DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

kuka wiwi tj yake yana tausaya wa kan sa da ƴar sa islam nima ina taya shi mimma ce ta lallashe shi sannan tace sa ya tashi ya kama hanya Allah yasa ya samu jirgin da zashi nigeria a ranar 

har bakin asibitin muka rako shi mukai sallama tare da ƙara yi masa ta’aziyya har ya tafi sai ya dawo
“don Allah kar ku gaya wa ɗan uwa salma ta rasu ku bari idan ya warke sai a faɗa masa”

gyaɗa kaina nayi nima dama hakan naso yi muka ƙara sallama ya kama hanya babu abinda zamuve sai dai muce Allah ya jiƙan musulmai baki ɗaya
[7:46PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

Page:55????

ina murna sannan da ban godiya ga mmn farida da ta kammala littafin ta samun wuri duk da dai da sannu sannu aka tafi amma dai an kai ƙarshe babu abin da zamu ce sai Allah ya ƙara basira

 *Sannan ina miki murna da fara sabon littafin ki faccala da fa'iza ƴar baba, Allah ya bada ikon gamawa lfy sannan da fatan ba za ai mana tafiyar hawainiya* ???????????????? 

Ko da aliyu ya farka ya tambayi tj sai nace masa ya tafi nigeria, ya nuna jin daɗin sa da matar ɗan uwan sa zata haihu har da addu!ar Allah ya sauke ta lfy na amsa da amin

Sai da tj ya sauka lfy sannan ya kira ni na ƙara yi masa gaisuwa tare da tambayar abinda aka samu sai yace min bata ma haihu ba Allah ya karɓi abar sa, wayyo na tausaya masa sosai

Ya tambayi jikin aliyu na ce masa da sauƙi yana ma ta tambayar sa, yai masa fatan samun lfy sannan mukai sallama

Aliyu ne ya matsa min na kira tj yayi masa ta’aziyyar ɗan kasancewar na faɗa masa ɗan be zo da rai ba amma ban faɗa masa rasuwar salmar ba don yanzu neman hanyar da zuciyar da aka dasa masa ta warke muke yi

 Aliyu yana da sati 3 a asibitin na tashi da naƙuda anan asibitin Allah ya sauke ni lfy na samu saurayi na kyakkyawa fari tas da shi duk yafi ƴaƴa na fari har shi ma aliyun ya fi shi haske 

Mimma da aliyu sukai murna da wannan ƙaruwar da muka samu a donga waya ina faɗawa mutane ƙaruwar da muka samu, aliyu ne ya kira tj ya faɗa masa, tj yai masa murna da kuma alƙawarin zai zo

Ko da ranar suna ta zagayo aka saka wa ɗana suna yahya sunan wanda ya bawa aliyu zuciya mimma ce ta ce a saka sunan nima da aka faɗa min sai naga dacewar hakan don babu abinda zamu iya ce masa sai dai muce Allah ya jiƙan sa

  Watan aliyu biyu aka sallame mu, muka koma makka inda dangin mimma suke ta gabatar da da aliyu a matsayin ɗanta da aka ce mata ya ɓata, da ni kuma a matsayin matar sa 

Sun sha koke koke sun kana gada ƙarshe aka kaimu masauƙin mu, dangin mimma babban dangin ne sosai a cikin garin makka, mun zazzaga su kana daga bisani muka koma ainihin gidan mimma wanda ta gada a wajen mahaifin ta

Sai da na kusan arba'in sannan tj ya zo duk ya rame kamar ba shi ba sai a lkcn ya sanar da aliyun mutuwar salma, kuka ne kawai aliyun be yi na tausayawa ɗan uwansa da yayi tare da kuma ƴar ta da ta bari 

Sai da tj ya nutsu ne sannan aliyu yace masa yana son ya raka shi gidan ummu yahya zai mata godiya, tj ma ya yadda da hakan don haka sai muka fara shirin zuwa madina gurin ummu yahya,

Da sassafe muka shirya muka kama hanyar madina, bamu isa ba sai azahar don haka directly masallaci muka wuce inda tj ya tafi kama mana hotel

 Sai da muka sallaci isha'i sannan muka koma hotel ɗin da aka ka mana wanda bashi da nisa da haram ɗin, wanka nayi kawai na hau gado sai bacci, ina jin aliyi ya shigo yana min mitar 

“matar nan tun da akai min aikin nan na fahimci gudu na kike yi yanzu ma dana gama budgeting in mun zo madina muyi honey moon shine kafin ma in shigo har kin yi bacci ko”

Ban kula shi ba bacci na kawai na cigaba da yi don bacci ne sosai a kai na, kyakkyawar runguma naji yayi sannan shima baccin ya kwashe shi

Kashegari sai da azahar sannan muka koma harami sai da mukai la'asar sannan muka fito don zuwa gidan ummu yahya, wani kanti muka fara tsayawa tj yai musu siyayya sannan muka kama hanyar gidan, ɗan tafiya ne babu laifi sannan muka zo, inda mukai parking mota muka fito, gangarwa za a yi a shiga wani lungu don haka sai tafiyar ƙafa

Su aliyu suka samu wasu yaran suka ɗau musu kayan sannan muka kama hanya, gida na uku a layin muka tsaya inda tj ya ce mu shiga ni da mimma muyi musu magana

Ƙwanƙwasa ɗan ƙyauren gida mukai, wata ƴar dattijuwa ta zo ta buɗe da fara'ar ta, muka gaisa sannan tace bata gane mu ba, tj ne ya matso ko da ta ganshi sai ta ɗan tsorata don ta san bata nuna masa gidan ba 

Hanya ta buɗe mana muka shiga gidan, ɗan ƙaramin gida da ɗan tsakar gida sai ɗakuna guda uku da banɗaki ɗaya da kitchen a cikin gida sai kuma uban shirgi daga wani lungu can ƙarshen gidan

Ɗakin farko tai mana izinin mu shiga, muka shiga da sallama, babu komai a ciki sai dadduma sai tv akan tv stand ɗinta da wani yaro yana zaune yana kallon cartoon 



Ko da muka shiga yaron kawai bin mu yayi da kallo tj ne yace 

“al amin ta’al” da ɗan gudun sa ya taho ya faɗa jikin tj yana dariya tare da ce masa abbu,

"ɗan yahya ne wannan" inji tj, wayyo Allah na sai naji tausayin yaron har ƙwalla ta cika min ido, aliyu ne ya miƙa hannu ya ɗauke be ƙiba shi ma aliyun sai al amin ya kira shi da abbu

A daidai lkcn ummu yahya ta shigo da tray da lemu da ruwa akai inda naji tana yi al amin larabci, mimma ce ta tanka mata, inda daga baya mimma take faɗa mana wai ummu yahya tace al amin kar ya ƙara kiran mutane da abbun sa ba ta faɗa masa abbun sa yayi tafiya ba

Aliyu ne ya gyara zama sannan ya kalli ummu yahya ya tambayeta tana jin turanci, da murmushin ta ta gyɗa kai

“daga yanzu nine abbun yaron nan, don zuciyar abbun sa a jikina don haka babu abinda ya baban tani da abbun sa, baƙi idan kin ce masa kar ya kira wasu da abbun sa ba amma ni abbun sa ne”

Hawaye taf ya cika a idon ummu yahya inda take faɗa mana tunda mahaifin yaron nan ya rasu duk wanda ya gani sai ya kira da abbun sa

“to kar ka samu damuwa ga abbun ka ya dawo kaji al amin” aliyu ya faɗa yana shafa kan yaron kamar al amin ɗin yana ji

 Tj ne ya ɗan tambayi matar yahya inda ummu yahya tace tana wajen aiki,

“aiki kuma, ai bata fita takaba ba”
“addini ya halatta mace ta nemi abinda zata rufa wa kan ta asiri koda tana takaba” ummu yahya ta faɗa

Haka ne amma ummu yahya ina dangin ku” inji mimma, sai da ummu yahya ta ɗan nutsa sosai sannan ta fara magana

” mu mutanen syria ne yau shekarar mu uku kenan a nan yaƙi ne ya koro mu daga syria, inda muka rasa duk wani dangi namu a cikin yaƙin yayana wanda ya kasance mahaifin nadia matar yahya kenan da matar sa da ƴaƴan sa, a gabana aka harbe su ina laɓe ya hana ni fito wa

Mijina uban yahya shima aka kashe shi a kan idon na don haka sai mukai ƙaura da ni da yahya da nadia muka taho da taimakon wani ɗan uwan mahaifiyar nadia wanda yakan sance yana taimakawa mutane suna tsira daga tashin hankalin nan

Tunda muka zo nan na ɗaura wa yahya da nadia aure don bana son in tafi in barsu su kaɗai ba tare da aure ba amma kunga inda aure a tsakanin su bazan ji komai don Allah ya ɗauki raina ba nasan na bar su a matsayin ma'aurata" ta daka ta 



"daga yanzu ni zan ci gaba da kula da ku ni zan maye gurbin yahya in shaa Allah" inji aliyu 

ummu yahya ƙi tayi sai da su mimma suka ba ki sannan ta yadda har da kukan ta,mimma ce ta ɗauki baby yahya wanda muke kila da mu’allim ta bawa ummu yahya

“ga yahya mun kuma samu, matar aliyu ta haifa” da hawaye a idon ta ta karɓe shi tayi kissing ɗin shi sannan ta rungume shi,

mun jima acan inda aliyu da tj  suka fita suka barmu 



ni nayi wa ummu yahya girki, sai kusan shida sannan nadia ta dawo, mun gaisa sosai da inda inda ummu yahya tayi mata bayanin mu muƙa ɗan taɓa yar hira sannan su aliyu suka zo muka tafi 




  Satin mu biyu muka koma nigeria mimma ma nigeria ta bimu, ashe ta kashe auren ta bamu sani ba wai dama rashin aliyu ne yasa ta zaman auren amma yanzu taga ɗan ta baza kuma rayuwa babu shi kusa da ita ba 

Bamu daɗe da komawa ba su mama suka zo da su maryam suka zo duba aliyu, inda aka dawo da su haidar

Ko da suka tashi tafiya sai aliyu yace amina ta zauna, mama taji daɗi sosai da aliyi yace zai riƙe amina, ko da suka tashi tafiya aliyi yayi musu kyauta sannan ya kuma tuna musu da tafiyar su hajjin su

Aliyu ya ɗora tj akan kula da su ummu yahya, komai suke so da komai na al amin tj ɗin yayi musu

Nima naje kano nayi wa ƴen uwan salma gaisuwa tare da ɗauko islam ta dawo hannun na don naga sai pasin pasin akeyi da ita tj yaji daɗi sosai aliyu ma ya dawo da tj aiki nan kusa da mu a abuja inda ya gina musu gida kusa da juna shi da mimma wanda yake ƙasan jikin namu

Kowannen gida part biyu akai masa mimma tayi ta mita wai ita gidan da aka gina mata yai mata girma sosai don haka sai aliyu ya bata haidar da mohd su koma wajen ta duk da haka gidan part ɗaya kawai take anfani da shi

lkcn tafiyar hajji yayi su mama suka tafi mu kuma muka bi ta international muka je hajji ban ma san dani za ayi ba mun yi aikin hajji lfy mun gama sannan muka dawo, muka je madina domin gaisawa da ummu yahya
[7:47PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: [12/7, 7:20 PM] Mmn Waleed????: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

Page:56????

*last page in shaa Allah tank u sooo much 4 ur support babu abinda zance sai shukran gare ku masoyan dangin sa yau Allah ya kawo ƙarshen littafin da fatan kun ji daɗin sa*

ina fatan zaku saurare ni a sabon littafina me sunan
???????? RABO NACE????????????

*ana mugun tare*????

[12/7, 7:20 PM] Mmn Waleed????: Mun je gidan ummu yahya inda muka same babu lfy sosai amma kuma tace an sallame ta ne ma daga asibiti, aliyu yai ta faɗan tj be faɗa masa amma sai ummu yahya tace ai shima be sani ba itace ta faɗawa nadia kar ta faɗa don kar hankalin wani ya tashi

Karɓar mu’allim yahya tayi a hannuna tana shinshinashi tare da sunbatar sa ina iya hango wasu hawaye a idon ta amma si tayi koƙarin mai da su nima sai nayi kamar ban gani ba

Aliyi ne ya matsa kusa da ita
“ummu yanzu kema fa uwa ce gare ni don me zakice kar a faɗa mana ciwon ko gaskiya ban ji daɗi ba”

Haƙuri ta dinga bashi, muka tambayi nadia da al amin ummu yahya tace sun je kasuwa don kuwa nadia ta fita takaba, mun ɗan jima sai ga nadia ita ma aliyu yai mata faɗan cewar kar ummu ta ƙara ciwo bata kira shi ko tj ta faɗa ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Leave a Reply

Back to top button