
“to menene kuma abin kuka, ba ke kikai min auren ba kuma wai yanzu ba kya son inyi maganar auren” wa’azi ya shiga yi min akan mace me gudun miji babu yadda na iya haka na sallama masa
Kashegari da wuri muka shirya a gida mukaje muka ɗauke su nadia taci laffayar sai ƙamshi take yi haushin ta ne kawai ya kamani kamar in kai mata duka, wai don Allah dama haka kishi yake
Aliyu naji kusa dani
“uwargida don Allah a rage kishin nan mana kinga yadda kike dokawa nadia harara” ya faɗa yana min dariya, ban kula shi ba nayi wajen su muka gaisa jikin ummu yahya da sauki don haka sai muka kama hanyar airport don ta madima zamu wuce
tunda muka shiga jirgin na wuce ɗan ɗakin dake cikin jirgin kasancewar private plane ɗin aliyu ne ze mayar da mu don ummu yahya suna da kaya sosai
tunda na shiga ɗakin na kulle ko ƙaunar ganin nadia bana yi wani haushin ta ma nake ji kawai daurewa nake
[12/7, 7:21 PM] Mmn Waleed????: Lfy muka sauka nigeria kuma abuje directly gida muka nufa nai mamakin dana ga an kai nadia gidan da tj yake wanda yake kusa da gidan mimma ita kuma ummu yahya zata zauna a ɗayan part ɗin dake gidan mimma tunda dama n part ɗaya take anfani da shi
Har ɗakin aliyu na bishi na same shi
“me yasa ba za ka haɗa mu a gida ɗaya ba”
“habibti naga alamar idan na haɗa ku wataran sai dai in dawo in ga kin mata duka” ya faɗa da dariya a fuskar sa
Ƙarasowa nayi kusa da shi ina taimaka masa cire button ɗinrigar sa
“kana ganin zan iya dukan ta don tana matar ka”
“kinga irin hararar da kike aika mata kuwa, ko ni kika aiko min da wannan hararar shiga taitayina zan yi balle nadia” shiru kawai nayi na fice
Banyi niyyar girki ba don a agijiye nake don haka saina aika part ɗin mimma tasa ayi abinci da mu, ko da aka gama sai ta aiko amina ta kawomana
Ƴar iskar yarinyar ni tunda na dawo sai yanzu ma na ganta tana part ɗin mimma ita da islama da su haidar can suka koma, ko da nace ta dawo part ɗina sai tace wai part ɗina bavu daɗi haka na haƙura na ƙyale ta acan
Da daddare na tafi part ɗin aliyu don in raka shi gidan amarya nai mamakin dana ganshi a azaune ko shiri be yi
“yanzu abu haidar sai yaushe zaka je gidan amarya”
“oooh wannan matar tawa muguwar ƴar ƙauye ce wai ke har yanzu ɓaki fahimci tj ne ya auri nadia ba ba ni ba” kuka na saka masa tare da zuwa gurin shi ina dukan sa
Dariya ya dinga min, yana ƙyaƙyatawa
“shine baka faɗa min kasa nake ta jin haushin baiwar Allah”
“so nawa na tambaye ki kina son ji abinda nadia ta faɗain sai kika ce bakya sonji” sai yanzu na fahinta
“me tace maka” na tambaya a ƙage
“oho” ya ansa
“au oho ko bari ka gani” sai na fara yi masa cakulkuli, dariya ya dinga yi sannan yace yayi surrender zai faɗa min
Ashe nadia da tj sun riga sun haɗe kansu tinda ta fita takaba tj ya nuna mata yana ra'ayin ta itama kuma taga ɗan fulanin bauchi yasa bata wani ja aji ba sai ta yadda suna cikin soyayyar sune ummu yahya ta kawo zancen barin su madina nadia taso ta faɗawa tj don ya faɗawa ummu yahya ke kuma sai kikai shigar sauri kika ce nace zan aure ta
Ana gobe ɗaurin aure ummu yahya taji nadia tana kuka suna waya ita da tj shine bayan ta gama sai tace ta kira ni ta faɗa min gaskiya tunda taga alamar nima ba son ta nake yi ba shi ne ta kira ni, wallahi nai farin cikin sosai dana ji ni na tsira sannan zan bawa ɗan uwana abinda yake so kinji yadda abin ya kasance
Kwanciya nayi sosai a jikin mijina tare da godewa Allah ubangiji (swt)
***************
Babu abinda yake faruwa a cikin gidajen mu sai alkhairi aliyu ya bawa ummu yahya al amin da mu’allim bayan na yaye shi don kar ta zauna a wurin ta babu hayaniya, inda su haidar suke wajen mimma ita kuma islam ta koma wajen nadia, a gidan ni kaɗai ce banni da ɗa ???????????????? innai magana sai aliyu yace wai in dage in ƙara kawo wani be san ina na ɗauke da ɗan passenger ɗina ba
Ummu yahya tacewa aliyu tana son ta buɗe islamiyya a cikin gidan ta tunda akwai ɗakunan da babu kowa a ciki don ta dinga karantar wa tunda dama can aikin ta ne,
Gini sosai aka fara yi na ɗauka ƴar islamiyya zai baɗe mata dana ji yace ta bari zai ga yadda zai ashe gini zai yi
Babbar makarnta ce wacce taci sunan yahya memorial islamic scl aliyu ya ɗauko ma’aikata da malamai sannan yai wa ummu yahya maganar an kammala ko da taje taga ginin har kuka sai da tayi ta dinga godewa aliyu ciki lck ƙanƙani akayi launching makarantar aka fara karatu
Ita ma mimma ta koma asibitin national hospital dake abuje ta cigaba da aiki itama aliyu ya buɗe mata pediatric hospital babu abinda ake yi a asibitin sai kula da yara da duba matsalolin su ya samo mata specialist akan harkar yaran da nurses ya cika asibitin da su, sannan ya aurar da ƙanwata amina zuwa ga pA ɗin sa al mustapha suka tare a lagos don yanzu al mustapha yana lagos gurin kular wa da aliyun sifirin jiragen sa wanda shi kuma aliyu suke yin zuwa in lkcn yayin zuwan yayi shi da tj
BAYAN SHEKARA 10
Alhamdulillahi yanzu gidan mu ya cika don bayan mu’allim sai Allah ya azurtani da mace me sunan hjyr aliyu wato furairat amma muna kiran ta da walida sai namiji me sunan bbn mimma wanda muke kiran shi walid sai mata guda biyu wato yen biyu masu suna fatima da kuma rabia
Itama nadia tana na tana da ƴaƴan ta guda huɗu wanda ta haifa da tj ɗin mata biyu maza biyu babu abinda zamu ce sai dai ince Allah ya ƙara bamu zaman lfy da mazajen Allah ya ƙara bamu haƙuri da juriyar zaman tare
*tammat bi hamdulillah*
ina miƙa godiyata sosai da jinjina ga masu karanta wannan littafin nawa na gode da soyayyar ku da adduar ku gare ni Allah ya biya mana buƙatun mu na yau, da kullum ya haɗa mu a aljannar fiddausi baki ɗaya
don Allah mu dinga kuƙa da zuciyoyin mu mudinga sauke wa zukatan mu nauyin da muke ɗara musu na baƙin ciki ko hassada ko kuma ƙullatar mutane mu zama masu yafiya ko da mutum ya tambayi a yafe masa ko bai tambaya ba kai dai ka kasance me yin afuwa hakan ne kawai zai sa mu zaunablfy da zuƙatan mu, mu cika zuƙatan mu da soyayyar ma’aiki (saw) babu abinda zaka cika zuciyar ka dashi daya wuce wannan ya kasance zuƙatan mu babu hassada babu ƙyashi babu baƙin ciki, YA ALLAH KA KULAR MANA DA ZUƘATAN MU BA DAN HALIN MU
SALAM ALAIKUM
Taku ce akullum mmn walid nd walida ce (mrs aliyu) a kullum ???? ana tare