
Tunani ne ya dinga faɗo min a raina ni kaɗai, shigowa ɗakin ne ya dawo dani daga tunanin nawa, mimma ce ta shigo
“an samu zuciyar da za a saka masa”
“alhamdulillah na faɗa” ashe samun zuciyar ma babu wuya
“mimma ta musulmi ce” gyaɗa min kai tayi sannan ta koma kusa da aliyu kissing ɗin shi tayi sosai a goshin sa, sannan naga hawaye suna fitowa daga idon ta suna ɗiga akan fuskar sa
“pls 4 give me, don Allah ka yafe min zan so ace inyi ma bayanin dalilina na barin ka amma hakan bazai yuwu ba,
don Allah idan ka farfaɗo kayi rayuwa me daɗi na yafe maka a matsayi na uwa, kaima ina roƙon ka ka yafe min” mimma ta rinqa rokon Aliyu ya yafe mata tana kuka,
Ni na rasa dalilin da mimma take cewa bazai tashi ya same ta ba, dr. ne ya zo ya kira mimma sai naga ta kuma sunbatar aliyu sannan ta fita, me mimma take nufi da hakan
Fita nayi na bi bayan su, wani ɗaki suka shiga sun ɗan jima si gasu sun fito dr. ɗin yake cewar result ɗin zai fito gobe
Murmushi tayi masa sannan tazo inda nake sai nace
“mimma wane result ne zai fito kuma”
“am donating my heart to him”
“no no no and no u r not” na faɗa ina kuka
“mimma u cant donate ur heart, aliyu ba zai so zuciyarki ta kasance a jikin sa, mutumin da yayi missing ɗinki all of his life kice shi zaki bawa zuciyarki, tayaya kike tunanin zai yi rayuwa idan ya fahinci kin rasa rayuwar kine saboda shi, mimma idan kika bawa aliyu zuciyar ki kin kuma kashe shine don zai zauna iyakacin rayuwar sa da tunanin kin kashe kankine saboda tayaya kike tunanin zai rayu da wannan guilt ɗin pls mimma ki bari muje 4 donation mu samu zuciya pls ba taki ba he really need u by his side”
“zainab ya kike tunanin zan bari in rasa ɗana 4 d second time in my life da farko na rasa shi yanzu ma so kike yi in kuma rasa shin, ba zuciya ba ko komai na jikina aka ce inba ɗana zan bashi”
“pls mimma kar kiyi haka”
” na riga na gama magana in shaa Allah gobe result zai fito in yaso sai kawai ayi ni dai fata na ki riƙe min shi amana”
Kuka ne ya ƙwace min sarai na san halin aliyu ya za ayi mutimin nan ya tashi yaji cewar zuciyar mahaifiyar sa ce a qirjin sa ya za ayi ya iya rayuwa da wannan ko nice ake ansa wa zuciyar wani nawa dole in tausayawa wanda aka kashe don kawai a rayani balle shi da ba abinda ya taɓa yi wa mahaifiyar shi sai rashin kyautatawa tun da ya gane ta,
Don Allah ya za ayi mijina ya zauna da wannan guilt ɗin wannan kamar an kashe shi ne amma kuma yana rayuwa haka zai rayu da wannan guilt ɗin,komawa nayi ɗakin yana ta bacci kuka ne ya ƙwace min ɗa na tuno irin rayuwar da zaiyi nan gaba da zuciyar mahaifiyar sa aqirjin sa
Tj na ɗauki waya na kirashi na faɗa masa halin da aliyin yake ciki da kuma abinda ya dace ayi masa da kuma hukunci da mimma ta yanke
“wacece kuma mimma” shiru nayi sai yanzu na fahinci
ashe tj be san anga mmn aliyu ba
“mahaifiyar aliyu ce mun gano ta a nan”
“noo baza ta bashi zuciyarta ba aliyu will kill himself”
“nima haka nace, don yanzu zancen da nake maka ma an yi mata duk wani bincike da za ayi mata na cire zuciyar”
“no koma dai menene kice mata sai nazo kar a sake a taɓa min ɗan uwa sai na zo in bahaka ba sai na maka ta a kotu”
Ya faɗa da zafi tabbasa nasa cewar ciwon aliyun ne yasa tj ɗin hakan amma tj shi me sanyi ne, muka gama waya yace za ɗauko private plane ɗin aliyi ya taho a ranar don be sani ba ko akwai flight ɗin da zai zo nan liverpool ɗin a ranar mukai sallama ni da shi
Ko da dare yayi sai wata nurse tace min mu tafi gida don ba a kwana, muka fita amma ni sai na ƙi zuwa gidan mimma don bana son ganin waɗannan ƴen iskan yaran, mimma ta raka ni na kama hotel sai da taga nayi settling sannan tayi min sallama ta tafi
Kashegari da wuri mimma ta zo ta kawo ɗan abinda baza a rasa ba na jinya na riga ta zuwa don ni da sassafe na zo, wata takarda ta bani wai idan aliyu ya warke in bashi
Hannuna yana rawa na karɓa idona taf da hawaye na faɗa mata abinda tj yace murmushi tayi “ba komai duk abinda ya kamata ayi za ayi” ta faɗa tana shigewa office ɗin ɗr. ɗin
Jimawa kaɗan sai gata ta fito idon ta cike da ƙwalla binta nayi na riƙe ta mimma lfy
“wai dr.yace my heart is weak ba za a iya bawa aliyu ba he need a strong heart” kuka ta fashe da shi babu abinda nake yi sai hamdala don nasan mijina ba zai so ya rayu da zuciyar mmn shi ba
Tj be ƙaraso ba sai dare asibitin ya wuto direct, nan ya samu halin da ɗan uwansa yake ciki shima keɓewa yayi da dr. yace wai a cire tasa a sawa aliyun tooooo????????????
Shima dr. ɗin yace ba za a cire tasa ba don he is very healthy kuma basa cire zuciyar lafiyayyen mutum su sawa mara lfy don ba shi da 100% na surviving bayan opperation ɗin, sukan fison zuciyar mutumin da yayi accident kuma aka fidda ran shi amma mutumin da yake da rai basa wannan gangancin
Sai alkcn na fahinci kenan hakan ne amma yayi wa mimma ƙarya, cakumar wuyar rigar shi mimma tayi tace
“ka cire min zuciyar da ke jikina ka sawa ɗana gwanda in mutu shi ya rayu, bazan iya rayuwa babu shiba pls pls pls” sai ta sa kuka
dr ɗin ya basu haƙuri tare da cewar ai samun zuciya ba wani abun bane kullum sai an mutu don haka kawai suje donation office su cike form the earlier the better
Tj ya faɗa masa cewar “mu musulmai ne zamu fi buƙatar zuciyar musulmi”
“dont worry if u r lucky u can find a muslin dying” ya faɗa yana fita
Donation dept ɗin muka je muka cike form, sannan suka ce mana muje idan an samu za a yi mana magana, da daddare bayan mun fito daga asibitin muka wuce manchester muka ɗauko yaran anan nake faɗawa junior abinda ya samu aliyun ya tausaya mana sosai sannan yace akwai abokin sa a nan asibitin manchestan zai yi masa magana ko za a samu zuciyar”
Godiya mukai masa sosai sannan muka fito da yaran, mama na kira na faɗa mata halin da aliyun yake ciki har da kukan mama, na ce mata zan turo su amina can har da su haidar su zauna a wajen ta har sai abinda hali yayi
A ranar su haidar su kar england kuka kawai nakeyi ina tausayin ƴaƴa na yanzu idan aka ce ba uban su ya zasu yi duk da de dukiyar da aliyu ya tara tafi ƙarfin ace ta ƙare nan kusa ko da juyata akeyi amma kuma uba kuma faaa Allah ka tashi mijina kasa a samu zuciyar nan
a daren muka koma liverpool ɗin, muka koma da sassafe muka je asibitin muna zuwa akai mana albishirin an samu zuciya murna kamar me amma kuma ba ta musulmi bace, nan fa murna ta koma ciki
*****************
yau kusan watan mu biyu a asibitin aliyu yana dai kwance a gaskiya innace a kwanciyar mu ba a samu zuciya ba nayi ƙarya don har wani aka kawo shima da irin matsalar aliyu amma ana samun zuciya aka biya aka yi masa dashen tunda shi kafiri ne, zuciyar musulmi tayi wuya sosai kasancewar ba garin musulmai bane
Kuma da in bari a sawa mijina zuciyar wanda ba musulmi ba gwanda in barshi a haka ƙia yanzu idan ya mutu ya wuce aljanna wacce haka muke fata amma idan aka saka masa ta kafiri fa ya zo yana kafirci bayan shekaru ɗari ya mutu ya shiga wuta fa ai ba ƙaunar sa nake yi ba
Tj da mimma sun so a saka masa kowacce ce amma ni na dage akan bazan yadda ba, bawai ba sa ƙaunar sa ba amma suna tuananin yadda zasu ne idan baya nan, mimma tana ganin Allah ya haɗa ta da ɗanta don haka bazabta bar shi ya mutu ba shi kuma tj yana ganin ba zai iya ba in babu ɗan uwan sa, inda na biye musu da tuni anyi aliyu aikin nan amma naƙi, naga gabaki ɗayan su hankalin su ba a jikin su ba don haka ni kuma sai na zama jaruma dole a cikin mu a samu jarumin in ba haka ba sai yadda hali yayi
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:53????
Bayan zaman asibitin ya ishi dr. ɗin aliyu ya ga babu wani cigaba ganin munƙi yadda da kowane zuciya indai ba ta musulmi ba, dr. yai mamaki sosai wai ne yasa bama son kowace zuciya, nai masa bayani zuciya ita ce mutum hadisi ne guda da ma’aiki saw yake cewa “akwai wata tsoka a jikin ɗan adan idan ta gyaru komai na jikin sa ya gyaru idan kuma ta ɓaci komai na jikin sa ya ɓaci” idan kuwa haka ne don me zan bari a sawa mijina zuciyar kafiri, bayan wnnan tsokar da ma’aiki (saw) yake magana ba kowacce bace face zuciyar ɗan adam
Don me zan bari a sawa mijina zuciyar da take ba a gyare ba, ko kaɗan dr. be fahimta ba, a zuciyata nace tayaya zaka fahimta tunda ba imani gare ka ba
“to yanzu zaku so kuga ɗan wanku ya mutu bayan ga zuciya,” murmushi nayi tare da gyaɗa kaina
“in dai har haka ƙaddarar sa tace zan barshi ya mutu a matsayin sa na musulmi zan fi son haka akan in bari a saka masa zuciyar kafiri”
Sam dr. kasa fahimtar mu yayi don haka sai ya kawo mana shawarar mu canzawa aliyu asibiti wai akwai wani dr. Shima cardiologist ne tare sukai karatu kuma musulmi ne a ƙasar musulmai yake mu koma can ko Allah zai sa mudace amma zaman da mukr yi anan kamar zaman jiran mutuwar sa muke tun da babu wani hope
Nayi murna sosai ko ba komai akwai chances ƙila aliyu ya samu zuciya, a saudiyya cardialogist ɗin yake dr. ɗin namu yai masa magana tare da tura masa duk wani halin da aliyu yake ciki, ƙasancewar aikin sa ne nan da nan yace mu taho
Ƴ
Muka fara shirye shiryen komawa saudiyya, garin ta’if da ke ƙasar saudiyya anan asibitin yake, akan babban titin shiga garin yake kafin ma ka shiga cikin gari, ƙaton asibiti ne, wanda kamar branch ne na asibitin amri hospitals wani asibitin aikin zuciyane a india