DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kanta a ƙasa ta ansa, sai magariba sannan muka tashi tafiya sai ummu yahya tace
“Aliyu zamu koma syria ni da nadia da al amin mun gode sosai da ɗawainiyar da kake yi da mu”

Daga ni har shi ɗin bamu san lkcn da muka dawo ba daɓar haka na zauna a ƙasa
“ummu yahya syria me zakiyi a syria yanzu”

Murmushi tayi sannan tace
“bana son in mutu in bar nadia ita kaɗai sai wannan ɗan yaron shiyasa nake son maida ita cikin dangi, ko da de babu na kusa amma ai bazamu rasa dangi ba”

Kuka na saka mata
“don Allah ummu yahya karki koma syria ya za ai al amin ya tashi a syria a wannan tashin hankalin da ake fama da shi a syriar zaki kai yaron da bai son tashin hankali ba can, don Allah ummu yahya ku zauna anan”

Aliyu ne ya katse min maganata
“nima gaskiya hankalina be kwanta da zaman da kuke yi ku kaɗai anan ba, amma kuma syria ba gurin zuwa bane, me zai hana ku bimu nigeria sai ku zauna da mu tunda mun ruga mun zama ɗaya” aliyu ya faɗa

Kallon kallo muka tsaya muna yi inda daga ƙarshe ummu yahya tace ita bata yadda ba tunda take bata taɓa zama liability ba kuma in shaa Allah da tsufanta baza ta zama ba

Babu yadda bamu yi ba amma ummu yahya ta riga ta kafe sai sun koma syria haka muka tashi muka koma masauƙin mu ni dai zuciyata gabaɗaya bata kwanta min da tafiyar nan syria ba garin da kwata kwata basu da zaman lfy

Ko da muka zo kwanciya na so imu ƙara maganar amma sai aliyu ya hana ni yace da safe zai ƙara komawa wajen ta in shaa Allah

Da gari ya waye aliyu be samu damar zuwa gidan ummu yahya ba sai ni naje na same su suna ta haɗa kayan su wai ƙarshen watan nan zasu koma

Ɗaki na shiga kusa da ummu yahya na zauna akan tafiyar na cigaba da yi mata magiya amma sai tayi murmushi tace

” zainab na riga na gama yanke shawara, kuma in banda abinki in muka biku a wane matsayi muke a wajen ku”

“aliyu yace zai auri nadia” kawai naji baki ya furta

Ɗagowa tayi ta kalle ni sosai taga a magana ta babu ƙarya duk da dai ƙaryar nake yi, don Allah ya za ayi in bar ɗan yaron da zuciyar uban sa take ƙirjin mijina shiga cikin tashin hankalin bayan nasan cewar ƙaddarar uban sa ta haɗu da ta mijina in ban taimaka masa ba ai na zama butulu ban gode wa Allah ba ƙenan

Ajiya zuciya ummu yahya tayi sannan tace 

“Zainab kin gani auren nadia da yahya ni na haɗa su ba wai son take yi ba amma saboda ni nawa tunanin ya bani cewar wannan shine mafita bata so haka na haɗa, yanzu kuma kice in kuma tursasata ta auri mijinki saboda wai mu je mu raɓu kusa da mu wallah bazan iya ba, amma kuma bazan hanaki tambayar ta kije kiji inta yarda ni banni da ta cewa”

Fita nayi na samu nadia tana haɗa kayan su al amin yana wasa kusa da ita zama nayi na zayyano mata ban ɓoye mata komai ba amma sai na ɓoye mata cewar ni na nemi auren

Shiru tayi kamar bata yadda ba sai dana ƙara nuna mata illar komawar su syria ko ta yadda zai shafi rayuwar ɗan ta sanna da ƙyar ta aamince tana kuka ban san ko kukan me take yi ba amma daga dukkan alamu tana tuna tsohon mijin ta ne

Ɗakin na koma na faɗawa ummu yahya murmushi tayi sanna tace maa shaa Allah

Sai da aliyu ya dawo gida da ddare sannan na faɗa masa ɓaran ɓaramar da naje nayi kamar ya rufe ni da duka haka yai ta min faɗa ni dai shiru nayi ina kallon ikon Allah be haƙura ba har sai da na kira mimma na faɗa mata itama tace hakan shine dai dai sai da tayi masa magana sannan ya sauko ya yadda

Oh Allah ni abu naga ta kaina wai macen da za ayi wa kishiya zaka ganta ana lallaɓa ta amma banda ni wai ni nake lallaɓa mijin na nayi abu kaɗan sai yace
“wallahi kika ɓata min sai ma ince na fasa auren” sai in bishi da ban haƙuri

Dole na danne kishi na na ci gaba da lallaɓa mijin nawa wanda aka saka ranar ɗaurin sa sati biyu masu zuwa, na kira tj na faɗa nayi mamakin da naji kamar be yi murna ba amma kuma sai na share don tunda salma ta rasu tj ya koma wani salihi

Aliyu ya tubure shi ƙwandalar shi ba za tai ciwon kai ba a auren ni dana ɗauko auren sai in yi masa, haka na zage dantse don ma su nadiar sunce basa son komai na bidia kawai a bada sadaki amma kuma dole ayi wa amarya sutura, don haka kullum sai na fita kasuwa don siyowa amarya lefe 

In na dawo gogan ko ta kaina baya bi sai dai kawai yai ta cewa aikin sa kai nake yi don haka bana buƙatar sannu sai kace in na aura masa ita ni zan more ta, don Allah ƴen uwa ba daga ya shiga wannan babban ɗakin ya kwashi roman damokaraɗiyyar da ke tattare da ɗakin ba ba kuma sai a hankali ba, namiji fa duk inda yake namiji ne daga an buɗe masa wannan ƙofar ya shiga ya ji abinda ke ciki shike nan an gama zance, amma dubi yadda yake min

Ana gobe ɗaurin aure ne muna zaune da shi yana kallon news ni kuma ina ƙara haɗa kayan mu don ana gama ɗaurin auren zamu koma nigeria
“habibi na ɗauka tj zai zo”
“me ze zo yayi miki” ya tambaya ba tare da ya kalli inda nake ba

“auren ka mana ya kamata ace yana nan”
“auren dolen de da kike son yi wa mijin ki, ni wallahi ban taɓa ganin mace irin ki ba wai da yiwa miji aure” ya faɗa yana yatsine fuskar sa, taɓe bakina nayi don banni da ta cewa

Wayata ce ta fara ringing dubawa nayi naga number nadia, ɗauka nayi da fara a ta
“our bride to be in shaa Allah” na faɗa a zolaye murmushi tayi sannan ta gaishe ni

“dama number abu haidar nake”
“zakiyi masa magana ne” na tambaye ta

“eeeh ina son magana da shi ne”
“ok gashi ma kusa da ni” miƙa masa waya nai sannan na tsokane shi

“amaryar ka tana son jin muryar ka” ƙin karɓa yayi da farko sai da na tashi daga inda nake na zauna akan ƙafar sa sannan na kara masa wayar a kunne sa, sai da naji ya ansa sallama sannan na sakar masa wayar na bar wurin don kar zuciya ta kwashe ni

Sai da ya gama sannan ya shigo ɗakin da fara'ar sa daga gani ta faranta masa ne, kusa dani ya zauna

“habibti ga wayar ki, ashe yarinyar nan haka take kai gaskiya na gode da kike son haɗa ni da ita hmmmm rangaɗi gaskiya ta haɗu”

Wani ƙululun bakin ciki ne ya tokare min wuya sai nayi kamar banji shi ba, surutun shi ya dinga yi dana gaji kawai sai nahaɗe bakin da nashi don bana son in furta komai don in dai nace zanyi magana to kuwa kuka ne zai biyo baya

Tuni na canza wa mijina lissafin sa yana lissafin maths ya koma english don Allah waya taɓa jin lissafin english, ko da yake wannan karatun na masu aure ne????????????

Kashegari da wuri ya fita sai ɗoki yake yi na rasae nadia ta faɗa masa da ya saka shi jin daɗi haka ana gama ɗaurin auren ya dawo na tambaye shi da fara'ar shi yace aikin gama ya gama 

Wasu hawaye ne waɗanda nake ta ɓoye su, aliyu ne ya share min su sannan yace
“zainab har gobe babu wata mace a zuciyata sai ke kuma baza a kuma ba in shaa Allah, ke kaɗai ce har abada babu wata bayan ke ke kadai nake jin daɗin keɓewa da ita ke kaɗai nake kalla naji daɗi a raina din haka don Allah kar ki kuma anan gaba kice zaki kuma haɗai ni da wata, ke kaɗai ce bazan iya haɗa ki da wata ba” ya ƙarashe zancen sa tare da rugume ni

“abu haidar yanzu wannan zancen na da ne yanzu mun zama mu biyu dole ka koyi danne zuciyar ka don ka zama adali a gare mu don kar ka cutar da nadia ba zanso inga hakan ba”

“baki tambayi me nadia ta faɗa min jiya ba” mintsinin shi nayi don naga so yake yi ya sani kuka again

” to shi kenan tunda abin naki ya zama harda mugunta na fasa faɗa miki, ki haɗa kayan ki gobe zamu bar gari zuwa nigeria, su nadia ma na saka su haɗa kayan su”

“kace sai ƙarshen watan nan zasu koma”
“ke ina kika taɓa ganin an bar amarya tana jira” ya faɗa azolaye, duka na kai masa aƙirjin sa sannan na saka masa kukan shagwaɓe

Ɗauka ta yayi sai gado, ina ta kokawar ya sauke ni amma ina sai da ajiye ni akan gado sannan yace
“bari in kwashi don Allah ne kaɗai ya san lkcn da zan dawo wajen ki gwanda in more kafin mu koma a fara sharing kooo”

Haushi ya bani na hankaɗe shi amma kasancewar yana da ƙarfi sai beji ba kokawa muka dinga yi inda shi in banda dariya babu abinda yake min, kukan gaske na saka masa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Leave a Reply

Back to top button