DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

Iya ce a tsaye a soron gidan wandabyanzu ya sha fenti suna ciniki da me man ƙuli haidar a goye a bayan ta, tun da aka kawo su kullum in dai ze yi bacci sai iya ta goya shi haka ta saba masa don haka ko bacci yaji sai kawai ya ɗauko zani ya taho wajen iya, ita kuma bata gajiya sai ta saɓa abinta abaya tai ta hidimar ta, 


Aliyu yai mamakin ganin haidar a bayn iyar ba haka yayi tunanin zai samu iyalin nasa ba, tj ne ya fara sallama, iya ta juyo zata ansa amma sai taci karo da fukar aliyu, mamaki ne cike taf a fuskar ta amma sai ta dake kasancewar ta kasa karanta halin da yake ciki 

“ahmadu kune tafe da ranar nan” iya ta tambaya
” mune iya mun biyo matar mu ne” tj ya faɗa da niyyar ya ƙona wa aliyu rai ai kuwa ya ci karo da wata muguwar harara

“ai kun kyauta” inji iya

Aliyu ne ya ƙarasa bayan iya don ya karɓi ɗan sa, amma abin mamaki sai haidar ɗin ya noƙe kafaɗarsa tare da ƙara shigewa cikin iyar, tj ne yace
“ai wannan in iya ta ɗauke shi babu wanda ya isa ya raba su sai don ganin kansa”

Janye hannun sa aliyu tare da ɗan basarwa,
“amadu ka raka shi mana wurin abun ko kuma tsaye anan ga zafi ga rana”
“to iya ai da wai mufara gaisawa da ke ko, ina wuni” inji tj
“lfy lau kun zo ƙalau” tj ya ansa Allah Allah yake aliyun ya gaida iyar amma sai yaji shiru, can kuma sai yaji aliyun yace
“ina yuni ya muka same ku” kamar baya so haka yayi gaisuwar

Iyar ta ansa da fara'ar ta tare da tambayar shi hanya, ya ansa ba yabo ba fallasa, sannan tj yayi masa jagoran cikin gidan 


 Tas tsakar gidan yake shima ya sha gyara da siminti wanda akayi masa gyara bayan an gama min, kowacce mace tana ɗakin ta kasancewar zafin da ake tafkawa ga babu wuta, sai solar da aka kunna inda kowacce ta gudu ɗaki ko tana kallo da iyalan ta tana shan fanka ko kuma dai sina shan fankar kaɗai 



Ko da su aliyu suka shigo gidan a share yake tas ba kowa don haka  directly bangaren zainab ɗin suka wuce wanda aliyun yai mamakin ganin ita ma wai bangaren ta daban



 Zainab tana zaune a falo ta gama girki kenan ta ci tana jiran kiran sallah tayi ta ɗan kwanta, gaskiya yau ana ƙwalla rana sosai


Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin naji wanda hakan ya dawo dani daga tunanin zafin da ake dokawa 

“waye”
“yayata nine”
“lallai tj yau an kawo mana ziyara ne gaskiya baka gajiya Allah ya saka da alkhairi, da ɗan uwan nan naka zai ga yadda kake kula da iyalinsa da ya wulaƙanta da ……………….”

Maƙwat na haɗiye ragowar maganar da zanyi ganin aliyu a bayan tj lkcn dana buɗe kofar, duk sai naji kunya, matsa musu nayi suka shigo, tj dariya ce take son suɓuce masa ina kallon shi yana toshe baki tare da kallon aliyu wanda shi kuma ya haɗe rai daga gani be ji daɗin maganganu ba 


 Suka shigo kowa ya nemi wuri ya zauna

“tj ina wuni ya salmar ta daɗe bata leƙo ni ba” na faɗa da ɗan borin kunya ta

"Tana nan tace ma in gaishe ki"

“ina wuni” na juya na gaida gogan wanda gabaɗayan hankalinsa yake kan mohd wanda yake dabo yanzu

Tashi yayi yaje ya ɗauko ɗan ɗan nasa tare da rungume shi daga gani yai missing ɗin shi sai ya bani tausayi, shin shina shi kawai yake da sunbatar sa duk sai na tsargu na raba wannan soyayya, tashi nayi tare da shiga kitchen na haɗo musu abinci 


Ko da na kawo sai da tj yayi wa aliyu magana sannan ya sauko ya fara ci don gabaɗaya hankalin sa yan kan mohd

Saukowa yayi ya zauna tare da taƙwashe ƙafar sa ya fara cin abinci tuwon shinkafa ne da miyar kuka wadda ta sha wake sai tantaƙwashi ga kuma man shanu wannan ne yasa aliyu babu abinda yake yi da ya wuce loma

Sai da suka ci suka ƙoshi sannan na kwashe kayan, aliyu ya so bayan sun gama cin abinci tj ya tafi, Amma tj sai ya gyara zama ya fara hira da zainab

Tun be lura ba har ya lura da kallon da aliyun yake masa kan ya fita don har nuni yake masa da kai inda yake nuna masa hanyar ƙofa amma sai tj ya yi kamar be san me aliyun yake nufi ba




Ai har yanzu ban gama wana ka ba, tj ya faɗa a ransa, sam ban san wainar da suke toyawa ba don hankalina gabaɗaya yana kan tv, na kan dai ji dariyar tj akai akai, ashe kunna mutumin yake yi 


Kiran sallahr azahar ce ta katse mana hirar tamu 

“sai ka tashi mu tafi masallaci” inji aliyu

Miƙewa sukai yi,
“yayata bari muje muyi sallah sai mu dawo don yau agidan nan zan ci na dare” tj ya faɗa a zolaye ban gane zolayar aliyu yake ba amma naga dai bayan ya gama maganar tasa ya sa dariya, ban kawo komai ba suka fice

Ko da suka fi sai da aliyu ya kai wa tj harbi da ƙafar sa,

“haba ɗan uwa me kuma nayi”
“dan uban ka baka ganin lkcn da nake maka signa ka tashi ka tafi, ka zo ka tsare mutane da surutun ka na banza, har da cewa wai anan zaka ci na daree wallahi muka idar da sallah baka kama gabanka ba sai nayi mugun saɓa maka” ya faɗa yana yin gaba, dariya ce sosai take cin tj amma sai ya dake tare da nuna shi be ma san me yayi

 Ko da suka idar da sallah sai suka shiga sabgogin su, basu koma gidan ba, sai bayan sallah isha sannan aliyu ya samu kansa don duk wata kadara tasa ta kano sai da tj ya nuna masa ita, kuma duk da haka basu gama, 

Karɓar motar yayi a hannun tj inda ya wurgar da tj ɗin a hanya wai ya nemi hanyar gidan sa don shi be iya cin ƙwan makauniya ba, yj sai ɗan adai dai ta sahu ya ɗauka ya kama hanyar gida tare da murnar shiryawar ɗan uwan sa da matar sa

 Har ya kama hanyar gida sai ya ga bazai shiga haka salin alin ba don haka sai ya karkata akalar motar yayi wajen yahuza suya, ya siyo musu tsire da kuma gasashshiyar kaza sai youghurt me sanyi, har ya kama hanya sai kuma ya dawo yace a sake masa irin haɗin da ya siya 





Sai ƙarfe tara na dare ya shiga gidan yana nan dai tsakar gidan shiru, ɗakinɓiya ya shiga direct inda yaci karo da ƴen uwan baban sa



Sun gaisa amutunce sannan ya zauna kowanne sai ya rasa abinda zai ce don ba sabawa suka yiba, da aliyun yaga shirun yayi yawa sai kawai ya ɗauko ledar yahuzar guda ɗaya ya miƙa wa iyar 

“ga wannan kici” ya faɗa atakaice
“an gode Allah yayi albarka, ya ƙara buɗi”

A ciki ciki ya ansa amin ɗin, ya miƙe yai musu sallama tare da fita daga ɗakin ya nufi ɓangaren  zainab ɗin

[7:46PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

 *wannan page na wata me ƙwadayi ne da tace zata ciii yahuza suya kin san kanki ko sai na kama suna* 

???????????????????????????? ba a samu yahuza ba amma ga wannan

F. B da ke nake ????????????

 Page :45????



   Tun bayan azahar nake sa ran dawowar su amma sai naji shiru, bayan la'asar na tashi na ɗarao na dare, ko dana gama na kintsa komai  Wanka nayi na shirya sosai, don nasan yau ba sauƙi iya ta kawo min haidar bayan yayi bacci na haɗa shi da mohd na kwantar da su, don bana son su ɓata mana hirar mu ta yau 

ba su suka dawo ba sai ƙarfe 9:10 na dare nayi mamakin dana aliyu shi ka ɗai, ko daya shigo sai nayi masa tayin abinci, sai yace sai ya fara wanka

     ruwan wankan na haɗa masa tare da gayyatar sa toilet ɗin, ya shiga ya watsa ya fito, sannan ya canza zuwa ɗan gajeran wando sai ƴar vest kasancewar zafin da ake yi, don ma da wuta



 gabatar masa da abinci nayi tare da tsarabar da ya kawo yaci ba yaba sai ya ce 

“naman ai na siyan baki ne kin ga ban isa in ci ba sai da yardar ki” kunya ce ta ɗan kama ni wai siyan baki

 tura masa plate ɗin nayi gaban sa 

“muci tare”
“ni na isa yanzu inna ci wayasan ina za akuma guduwa” Ya faɗa a zolaye ɗan murmushi nayi, duk na kasa sakewa sai kace ba aliyun da sani ba duk ya wani rikitani

 "ai nace kaci ko ba inda zan kuma tafiya"na faɗa kaina a ƙasa

“ban yadda sai dai a bani a baki” wata sabuwa inji ƴan caca

 rasa yadda zanyi na yi ƙatse min tunanin yayi

“to kinga alamar da naci da na ciwo wa kaina kenan tunda gashi kinƙi ki bani da kanki”

  gutsuro tsokar naman nayi na kai masa bakin sa, riƙe hannuna yayi wanda hakan ya sa na kalle shi cikin idon sa

“pls habibti kar ki ƙara guduna kinji, u r my everything u nd d kids r all i have”

  gyaɗa masa kaina kawai nayi hawaye taf idona 

“i really miss u dat it really aches here” ya faɗa yana kai hannuna me naman zuwa wajen zuciyar sa, sakin naman nayi don sai in ɓata masa rigar sa

   "pls stay by my side am not perfect buh i will try my possible best nd be a good husband to u" 

“i miss u too” na iya furtawa daga ƙarshe, kalmar ta dake shi sosai don ya nuna jin daɗin sa da na faɗa haka
“really den show me how much…………..”
Ban barshi ya ƙarasa ba na kai lips ɗin bakinsa inda na barshi ya ƙarasa ragowar aiki

Cak ya ɗauke ni sai bedroom, yahuza da bamu ci kenan, ni kuma mmn waleed da kwaɗayi sai na zauna cin kayana abinda da za suyi a ɗakin matsalar su ne ni dai inyi kwaɗayi na ko da yake bani kaɗai bace can na hango *FAIZA BABA* leƙowa ta taga wulla mata tsoka nayi na cafe da baki oohhh su fa'iza da kwaɗayi




    Mun sasanta sosai da ni da mijina inda duk wani bashi da ke kaina ban yi wani yunƙura kasa biya ba tas na biya sai dai sam barka, soyayya muka shiga  zubawa ni da ɗan mijina yanzu babu laifi yana kula *dangin nasa* sosai matsalata ɗaya itace shin mahaifiyar sa tana da rai ko kuma bata da rai 



 Ina son tambayr shi amma sai na ɗan ja ɗan lkc ganin bamu daɗe da shiryawa ba komai a hankali za ayi shi, aliyu be nemi in bishi abuja sai dai yakan je in ya samu lkc kuma ya zo, har da tsaraba yake zuwa da shi ai ta rabo a cikin gidan 



 Yaran gidan har sun san bbn haidar don in aka ce yana kano, to haka zaka ga gidan cike da kayan ciye ciye ina jin daɗin yadda yake kula da *dangin sa* duk da dai daga gani har yanzu be gama sakin jikin sa da su ba, don baya zama yayi hira da su



Daya dawo ya shiga ɗakin iya suka ɗan gaisa idan ya fito ya dawo part ɗin na baya kuma fita sai masllaci ko kuma in tj ya zo zasu fita shine yake fita, duk ƴen samarin gidan da basu da sana'a ya kwashe su ya basu abin yi, wannan ne yasa mijina ya zama zakaran gwajin dafi,



        Yau na tashi gabaɗaya ba na jin daɗi jikina, sai na ɗauka ko yau da gobe ne kun san ance tafi ƙarfin wasa, amma ga mamakina tafi tafi sai abin ya zame min jiki bana jin da daɗin komai sai kwakwa ga miyau da yake yawan tarar min wannan ne ya tabbatar min na kuma samun passenger a tare da ni 

Shiru nayi ban faɗawa aliyu ba ko da yazo yai ta dai mitar nayi kyau nayi ƙiba nayi freash ni daɗi na nake ji a kano shi kuma yana abj yana cin kwakwa(wahala)

 Duk da nasan ba wani kwakwa da yake ci kawai dai mita ce irin ta ɗan adam yai mamakin ganin yadda nake cin kwakwa ta, sai yace 

“ashe bani nake cin kwakwa ba ke kike cinta”

Ko kaɗan ban so y fahici ina ɗauke da ciki don haka sai na bishi da cewar lkcn ta ne shiyasa nake sha'awar ta, ganin yadda nake cin kwakwar nan ba dare ba rana ga miyau ya sa shi ɗauka ta ya kaini asibiti wai ko banda lfy ne, har da cewa

“dauɗar ciki yake damun ki, ke da kika taso cikin yarbawa ya kamata ki din ga shan magani jedi jedi don shan zaƙin ki yayi yawa”

Har muka je asibiti yana lissafo min magungunan dauɗar ciki daya sani, ni dariya kawai yake bani yadda ya daddage da dauɗar cikin nan ko ya zai yi idan yaji dauɗar cikin nawa babyn sa ne 



  har cikin consultation room ɗin muka shiga tare, dr. ya rubuta sunana da shekaruna sannan ya ɗago ya kalle ni

“hjy me yake damunki” kallon aliyu nayi don ni ba bu abinda yake damu kawai tattago ni yayi ya kawo ni asibiti
“ni dr. babu abinda yake damuna kaga wanda ya kawo ni nan”

Dr.  ɗin ya kalle ni da mamaki sannan ya kalli aliyu, sai aliyun yace 

“dr. Ƙyale ta dauɗar ciki take fama da shi tai ta tara miyau ga kuma cin kwakwa ba adadi, ni ina tsoron kar tuƙar kwakwarbtai mata illa ne”

 Murmushi dr. yayi tare da tambayata last dana ga period ɗin, wannan ya nuna min dr.  ɗin ma ya harbo jirgin nawa



Na faɗa masa ya fara ƴen rubuce rubuce sa sannan ya bamu test da scanning, muka je nayi a wajen scanning ɗin ne nace wa aliyu ya biyo ni muje scanning room ɗin 



 Macece tayi mana scanning ɗin don haka a sake nake ko da ta zo daidai wajen da babyn yake wanda be fi sati 12 ba sai tayi pause din monitor ɗin tare da nuna shi 

“alh ga babyn naka” ta faɗa wa aliyu

Shi aliyun da ke gefe har yanzu be san me ake ciki wai shi duk a tunanin sa abinda yake sani zubda miyan ake nema 

“baby faa kika ce” ya faɗa da mamaki
“yes kusan 12weeks babyn yake” ta kuma faɗa

Ƙara matsowa yayi kusa da monitor ne amma ba'a iya gani komai sai wani hatsa hatsa don haka sai dabya kai fuskar sa har gaban monitor sannan yace 

“ni fa babu abinda nake gani sai wani hatsa hatsa” ya faɗa kuma kalƙon monitor

"alh ai ba a gani sosai kaga har yanzu babyn ba wani fara halittasar akayi ba"

“ok kin dai tabbatar da ba dauɗar ciki bace baby ne” murmushi tayi tare da gyaɗa kai

 Ya juyo ya kalle ni h

“habibti kinga ashe ba dauɗar ciki yake damun ki ba baby na ne”, shafa min ciki yayi tare da kissing lips ɗina tare da ce mi “thank u 4 everything”

 Har muka koma gida yana cewa 

“dama nace ba lallai bane dauɗar ciki bane amma ban taɓa kawo cewa ciki gare ki ba” kallon shi kawai nayi kamar ba shi kaɗai yai ta mitar dauɗar ciki gare ni amma wai yanzu kuma ya canza zancen

A hanyar gida ya tsaya ya siya min kwakwa ta wannan karon harvda dabino ɗan agadas don kwakwa da dabino ba dai daɗi ba ga daɗi a baki ga aiki a jiki ????



  Mun koma normal life ɗin mu amma yanzu gabaɗaya zaman garin kanobya fita raina don haka ko wannan zuwan da aliyu yayi sai na tuntuɓi ko yana sha'awar mai da mu abuja


Rungume ni yayi sosai wanda har sai da naji ɗan zafi a rungumar tasa daga gani in ya tafi yana kewar mu ba kaɗan ba 



Ana gobe zamu tafi muna zaune a falo duk na gama haɗa duk wani kayana yara ma sun yi bacci muna ɗan kallo aliyu yana zaune ni kuma ina kwance akan cinyar sa sai nace

“habibi ina da wata alfarma ɗaya”
“anything 4 u habibti”

 Kamar bazan yi magana ba sai kuma na buɗe baki na 

” ina mahaifiyar ka” shiru yayi kamar yana nazari
“wallahi ban san inda take ba”
” baka ganin ya kamata mu neme ta”
“kina son ganin ta ne” gyaɗa masa kai nayi
“in shaa Alƙah zan nemo ta ko don ke, amma ganin ta zai yi wuya tunda bansan komai nata ba sai sunan”

“ba komai in shaa Allah zan taya ka”
“no sweetheart just concentrate on dis” ya faɗa yana dafa min ciki na

“Ok buh promise me to look 4 her soon”
“in shaa Allah habibti”

Muka ci gaba da hirar mu har lkcn bacci muka koma ɗaki muka kwanta sai da safe
[7:46PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

Page:46????


 Kashegari da wuri muka fara shirye shiryen tfy ƙarfe 8:00am muna airport, domin hawa jirgen da zai kai mu birnin tarayya abuja, aliyu ne ɗauke da mohd inda ni kuma na riƙe hannun haidar, tj ne ya rako mu airport, sai tsokanar aliyu yake yi 

“ɗan uwa nan gaba in aka kuma daka maka yajin nan gidana zan kawo yayata in ɓoye ta” shiru mayi banɓtanka musu ba don maganar ba tawa bace

Shima aliyu be tanka masa sai ma cigaba da yayi da anfani da wayar sa wacce take hannun sa tun da muka shiga motar ko me yake yi da ita oho

 mun hau jirgi lfy mun kuma sauka birnin tarayya ƙalau muka kama hanyar gida, Alhamdulillahi na je na samu gida kamar yadda na barshi tsab da shi,  sai ma ƙarin gyara daya samu 


Hankali na a kwance na ci gaba da tafiyar da hidimar gidana ba tare da wani matsala ba muna waya da su iya sosai ina jin halin da suke 


idan akwai wani taimako ko wani sabga ta tashi suna faɗa min zan faɗawa aliyu shi kuma sai ya aika musu da abinda ya samu

gaskiya aliyu ya canza ba laifi don ya fi da, matsalata ɗaya dashi yanzu na rashin ƙara yi magana akan neman mahaifiyar sa

ko da irin nayi masa magana akai sai yace shi ya ki kyautata zaton ta mutu, amma ina ƙara ƙarfafa masa gwiwar akan ya neme ta 



 rannan muna zaune aka kira shi a waya cewar an samu me irin sunan mmn nashi, sai yasa aƙara bincike sosai akanta 

amma abin mamaki sai aka gano ba ita bace, na ɗauka zanga hankalin shi ya tashi ko be ji daɗin abin sai na gan shi je ia very calm kamar ba abinda ya faru wannan abun ya bani mamaki don haka sai na tunkare shi in dalilin shi na nuna ko in kula
“habibi kamar bakayi baƙin ciki daya kasance ba ita ce mmn ka ba ko” murmushi yayai ya juyo ya kalle ni
“na rantse miki da Allah ko kaɗan bana son haɗuwa da ita”
“me yasa”
“saboda ita ma ɓa ƙauna take yi ba”
“ya akayi kasan hakan”

juyowa yayi sosai ya kalle tare da riƙe min hannuna 

“habibti matar da ta yarda ni ta gudu ranar da ta haife ni kina ganin zata kuma biɗa ta, kin san me yasa ta yadda ni”

girgiza kaina nayi don ni a labarin daya bani kamar ƙuruciyace take ɗawainiya da ita a lkcn

“ta yarda ni ne don ta manta da ni da kuma mahaifina, inda ta yarda ni ko don wani abun ba wannan ba ya kamata ko so ɗaya ne ta neme ni amma ko da wasa bata taɓa tunanin in ɗan jaririn dana ajiye ba” maganar shi akwai ƙamshin gaskia

Fisabilillahi abinda mijina ya faɗa gaskiya ne amma tunda sulhu nake neman yi da shi da mahaifiyar sa sai na kaɗe baki nace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Leave a Reply

Back to top button