
tun ina kuka da roƙon a sanyaye har na fara zunduma ihu za a kashe ni a jirgi kasancewar private plane ɗinsa ne yasa ba mutane sosai muna ƙara dosa jirgin naganshi wani tanƙameme da shi da zuciyata ta buga sai na wani luuuuu zan faɗi ni ban yadda ba na suma cak naji ɗaya daga cikin matan ta ɗagani sama ta ci gaba da tafiya ganin suman nawa na ƙarya bazai min ba yasa ni na wani miƙa sai gani sauran kaɗan in suntumu a ƙasa da saurin ta ta taro ni suka ƙara riƙe ni ita da ɗaya
a matattakalar benen hawa jirgin ma sai da akayi artabu da ni inda daga ƙarshe de sai ɗaukata akayi ina ihu iya ƙarfina, ko da muka shiga jirgin sai na nutsu don gani nake yi kamar idan nace zanyi kokawar sai in ruguza jirgin cikin jirgin ya sha kujeru na aƙfarma har wani bar ne acikin sa inda ake jera lemuka kala, kamar falon wani hamshaƙin me kuɗi sam beyi kama da cikin jirgi tunda a film mun saba gani cikin jirgi kujerunsa a jere suke kamar a class wannan kuwa a zagaye yake kamar kana falo tsayawa nayi kawai ina kallo amma yanzu ba lkcn ƙarewa cikin nan
zaunar dani matar tayi ta ɗaura min belt sannan tayi gaba, ɗan takari ne naga ya fito daga wata ƙofa a jirgin ya doso ni yana murmushi duk da firgice nake amma hakan bai hanani gani kyan da yayi ba
“naga alamar kina tsoron shiga jirgi ko, to da fatan dai baza ki kayar mana da jirgi ba da kokawar nan taki ba idan mun tashi” zare ido nayi alamar tsoro ne tattare da ni, murmushi naga yayi sannan ya juya ya wuce tunda na zauna bani na tashiba har sai da muka sauka ko ƙwaƙƙwaran motsi bana yi don kar in kada jirgin sukuwa sai wani kaiwa da kawowa suke yi ko a jikin su
kasancewar na gama tsorata yasa ko da muka sauka ban wani yi taurin kai ko ma dai ina za a kaini yanzu munyi nisa da gida kokawa ya ƙare,
mota ɗaya aka kuma samu da ɗan takari wannan karan ko kallan inda yake banyi ba har muka isa masaukin mu, fitowa nayi nan ma na bi bayan matan inda muka doshi wani tafkeken gini kamar ba mutun ne ya gina shi ba
door bell ta danna inda wata mata again ta buɗe suka gaisa sannan ta nuna mata ni tai wuce warta ni kuma na tusa kaina ciki
tsayawa faɗin tsaruwar falon nan ƙauyanci, tafkekene na faɗa inda aka sa ma kujeru kusa set 7 a kowane angel inda ba wata kujera da take kusa da ƴar uwarta ga ƙofofi nan barkatai ba iyaka
tafiya mukayi muka ɗan wuwwuce wurare da dama kafin mu zo wata takekiyar kofa buɗewa tayi inda turaren da aka sa ya doki hancina na lumshe ido don tsabar ƙamshin sa ɗaki ne pink komansa pink ne gado, kwaba komai dai na ɗakin pink ne
come in naji tace binta nayi har ciki ta buɗe wata ƙofa nan ma muka shiga sai na banɗakine tafkeke shima ba abinda babushia kamar ɗakin komansa pink ne
wani tafkeken Jacuzzi tub ne a tsakiyar toilet ɗin da girman sa wanda ya gani cike yake da ruwa da red flowers da aka watsa a cikin ruwan sai wsu ƴammata da suka kewaye ruwa su shida ko wacce da uniform a jikin ta
bath her” kawai naji tace, kut tana nufin su min wanka yau fa ake yinta na faɗa araina ruƙunƙume jiki na nayi sai gasu gaba ɗaya sun doso ni kamar wasu karnuka kokawar cire kayan muka dinga inda daga ƙarshe wacce ka ta kawoni tace su ƙyaleni
ko da suka sake ni da murmushinta ta matso kusa da ni
“madam they r going to help u take a bath nothing more”
“no i can bath my self i have being taking my bath since when i was born” dariya tayi
“indeed” ni nama manta ashe sai mutun ya girma yake fara yiwa kaansa wanka
“ok here’s how we will do it they will help u nd u Will do d rest okey” gyaɗa mata kai nayi
wani towel ta bani na cire kayan jikina na ɗaiur shi sannan na shiga cikin jacuzzi ɗin ruwan yai daɗi dai dai yanayi, fara massaging ɗina sukayi
wayyo me kwance min kai tanayi me gyaramin ƙafa tanayi me min gyaran hannu kowacce dai ta kama aikin da ta ƙware akai, mun kusan awa anayi min gyaran jiki ga matsa da nake sha akai a kai sai da suka gama sannan suka canza min ruwa suka fita suka barni inyi wanka na
da ƙyar na iya wankan na fito don tsabar daɗin ruwan da nake ji ko da na fito daga toilet ɗin wasu saitin ƴanmatan na kuma gani masu irin uniform ɗin waɗancan suna jirana nan suka jani suka fara aikin su a kaina me gyaran gashi me kwalliya sai da suka ga nayi tsab da ni sannan suka ƙyale ni inda suka ɗauko min wata strapless armani gown na saka daa ganin rigar nan taci kuɗi nan na kalli kaina kamar wata tauraruwa haka na ganni na yi kyau sosai murmushi wanda ya kara min kyau sosai
jagora sukai min zuwa dining room don inyi breakfast sai lkcn na tuna ko break fast ban ba abinci aka shiga jera min kamar abin arziki na kai hannu zan buɗe kenan sai matar da ta karɓe ni tun bayan shigowata wato linda kenan naji ta doke min hannu da bulalar da ke hannun ta auch nace na juya na kalle ta tare da zubɓuro mata baki
sawa tayi ƴammatan da ke wajen suyi serving ɗina breakfast ikon Allah, wato ba wani abin arziki a cikin abin,
fruits ne kala kala akai masu wani irin decoration me kyau shi aka fara turo min, hannu na daga zan ɗauka nan ma naji bulalar Linda ƙwal a hannuna auch njena faɗa da ƙarfi tare da sosa wajen fork ta nuna min na ɗauka sama sama naci fruit ɗin don ni yunwa kawai nake ji ba kwaɗayi ba
ko
da na ture sai aka kawo min main breakfast ɗina aikin banza na faɗa araina ƙwai ne guda ɗaya jal aka soya wanda ba a kaɗa ba don kana iya ganin ƙwaduwar a tsakiyar sa, sai fatan wake shima baifi cokali biyu ba sai kuma, timatir wanda aka akayi slicing ɗinshi sa bread slice ɗaya, sai tea rabin kofin tangaran
kallan abincin nayi wanna idan na daddage gabaki ɗayan abincin zan kwaso su in musu loma ɗaya a lkc ɗaya amma wai shine breakfast kallan linda nayi inda tayi min nuni da fork nd knife tooo faaa yau ake yin ta wa ya iya cin wai abinci da fork da wuƙa
ɗauka nayi na fara ci bazan dai faɗa muku yanda na ci abincin ba amma na sha bulala ya fi a ƙirga ina gamawa aka kawo min soup na sha shi wannan bashi da matsala don da spoon kawai na sha bayan na gama ne tasa wasu ƴammata suma na daban su fita da ni nasha iska aikin banza mutun be ƙoshi ba amma an sa shi zagayawar dole tashi nayi na bisu ko ba komai na ga guri
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page: 9????
Mun sha zagaye sosai a cikin gidan inda ƙara ganin girman gidan, tanƙameme ne sosai garden suka kaini inda ya sha shuke shuke masu ƙayatarwa launi daban daban masu kyau da ƙamshi
ga table da kujerun sa daga gefe na zama sai swimming pool wanda kusan guda uku ne kowanne da shape ɗin da aka yi masa, can daga gefe kuma wani fountain ne da akayi masa shape ɗin tukunyar ƙasa inda ta saman ta ke zubar da ruwa cikin ta ƙasan, gurin yai kyau sosai
wuri na samu na zau a kan grass carpet ɗin daya zagaye ko ina yai kore shar da shi ga shi kuma yai lif lif da shi daga gani yana samun kulawa sosai
fruits aka kawo min da juice sai kuma ruwan roba ga snacks nan abin dai sai kace mutane goma ne zasu don tsabar yawan sa, wanda inda ace hankalin mutun a kwance yake sai kaci iya cin ka amma ya za ayi in zauna in ci bayan ban san dalilina na zuwa gidan na ba
kuka na saka me sauti sosai wanda ya janyo hankalin masu kula da wurin da ƴammatan da suka rako,
“madam do u need anything” naji wata tace
Abin takaici bama Hausawa ya haɗa ni zama da su ba ƙabilu ne, harara na doka mata
“where is ur oga” na faɗa in me shaƙar wuyan rigar ta
shaƙar da tajine yasa ta kakari wanda ya janyo hankalin mutane suka zo agajin ta, ko da aka ƙwace ta daga hannu sai na fara zunduma ihun
“take me to ur oga” shine kawai abinda nake faɗa ina ihu, ƙattin matan nan ne dai suka zo sukai ciki da ni sai ɗakin da aka sauke ni da farko garam naji an rufe ƙofar tare da sa key
zaman daɓaro kawai nayi a ƙasan ɗakin ina ci gaba da rafsar kuka na wanda ban san ranar denawa ba ƙila sai ya mayar da ni gida,
sai 1:30 sannan na tashi na gabatar da sallah azahar ban idar ba naji an buɗe ni linda ce
“is time 4 lunch ma’am” naji tace
kau da kaina nayi lunch ɗin banza da wofi bayan ba lallai bane su bani abinda nasa ci ba, ganin alamar bazan tashi bane yasa ta juyawa ta tafi, haka na zauna banci na rana ba haka ma da dare
wajen ƙarfe takwas da rabi sai sai ga linda
“time 4 ur bath” kallo bata ishe ni ba na ci gaba da kwanciyar da nake akan sallayata,
matsowa tayi kusa da ni kizo kiyi wanka don kiji daɗin bacci kuma acire miki wannan make up ɗin na fuskar ki, tayi ta banbamin ta ta gaji ta fita ta ja min ƙofar, wani sabon kuka na kuma saki a hankali wannan karon ina tunaningurin da nake kwanciya a gida wai yau nice a wannan kayataccen gidan amma sam ban san dalilina na zuwa wannan gidan ba
Ina tunanin na ban san lkcn da wani wahalallaen bacci ya kwashe ni ba, sai ƙarfe goman dare sannan na tashi inda naji cikina kamar an min satar kayan ciki
Gaba na ne ya bada dam kar dai mutanen sun kwashe min kayan ciki ne na faɗa ina yamutsa cikin, alamar yunwa naji atattare da cikin wanda hakan yasa na tuna cewar na daɗe rabona da abinci tun wanda na ɗan tsakura da safe
Sakkowa nayi daga gadon na murɗa kofar ɗakin inda na same ta a buɗe, buɗewa nayi na shiga ɗan corridor ɗin da zada ka da falon na tarar da falon nayi dining room ɗin, dining table ɗin tsap yake an goge shi kamar ba a taɓa cin abinci akan sa ba
kitchen ɗin na shige shima a gyare yake na samu wuri na tsaya ina kallon ikon Allah tun da nake ko a film ban taɓa gani tsaruwar kitchen irin wannan ba, shi kanshi gas ɗin saman shi glass ne ba bu wurin sa ashana tsayawa nayi ina ƙarewa gas ɗin kallo
*maxi flameless cooker* naga an rubuta wannan ya tabbatar min da irin gas din nan ne da ba a ganin wuta sai da kawai aita girki, danne danne na nayi tayi a jikin wurin da naga kamar nan ne wuri opperating ɗin gas ɗin har Allah ya taimake ni na kunna
Tukunya na ɗauko na ɗaura ruwa na dafa indomie ta wadda na gani a cikin store ɗin wanda don girman sa da kuma kayan abincin da ke ciki kai sai ka ɗauka wani kanti ne a singa
ina gamawa na kashe sannan na sauke tukunyata a ƙasa na zauna na daki abata juice na duba fridge na ɗauka na share na gode wa Allah, na koma store nayi guzurin snacks ɗina na ciki leda da cake na zuba aleda na kama hanyar ɗakina na adana kayana na kwanta sai bacci.
**********
Lagos
tun bayan da motocin da suka zo suka yi masa awon gaba da ƴarsa ya doka wa ƴen uwanta kira suka zo, haka aka taru ana ta jajanta masa inda in banda kuka ba abinda baba yake yi, su khadija da maryam ma kukan kawai suke yi
har wurin sakin hausawan lagos akaje amma babu abinda da zai iya yi musu kasncewar ba a san wanda yazo ya sace tan ba
haka suka dawo gida jiki a sanyaye suna mai roƙon Allah ya bayyana ta amma abin da mamaki har cikkn mutane azo a ɗauke maka ƴa Allah ya kyauta, masu faɗan alkhairi nayi masu faɗan sharri nayi don wasu har cewa sukai wai matar ajaban ce ta sa a sace ta
*************
ajaban resident
Yana zaune ya gama kallon ta ta camerar dake kitchen ɗin yadda ta dafa indomie ɗin, tun da linda tayi masa waya akn taƙi cin abinci sai yaji ba daɗi a ransa, ya kunna security cam ɗin dake ɗakin ta yana ƙare mata kallo da nazarinta daga ganinta tana jin yunwa dakiya ce kawai irin tata, sai kuma yaga ta tashi ya ɗauka guduwa zata yi sai yaga ta nufi kitchen wannan yasa ran shi nutsuwa wato yunwa take ji kenan,
ta camerar yake kallon yadda take cin indomie ɗin tata kamar tana cin wata duniya shi baiga meye abin daɗi a indomie ba abincin yara ko dayaga taje ta kwanta
bawai na kawo ki bane don in takura k na kawo ki ne don in tserar da ke daga sharrin mutane da wannan haniyar ta hotunan ta kwanta zan maida ke gaban iyayenki ya faɗa yana mai ƙare mata kallo, da sauri ya kashe don shaiɗan har ya fara masa kiɗa a kan sa
ko da safe da suka gayyace ta wanka bata ƙiba don tanasan matsan nan da ake mata a jikin ta, ta shiga akai mata wankan ta shirya da taimakon su amma da aka gayace ta cin abinci sai tace ta ƙoshi, babu yadda linda batayi ba daga ƙarshe da ta dameni ma sai na juya mata baya
“sai oganku yazo ya maidani gida sannan zanci abinci” na faɗa
ba yadda ta iya haka ta juya ta tafi tana fita na bita na kulle ƙofar leda ta naɗauko na zauna naci abuna na ƙoshi naje banɗaki na ɗaɗɗaki ruwana na gyara wajen na koma na kwanta
duka abinda yake faruwa akan idon sa da ƙin cin abincin nata da tace wa linda da cin snacks ɗin nata tana lumshe ido abinma sai ya dinga bashi dariya wai ita jaruma
ko daya fito zai tafi office ma’aikatan gidan suna ta kwasar gaisuwa yana ansa musu da fara’ar sa, aguje ya ga linda ta taho
“sir tun jiya madam bata ci abinci ba at dis moment zata iya suma fa” ta faɗa hanklinta a tashe
“dont worry linda ba abinda zai same ta”
tsayawa tayi tana kallon uban gidan nasu tasan mutun ne me tausayi amma ga mamakin ta wai yace a kyale wannan da mamaki har ya shiga mota sai taga yana kiran ta ƙarasawa tayi
“daga yanzu a dinga yin snacks different veriaties ana ajiyewa a kitchen musammamn da daddɗe bana son inga kitchen ɗin nan babu snacks da daddare kinji ni ko” ya faaɗa yana jan kunne sa gyaɗa kanta tayi alamar ta fahimta yana murmushi yace wa driver lets go
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????