DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

 By mmn walid nd walida (mrs aliyu)


  ???? *NASIBI WRITERS ASSOCIATION*???? we shine with the smile ☺ ????????☺ of our readers, so keep smiling while we keep shining ND entertaining u with amazing story love y'all mua Mua ????????????????




 Page :6????




  can daga nesa daga wurin partyn na samu wuri a yashi na zaina ina kallon yadda ruwa yake yo anbaliya ya na koma wa tekun ba tare da wani wani matsala ba ko wani takura khalil na zaunar akusa da ni don in samu inyi tunanin rayuwata sosai, dama nima zan zama kamar ruwan nan in ta sha'anina batare da damuwa ba ohhh Alƙah ka kawo min ba don halina ba na ɗaga kai sama ina roƙon Allah a ziciyata 




   kamar an jeho mutum haka naji an zauna kusa da ni haki, a ɗan tsorace na juyo inda mukai huɗu da wani balarabe, balarabe ne sosai ba wai kamar labarawa yake ba kana ganin shi kaga jinin larabawa a tattare da shi, ƙura mai ido nayi ina ƙarewa ƴar kyakkyawa fuskar shi kallo wanda kallo ɗaya zaka gane tsabar kyan da yake ɗauke a fuskar tasan 



  "Baby kallon ya isa haka, zan ɗan dade a kusa da ke" ƙara sakin bakin nayi ga hausa kuma raɗau abakin ɗan balaraben mintsinin kaina nayi kodai mafarkin nayi yana magana,ƙara katsemin tunanina yayi da cewar "baby am talking to u" baby kuma sai a lkcn na dawo hayyacin na inda na zunburar masa baki nace "baby kuma, wace babyn ka, ko ka zo da babyn kane ka ɗauka nice"



 Murmushi yayi wanda ya ƙara fidda masa da tsantsar kyan sa, "am talking to u" ya ƙara faɗa juyawa nayi ko zanga wata a kusa dani ganin babu kowa yasa na tabbatar dani yake 

“excuse mr man am not ur baby……….. Bai barni na ƙarasa zancen nawa zancen nawa ba ya ɗora da cewar “wasu ƴammata tun ɗazu suke ta bina shine ni kuma nace musu da matata nake suka ƙi yadda shine kawai ganin ki a zaune ke kaɗai ya sani garzayowa don in ɗan lape kafin su gaji su tafi,”

Harara na banka masa ina ƙoƙarin miƙewa ya ma rainani, “noo babay karki ƙoƙarin tashi ya kamata ki juya ki kalli yadda suke binki da kallo” ni har yanzu ina mamaki hausar da take fita daga bakins, zama nayi sannan na kalle shi “a ina suke”
“kalli hannun daman ki zaki gansu su huɗu”

juyawa nayi a wayance wasu ɗima ɗima matan lagos na gani kowacce sai zare min ido take kamar zasu cinye ni, bansan lkcn da juyo na daina kallon su ba, dariya naji yana min “kinga in kika tashi Allah ya haɗa ki da waɗancan ko ƙashin ki baza a gani ba”harara na banka masa tare da murguɗa masa baki

 "baby ba a harara ta don dai ni nakawo kaina amma ni mutum ne da bana ɗaukar raini" wata hararar na kuma doka masa na juyar da kaina 



   wayar sa ya ɗauko yana ta ƴen wayoyin sa inda khalil da ke tsakiyar mu ya fara yi masa gwarancin sa ni shap ma na manta da yaron kawai sai ji nayi ya ɗauke shi yana mai wasa ban kula su don san duk abinsa ina zaune de baze  sace yaron ba 





 wayar sa ce ta fara ringing ya ajiye khalil sannan ya ɗau wayar 

“ɗan uwan ya kwana biyu ya garin da jikin hjy kuwa” shiru yayi daga dukkan alamu ɗan uwan nasa yana ansa tambayoyin da yayi masa ne, sun ɗan taɓa jira irin tasu wadda su suka san ko akan menene sannan naji yana cewa “haka tace hjyr, to kace ta kwanta da hankalin ta Allah ya amshi addu’ar ta don gani ma yanzu ga yayar taka”

jin haka yasani tunani waye daga cikin ƙannena,

” a a ai ka bari kawai sai kazo lagos ɗin sai ku gaisa” aka kuma magana daga can ɓagaren
“a haba wannan karon ba ƙarya nake yi ba ɗan uwa, gata akusa da ni” muhawarace kamar yadda na fahimta ta kaure tsakaninsa da ɗan uwan nasa akan sai yayi magana da wadda yace yayarsa ce daga ƙarshe dai aka kada ɗan balarabe, juyo wa yayi ya kalle ni inda ni kuma na haɗe rai

“baby don Allah ga ɗan uwana zaku gaisa”
“a wane dalilin na faɗa ba tare da na kalle shi”
“a dalilin in baki karɓi wayar ba zan tashi in barki da zakunan cen da suke ta kallon ki da tsana har yanzu” ya faɗa yana kare zancen nasa da dariyar mugunta

fusge wayar nayi daga hannun sa na kara akunne na tare da sallama

” wa’alaikis salam yayata ya garin lagos ɗin, ya mutanen gidan” lfy na ansa atakaice

    "yayata kece ta farko da ɗan uwa ya fara gabatar mana amatsayin wacce yake so dan Allah ki riƙe mana shi amana, har Allah ya kaimu lkcn da zaki zama tashi kinji" tooo kawai na iya cewa 





hira sosai ya dinga min akan mahimman cin ɗan uwan nasa wanda ni kuma wasu in gane wasu in bishi da too kawai, 

“ya sunan yayata tawa ne” ya jeho min tambaya kallon inda balarabe yake nayi inda hankalinsa yake kan khalil suna wasa kamar baya sauraren mu
“ka tambayi ɗan uwaan naka mana sai ya faɗa maka”
“to shikenan ga hjyr mu kinga yanzu ta tashi daga bacci bazan bari wannan ɗaɗɗadan zancen ya huce ba ungo ku gaisa”

sai da ɗan ji ɗan jim sannan naji sallama cikin wata kamilalliyar murya, na ansa sannan na gaishe ta addua tai ta doka min akan in kular mata da ɗanta amana, wayyo Allah ni ban san mutum ba amma ƴen uwansa suna ta bani amanarsa to kawai nake binta da shi da kuma in shaa Allah ɗuk ilahirin jikina yai sanyi







"ya sunan ƴar tawa naji tace, bazan iya yi mata musu ba yasa ni nace zainab, Maa shaa Allah babban suna Allah yayi wa tarayyarku albarka ya baku zuri'a ɗayyiba amin nace yo dan Allah me zance 

“ina ɗan nawa” ta tamabaya miƙa masa wayar naiy ya karɓa jin wacce ke maganar ne yaga ya ɗan nutsu sai wani shagwaɓa yake kamar wani yaro har da wani cewa baya iya bacci saboda basa kusa da shi

ya ƙaraci dai shagwabaraa sannan ya miƙo min hjy tace zakuyi sallama, karɓar wayar nayi sal da ta ɗan ƙara yi min nasiha mai shiga jiki sannan mukai sallama bashi wayar suka ƙarasa sallamar sannan ya ajiye

shiru ne ya biyo bayan haka ba wanda ya kuma tanka wani daga cikin mu ni ina tunani n hrar mu da baiwar Allah nan shi kuma yana danne danne a wayar sa

hayaniya na jiyo a bayan mu kamar ana kokawa wanne ne yasa muka juya atare da shi don ganin ko me ke faru, hasken camera camera ne kawai yake ana walƙiya afuskokin mu kasancewar duhu ya farayi shit kawai nahj yace ya sunkuci khalil ya riƙe mun ya fara jana muka fara gudu inda masu cemerar suke binnu suna.ci gaba da ɗaukar hoton su

kasancewar yashine a ƙasa don haka bashi da daɗin yi gudun a kai wannan ya bawa masu ɗaukar hoton daman samun hotunana namu sosai duk da naga akwai masu karesu da hana su ƙarasowa wajen mu, haniniyar doki kawai naji a bayan mu wanda wannan ne ya bamu damar tsayawa ya wuce sai naga nakan dokin ya sauko ya miƙawa balarabe linzamin ya kama ya hau hannu ya miƙo min na noke

“ya zakiyi da waɗannan vultures ɗin da suke binki” juyowa nayi na ci karo da mutane sunfi biƙa adadin da suke bin mu a guje da camera sasu kuma da abin magana a hannu dats mic daga gani ƴen jarida ne bansan lckn da na miƙa masa hannun ba yai sana dani sai kan doki ya karɓi khalil daga hannu mutumin nan, ya zaburi dokin tuni mukai gaba ba abinda kake gani sai haken camerar tana ɗaukar hotuna too shi wannan ɗin waye shi haka da ƴen jarida suke ta binshi ????????????
[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

    By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 


????nasibi writers association???? 


Page :7???? 


  Wani keɓantaccen waje muka nufi inda muka shiga ni dai har yanzu jikina bai daina rawa ba 

“ke da kuka zo, don in san inda suke in kaiki”
“da ƙanwata da mijinta”
“kawo wayar ki sai in kira su” ɗauko wayata nayi wadda ta sha jiki, kallon wayar yayi sannan naga yana ƙoƙarin buɗe ta ciro sim ɗin yayi sannan yai wurgi da wayar tasa wayar ya cire sin ɗin ya samun nawa,

"wane suna zan kira" ya tambaya bayan ya gama daidaita wayar 

“maryam” na amsa atakaice, sanin cewar ba kuɗi awayar ne ya sani kau da kai aikuwa yana dannawa yaji ba kuɗi sai ya ja tsaki

“jira ni anan bari in siyo credit naga wayar taki ba ko asi”

Ficewa yayi na bi bayan shi da kallo a tsaye yake me ƙirar ƙarfi irin waɗanda ake cewa giant ga tsayi ga faɗi oohh wannan matar shi zata more irin waɗanda idan sun rungume mace ne zata ji kamar babu wata damuwa a rayuwa lif zata lafe a faffaɗan ƙirjinsa 




 Bai daɗe ba sai gashi kiran maryam yayi tayi mai kwatance sannan ya ɗauki khalil muka ƙarasa har wajen motar mu ya raka ni 



ko bayan da muka shiga wayar tashin ya miƙo min tare da cewa "sai munyi waya" juyawa yayi ya ɓace cikin duhin daren nan kamar walƙiya ajiyar zuciya na saki wanda sai alkcn na fahimci ashe duk waɗan da ke motar hankalin su na kaina zunɓurar baki nayi na ce "menene"



 "a ina kika samu wannan yaya" inji maryam ba irin tambayar da basu yi min ni dai bance musu komai hankalin khadija ne yaje kan wayar sa da ya bani 

“wannan kamar iphone 7 latest version ko” gefe sadiq ya faka da motar ya karɓa

“ai kuwa ita ce, a ina kika san shi” oho kawai na iya faɗa

“kinsan nawa wayar nan kuwa yaya tana fa kaiwa dubu 350” zare ido na nayi ina kallon wayar da zata kai wannan kuɗin wai a hannuna dariya na ɗan yi ku china ce

    dariya suka dinga min wai basu taɓa jin iphone china ba sai a wajena ni dai har ni dai ban kula su har gida su kaini na ɗauki saƙon mama na kayan snacks nai ciki 



ko dana koma baban mu bai dawo ba don haka kawai sai na ba mama bata tambayeni ina na samo ba nima ban damu ba sallolina nayi na kwanta amma kuma sai na kasa bacci tunanin ɗan takari ne ya faɗo min to ɗan takari mana muma ƴen uwan mu idan suka je garinsu takari ake ce musu to muma ba dole muce musu takari ba ( har na tuno littafin makawa, ki ci gaba da gashi lbrn nan yana ƙawata mu) 



 da asuba na tashi da wuri sakaka haka na wuni ba abinda yake min daɗi ko abinci kasa ci nayi abi kaɗan kuma sai induba wayata ko zanga ankirani shiru kakeji 



  da daddare bayan sallahar isha mun zauna muna kallo har da su baba sai ga breaking news an rubuta da manyan harufa *ajaban caught off guard with wife nd son* sai ga hoton mu da ɗan takari danɓarere akan akwatin tv 




baba ne ya fara magana "wannan kamar zainab ko dai ido nane" shiru nayi 

“itace mana baha khalil nan ba ɗan wajen khadija”

ni dai bance komai ba sai ga news an ci gaba “a jiyane muka samu daman samun hoton matashin yaron nan me multi billion dollars shipping, company da yayi ƙaurin suna suna a dunuya wato mr ajaban da kuma me ɗakinsa tare da ɗan ƙaramin ɗan su wanda suka je shaƙatawa a beach, rahotanni sun nuna cewar mr ajaban ya daɗe da aure inda ya ɓoye wa ƴen jarida da duniya kasancewar baya san iyalinsa su shiga cikin hayaniya, sao jiya Allah yasa muka samu daman ɗauko hotonsa sai asha kallo lfy”

kamar afilm haka naga abin namu da yadda muke gudu ƴen jarida suna bin mu abin gwanin sha’awa Allah nidai kam ya birge ko don ban saba ba be ohho

saukar mari ne ya dawo dani hayyacina ashe baba yana ta magana banji ba babu yadda ybaiyi ba in faɗa masa ko waye nayi shiru ba urin zagin da ban sha har cewa yayi in ban fidda miji ba cikin satin nan gezawa zai kaini ya bada ni sadaka

 Ya gama bam bamin sa ya shige ɗaki ita ma mamahaka kwanciya nayi ina tunanin to wannan wanene shi wane irin suna ne *ajaban* a haka bacci yai awon gaba da ni 



    kashe gari da sassafe bayan na idar da sallah ina zaune sai naji wayata tana ringing kamar kar inɗau amma sai na daddage na ɗauka a lkcn ta kusa tsinkewa sallamar sa naji wanda ko bacci nakeyi naji muryarsa zan gane na amsa ga drivwr kiyi masa kwatancen gidan ku too kawai nace 

drivern ya karɓa nayi masa kwatance sosai yace ya gane sannan ya kashe wayar murna naji ko ba komai zai zo zance, ko yaushe zaizo na tambayi kaina ima murmushi

  komawa nayi na kwanta ina tunanin ɗan takari na wani daddaɗan bacci me ya fafa kwasata, kamar a mafarki naji ana buga mana ƙofa kamar za a karya a firgice na tashi wanda yai dai dai da fitowar bbn mu daga ɗakin yana mitar waye 

buɗe ƙofar yayi yaci karo da wasu ƙarti su biyu cikin baƙaƙen kayan su da baƙin glass
“sainob in ko” wato ina da zainab
Hannu baba yana rawa ya nuna ni da yatsa

 kirawo ƴen uwan su suka yi akan gani nan wasu mata ne suma cikin irin shigar mazan suka shigo suka kama ni suka fara ja zasu fita da ni bbnmu na ruƙo ina kuka, doke min hannu yayi nina aike ki ya faɗa muryar sa tana rawa daga gani atsorace yace 

a haka suka jani har waje duk ƴen gidan mu sun fito ganin wannan ikion Allah nikuma sai kuka nake yi ina ihu na a taimake ni amma ba wanda ya kawo min a gaji

a tsakiyar layin mu sukayi parking motocin su waɗanda suka kai kusan guda goma duka baƙaƙe sai ƙyalli suke yi a ta tsakiya suka saka ni suka rufe nayi nayi in buɗe ƙofar amma na kasa sai kawai na saki wani sabon kukan
[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

By mmn walid nd walida mrs aliyu

????nasibi writers asso????

Page:8????

   Kuka nakeyi ina yin gunji sannan muna tafiya a hankali, tsaki naji an ja min wanda yai min nuni da cewar ba ni kaɗai bace a motar ba waigowa nayi don inga ko waye hmmm "ɗan takari" na faɗa da karfi da kuma mamaki 

“ɗan takari kuma kinga nayi miki kama da takari ne”
“oho maka naga in ƴen nan sunje garin ku takari ake ce musu to muma in kun zo garin mu ba dole muce muku takari ba”

Useless kawai najo yace ya juya ya ci gaba da danna laptop ɗinsa

“me yasa ka sato ni” na tambaya be kalle ni yaci gaba da abinda yake yi ba irin tambayar da ban masa amma ko ƙala baice min ba har muka isa inda zamu,

Parking na ga anyi
“ki fito”
“walƙahi ba inda zan je sai ka gaya min me nayi ma ka sato ni” be kula ni can sai naga waɗannan ƙattin matan nan sun zo sun kuma kamoni ina ihuna ina komai naga mu nufi wani jirgi da yake gaban mu

Nutsuwa nayi donni in akwai abinda da tsana yabi bayan jirgi tun wani haɗarin jirgi da na gani nake tsoronsa 

Juyowa nayi na kalli ɗaya daga cikin matan nan mausu jana na fara mata yarbanci akan don Allah kar ta sani cikin jirgin nan mutuwa zanyi, kamar ba da mutum nake

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Leave a Reply

Back to top button