
Washe baki mr muktar wato mijin mimma yayi,
“ai babu komai if dey r available zamu zo da su, i really hope ba kallon ɗaya daga cikin ƴaƴana kake yi don babu ruwana kai da matar ka” ya faɗa a zolaye
“no no no kawai de dey r fun to be around” ya faɗa yana sosa ƙeyar sa wai yaji kunya, haushi ya bani na riƙe hannun sa tare da kai masa mintsi ni
Duba na kai ga fuskar mimma wanda hakan da aliyu yayi yasa bata ji daɗi ba har hakan ya nuna a fuskar sa, wanda shi kuma aliyun ya kalle ta yayi murmushin mugunta
Sai yanzu na fahinci dalilin daya sa aliyu cewar ze bi mr muktar boat trip ɗin shi, wato so yake ya kuma ganin yadda ƴen iskan yaran zasu wulaƙan ta masa ƴaƴa uwa ko, ohhh Allah naah wannan miji nawa, ɓacin ran mahaifiyar ka ya kai mijina ɓacin ranka ne baka sani ba na faɗa a raina
“zo muje muyi rawa” naji ya faɗa, binshi nayi ba tare da nace komai ba, kasancewar slow music ne sai kawai na kwanta a jikin sa, don gaba ɗaya ba a cikin hayyaci na nake ba
Da wuri muka baro dinner don duk na gaji sai aliyu yace kawai mu tafi, a mota ne nace masa
“me yasa kace wa mijin mimma ya taho da ƴaƴan sa”
“kar dai kina nufin kin yadda son ɗaya daga cikin su nake yi”
“ko ɗaya ai nasan duk cikin su babu type ɗin ka don ba kunya gare su”
“yes rashin kunyar tasun nake son gani” ya faɗa da murmushi a fuskar sa
“kana nufin kana jin daɗin rashin kunyar da suke wa mimma”
“more than everthing i really enjoy watching her suffering”
“me yake damun ka, me matar nan tayi maka, baka tunanin kana ɗaukar hakkin ta, randa muka je gidan ta ka sa ta kuka u insulted her in directly yanzu kuma zasu boat trip da mijinta ka sa ya zo da ƴaƴan sa don kawai kaga suna wulaƙantata me ta tare maka”
“sweatheart dont worry ta chanchanci abinda ya fi haka ma saboda abinda tayi abaya”
“kana nufin na ajiye kan da tayi ranar da ta haife ka ta tafi” juyowa yayi ya kalle ni sauran kaɗan mu buge wani don haka sai ya koma gefe yayi parking, tsayawa yayi sosai yana kallona
“how do u know”
“yanda kake yi mata ne yasa ni na fara tunananin ƙila ka san ta kuma Allah sai ya taimake ni naci karo da pic ɗinta a ɗakin ta sak irin wanda kake da shi a lkcn na fahimci daliliɓ da yasa kake mata haka wai ka rama abinda tayi maka, ina tunanin ka yake, da har kake son ɗaukar fansa aka wacce ta kawo duniya”
Na faɗa ido na cike da ƙwalla don gaskiya yanzu abin aliyu tsoro yake bani
“yanzu meye na kuka kina ganin abinda nake mata ban kyauta bane”
“mahaifiyarka ce kake mata haka”
“me tayi min da zai nuna ya kamata in bata matsayin ta na uwa”
” ta kawo ka duniya, wannan be isa ba”
“ko kaɗan be yi min ba, matar da ta gudu ta barni ranar da ta haife ni kike son in kula ko me, ni ko kaɗan bana jin ta a raina”
“Aliyu duk abinda yake samun ka kaine kake jawo wa kanka” murmushin takaici yayi
“wato laifi nane ma yasa mahaifiyata ta gudu ranar da ta haife ni ko” girgiza kaina nayi
“ba wannan nake nufi ba matsalar zuciyar ka da kashe kanka da kake son yi saboda takurawa kanka da kake yi da sawa zuciyar ka ƙiyayyar mutane, ka taɓa tunanin wane hali zamu shiga ni da yara idan muka wayi gari zuciyar ka buga mun rasa ka, ko kana son yaran ka suyi maraici kamar yadda kai kayi, idan kana abun ka na san kai kana samu a cikine ko kuma kawai burinka ka ɗau fansar wanda ya ƙuntata maka, babu yafi a lamarinka ne ko menene” a wannan halin kuka ne kawai ya kubce min wanda hakan ne ya sani yin shiru
Rungume ni najo yayi wanda ni kuma na dinga kokawar ya sake ni ammabina da ƙarfi ya rungume nin
“aliyu tsoron ka nake ji yadda kake yi wa mutane idan sun ɓata maka kar nima wataran in ɓata maka ka guje ni, don Allah ka sawa zuciyar ka salama ka cire duk wasu ƙiyayyar ɗan adam a zuciyar ka ko ka zauna lfy, bana son rasa ka i really love u sooo much dat it ache me” na ƙarasa da kuka
“habibti am urs and will 4ever be amma mamana ta wulaƙan tani tun randa aka haife ni ta gudu ta barni baki ganin nima ya kamata in rama ita ma taji abinda naji througout those years i spent alone”
“talk to her don Allah kayi mata magana kaji dalilin ta na rabuwa da kai don Allah kayi mata magana” na faɗa ina haɗa hanne na tare da murza su a salon roƙo ????????????????????????
“babu ita a cikin tsarin rayuwa ta abinda take fuskanta yanzu a gidan ta sakayya ce”
“i know na sani don Allah kayi mata magana ita kanta she is suffering, cant u see, she thought u r dead”
“ta sa aranta cewar am dead ne shiyasa cant u see bata so na tunda har zata iya yin ƙarya dan da ta haifa ya mutu bayan ita ta gudu ta barshi yet kina son kice min in yi haƙuri in mata magana, pls let’s stop here is ok”
“habibi………………”
“shhhhhhhh mu daina musu akan hakan ya isa da mun gama abinda muke a nan zamu wuce nigeria mu man ta da ita, kuma kema ina son ki yanke duk wata hulɗa da ita, don bata buƙatata ta shi yasa ta ce na mutu let me just act as dead ɗin kamar yadda take so”
“pls pls plsssssss”
“zainab, can u pls stop it” ya faɗa da ƙarfi wanda har sai ɗan da ke ciki na ya motsa saboda tsawar daya daka min
Shiru nayi na kifa kaina tare da sakin sabon kuka, wayyo yau Allah ya haɗa ni da wani murɗaɗɗaen miji ya zanyi
Har muka koma gida babu wanda ya kuma kula ɗan uwansa ina shiga ɗaki kawai na shiga na kwanta ban daɗe da kwanciya ba bacci ya kwashe ni ko sallah isha ban yia ba
Cikin dare aliyu ya kuma tashi na da ciwon zuciyar sa tashi nayi na dinga yi masa kuka yadda ƙiri ƙiri yake son kashe kansa don kawai ya ɗauki fansar abinda mahaifiyar sa tayi masa alkcn ƙuruciya
Maganni na bashi ya sha Allah ya taimake shi bacci ya kwashe shi salla na tashi nayi na daɗe a sujjada ina gayawa ubangiji buƙatuna na Allah ya sanyaya mijina zuciyar sa da wannan halin nasa
Nai kuka nai majina duk wajen kaiwa ubangiji kukana, sai gab da sallah asuba sannan na sallame
Fes na jini don haka sai na tashi na shiga kitchen na ɗan haɗa ɗan abinci na ci sannan nayi niyyar ɗaukar azimi don a gaskiya lamarin aliyu yanzu tsoro yake bani
Da zazzaɓi ya farka don haka sai na koma jinyar sa ko kaɗan ban yi masa tunin abinda ya faru jiya ba
Na ce masa muje in raka shi asibiti ya ƙi sai kawai na saka masa na mujiya ????????, haka ya wuni yana ta nurƙususu a gado in ciwo ya ci yai ta salati tare da kuka yana kiran sunan Allah ko ta kanshi ban bi iyaka cin dak nace masa
“idan Allah yayi maka rasuwa dana fita takaba aure na zanyi” ya bani haushi ne iyakar bani haushi
Be kula ni sai ma kulle ƙofar ɗakin da yayi bayan na fita, sai la’asar ya fitƙ daga gani zuciyar tasa tayi sauƙi, be min magana ba kawai ya fice ni ma sai nayi kamar ban ganshi ba
Har ƙarfe 11:00 na dare be dawo ba kiran wayar shi nayi
“ina ka shiga ne har yanzu baka dawo ba”
“ina ruwanki ke da idan na mutu aurenki zaki yi ai se kije kiyi yanzu ma na barki”
“am sorry in shaa Allah kai kaɗai ne mijina duniya da ƙiyama”
“wannan cin hanci ne ko me”
“ni dai kawai ka dawo”
“to ya zanyi tunda na riga na mallaka miki zuciyata”
“a wannan zuciyar taka tana buƙatar wanki, in da gaske ka mallaka min ita to ka barni in wanke ta”
“tayi dauɗa kenan” ya faɗa
“bance ba ni dai kawai ka dawo”
“too shiken gani nan tun ance in dawo”
Be daɗe ba sai gashi, muka a jiye differences ɗin mu muka raya sunna a daren sai dai in ce sai da safen ku readers
*ina godiya sosai ga masu miƙo min addu'a Allah ya biya mana buƙatun mu na yau da kullum da ku da ni*
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????