DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

  Page 51????

wannan shafin naki ne ke kaɗai mummy rabi ta grp ɗin dangin sa, Allah ya biya miki buƙatun ki, adduar ki tana kashe min jiki na gode jazakilla bi khair Allah ya barmu tare????????????????????????????

Kashegari da safe da wuri muka shirya, suma su amina muka sa suka haɗa kayan su dana su haidar don baza mu bar su su kaɗai a gidan ba

Manchester muka fara zuwa gidan wani abokin aliyu me suna junior sukka( tawa kaddarar ) da matar sa fatima da ƴen ƴaƴan sa masu kyau masu kama da ƴen korea

Sun mana iso sosai, sannan muka keɓe da fatimar macece me mutuƙar kirki sosai mun sha hira da ita, na yadda take juya mijinta sosai kome tace sai yayi ta rawar kai yana yi

Abin ya bani mamaki ban yi nauyin baki ba na tambayeta irin wannan hidimar da mijin ta yake yi da ita haka

Murmushi tayi tace kafin in zo nan junior babu irin kukan da be sani ba har ƴaƴan mu na fari ya kira da shegu amma kinga da nayi haƙuri yanzu ya zama labari,

Don haka kema kiyi haƙuri shi aure akan haƙuri ake gina shi, na so ta bani lbrn auren ta amma sai tace min yanzu babu lkc sosai in bari indan mun sake haɗuwa zaki ji lbrna

idan da me son jin lbrn auren fatima da junior ya nemi littafin TAWA KADDARAR

Sai bayan azahar sannan muka bar manchester muka kama hanyar liverpool, sai dare muka je, hotel muka kama muka kwana don sai kashegari zamu wuce gidan mimma, fatana de kawai shine Allah yasa marasa kunyar ƴaƴan mijinta bazasu ba 



Kashegari da wuri muka fita muka je gidan mimma acen ma mukai breakfast, sannan muka kama hanya da ƴaƴan mr muktar amma matan kaɗai banda namiji ko ba komai an rage iri na faɗa


 muka kama hanyar bakin ruwan inda zamu shiga jirgin domin zuwa trip ɗin, muka hau muka fara tafiya, ɗaki uku ne a jirgin sai kitchen wanda akwai cook sai kuma masu tuƙa jirgin su biyu suma a ɓangaren su, muka ɗau ɗaya mimma ma suka ɗau ɗaya sai marasa kunyar ƴaƴan su suka ɗau ɗaya


 Da rana muka fito ɗan farfajiyar jurgin domin cin abinci, table akai setting duk muka zauna muka fara cin abinci ina lure da mimma duk wani abun da zai haɗa ta da yaran nan tana gudan sa 




  Muna cin abincin hana wacce take yar yusra ce ta ce wa mimma

“yau salma lfy kike acting kamar wata saliha” yusra tayi dariya
“ƙila bata son embarrassing kanta ne”

"ku kuma da kuke lacking manners baza ku iya gani kuyi shiru ba" na faɗa, daga aliyu har mr muktar duk sai suka ɗago suka kalle ni shiru nayi na ci gaba da cin abinci na kamar ba ni na faɗa ba 


Shiru suka yi na sha alwashin muddun a wannan tafiyar suka ce zasu yi wa mimma rashin mutunci sai na rama mata da su da uban su suji inda daɗi

Babu wanda ya kuma cewa komai har muka tashi, mr muktar da aliyu suka koma gefe suka fara kamun kifi wai da shi zamuyi dinner wanda zasu kamo ɗin

Su yusra suka koma ɗakin su don sun lura da irin kallon da nake musu na rashin M
muka zauna ni da mimma muna ta hirar mu yawanci jirar su haidar ne take tambayata ina bata ansa dai dai abinda nasa ni, tai min alƙawarin idan na haihu zata zo har nigeria ganin baby

Nayi murmushi na kalle ta a zuciyata na ce Allah sarki shi yasa kike son su haidar ashe su jininki ne ya za ayi in iya faɗawa matar nan cewar mijina ɗan ta ne

Zuwa dare cikin ikon Allah sun kamo kifin da zai ishe mu dinner amma tare da taimakon cook ɗin, grilled fish da potatoes sai kidney sauce akayi mana dinner, sai lemon curd a matsayin dessert,



 Mun ci nan ma lau babu faɗa na fahimci su yusra matsoratan ƙarya ne, da wuri muka kama hanyar ɗaki don a gajiye nake bacci nake ji sosai

Da safe ba da wuri muka tashi ba, sai da muka makara, mun fito mun tarar da pancake wanda akai masa cream me strawberry flavour, ƙamshin pancake ɗin ma ya isa ya sa mutum ƙoshi sai cafe latté,

Ban taɓa shan café latté ba amma yau danayi tasting ɗin shi na fahimci dalilin daya sa mutane son shi, zaki ne haɗe da ɗaci wanda yake fitar da wani aroma me daɗi, ko daɗin aroma ɗin cafe ɗin ma ya isa ka sha shi, na ci pancake ɗin nan sosai, taste ɗin strawberry ɗin da ke cikin cream ɗin shi ya ja ni na ci dayawa ban sani ba, har aliyu yana tsokana ta
“habibti ko da cook ɗinnan zamu koma nigeria ne, yada naga kina cin pancake ɗin nan ban taɓa ganin ki kina cin abinci haka ba”

Ban kula shi don shiru ma magana ce, da rana aka kawo mana bufferlo chicken wings, da braised chinise rice wacce aka mata irin dahuwar fried rice, amma ita ta ɗan fi fried rice yin laushi, sai pasta salad

A ɗaki na zauna na ci abinci na don bana son fita inci karo da waɗancan ƴen iskan, muna cikin cin abincin ne naji hayaniya har na tashi aliyu yace in zauna in cigaba da cin abinci na shi bari yaje yaga menene,

Fita yayi amma maimakon inji shiru sai naji muryar hana tana faɗa da ƙarfi harda zagi, wannan jarababbiyar kuma ita da wa na faɗa ko kafan ban kawo a raina cewar mimma take zagi ba



Jin muryar mr muktar nayi yana cewa duk ba ke kika jawo suka raina ki ba, kukan mimma naji ai ban san lkcn da na fita a guje ba, na doshi inda suke amma kafin inƙarasa sai na hango mijina a durkushe riƙe da ƙirjin sa yana ta kakari kamar ya kasa numfashi ko kuma numfashin ne yake neman ɗauke wa



a guje nayi wajen sa ina kiran sunan sa *ALIYU* jin kiran sa da nayi ya jawo hankalin su ko kafin in ƙarasa inda yake jikin shi ya saki ya daina nunfashin gaba ɗaya ma 




 Da gudu na isa wajen sai ga su mimma, itace ta ƙaraso ta janye shi daga jikina da na rungume shi don ni a tunanina ko ya mutu ne taɓa pulse ɗin shi tayi taji yana nunfashi sai ta kwantar da shi a ƙasa tace duk a ɗan matsa sabida iska 

“ki toshe masa hancin sa ki hura masa iska ta bakin sa” ta umarce ni, hakan nayi, ko bayan da iskar ta shige shi ita kuma sai ta fara danna masa kirjin sa don zuciyar sa ta fitar da iskar dana ɗura masa

haka muka dinga yi babi abinda nake yi sai kuka, wannan abun da aka yi yaƙi yi don haka mimma ta sa aka ɗauke shi sai cikin daƙin mu

wayar wuta ta ɗauko ta sa masa a ɗan yatsan sa babba ko wanne, tsirarar wayar kana ganin ɗan ƙarfen nan na ciki, sai da ta tabbatar da komai ya zauna dai dai sannan tace in matsa daga kusa da shi 




matsawa nayi sannan ita ma ta koma gurin switch ɗin ta kunna sai gashi wayar ta fara shocking ɗin sa yana girgiza, kuka na saka sosai wai mijina ne wannan 

sakon ɗaya sai ta kashe ta zo ta duba shi be dawo ba ta kuma komawa ta kuma kunnawa tana kunna wa ya fara tari sauri kashewa tayi tare da zuwa ta kwantar da shi ta cire masa wayar a hannun sa can sai gashi ya dawo hayyacin sa rungume shi nayi na saka kuka me ƙarfi

Asibitin su ta kira tayi reportig abinda ya same shi, a wayar suka dinga gayamata abinda zata yi masa, nima ta tanbaye ni a game da ciwon sa na faɗa mata an taɓa masa aiki a china, ta faa musu a binciken da sukayi sun gano ya samu heart attack ne kuma it is very serious don haka mu juyo don a kwantar da shi

Magani ta bashi ya karɓa ya shi sai bacci ita kuma ta fice daga ɗakin, abin mamaki cikin aljihun aliyu hoton mimma ne, nayi mamakin dana ga haka

sai yanzu na fahimci abinda ya sa shi heart attack ɗin nan wato jin zagin da hana take wa mahaifiyar sa ne yasa shi haka kuka na saka gaskiya lkc yayi da mimma zata san komai

tashi nayi na fita daga ɗakin zuwa ɗakin ta, ƙwanƙwasawa nayi muryarta a dashe tace min in shigo, idon ta ya kaɗa yayi jajir daga gani kuka tasha

gaban ta naje nace “mimma me ya saki kuka, me yasa baza ki bar mr muktar ba kije kiyi rayuwar daban da su, irin wannan abinda suke miki watarana sai ki kamu da ciwon zuciya ke ma rana ɗaya a rasa ki kinga kin jawowa masoyan ki” murmushi tayi

: “babu wanda zai yi missinga ɗina idan bana nan, more over kinga duk wannan abun da nake yi alhakin ɗana ne yake bina shiyasa duk abinda su hana zasuyi min bana cewa komai nasan cewar alhakin ɗan ƙaramin ɗana ne”

“mimma baki ganin ya kamata kije ki nemi ɗan ki yanzu” murmushi tayi
“zainab my son is dead” na ta shiga rattabo min tarihinta kamar yada aliyu ya faɗa amma ita daga ƙarshe sai tace bayan wata guda da tafiya sai iyayen ta suka ce ta zo ta ɗauki ɗanta

Ko da tazo gidan iya sai ɗan iyar yace mata ɗan ta ya mutu don yunwa don babu nonon da zai sha, anan sai kawai ta kuma fashe wa kuka, sai a yanzu na fahinta Allah sarki ba laifin ta bane kamar yadda aliyu ya faɗa ta dawo sharrin ɗaya daga cikin kawun sa ne 

“mimma ɗanki be mutu ba” ma faɗa
“what” tace
“mijina shine ɗan ki da kike tunanin ya mutu”

A firgice ta kalle ni me kike nufi, hoton da ke cikin aljihunsa na ɗauko na miƙa mata, karɓa tayi hannun ta yana ta kalli hoton, wannan ai sune pics ɗin da sani ya haɗa musu cikin kayan da zasu nigeria da shi wanda suka bar wa buhari ya taho musu da shi

Kuka ne ya kubce mata nai mata duk baya nin da nasani game da aliyi ban gama ba ta tashi a guje tayi ɗakin mu, binta nayi naje na tarar ita akansa tana kuka

"Pls kar ka barni, na rasa ka kana jariri don Allah bana son in rasa ka so biyi u have to be strong don Allah ka tashi don ka rama abinda nayi maka ko sau nawa zaka rama indai zan ganka da lfyr ka i will be ok" ɗago ta nayi na rumgume ta alkcn ne mr muktar ya shigo yana tambayar me ya faru 



Faɗa masa nayi sai naga yayi shiru kuma jikin sa yayi sanyi ya fice, mimma ko kuka ta ɗinga yi nima shi nake yi 

Sai cikin dare muka iso bakin shore inda muka tarar da ambulance tana jiran mu ɗaukar shi akayi, sannan aka fara duba shi tun a cikin ambulance ɗin aka saka masa oxygen a hanncin sa don ya taimaka sa numfashi

muna shiga asibitin directly theater room aka shiga da shi, mu kuma muka tsaya a wajen duk ran mu a dagule daga ni sai mimma inda mr muktar ya tafi kai ƴaƴan sa gida 




 Har asuba sannan likitoci suka fito, bin ɗaya muka yi wanda daga ganin su shine team head ɗin su, office ɗin shi muka bishi, ya zauna ya ɗauko wani file ya gama ƴen rubuce rubucen sa, ya dube mu 

“ku kwantar da hankalin ku abinda zan faɗa muku ba a kanshi aka fara ba kuma idan ya samu treatment zai warke” hankalina gaba ɗaya baya jikina burina kawai inji me zace, sai kawai naji yace

“zuciyar sa ta buga, ta tashi daga aiki, yanzu mun sa mana machine ne wanda yake taimaka mata take ɗon functioning, don haka yana buƙatar heart transplant” suman zaune kawai nayi

Subhanallahi ya Allah shi ne kawai na iya faɗa
[7:46PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

Page:52????

Service ɗina ɗaukewa yayi kasancewar wannan mummunar lbrin da nake ji ya samu mijina,

mimma naji ta dafa ni juyowa nayi na kalle ta
“zo muje mu ganshi” tashi nayi na bita amma gabaɗaya ba a cikin hayyaci na nake ba

Yana kwance a gadon marasa lfy sai oxygen da aka saka masa sai kuma wasu wayoyi da akayi connecting zuwa babban ɗan yatsan sa duka biyun, sannan kuma wasu abubuwa da aka manna masa a ƙirjin sa

Duk sai yayi wani fayau ya ramew sosai, kuka ne kawai ya ƙwace min ina yi mimma nayi mun rasa me share mana hawaye 

Mimma ce ta fita ta barni ni ɗaya tausayin kaina ne ya kamani wayyo Allah ya tashi kafaɗar mijina ga ciki ina da shi fa mijina yana buƙatar zuciya ko tawa zan bashi ne inyaso sai a cire min cikin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Leave a Reply

Back to top button