DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Habibi me kayi wa baƙuwata kenan” na faɗa lkcn da na shigo ɗakin mu wanda na tarar da shi a kwance yayi rigingine yana kallon ceiling

"habibi kasan mimma ne da yasaka yi mata wulaƙanci bayan ta zo daga liverpool kawai don ganina da yaran amma shine kake wulaƙanta ta" 

Tashi yayi zaune
“a ina kika santa” ya faɗa ba tare da wasa afuskar ba
“so nawa zanɓfaɗa maka a yadda muka haɗu da ita”
“just tell me for GOD’s sake” ya faɗa da tsawa

Na faɗawa aliyu yadda muka haɗu da mimma, shiru kawai ya yana saurare na, ko da na gama sai yace min
“ki rabu da ita Hippocrate ce”
“huuuh ???? subhanallah, abu haidar a ina kasan ta da har zaka kira ta wannan sunan”

“just shut up an leave me alone” ya faɗa haushi naji na tashi gaba ɗaya na bar ɗakin, a cikin abinda yake yi kamar ya san mimmar amma me yasa baya son faɗa min ko wacce ce ita

ban kuma kula shi ba da magana mimma ba, gashi nayi mata alƙawarin zuwa ko ya za ayi inje, na faɗa araina

Bayan kwna biyu sai gashi ya zo da rana yana shiryawa, tashi nayi na je wajen sa tare da tambayar sa ko ina zashi don yai mana alƙawarin zai kai mu zaga gari da yamma

“habibi yaushe zamu fita ganin garin”
“sorry habibti ba yau ba kinga peter ya haɗa min dinner da wani mutumin ɗan ƙasar saudiyya, wai yana da kaya sosai da za ai masa shipping, shine yace pls inje gidan sa muyi dinner da iyalen sa”

“ohh cikin garin nan ne”
“noo liverpool ne, akwai train da zai tashi zuwa liverpool nan da 00:30 mins idan nayi sauri zan samu”

Jin an ambaci liverpool ya sani miƙewa,
“don Allah habibi zani”juyowa yayi ya kalle ni
“are u sure” ya tambaya, gyaɗa masa kai nayi

“ok hurry up and get ready we have a train to catch” da sauri na tashi na fara shirya wa in shaa Allah sai naje gidan mimma
“yaran faa” na tambaye shi

“ohh barsu kawai ai dinner ce kawai bana son yaran su kawo wani matsala, kin san official meeting ne”
“ok kawai nace

Cikin shadda ta greenish blue me ɗinkin fitted gown wacce ta sha surfani tun daga sama har ƙasa na sako tare da ɗauko pendants ɗina silver wanda ya shi sosai da kayan

 Mayafina na ɗauko wanda yai dai dai da kayan sannan na ɗauko stiletos hill ɗina na saka sai na fito kamar wata tauraruwa



muka fito muka kama hanyar station ɗin mun yi sa ar samun train ɗin on time mukai boarding muka fara tafiya zuwa liverpool tare da burin zuwa gidan mimma in dai muka je liverpool ɗin

[7:46PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: [11/27, 8:09 PM] ilyaszainab95: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
[11/27, 8:09 PM] ilyaszainab95: Page: 48????

  Lfy muka isa liverpool a train muka sauka sannan muka hau cab tare da ba driver ɗin address ɗin gidan da zamu, ƴar purse ɗin da ke hannu na na ɗauko na fito da address ɗin mimma 

“Habibi don Allah in mun fito daga dinner sai muje ko” hankalin shi gabaɗaya yana kan wayar don haka be kalli ƴar paper da na bashi ba, sai cewa yayi

“wa kika sani a liverpool da zaki gidan sa”
“gidan mimm ne nayi mata alƙawarin zanje”

“stop dreaming dear babu inda zaki” ya faɗa
“kamar yaya” juyowa yayi sosai har ina iya jiyo nunfashin sa dake sauka akan fuskata

“sweatheart ba nace u should 4 get about her ba, i dont like dis relationship”
“amma …………….”
“no amma just do me a favour nd stop talking about her u aint going any where, i hate d sight of her”

Oh my goodness wai sai yaushe mijinta zai bar halin sa ne,

Tafiyar 00:30 mins ne ya kaisu gidan da za suyi dinner, ran zainab a ɓace yake don haka kallon ma batayi ita da take cewa in suka fita zata yi using oppurtunity don ƙarewa garin kallon amma tun bayan ɗan faɗan su da aliyu ta cushe fuskar ta tare da juyawa gefe ta share shi

Ko da suka zo gidan ya biya me cab ɗin sannan suka ƙara ƙofar gidan inda suka dan na door bell ɗin

Wata yarinya ce ta zo ta buɗe daga gani bata fi sa ar zainab ɗin
“u r welcome” ta faɗa

shiga suka yi inda tayi musu jagora zuwa sitting room inda iyayen su suke,
“mr aliyu its a pleasure seeing u in my home u r highly welcome”
“the pleasure is all mine” aliyu ya faɗa suna musabaha da me gidan

“i believe this is ur wife” ya faɗa yana nuna zainab wacce ita kuma take ɗan murmushi
“yes she is zainab”
“oh wat a nice name, nice meeting u mrs aliyu”
“nice meeting u too” na maimaita

“yusra habibti tell ur mum our guest r here” ya faɗawa ƴar sada ta buɗe mana gidan
“yes dad” ta tashi ta fara hawa bene

Me aikin su ya kira ta kawo mana ruwa da lemo, ni dai gabaɗaya raina a ɓace yake abinda aliyu yayi, mmn tasun ta sauko tana maganar ina baƙin, to my surprise mimma

da murna ta na ƙarasa wajen ta tare da rungume ta,
“mimma” na faɗa
“habibti” ta faɗa tare da ƙara rungume ni

Nayi murnar ganin ta, ƙarasowa tayi cikin living room ɗin don su gaisa da aliyu, haka ya ansa gaisuwar tata fuskarsa babu yabo ba fallasa,

jana tayi zuwa kitchen

“zo muje mu haɗo wa boys ɗin mu ɗan snacks” binta nayi ina jin daɗi duk da dai ina feeling guilt na yadda mijina yake mata amma ita sam bata damu ba

A kitchen take tambayar yaran sai nace mata ai ban san nan zamu zo ba, Bata kawo komai ba ta yadda da abinda na faɗa

Muka haɗa ɗan snacks wanda yake a cikin leda ne a fridge kawai reheating muka sake yi a micro wave sannan muka ɗauko muka fito 


 Ajiyewa mukai agaban su sannan muka zauna muka fara hira, bamu daɗe da zama ba wani ya zo ya hankaɗo kofa ya shigo, gabaki ɗayan mu hankalin mu ya koma kanshi

Mimma ce tayi masa magana
“hisham come and say hi to our guest” ta faɗa masa, kamar ba ze zo ba sai kuma ya zo

miƙawa aliyu hannu yayi suka gaisa ni kuma ya min sallama, daga nan sai yayi sama, mu kuma muka koma hirar mu, sam ban ga tarbiya a tattare da yaron da mimma ta kira da hisham ba kanshi a tsaye yake daga gani kan nashin yana hayaƙi

  cook ɗin su ta gayyace mu dinner ta gama muka tashi muka tafi, kowa ya nemi wuri ya zauna, inda mijin mimma yake zaune kan kujerar da take kallon ta mimma sai ni kuma na zauna kusa da aliyu, 


  Aikawa tayi a kira yaran gidan su zo muyu dinner, matan ne kawai suka sakko amma ban da hisham ɗin, mun ɗan jima kafin mijin yace kawai muci abinci ƙila hisham ɗin ya ƙoshi ne 

Muka fara dinner sai ga hisham ya sauko a gadarance ya samu wuri kusa da bbn shi zauna, fara cin abinci yayi babu ko bismillah mun lura gabaɗayan mu, mimma ce tayi masa magana
“hisham baka yi bismillah ba”
“ina ruwanki da ni ko plate ɗin mu ɗaya ne” ya faɗa a wulaƙance

Abun ya bani mamaki ɗaga ido nayi na kalle su naga kowa babu abinda ya dame shi kamar dama sun saba

“ƙyale ta ta fiya sa kanta akan abinda da babu ruwanta, acting lika mother” inji ɗayar
“its ok kids, lets just eat we have guest today, salma behave ur self” shine abinda mijin yace

Mamaki ne ya kama ni, wannan rashin mutun ci ƙiri ƙiri amma abinda zai ce shine suyi shiru

Yarinyar da ake kira da yusra ne tace
“salma pass me d salt” tsayawa nayi ina kallon su

gabaki ɗaya babu tarbiyya a tattare da yaran salma ma suke ce mata kansu tsaye, itama mimmar sai ta share yusrar bata miƙa mata ba

“salma am taking to u”
“kinsan abinda ya kama ta kice kafin in baki salt ɗin”
“kina nufin in ce miki pls” Gyaɗa mata kai mimmar tayi

"da ince miki pls gwanda kar inci abinci" ta faɗa tana miƙe wa

“yusra habibti zauna lemme pass u d salt” inji yayar tatan, ƙin zama tayi ta shi ta miƙe ta hayewar ta sama

wani kallone uban ya bi mimma da shi wanda ƙiri ƙiri ya nuna itace me lefi
” ki daina yin abu kamar wata uwa a wajen mu, in tarbiyya kike son yi kije kiyi wa mataccen ɗan ki ba mu ba” hisham ya faɗa yana mike wa shima

yau naga ta kaina na kuma faɗa, ita ma yayar yusrar sai ta tashi har da cewa wai mimma ta sa loosing appetite ɗin itama ta bar wurin, kamar inyi mimma kuka haka neji, kanta yana ƙasa baza ka iya ganin fuskar ta don haka ba za iya faɗin mood ɗin da take ciki ba amma daga gani bata ji daɗin abinda ƴaƴan mijin ta suka yi mata ba

sai ya rage mu kaɗai tun marasa kunyar yaran sun fita 

“so aliyu kace maman ka ƴar saudiyya ce, a wane garin” inji mijin mimma

“oh ban sani ba don ban ma santa ba, bamu taɓa haɗuwa da ita”

“me ya same ta”
“she died the day i was born” ɗago kaina nayi ima kallon aliyi shi da yace mmn shi tana da rai amma yanzu yace ta mutu

“oh am so sorry may her soul rest in peace” in mijin mimma ita ma mimma sai tayi wa mmn aliyun addua

“amma baka tambayi bbn ka lbrn ta ba”
“ya mutu kafin a haife” sosai suka nuna tausayin sa

“amma gaskiya kaga rayuwa, ka rasa iyayen ka lkc ɗaya, lkcn da kake mutuƙar buƙatar su”

“haka Allah ya ƙaddara”
“do u miss dem”
“no babana kawai nake missing, ita kuma mmna lefin ta na gani da ta iya barina a wannan cruel world ɗin ta tafi without looking back how selfish of her”

“bata da zaɓi ne shi yasa alkcn mutuwa mutum bashi da zaɓi” Inji mijin mimma

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Leave a Reply

Back to top button