
a cike ƙofar gidan take taf kamar ɗaurin aure ake ba masaka tsinke hango fitowar aliyu daga motar ne yasa mutane suka yuuuu kansa kowa so yake yi yayi masa gaisuwa kuma a san ya zo, ansawa kawai yake yi amma baya ma iya gane komai, wurk ɗaya ya samu ya zauna ya ci gaba da karɓar gaisuwa
zaman makokk akayi wanda sai wanda ya gani abinci ne ake fitowa da shi kamar ba a san darajar kuɗi, kullum sai anyank sa da raguna huɗu banda iyayen kaji
mutane sai cicciɗowa kawai suke yi daga kowane ɓangare taf gidan yake cika har waje gurin zama har kaɗan yake yi, ko da akayi sadakar uku tj ya so ya cire canopies ɗin da aka kafa a wajen gidan amma ganin yawan mutanen da suke zuwa gidan ne daga ance agri ya waye ne yasa aliyu yace a ɓarsu haka aka ci gaba da ciyar da mutane
ran da ta cika kwana shida ana gobe sadakar bakwai aƙiyu ya kira pilot ɗin sa yace masa ya shirya zasu tafi saudiya kashegari da daddare yes sir kawai yace
ranar sadakar bakwai kamar biki akeyi saboda tsabar cika abin har ya bawa tj haushi yawancin su ba mutuwar bace a gabansu ba sudai suci su ƙoshi shikenan, ana sallah isha aliyu yai wa tj sallamar da cewa ya tafi saudiya, aliyun yana tafiya, tj yasa aka kwashe canopies ɗin da tabarmin wurin an tashi daga zaman makoki
kashe gari da sassafe sai ga wasu alarammomi da malun malun ɗin su wai sunyi wa aliyj magana cewar zasu dinga zama suna yiwa hjy addua har sai tayi arba'in, wannan abun ba ƙaramin ɓatawa tj rai yayi ba tabarmi ya basu suka shinfiɗa a waje aka fara karatu, kafin kace me wurin ya kuma cika ba masaka tsinke wasu ma akan talkalman su suke zaune a cikin rana, ko ƙala baice musu yayi fice warsa
to rana fa ta ke hantsi ya fara duban ludayi alarammomi da ƴen zaman makoki aka fara jin yunwa tun suna sa ran akawo musu har suka ga la'asar tayi ba aɗɗa'am ba alamar sai suka fara zamewa da ɗaya da ɗaya kafin biyar wurin nan kamar anyi shara ba komai ko da tj ya dawo yaga sun watse sai yayi murmushi ba baiyi musu haka ba ana arba'in ɗin ma sai suce sak ta shekara kuma tsab aliyu biye musu zai yi wannan ke nan
**********
*saudiyya*
ko da aka sauke shi direct madina ya je kwanan shi uku sannan ya baro ta don ya samu ya gabatar da ummara, tun daya shigo makka yake hawaye daya tuno zuwan su ummarar su ta ƙarahe shi da hjy, yai ummarar sa sannan ya samu wuri a haramin yai zaman sa ko hotel ma bai bi ta kamawa ba
daga shi rigar jikinsa sai wayar sa sai master card ɗinsa ya taho da shi, a masallaci yake kwana yana ibada tare da kashe wayar sa gabaɗayan ta, shi gani yake yi komai da yake nema na hjyr sa ne kullum ya tashi burin sa ya farantawa hjyrsa wai yau ace bata nan, shi to neman me zai yi gwanda kawai yayi zaman sa anan yai ta ibadar sa har shima tashi ta same shi tunda wacce yake ganin ta yana jin daɗi yana nema dare da rana ba ita to kuma yanzu neman me zai yi don wa zai nema
a cikin haramin yake komai ɗinsa sai dai in yaji rigar da ke jikinsa ta dame shi ne sai ya fita ya samu shagunan da ke jikin haramin ya siya ya canza ya bada sadakar wacce ya cire ɗin, haka ya koma yana rayuwa shi kaɗai har taimakwa ma’aikatan cikin haramin yakeyi idan zasuyi shara ko moping shima yanayi tun basu saba da shi har suka saba da shi sosai suna ganin shi kamar wani ɗan uwansu kasancewar yadda yake shiga cikin su yayi aiki sosai da iya ƙarfin sa ga kyauta da yake musu akai akai wanda hakan ya tabbatar musu da cewar wani babba ne ƙila ko matsala ya samu shine ya gwammaci ya keɓe kanshi har ya manta ba abinda basu kawo amma basu samu ansa ba kasancewar baya magana ko aiki yake yi zaka tsince yi yana tasbihi sa, ga bashi da san jiki ko kaɗan aiki zaka ganshi yana yi ba kama hannun yaro, duk ya canza ya rame sosai ga uban ƙasumba da ya tara afuskar sa wanda hakan ne ya sa kamannin sa suka canza wanda inba ƙwaƙƙwaran sani kayi masa ba sai ya wuce ka wuce baka gane shi ba
***********
*kano*
yau watan aliyu biyu bashi ba labarin sa, ba inda ba aje don duba shi ba amma shiru tj sau biyu yana zuwa saudiya amma baya ganin sa ba irin luxirious hotel ɗin da bai duba ba amma ko mai kama da shi bai gani ba gashi wayoyin sa duk a kashe, dole haka ya haƙura yasa su dinga cigiyarsa ko za a ganshi ko ya zasu iya gane shi yadda ya canza oho
dole ya dawo abj ya ci gaba da kula da dukiyar sa don baza abarta ba mai kula da ita ba, sai yanzu tj ya fahimci irin wahalar da aliyun yakeyi wajen kula da dukiyar nan tasa lallai ba ƙaramar wahala yake sha dukiya ce da inba ido kasa sosai ba sai a barka cikin ta hamma wato an washe ka,
Duk sati sai jiragen aliyu na ruwa manya manya guda ashirin sun fita da baƙin mai cike taf a cikin su zuwa ƙasashen da suke sarar man nijeria, sannan kuma duk satin sai wasu jiragen sun shigo da kaya kafin wasu su tafi wasu sun dawo haka tj yake wannan hidimaɗ sai yanzu ya fahimci dalilin daya sa aliyun ajiye private yau kana wannan garkn gobe kana wancan ba daman hutawa rabon shi da kano tun lkcn da ya fahimci aliyun ya gudun, ko abinci saboda tsabar hidima watarana mantawa yaƙke yi baici ba sai dai in yai yunwa zatai mai illa sannan zai nema
yaje gidan aliyun sau biyu ga zainab ɗin kuma ya yaba da hankalin ta ganin kaɗaicin yana mata yawa ne ya shi ya sai mata waya ko ta dinga gaisawa da ƴen uwanta baisan cewar bata da number kowa ba, ko daya koma yaga yanayin nata dai bai chan ja ba sai ya yanke shawarar ɗauko mata iyalin sa shima kuma on d other hand yana kewar matar tashi don wani lkcn ko lokacin yi mata waya baya samu
ɓangare guda aka gyarawa salma matar tj ɗin a gidan aliyu inda part ɗin ya koma gurin yinin zainab don ba ƙaramin daɗin ganin ƴar uwatar bahaushiya tayiba kuma gata me faran faran da sakin jiki, salma tana da yar ta ɗaya me suna islam sunan hjy taci wato furairat aka saya ana ce mata islam
duk wani ɗawainiya islam zainab ce take yin sa ganin hakan ne yasa salmar ƙara sakin jiki da zainab ɗin kunsan ance me ɗa wawa, tj yajawa salma kunne sosai akan kar ta faɗawa zainab ɗin cewa an ɗaura mata aure da aliyun abin ya bawa salmar mamaki sosai amma kuma da yake macece me kau da kanta akan abinda babu ruwan ta yasa ta ja bakinta tayi gum ????????????
[7:42PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Dis page is 4 u mmn farida ????
Hankalin tj ya kwanta sosai ganin cewar yanzu zainab ɗin hankalin ta ya kwanta, amma duk da haka kullum sai yayi tunanin in ɗan uwan nasa ya shiga, wannan abun yakan damu tj sosai da sosai
Ita ma zainab ɗin yanzu ta saki jikin ta fiye da daa, ganin salmar a gidan, ga kuma islam da koman ta zainab ɗin ce itama yarinyar hankalin ta ya kwanta sosai da zainab ɗin don in ba yunwa take ji bata damu da mmn ta ba
*************
*saudiyya*
Yau da wuri ya tashi ya fara share sharen na cikin masallacin tare da ma'aikantan inda yawan su suna yin aikin ne suna surutu saɓa'in shi daya duƙufa yana yi yana tasbihin sa gaba ɗaya yau baya jin daɗin jikin nasa, don haka ya gama ya nemi wuri da ba mutane sosai ya kwanta don ya huta don through out jiya baiyi bacci ba kasanceqar kwana da yayi yana ibada
ya kwanta kenan ya fara sai yayi mafarkin hjy, tana zaune ta sha kwalliya da wasu fararen kaya sai sheƙi taki yi tai kyua sosai sai murmushi take yi ga yara nan a gaban ta suna zuwa ɗaya bayan ɗaya tana shafa musu kai,
Da sauri sa ya ƙarasa wajen ta ya tsugunna da nufi shima ta shafa mai kan nasa amma ga mamakin sa si yag ta miƙe ta bar wajen,
binta yayi yana kira hjy hjy, juyowa tayi duk fara'ar dake fuskar nan tata babu ita jikin shi ne yai sanyi, ya ƙarasa gaban ta
“hjy kin tafi kin banni bayan in mutuƙar buƙatar ki a tattare da ni, kin barni ni kadai a cinkin wannan duniyar me cike da ƙunci da ƙyashi, kuma gashi yanzu na gani ina murna amma kuma kin juya min baya” ya faɗa yana ƙare zancen sa da kuka
kamar baza tayi magana ba amma kuma sai tace masa
“aliyu baka godewa ba” a tsorace ya ɗago ido yana kallan ta
“kafin Allah ya ɗauke maka ni ba yabaka wdda zata maye ma gurbi na, amma kayi facali da kyautar da Allah yayi maka ka watsar ka gudu daga ni’imar ubangiji tayaya zakayi tsammanin zan tsaya kula, kaji tsoran Allah aliyu yarinyar amana ce a wajen ka Allah ya baka, ka riƙe ta da kyau don Allah ka ji” ta ƙarashe zancen nata da sigar lallashi
jikin shi ne yayi sanyi sosai
“ka shirya ka koma ga iyalin ka da ƴen uwan da kuma mutanen da suke ci da kansu da iyalen su ta dalilin ka kaji aliyu na” ta faɗa tana me shafa masa kansa
kansa yana ƙasa kuka kawai yake yi yana gunji, girgiza yaji ana yi
“ya akhi ya akhi maa ha dathaa”
buɗe idon sa yayi yaga wani balarabe yana tambayarsa
tashi yayi zaune jikin sa yana rawa
“maa yusibuk” Ya kuma jeho masa tambaya, be kula shi yaci gaba da kukan da yarasa dalilin yin sa kuma ya kasa dainawa
“laaa tabki, ya akh, sa a tika bil ma’a”
ya faɗa yana miƙe wa tare da nufar coolers ɗin da ake ajiye ruwa na cikin harami, ruwan ya ɗebo ya kawo masa
“kuz wash rab” ya faɗa yana miƙa masa ruwa, karɓa aliyu yayi fara sha, sai daya shanye ɗan ƙaramin kofin nan tas sannan ya ajiye
“iɗɗaje was tareh” ya faɗa, kwanciya yayi kamar yadda balaraben ya faɗa masa, ganin haka yasa balaraben tafiya
ko da ya ga balaraben ya tafi sai ya fara tunani mafarkin hjyr da yayi nan wani sbon kuka ya kuma kwace masa mara sauti,
ganin kwanciyar bazata yi masa bba ya sashi tashi ya fara ɗawafi yana yi yana kuka yana roƙon gafarar ubangiji tare da yiwa hjy addua, sai da ya gama yaje yayi sallah raka' biyu wacce ake bayan anyi ɗawafi a bayan maƙaman Ibrahim yaje ya sha zam zam sannan yaji ɗan sanyi aransa
zuwa yayi gurin ma’aikatan da yake taya su aiki, sallama sosai yayi musu akan zai koma garin su, sosai sunji ba daɗi a ransu ganin yadda yake taimaka musu sosai ba kaɗan baamma kuma ya zasu yi dama ɗabi’ar baƙo ce in yazo wataran dole ya tafi
direct air port ɗin jidda ya nufa siyan ticket yayi kuma yai sa a jirgin da zashi nigeria zai tashi a daren amma kano zai sauka, bai damu ba shi dai burin sa ya ganshi a nijeria
rabon da aliyu ya shiga commercial flight har ya manta, don haka sai da samu taimakon flight attendance ɗin sannan ya samu wurin zaman sa kasancewar vip tickets ɗin an siyar sai commercial sit, a takure yai wannan tafiyar har aka iso nigeria bai sake ba, da asubar fari jirgin nasu ya dira a ƙasar mu wato nigeria
ko da aka sauka naija directly ya wuce wurin siyan domestic flight tickets ya yanki ticket ɗin zuwa birnin tarayya amma wannan karon ya samu vip sit ɗin
a flight ɗin har wani bacci wahala yayi kafin su ƙarasa abj ɗin
**********
*abuja*
Ko suka sauka directly ya wuce office safiya don haka yace bari ya fara biyawa office ɗin yaga abinda yake ciki kafin ya wuce gida, taxi ya tara don ta kai shi office ɗin, a get ɗin office ɗin nasu sukayi parking ya fito,
“bari in karɓo ma kuɗin ka”ya faɗawa ɗan taxi ɗin, bai jira ansaba ya nufi get ɗin kanshi tsaye ya ƙwanƙwasa, me gadin ne ya zo ya buɗe, ganin mutum da ƙasumba ya sa shi tsayawa yana ƙare masa kallo
“malam inuwa ya aiki”mutumin da kira da mlm inuwan ya tsaya yana kallon wannan baƙo me ƙasunbar da har ya san sunan sa
“don Allah ko kana da 2000 in biya me taxi ɗin nan idan na shiga sai in baka”mlm inuwa bai ce komai ba don shi gani yakeyi ma me ƙasunbar nan ya rai na shi wai ya bashi kuɗi
” mlm ina ganin ɓatan hanya kayi don ni ban san ka ba” murmushi aliyun yayi
“mlm inuwa nine fa yallaɓai” ya faɗa yana murmushin da ba’a iya ganin lebɓansa na sama saboda tsabar gashin da ya rufe su
kallon sama da ƙasa yayi masa, sannan ya mai da get ɗin garam ya rufe, don ma ya raina min wayo zaice wani yallaɓai ne yallaɓan da kayan sa kullum tsab tsab suke a goge yana tashin ƙamshin turare amma shi wannan yazo da wata doguwar rigarsa da ta yamutse sai ya sha kokawa ga wani uban ƙasunba da ya tara, zaice min wani wai yallabai ne ko da dai daga ƙauye na zo ai ba dabba bane ni ko a cikkn mutane million naga yallaɓai zan gane shi ya faɗa yana mita