
“Akodayaushe ka kasance me yiwa ɗan adam uzuri, ina lefin mu neme ta in ta nuna da gaske so take yi ta manta ka ɗin is fine by us in kuma wani uzurin sai muyi mata ko”
Kina ganin akwai uzurin da zai sa mace taƙi neman abin da haifa har zuwa shekara 30+ kina ganin akwai irin wannan”
Rasa bakin magana nayi don gabaɗaya maganar shi tafi tawa gaskiya haka na haƙura na sakko tare da cewar ni dai don Allah kawai ya neme ta don ni, yai min alƙawarin zai neme tan don amma idan ta nuna bata son mu’amala da mu bazan ƙara tada zancen ta
Na amince sannan yace min zai sake sa waɗan su su kuma bincika masa ita, godiya nayi masa sosai inda ya katse min tare da cewar
“kede kiyi fatan kada Allah yasa ta watsa miki ƙasa aido in kun haɗu”
“amin kawai nace tare da rungume ni
*****************
Tafiyace ta kama aliyu china inda ya nemi mu tafi tare ni kuma na nemi alfarmar in ɗauko ƴar autar mu mu tafi tare saboda da yara zamu ni kuma in fama da kaina
Aliyu be musa min ba yace mu tafi da hannatu ma ta dinga taimakawa aminar kula da yaran
Mama na kira na shaida mata tafiyar da zamuyi da amina, murna a wajen mama kamar me, ta haɗa amina ta hankaɗo min abuja, passport akayi masu ita da hannatun muka shiga neman visa barin ƙasa
Tun da amina tazo sai ta shaƙu da yaran sosai komai itace take musu tare da taimakon hannatu, kullum zaka tsince su ita da hannatun a tare ko a kitchen ko a ɗakin yaran wannan ne ya sani sakin jikina
Visar tamu bata fito ba ko ince tasu amina don tamu ta fito tun yaushe, aka aiko wa da aliyu gayyatar bikin ƙarasa sanin juna na masu manyan jiragen ruwa na duniya, tare da haɗin gwiwar masu manyan kamfononi na duniya, kasancewar ɗaya baya iya ci gaba da sai taimakon ɗaya
Taro akan sanin juna tare da sanin kan abinda ya dace ayi tare da gina kyakkyawar mu’amalat tsakanin masu company da masu yi musu dakon kaya zuwa garuruwa wanda sai kana da babban matsayi sannan za a gyace ke
A england za ayi, a garin man city, yaron aliyu na can ya kira shi don an bada iv ɗin har da aliyu kasancewar an san shima yana da manyan jiragen da suke shige da fice da kayayyaki
Ko da aliyu yaji saƙon sai yace wa da yarin nasa shi ya wakilce shi don shi bazai iya zuwa ba zai je china
“sir wannan harkar fa ta manya ce, manya manya ne na ƙasashe zasu taru, wannan zai bada damar ka haɗu da manya kaima ka ƙara bunƙasa taka harkar”
“shiyasa nace kaje”
“sir ai wannan dole sai kai, kasan manyan nan sun fison su haɗu da mutum in person”
“in son zanje china ne ni da iyalina faa”
“haba sir tun yaushe kake wannan harkar, wannan ai kamar dama ce muka samu, tun yaushe muke wannan harkar amma bamu taɓa samun daman irin wannan ba, kaga wannan damar zata sa ka ƙara bunƙasa sunan ka da kuma harkar tamu, muma adinga dama wa da mu” shiru aliyu yayi amma shi san zuwa england ɗin nan beyi masa be
Duk da duk abinda peter yake faɗi gaskiya ce ze kasance dama ce gare shi ya ƙara faɗaɗa harkar sa, barin ma ya haɗu da masu manyan kampononi kala kala, tunda yanzu iyakacinsa, ya kai ɗanyan mai china da america, ya ɗebo kaya daga china, america, thailand, saudiyya sai dubai
Amma hanyan zu be samu chance ɗin da jiragen sa zasu dinga duniya da kaya ba duk da dai cewar yana da jirage masu girma da ingancin da zasu dinga iya zaga duniyar tare da kwasar kaya ko a ina da kaisu duk wani loko da saƙo da duniyar
“ok peter make the preperation i will be there in shaa Allah”
“inn jaaa Allah” inji peter
“i will be coming with my family and my wife’s sister so look 4 a comfortably hotel 4 us”
“yes sir”
Ko da aliyu ya kashe wayar sai ya gayawa zainab cewar sai sun fara biyawa ta england domin ya halacci meeting ɗin kafin su wuce china
Da farko bata so hakan ba don ita bata da wani buri daya wuce ta gansu a china don aliyu ya je ya kuma ganin dr. sa don tana lure da shi yana fama da zuciyar sa kawai ɓoye mata yake yi, amma tasha farkawa da daddare ta ganshi a zaune riƙe da ƙirjin sa yana salati
Sam ita bata san wannanɓhali irin na mijinta ba, ace mutum yana ciwo amma ba zai je asibiti ba shine ma dalilin da yasa ta ce zata bishi chinar amma in ba haka ba me ze kaita birnin sin da wannan cikin duk da dai har yanzu be fi wata uku ba
Si da aliyu ya rarrashe ta tare da faɗa mata kwana goma kacal zasu yi a england ɗin sannanɓta sakko, sai kuma mimma ta faɗo mata,
Ai mimma tace a england take lallai kuwa in haka ne in shaa Allah in taje zata neme ta
Dole aliyu ya canza akalar neman visar su zuwa england, cikin ikon Allah suka samu sai shirye shiryen tafiya,
Ta lagos zamu tafi don haka nayi murna sosai ko ba komai zan ga gida, ana sauran kwana biyar mu wuce england aliyu ya barmu muka tafi lagos
Mun sha yawo sosai a lagos sannan Allah ya kawo mu lkcn tafiya,
Aliyu ya zo har gidan mu sun sha hira da baban mu sosai inda yayi musu alƙawarin kujerar makka da shi da mama da khadija da maryam
Baban mu harda hawayen farin ciki don be taɓa kawo ba, ko da yake naji su maryam suna cewa tunda na auri me kuɗi sunji mama tana cewa mijina zai kai su hajji ita da baba basu san har da su ba
Ni kaina ban san da tafiyar ba sai naji aliyu ya kuma shiga raina na kuma godewa Allah daya bani miji irin sa, mama har da rawa kun san idan aka ce mutum al’adar bayarabe ta shige shi doe sai an masa uzuri, ni ma nayi masa godiya sosai su maryam ma suka kira shi taka nas su kai masa godiya
Ran da zamu tafi har airport su mama suka rako mu mama sai rawar kai take yi ƴar ta zata tafi turai, muka yi sallama muka kama hanyar shiga jirgi sai turai ɗin gaske
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:47????
mun sauka lfy garin man city sannan muka kama hanyar hotel ɗin da peter ya kama mana, five star hotel dake kan titin neil lane, babban hotel ne me bene 95, inda peter ya kama mana presidential suite ɗin hotel ɗin
Suite ne me ɗakuna barkatai kitchen dining area, har da ɗan garden ƴar varender da ke kusa da living room, gaskiya ya ansa sunan shi presidential suite don komai me tsada ne
Unparking kayan mu kawai muka yi, ni da aliyu muka ɗauki master bedroom, amina ita da hannatu ko wannan ya ɗau ɗaki ɗai ɗai sai akar bar wa yaran ɗakin ɗaya, wanda yake kusa da na amina
ina cikin gyaran kayan aliyu ne naci karo da wasu pics daga gani na da ne, wata balarabiya ce ɗauke da ciki da wani ɓakin mutum kusa da ita ya rungume ta ta baya, ko wannen su ɗauke da murmushi, matar tana bala'in kama da aliyu kana ganin ta kaga mahaifiyar sa
Tausayi ya bani daga gani yana kewar ta sosai don dai bazai faɗa bane, amma yadda yake yawo da su ko ina har cikin wallet ɗin sa ma na taɓa ganin pic ɗin don de kamar baya son in sani ne ya sa nima nayi shiru
Pics ɗin kusa kala goma kala kala, ɗaukowa nayi tare da dawowa kusa dai
“habibi, su waye waɗan nan” na tambaye shi, sai da ya fara kissing ɗina, yakan yi kissing ɗina ne idan na tambaye shi magana me ɗan wuyar bada ansa
“ƴar ƙauye iyaye na ne”
“kuna kama da mmn ka sosai” hanci na ya ja min har na ɗan yi ɗan ƙara
“ki kalla sosai i resemble my innocent father”
“Allah habibi kunfi kama da mmn ka”
“shhhhh taya ma za ayi inyi kama da ita, am a photo copy of my papa” na san jin haushin abinda mmn tayi masa ne yasa baya son yace yana kama da ita
na kau da maganar don ko ɗan ƙaramin yaro yaga aliyu yaga mmn shi yasan sun yi kama ba kaɗan ba,
“i suppose wannan na cikin kai ne ko” na nuna cikin mmn shi daya fito sosai
“yep ɗat happens to be meee” ya faɗa da murmushi a fuskar sa
“do u miss her”
“no i never miss her, ban san ta ba bansan halin ta ba ban san komai nata ba ta yaya za ayi in missing abinda ban sani ba”
“i mean wataran kana cewa dama tana nan ko”
“no i never wish for 4 dat” ya faɗa yana tashi
“lets end d conversation here its boring” ya faɗa yana haɗa pics ɗin tare da yi musu ɓuya sosai
” na taho da su nedon kince sai na cigiyo miki ita don haka am going to use dis pics in shaa Allah, dont even think other wise”
sarai na san baya son hirar iyayen sa ne ko me yasa oho kai Allah ya kyauta na faɗa a raina
mimma na kira na shaida mata muna england a man city tai mamaki sosai don bamuyi da ita zan zo ba, dama naso ne onyi surprising ɗin ta, tai min alƙawarin zata zo, ni kuma nai mata kwatancen hotel ɗin da muka sauka
kashegari kuwa ta kira ni akan nayi expecting ɗin ta around 2:00 na ji daɗi sosai, da yake turai ya shige ta sosai ƙarfe 2:00 dai dai sai ga call daga reception wai ina da guest,
nace a barta ta shigo, minti biyu ne da ɗan sakons ya kawo ta suite ɗin mu, ina buɗe mata na rungume ta ban taɓa ganin ta ba sai yau
Kissing ɗina tayi a gefen fuskata duka biyun tare da ƙara rungume ni,
“ai nal aulad, where r kids” ta tambaya
Ƙwala wa hannatu kira nayi nace mata ta kawo su haidar,
Kawosu tayi, mimma ta dinga ɗaukar su tana kissing ɗin su sam ta kasa a jiye yaran ta taɓa wannan ta taɓa wancen, har ƴar ƙwalla sai da na gani a idon ta, wanda ya ke ɗauke da glass irin na likitoci,
Kallon mimma na dinga yi kamar na san kamar na san fuskar ta, amma shap na manta a ina na san ta, ko dai ban santa ba gaskiya na san wani me kama da ita, medicated glass ɗin da ke fuskar ta ne ya sani kasa tantance a ina na san fuskar ta, ko kuma a kalle kalle na na film ɗin larabawa ne oho ni dai nasan fuskar nan tata
“Mimma me za a kawo miki” na tambaye ta
“am full habibti”
“no mimma at least ko ba yawa ne ki ɗan ci kaɗan”
Gabaki ɗaya hankalin ta yana kan yaran, na sa akawo mata abinci da ɗan abin sawa a baki daga kitchen ɗin hotel ɗin
Da ƙyar ta iya ajiye haidar taci abinci ɗan kaɗan shima, pics ta dinga ɗaukar yaran, naso muyi hira da ita sosai amma sam hankalinta yana kan yaran,
Ba wani hira mukayi ba sosai sannan tace zata tafi duk da dai sai da ta kai kusan 5:20 sannan ta tashi nayi mata laƙawarin zuwa gidan ta
Ta bani address ɗin ta a liverpool take, na duba address ɗin nasu gidajen su na turai bashi da wuyar gane wa ba kamar namu ba nai mata alƙawarin zuwa gidan nata kafin mu tafi
Roƙo na ta dinga yi na don Allah in zo in kuma taho da su haidar na ansa mata da too
Har reception na rako ta anan ne ma muka ɗan tsaya muna hira kasancewar an tafi kira mata cab,
Aliyu ne ya shigo ya tarar da mu a reception ɗin yai mamakin ganina, sai na gabatar masa da mimma, yakan ji hirara ta a wajena sosai
“habibi ga ka yau ga mimma ta” na faɗa ina nuna masa ita
Da murmushin sa ya ƙaraso kusa da ita, amma abin mamaki suna haɗa ido sai naga fuskar shi ta canza, tsayawa yayi yana mata kallon mamaki kamar ya santa
Sai da nayi masa magana sannan ya dawo hayyacin sa
“habibi kasanta ne” na tambaya
“ta ina zan san ta” ya faɗa rai a ɓace
“ina jiran ki idan kin sallame ta”
Jikina duk yayi sanyi yadda yayi wa mimma sam ban ji daɗi ba ina laifi ta bar abinda take yi tazo kawai don tagan mu amma irin tarbar da zai mata kenan ohhh ni abu zan ga ran da mijina zai shiryu
Jiki a saɓule na raka ta itama bata ji daɗi ba amma kuma bata ce komai ba bayan ta tafi na dawo don yau aliyu yana da bayanin da zai min na wulaƙanta baƙuwata da yayi