar shi ya ɗauka tare da turawa tj da saƙon
“iyalina nace ka dawo min da su ba pic ɗin ƴaƴa na ba kuma idan baka dawo min da su ba zan ɓata maka rai”
ko da tj ya ga text ɗin sai ya turawa da zainab ita kuma zainab ɗin ta turawa da tj reply ɗin “bazan dawo ba sai dai ya tako ya zo inda nake da ƙafar sa”
ta turawa tj, tj yana ganin saƙo ya turawa aliyu, aliyu yana ganin reply ɗin yasan daga zainab ne sai ya rubuta sabon saƙo ya turawa tj ɗin
“sabida ke baki san darajar miji ba shine nace ki dawo zaki ce sai dai in tako koo” ya turawa tj, shi kuma tj ya turawa zainab ɗin
Ko da zainab taga text ɗin nan sai ta rubuta "ka manta lkcn da kore ni ina kuka ka rabani da ƴaƴa na, yanzu in kana son ganina sai dai ka tako da ƙafar ka" ta turawa tj shi kuma tj ya turawa aliyu
ko da aliyu yaga reply sai ya kuma turawa tj wani saƙon inda shima tj ɗin turawa zainab ita ma ta turo masa da reply ya isar da shi ga aliyu
haka suka dinga yi shidai tj ya zama shine middle man inna ya saƙon da be dace ba sai ya ɗan gyara ya tura wa wanda akayi saƙon domin sa, ya so su shirya amma ƙiri ƙiri sai kowannan su ya kuma fusa ta daya gaji da wannan baƙl ɗin da suke yi da shi sai ya turawa aliyu
“in kana son matar ka ta biyo ka, to ka neme ta a number ta na gaji” sannan ya turawa zainab da
“in kina son mijin ki ya biyo ki ki kirashi a number sa na gaji” yana gama wa ya kashe wayar sa gaba ɗaya don yau sun chaja masa ƙwaƙwalwa
aliyu ranshi ne ya ƙara baci yaji haushin yadda zainab tayi musu da shi, da ba haka take ba amma yanzu ta chanja sosai yana mamakon ko a ina ta samu wannan ƙwarin gwiwar yi masa musu da shi
tj ya ci gaba da turawa da aliyu da hoton ƴaƴan sa sai dai in baije inda zainab ɗin yake ba hakan ba ƙaramin farantawa aliyu rai yake yi ba, ta wani ɓangaren kuma yana jin haushin zainab da taƙi dawowa tace sai dai ya zo da kansa
rannan da tj ya turawa da aliyu pics ɗin sai yaga aliyun be buɗe last pic ɗin ba sai yayi mamaki don haka sai ya ɗauki waya ya kira ɗan uwan nasa amma wayar sa akashe take, ya haƙura, haka ya dinga trying kullum sai ace switched off yayi mamakin hakan aliyu baya taɓa kashe wayar sa don haka sai ya shirya ya kma hanyar abuja ko ya duba lafiyar ɗan uwan nasa
ko da yaje yayi mamakin da akce masa aliyun yana kwance a asibiti kusan sati kenan, asibitin ya wuce direct don ganin ɗan uwan nasa
me yasa ɗan uwan sa bashi da lfy amma ya ƙi faɗa masa ko kuma laifin zainab ɗin ne ya shafe shi, yana shiga ɗakin da aliyun yake kwance a zaune ya samu ɗan uwan nashi a zaune yana shan fruit,
ko da tj ɗin ya shiga da sallamar sa aliyun ansa shi kawai yayi tare da kau da kan sa don tj ɗin ba ƙaramin bashi haushi yake ba, ya ƙi dawo masa da matar sa
kusa da ɗan uwan nasa ya samu wuri ya zauna
“ɗan uwa ashe baka ji daɗi ba” be kula tj ɗin ba ya ci gaba da cin fruit ɗin nasa, ya rame sosai daga gani yana jin jiki
“ɗan uwa me nayi haka da zafi da kake jin haushina har baka da lafiya amma ka kasa faɗamin”ya kuma tambayar sa
“me kake so ince maka tunda kaƙi ka dawo min da iyalina gashi har ciwo ya kamani saboda rashin su”
“ɗan uwa tace bazata biyo ni bavya zan yi”
“ba sai ka kore ta daga gidan ka ba in taga bata da inda zata ai dole ta dawo gidan ta koo”
“ɗan uwa ai zainab bata gidana, haba da tana gidana da tuni na kaɗo maka ita”
juyowa aliyu yayi yana kallon tj
“ban gane bata gidan ka ba tana ina kake nufi” sai da tj ya ɗan ƙara gyara zaman sa sannan yace
“tana jakara gidan iya”
hankalin aliyu ne ya kuma tashi me zainab take nufi da zata tafi gidan mutanen da baya ƙaunar ko jin sunan su ta zauna ita da ƴaƴan sajuyowa yayi wajen tj yace
“tun yaushe take gidan ko kana nufin dama tun can tana can gidan shine baka faɗa min ba ka bar min ƴaƴa na gidan da nafi tsana a rayuwata” shidai tj shiru yayi kawai don daman yasan idan aliyu yasan cewar zainab tana jakara yasan sai anyi ɗan ƙaramin yaki da shi saukowa yayi daga kan gadon yana neman hanyar fita tj ne yayi magana “ɗan uwan ina zaka je ne”
“zan je in dawo da iyalina ne don bazan bar su su zauna awannan gidan ba” ya faɗa yana buɗe ƙofar ɗakin tare da bugo ta da ƙarfi tj ya bishi a baya yana kiran ɗan uwa ɗan uwa amma aliyu ko juyowa be yi ba babu yadda ya iya haka ya bi bayan sa shima gwan da ya bishi don daga dukkan alamar aliyun ranshi ya baci sosai da jin zainab ɗin tana jakara
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:44????
Duk irin kiran da tj yake yi wa aliyu be kula shi tafiyar shi kawai yakeyi yana hanyar fita daga asibitin, wata nurse ce ta zo da zunmar dakatar da aliyun amma irin kallon da yayi mata yasa ta kaucewa
“malam dr. be sallame ka ba” ta faɗa da ƙarfi
ko kula ta be yi ba sai nine na ƙarasa kusa da ita nace mata
“ki ce dr. ɗin patient ɗin sa ya sallami kansa ya tura bill ɗin office ɗin aliyun za ayi settling, gyaɗa kanta kawai take yi don tana mamakin wannan patient ɗin wai ya sallami kansa shida dr. ɗin yace case ɗin sa is serious it can even call for theater amma shine ya fice
Aliyu kasa jiran suje airport ma yayi yace wa tj kawai su tafi a mota, sai da suka biya ta gidan shi aliyun inda tj ɗin ya ɗan haɗa masa kaya, wand aliyun yai ta mita shi ba zama zaije yayi a kano ba ya na zuwa ya tattaro kan iyalin sa abuja zasu dawo
Suka kama hanyar kano wanda aliyun yake bayan motar sa crv, inda tj yake driving tare da rufe duk gilasen motar da sakin Ac dai dai yadda mutum ze sake, babu abin dabyake tashi face sautin ƙira'a na shaikh mahir al mu'aiqely aliyu yana son ƙira'ar bawan Allahn nan don haka sai yaji nutsuwa tana saukar masa ahankali duk wani baƙin ciki da yake ciki yaji yana yayewa a hankali tuni wani bacci me nauyk yayk awon gaba da shi
har suka iso garin kano karfe 11:15 na dare aliyu yana bacci ba magariba balle isha, tj directly gidan sa ya nufa da shi, don duk son dawo da iyalin sa be isa ya shiga gidan mutane da wannan daren ba,
ko dabya tsayar da motar yai mamakin da har a lkcn aliyun baccin sa yake yi hankalin sa akwance daga ganin ba ya samun bacci, tausayin ɗan uwan nasan ya kama shi sosai, ɗan tattaɓa shi sannan aliyun ya farka, ganin shi a gidan tj ya fara faɗa
“ce maka nayi ka kawo ni gidanɓka ka kaini can inda zainab ɗin take ayau zan kwaso su kuma mu koma abuja a yau ɗin”
“to duk dai abinka ka haƙura ka duba lkc ko inkaga ya dace ka ke gidan a wannan lkcn ga mukullin motar nan ni dai bazan kaika”
Tj ya faɗa masa tare da miƙa masa keys ɗin amma aliyun be karɓa ba sai ma duba agogon sa da yayi, yai mamakin ganin yadda lkc ya wuce haka, ko da yake da yamma suka baro abujar, fitowa yayi daga motar tare da bin bayan tj ɗin inda shikuma tj ɗin yayi masa jagora zuwa inda zai kwana
Wanka kawai ya shiga yayi yaji daɗin jikin sa sosaia kasancewar ya daɗe rabon sa da yayi wani baccin kirki, ko da ya idar da sllah a kan sallayar wani baccin ya kuma kwashe shi, in da tj ya kawo masa shayi don yasan atsarin aliyu baya cin abinci bayan 10:00, ko daya kawo masa sai ya tarar da ɗan uwan nasa ya bacci don haka sai ya ɗan ƙaro masa sanyin ac ɗin tare da lilliɓe shi ya ja masa ƙofa
kashegari da safe tun daya yai sallah asuba ya koma bashi ya tashi ba sai karfe 11:25 na safe gaskiya yayi bacci rabon shi da wannan baccin har ya manta duk sai yaji wani nauyi da yake ji a jikin sa ya ragu, wanka yayi inda yana fitowa ya tarar da tj ya shigo da break fast, be iya cin komai ba sai ɗan tea da slice bread guda ɗaya, sannan suka kama hanyar jakara da niyyar yana zuwa zai kwaso su su koma abj
a daidai inda ake parking a nan tj ya parker don mota bata shiga lungun su iyan da ƙafa suka ci gaba da tafiyar tasu, aliyu yai mamakin har yanzu unguwar ta nan yadda yasanta shekara 20 tun lkcn da ƴaƴan hjy sukai masa wulaƙancin nan, sai kuma in ya zo ganin hjyr sa aɓoye
yana ratsa cikin unguwar amma duk wasu memories na ƙuruciyarsa yana dawo masa kamar a lkcn abin ya faru, sai ya ji ya kuma tsanar unguwar da mutanrn cikin ta don babu wani memory na ƙuruciyar sa da yake tunawa ya ji daɗi duk na ɓacin rai, dake zuciyar sa kawai yake yi amma can ƙasan ran shi gabaɗayan sa aƙunci yake
suna karyo kwanar gidan iyar duk a tunanin shi zai ganshi a rakyakkyaɓe amma ga mamakin sa sai ya ga gidan ya fi kowane gida haskewa, tj kamar yasan tunanin da aliyu yake yi sai yace masa
“kaga gyaran da zainab tayi musu” harara kawai aliyu ya bishi da shi wato da kuɗin shi tazo tana yi musu burga ko to ko ma dai menene daga yau ya ƙare, ya faɗa a dai dai lkcn da suke zuwa ƙofar gidan