DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

“ba wai zaɓi ne bata da shi ba son kai ne kawai, ƙiri ƙiri tasan banni da wani bayan ita, amma duk da haka saboda selfishness irin ta da rashin imani da rashin tausayi ta iya barina a lkcn”

Daga maganganun aliyu kana ji kasan akwai baƙin ciki a tattare da su, riƙe masa hannu nayi alamar lallashi, juyowa yayi ya kalle ni yayi murmushi
“but who cares yanzu Allah ya haɗa ni da wacce ta fita a rayuwa so bana ji komai” Ya faɗa yana kallona

Murmushi nayi masa tare da shafa gefen fuskar sa wanda hakan yasa shi lumshe idon sa

“am soo sorry to hear dat, a wurin grans dinka ka tashi”

” no its a pity da babu wanda yake son ɗauka a lkcn da aka haife ni don ƙiri ƙiri tun kafin a haifeni babu jituwa tsakanin mum ɗina da inlaw ɗinta, amma yet bayan ta haife ni ta iya barina bata yi tunanin wa zai kula da ni ba, dats y i said she is selfish”

shiru duk muka yi maganar sa akwai tausayi sosai, kukan mimma kawai muka ji, ajiye table napkin ɗin da ke hannu ta tayi ta tashi da gudu ta bar table ɗin, binta muka yi da kallo sai da ta ɓace sannan mijinta yace
“kar ku samu damuwa ita ma ɗan ta ne ya mutu yana baby a hannun kakar sa shi yasa in taji lbrn baby ya rasa ɗaya daga cikin parents ɗin sa sai ta tuna ɗan”

“hypocrite” na kuma jin aliyu ya kira da shi, juyowa nayi na daka masa harara ,yaushe mijina ya ɓaci da zai dinga kiran mijina da hypocrite

tausayi ta bani sosai don haka sai nace
“bari inje in lallashe ta” aliyu ne ya riƙe min hannu na tare da zaunar dani,
“ba hurumin ki bane, kinga shima mijin daya ajiye ta be damu da ita ba sai ke uwar shishigi” ya faɗa da hausa yadda mutumin ba zai fahimci me muka ce

komawa nayi na zauna suka ci gaba da tattaunawa akan harkokin su, ganin na gaji da zama gashi ina son sanin halin da mimma take ya sani cewa don Allah a nuna min rest room

me aikin su ya kira yace ta kaini guest room, barin su nayi suka ci gaba da maganganun su na business ni kuma na bi me aikin nasu, sai da muka bar gurinsu sannan nace mata ta nuna min ɗakin mimma wurin ta zanje, tayi min kwatancen ɗakin na haura sama
[11/27, 8:09 PM] ilyaszainab95: A hankali na tura ƙofar ɗakin tana zaune a gaban mudubin ta tana kuka, kus da ita naje na dafa ta

Sai da ta goge fuskar ta sannan ta juyo da murmushin
“y r u crying” na tambaye ta
“lbrn mijiki ya sani tunowa da nawa ɗan”
“am sorry kin ce ya mutu ko” gyaɗa kanta tayi

“Haƙuri zaki yi ki tayi masa addu’a, shi kawai yake buƙata”

” ya za ayi ɗana ya yafe min” ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka
“ni na jawo ya mutu very innocent of him amma ya haɗu da uwa dat is full of childish, i just cant forgive my self for d death of my innocent baby”

Kuka ta kuma ci gaba da yi ina ta bata haƙuri, sai da ta ɗauki lkc sosai sannan ta haƙura bayan na tabbatar mata da cewar a kodayaushe ƴaƴa sukan yafe wa iyayen su balle nasan ɗan ta yana aljanna don haka bazai wani holding grudges against her ba

A hankali ta ɗan sakko har muka fara hira dai, irin na yadda ta zam successful likitan yara tace saboda son da take yi wa ɗan ta ne da dana sanin mutuwar sa da tayi ne yasa ta zama likitan yara

Na jin jina mata daga gani tana kewar ɗan nata sai dai muce Alƙah ya jiƙan sa, wani hoto ne ya ɗauke min hankali a kan mudubinta na ɗauko shi,da graduation gown a jikin me hoton tana dariya, tsaya wa nayi ina ƙarewa pic ɗin kallo, wannan kamar pic ɗin mmn aliyu

Juyowa nayi nace mata
“mimma wacece wannan” zuwa tayi kusa da ni ta karɓi pic ɗin
“nice lkcn graduation ɗina” ta faɗa da alamar alfahari

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un mimma ce mmn aliyu, kuma ya sani amma, ya subhanallah, ko shi yasa akan dining yake ta faɗa maman shi tana son kai don ya cusguna mata,

Hawaye ne ya cika idon na goge shi a don bana son ta gani, me yasa mijina baya son ya sanar da mmn shi ya nanan a raye, wayyo wannan wace irin ƙaddara ce ɗa yana son rama abinda mahaifiyar shi tayi masa da ƙuruciyar sa

Futowa nayi daga ɗakin inda naga aliyu yana nema na zamu tafi mimma har ƙofar gida ta rako ni mukayi sallama gaba ɗaya jikina a yayi sanyi ganin wannan irin relation ship ɗin nasu muka kama hanyar man city ni da miji kowanne mu zuciya ba daɗi, ni ina tunanin me yasa mijina zai yi wa mmn sa haka shi kuma Allah ne kaɗai ya san abinda ke ransa
[7:46PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

Page :49????    

na Sadauƙar da wannan page ɗin ga dukkan masoya na gidan aure da waɗanda suke shirin yi Allah ka barmu da mazajen mu ka ƙara musu son mu ka rufe musu idon su daga ganin aibin mu ka buɗe musu idanuwan su don su dinga ganin alkhairan da ke tattare da mu, masu matsala a gidan aure Allah ya kawo musu sauƙi, masu zaman lfy Allah ya kuma zaunar su lfy waɗanda suke shirin aure Allah ya sada su da nagari waɗanda har yanzu basu samu ba Allah ya haɗa da nagari, Allah ya barmu da masu son mu yau ina cikin murna????????????????????????????????????????????????????????

  Sai 12 :40am na dare sannan muka shiga gida, kowannen mu zuciya cike da tunani, ɗakin yara wuce direct don in duba su,  baccin su suke hankali a kwance ga amina ma a kan kujera 

Tashin ta nayi nace ta koma ɗakin ta sannan na kuma yi musu addua tare da kashe musu fitila na fice, ko da na shiga ɗaki aliyu yana toilet, kaya kawai na cire na zauna ina jiran ya fito

Wanka yayi don ya fito gashin kansa yana ɗigar ruwa, tashi nayi nima naje na yi wankan sannan na fito na shirya na kwanta kusa da shi

“habibi yau me kayi a gidan su mimma kace mmn ka mutu”
“she is as good as dead to me” ya ansa

“ba nace ka daina wannan abun ba, wai sai yaushe zamu zauna ne ba tare da ka kawo mana wani problem bane, wat u did to dat innocent woman is unfair”

“unfair me na mata da ya zama unfair don kawai na faɗi tahirin rayuwata”

“labarin naka kamar kasan zai ƙona mata rai ne shi yasa ka dinga faɗin shi haka, did u intend ta hurt her”

 "why will i hurt her wen i dont even know her"

“ranar da ka fara ganin ta ka kira ta da hypocrite wannan ya nuna ka santa”

“less stop dis conversation here bacci nake ji kinsan gobe akwai partyn da zamuyi attending kuma kin san ba nigeria ba ne don haka babu african time, we have to be there on time” shiru nima nayi aliyu baya son ya faɗi wani abu, amma ina da tabbacin mimma ce maman sa na so mu ci gaba da conversation ɗin amma ba hali

Bacci ne ya kwashe ni don na gaji, cikin dare na ji nishi a kusa da ni, farkawa nayi naga aliyi yana murƙususi riƙe da qirjin sa


Ohh my goodness zuciyarsa again na faɗa tashi nayi na dafa shi sai naji ya ce 

“magani na pls” tashi nayi na ɗauko maganin nasa na ɓallo su dai dai yadda dosage ɗin yace miƙa masa nayi tare da bashi ruwa

Da ƙyar ya iya karɓa ya sha, cikin minti biyu bacci ya kwashe shi amma kafin yai bacci ya bani tausayi sosai daga gani yana fama da zuciyar nan tasa don har kuka sai da yayi

Gyara masa kwanciya nayi don ya ji daɗin baccin sai na ci karo da pics ɗin mimma na wajen sa, ohhh my goodness mijina ya gano mmn sa amma ƙiri ƙiri ya ƙi nuna mata cewar har yanzu yana a raye

Cuzguna mata yake son yi amma on d other hand shima he is suffering, gwanda ma ita bata fama da matsalar zuciya amma shi fa, zuciyar sa bata da lfy yet duk da haka ya hana ta ta samu sassauci kullum ƙara danƙara mata ƙiyayyar mutane yake 

Sai yanzu na fahimci dalilin daya sa mijina ya samu ciwon zuciyar nan sabida gabaki ɗaya rayuwar sa ya taso cikin ƙunci da cuzgunawa daga mutane don haka zuciyar mijina babu komai a cikin ta sai ƙiyayya

Zuciyar da ke cike da soyayya na ba kowacce take lafiya ba balle ta mijina tun yana yaro ya cika zuciyar sa da tsanar dangin sa ya za ayi a samu lfy a tare da zuciyar da tun tana ƙarama babu abinda ke cikin ta sai ƙiyayya

Shi aliyu be fahimta bane shine maganin zuciyar sa inda zai dena ƙiyayyar da yake da ya zauna ƙalau amma burin shi yanzu naga alamar ya ƙuntatawa mahaifiyar sa, bayan kuma na san koda zai ji daɗi ya ganta a halin ƙunci yet shima a ƙasan zuciyar sa sai yaji ciwon nan kasancewar mahaifiyarsa don an ce blood is thicker than water, no matter stage ɗin da ɗa ya kai wajen resenting iyayen sa dole deep down in him dole a samu ɗan tausayi ko da ƙalilan ne na iyayen

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Leave a Reply

Back to top button