DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kana ƙarasowa zaka ga sunan asibitin wato *amri hospitals (annex)* muka shiga da shi wanda tun daga airport ɗin jidda ambulance taje ta ɗauko kasancewar aliyu bazai iya ci gaba da numfashi ba in dai babu oxygen don haka dole ne sai da medical practitioner kusa, duk da dai mimma pediatric ce amma ba za ayi bata kulawa da shi ba kasancewar mahaifiyar sa ce 



 Muna shiga da shi aka shiga da shi theater again don sai sun sake duba shi, sun daɗe don kusan awan su takwas da shi a theater inda daga ƙarshe suka fito 



Binsu mukai gabaɗayan mu inda muka damu dr. Hisham shi kaɗai a office ɗin sa, wurin zama ya nuna mana muka zauna sannan shima ya zauna tare  da ɗauko file ɗin aliyu

“a binciken da muka yi ya nuna aliyu is in a critical condition, ya buƙatar urgent heart transplant, don haka dole muyi yadda zamuyi don samun zuciyar don kuwa nan da 2weeks in bai samu zuciyar ba komai ze iya faruwa”

Ya faɗa da confidence a tattare da shi, shiru kawai mukai dukan mu, mun rasa ma me yin magana a cikin mu wai sati biyu, nice ma nayi ƙoƙarin yin magana
“yanzu kana ganin nan da sati biyun zamu iya samun zuciyar”
“ya dangan ta, amma akwai chances na za a asamu tunda kullum mutuwa ake yi a duniya, in shaa Allah yau na daka team akan su ne mo mana zuciya a kowane asibitin in shaa Allah za a samu”

Anan ma sai da mimma tace a saka masa zuciyar ta dr. Hisaham dariya yayi, yace mata mu musulmai ne wannan abinda ya samu ɗan uwan naku ƙaddara ce, ba abinda ya kamata da ya wuce muyi masa adduar Allah ya bashi lfy,

Amma ina kuka taɓa ganin an cire zuciyar lafiyayye don a sawa mara lafiyar da chances na survival ɗin sa is not stable, ku bari kawai mu duba yadda muka saba ba yau na fara wannan aikin ba, kuma in shaa Allah zai warke, ɗan uwanku bashi da wata matsala da ta wuce ta zuciyar sa mun duba duka organs ɗin jikin sa they are ok and fit don haka daga anyi transplant ɗin in shaa Allah shike nan”

Allah ya sa muka ansa baki ɗaya sannan dr. Hisham ya sallame mu,aka fara neman zuciya

 Kullum sa rai muke yi ko zamuji an damu zuciya abin takaici yawancin mutanen da ake kawo wa zuciyoyin na da matsala, ko ace hayaƙin taba yayi wa zuciyar illa ko kuma dai wani matsala na daban ga kuma lkc kullum ƙara wucewa yake yi



Kuma jikin aliyu a kullum ƙara tsanan ta yake, inda dr. Hisham yake shaida mana cewar da lkc ya cika zai cire wa aliyu abinda yake taimaka maka bugun zuciyar, don shima yana da lkcn expiring

Ko kaɗan kasa fahimta nayi sai na tanbayeshi to idan ka cire masa kuma yaya zai yi, shiru likitan yayi sannan yace
“shi wannan abun da kike gani akwai lkcn da yake aiki, idan zuciyata ta kai certain point na weakness to barin abun a jikin mutum ya fi cire shi haɗari, don me makon ta taimaka masa sai ta kashe shi so gwanda a cire in dai har lkcn ya yi”
“to in aka cire kana ganin zai daɗe har mu damu zuciyar”
“a yadda zuciyar mijinki take yanzu in aka cire masa zai iya yin awa sha shida, amma daga nan sai yadda hali yayi bazan muku guarantine zai ci gaba daga nan ba” shiri kawai nayi ni yanzu ma bana kuka idan naji halin da ake tunanin mijina nan gaba don kullum sai ka ƙara jin wani matsalar

 Yau ana saura kwana biyu appointment date ɗin cirewa aliyu abinda yake sa shi bugun zuciya yayi, ya tashi tun da muka zo saudiyya sai yanzu ya farka, yayi fari ya wani ɗashe kamar ba shi ba 

Zuwa nayi kusa da shi na tashe shi a daidai lkcn tj da mimma suka shigo don sunje neman zuciya amma daga ganin fuskokin su an san ba a dace ba

"ɗan uwa ka farka"

“gyaɗa masa kansa yayi amma be ce komai ba” kira likita mukai yi ko za a iya bashi wani abun yaci, amma likitan yace kar a bashi komai nurses ɗin su zasu masa preparing abinda zai ci

Aliyu ya gyara zaman sa sosai inda mimma ta zauna kusa da shi tare da dafa shi ya kalle ta yayi murmushi nayi mamakin da ya canza na ɗauka idan ya farka ya ganta zai haukace amma sai na ga saɓanin hakan 

“pls ki yafe min da duk abinda nayi miki……………….” bata bari ya ƙarasa ba ta rufe masa bakinsa, ta fara kuka tana bashi haƙurin itace ya kamata ta roƙi gafarar sa

Nima sai suka bani tausayi, aliyu sai ya fara barin wai wasiyya……………. Hmmmm babbar magana

“tj don Allah idan na mutu ka auri zainab ka riƙe min ƴaƴa na” ya juyo gare ni
“naso ace na zama uba da miji da jigo gare ku ke da ƴaƴa na amma ban ga hakan na shirin faruwa ba don Allah ki kular min da ƴaƴa na kuma ga ɗan uwanan ki aure shi shi kaɗai ne zai iya kular min da ku” kuka ne ya kwace min inda tj ya matso har kusa da aliyun sannan yace

“ni ban karɓi wannan amanar taka ba idan zaka tashi ka kula da iyalinka ka tashi idan kuma baza ka tashi ba shike nan ni dai ban karɓi wannan amanar ba” yana gama faɗin hakan ya fice sosai na ga alamar kuka a tattarebda shi daga gani baya son yi ne a gaban mu

Mimma da bata san abinda yake faruwa ba ta tambayeni na faɗa mata ita ma kukan take yi
“haba ya za ka faɗi haka na rayu akan rashin sanin kana raye yanzu na ganka kace kuma zaka kuma barina, tayaya kake shirin inyi iya rayuwa babu kai, ada ina da ƙuruciya shi yasa na iya jurewa amma yanzu i cant do wihtout u”

Kuka duk muka sa inda aliyun yake ƙara jaddawa mimma ta kular masa da mu ita kuma tana girgiza kai, muna cikin wannan halin ne zuciyar aliyun ta kuma motsawa wayyo Allah dai kun tausaya masa yadda yake yi gaba ki ɗaya lkc ɗaya ya fita hayyaci sa switch ɗin da ke kusa da gadon sa na danna nan da nan sai ga likitoci sun danno suna zuwa kora mu waje sannan suka fara aikin sun babu kama hannun yaro 

Fitar mu ke da wuya sai ga wata mata ta shigo tana rusa ihu wai a taimaka mata ihu take yi iya ƙarfin ta, nurses ɗin asibitin ne suka fito da gudu sai ga shi an shigo da wani akan wheelchair duk jikin sa jini barin ma kansa an ɗaure kan da wani ƙaton bandage amma duk da haka jinin zuba yake, theater aka wuce da shi directly

Basu jima ba sai ga dr.hisham ya fito daga theater room ya doso wajen matar, da larabci naji yana mata magana don haka ban ganr me yake cewa sai kukan ta kawai na kuma ji sai ta bani tausayi

  Lallashin ta ya dinga yi sannan ya ce wata nurse ta kawo masa file matar ta sa hannu ko da aka kawo file ɗin mema kon matar ta sa hannu sai kawai ta fara ihu tare da tsalle kamar ana dukan ta 

Abin ya bani mamaki ban gama mamaki ba sai ga dr.hisham ya zo wajen mu
“mr aliyu kinga waccr matar da take kuka” gyaɗa masa kai nayi,
“ɗanta mutuwa zai yi nan da yen mintina don haka naso ta sa hannu a cire zuciyar sa idan ya mutu kafin zuciyar ta daina bugawa amma kamar bata fahinta ba amatsayinki na mace ko za ki iya yi mata magana aka……………

Be gama bayanin nasa ba na warce file ɗin nayi wajen matar me ihu, sai da na fara lallashin ta da turanci kasancewar tana ji dai da naga zuciyarta ta nutsa sannan nayi mata maganar signing

Aikuwa kamar na kuma tursasata sai ta kuma zunduma uwar ƙara wai za a kashe mata ɗa ne, babu yadda ban yi ba, tun ina yi ni kaɗai sai ga mimma ma ta shigo taji halin da ake ciki

Mimma har durƙusawa matar nan tayi akan ta sa hannu amma matar nan ƙiri ƙiri ta shafe wa idon ta rashin M, da anyi mata maganar sai ihu

Tun likitocin suna tausaya mata har suka gane bata son bayar wa ne, wani dr. ne ya fito daga theater room ya zo yayi wa dr.hisham magana a kunne nan da nan naga hankalin dr. Hisham ɗin ya tashi

Karɓar file ɗin yayi yaje kanshi tsaye yace mata ɗan ta ya mutu ɗin hakabta sa hannu a cire zuciyar tasa, wallahi matar nan sai ta fara abu kamar me bori, tana ihu tana tumuwa a ƙasa tana abu kamar na mahaukaciya

Ɗaga ta nayi ina kuka ina cemata don Allah ta dubi girman Allah ta bamu zuciyar nan ko bata bamu don komai ba ta dubi cikin da ke jikina ta ba mijina zuciyar ɗan ta ko na haihu abinda zan haifa ya ga uban sa amma matar nan ƙiri ƙiri ta ƙi

Can zuwa anjima sai ga wannan dr. ɗin ya kuma fitowa ya kuma faɗawa ɗr.hisham magana again a kunnen sa, kawai sai naji dr.hisham ya ce mata
“zuciyar ɗanki ta daina harbawa i hope u are happy 4 not helping those in need” wulla mata takardar yayi a fuskarta yayi gaba

Zama nayi a gaban matar nan ina kallon ta ina kuka ita ma mimma haka dai naji kamar wannan itace damar mu ta ƙarshe amma matar nan ta nuna rashin imani a tattare da ita

Tashi nayi da naji dr.hisham da wasu likitocin suna guje gujen shiga ɗakin aliyu don na’urar dake ɗakin sa ce take alarming ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit ɗit alamar danger muna zuwa kusa da ɗakin aka dakatar da mu

Kuka kawai nake yi sun jima sosai sai ga su sun fito inda dr.hisham ya buƙaci ganin mu, muka bishi office ɗinsa, sai daya zauna sannan ya fara magana

"a bisa binciken da mukayi mun gano cewar gaskiya aliyu inbai samu theater nan a yau ba in shaa Allah gobe zamu cire masa duk wani ƙarfe na jikinsa don yanzu a haka ma they not helping him, but hurting him don haka in shaa Allah gobe da ƙarfe 12:00 na safe zamu cire daga nan kuma sai yacce hali yayi" kasa kuka nayi don nasan bashi da amfani 


 "dr. ya shi aliyun yake"

“well am sorry to say he is not helping at all, zan iya faɗa muku a halin yanzu aliyu is not fighting 4 his life he has already given up, don haka yanzu kawai sai yadda hali yayi, kunsan wataran idan mutum yana da burin ya rayu to sosai yaka taimakawa likita amma aliyi yanzu ko kaɗan baya taimaka ya riga ya losing hope na rayuwa don haka sai haƙuri”

Jikina a sanyaye na fito daga ɗakin, directly ɗakin aliyu na nufa ina kallon sa gobe iyanzu bamu da tabbacin kana raye ko ka mutu ko na faɗa,

Ko da tj ya dawo da daddare mimma ce ta iya faɗa masa kasa cewa komai yayi sai hawaye kawai, kasancewar bama kwana a asibitin yasa da dare yayi tj da ƙyar ya lallashe mu muka tafi ni da mimma

Tunda muka je ɗakin da muka kama na hotel sai muka kasa duk muka zauna mukai jugum jugum nice ma na gaji daga ƙarshe na tashi na ɗauro alwala na fara gabatar da sallah don in roƙi Allah ya kawo mana sauƙi a wannan lamarin, ita ma mimma sai ta bini ta fara sallahr

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Leave a Reply

Back to top button