
kuka na sa masa shi kuma ya shiga lallashina tare da shafe ilahirin jikina yana wani irin numfashi
“4 God’s sake zainab wat do u want” ya tambaye ni
"ni ka kaini gida"
” gida kike so nan ba gida bane me yasa bazaki saki jikin ki da niba” azzalimmi in saki jikina ka cuce ni na faɗa araina
“ni dai don Allah ka dubi girman Allah ka maidani gida gaban iyayena” na kuma faɗa
“to shike nan kije zan yi tunani tukun na” ya faɗa yana sakina
a guje na kama zan bar ɗakin ƙara kamoni yayi yan ƙara mannani aqirjinsa tare da kissing ɗin wuyana sannan ya sake ni
“ki zauna kici abincin ki ni zan fita inci a waje naga alamar nine ba a son gani” ya faɗa yana yin hanyar waje
wanda ni kuma hakan yai dai dai da tsugunna wata ƙasa tare da dasa wani sabon kukan, in da naji islam ta hau kaina itama tana nata kukan, dole na share hawaye na na lallasheta sannan na zauna na ci gaba da bata abincin ta
tun daga lkcn na tsiri yawo da hijabi ko ina in dai zan bar ɗakina to da hijab ɗina a jikina, ban san cewar duk aikin banza nake yi ba shi ta ɗakina ma yake shan kallon sa ya more, mun sha cin karo da shi sai in zura a guje inyi ɗaki in barshi anan
rasa yadda zaiyi da ita yayi ta zauna ma suyi maganar fahimta taƙi da ta ganshi kamar taga wani dodo sai gudu ga wani hijabi da ta tsiri sawa duk yasan don shi takeyin hakan bosho ke nan ya faɗa
yana zaune a ɗakinsa yana tunanin ta yadda zai ɓullo mata ko ta saurare shi
“khadija khadija” shine abinda da iya faɗa, lallai ya ƙura yarinyar tana da saukin kai zata iya shawo masa kanta, wayar sa ya ɗauka ya lalibi number khadijan ya kira sai da ta gama ringing ta tsinke ya kuma kira sannan ta ɗauka da sallamar ta
“khadija ce” ya tambaya bayan ya ansa sllamar
“e ni…..ce……” Ta faɗa tana ɗan jan harufan alamar mamakin jin muryar namji ya kira ta
“ok aliyu ne mijin zainab”
“laaaaa ina wuni” ta faɗa da fara’ar ta wadda yana iya gane wa ne ta yadda tayi magana
“lafiya ƙalau ya gidan da me gida”
“lfy lau, ina yayar tun da ka tafi muke tasa ran ta kira mu amma shiru”
“wallahi khadija yayar nan taki ce ta matsa sai na kawo ta gida ni kuma gaskiya banni da ra’ayin haka”
“kash amma yaya bata kyauta ba”
“shine nake cewar idan kinga ba damuwa ko ku zaku iya zuwa ku ganta kinga ƙila idan taganku wataƙila hankalinta yafi kwanciya ko”
“to shike nan bari in kira maryam sai inji yadda zamuyi in zamuje sai mu sanar da mazajen mu inyaso zuwa magariba zan kira kaji duk yadda mukayi” godiya ya dinga zankaɗa mata har yasa ta jin kunya sannan sukayi sallama
oohh yaya ban sanki da wannan hali ba,wayar ta ta ɗauko ta kira maryam inda suka tsaida shawarar kowacce ta tambayi mijinatan, haka akayi kuma cikin sa a kowacce mijinta ya yarde mata
ko da aliyun ya kira khadijar ta shaida masa yai murna sosai sannan yace mata akwai flight gobe da ƙarfe 11:30 na safe lagos zuwa abj in zasu biyo yasa ayi musu booking
“to shi ke nan Allah ya kai mu” ta faa ta kira maryam ta shaida mata tafiyar tasun gobe da safe ce
ƙarfe goma dai dai na safe aliyu ya turo da driver ɗin sa na lagos ƙofar gidan maryam tare da taimakon ta wajen yi masa kwatance, a shiye suke tsap don har maryam ma tazo suka shiga suka kma hanyar airport tare da rakiyar mijin maryam, sun biya ta gidansu sunyi bbn su sallama inda mama ta dinga faɗan ba a gaya mata ba aida ƙafar ta ƙafar su, shidai baba cewa yayi da sun sauka su kirashi, da haka sukai salama
A airport ɗin duk aka gama duk wani abinda za ayi suka hau jirgi ya ɗaga da su birnin tarayya
[7:43PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page: 17????
Khadija bata ga wautar su ba sai da sukayi kane kane a jirgi sannan wani abu ya faɗo mata, to in banda ma rashin tunani irin nasu tun da yayar nan ta tafi babu wanda ya taɓa ganin ta ko jin labarin ta, sai dai shi mijin, amma daga zuwa yace musu wai taƙi sakin jikin ta kawai sai su kuma suka kamo hanya suka taho ganin ta, oh Allah kasa ba ajalin mu yake kiran mu ba
juyawa tayi ta kalli maryam wacce take ta ƴen kalle kallen ta ga farhana a hannun ta tana ta bacci, ita ta baro khalil a wajen mama kasancewar yanzu cikin ta ya fito sosai don haka bata yawo da shi
suna sauka ta kunna wayar ta sai ga kiran aliyu nan
“na turo driver ya ɗauke ki na bashi number ki don haka zai kira ki, ni na shiga meeting ne sai dare” To kawai ta iya cewa jiki a sanyaye
“Allah yasa ba meeting ɗin siyar da mu ya shiga ba”
ilai kuwa sai gashi driver ɗin ya kira ta, tai masa kwatancen inda suke ya ƙaraso tare da ɗaukar kayan su zuwa wurin motar, wata baƙar continue discussion ce suka dosa glass ɗinta duk tinted ne baka ganin na ciki (ta wata tace *ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba* ????????????????
cikin khadija ne ya ƙara ɗurar ruwa shike nan su tasu ta zo ƙarshe ta faɗa tare da yin bismillah tana shiga motar tare da yiwa Allah addu'ar ya tsera tar da su
ko da suka je gidan ma khadija ganin irin girman gidan yasa ta kasa hakuri
“maryam nifa tsoro nake ji”
“tsoron me” inji maryam ɗin wacce hankalinta gabaɗaya yan ga kallan kataferen ginin da suke ƙoƙarin shiga
“yaya khadija don Allah dubi irin gidan da yaya take rayuwa acikin sa”
lallai har yanzu maryam ba nazari a lamarin ta wato ita kyawun gidan ma take hangowa ba irin hatsarin da suke shirin shiga take yi ba yanzu idan aka garƙame ka awannan tafkeken gidan ko tokar ka a ganine
share maryam tayi ta ci gaba da addu’a suna shiga cikin kataferen gidan kamar na shugaban ƙasa, sai da suka ɗanyi tafoya a cikin a cikin farfajiyar gidan, sannan suka samu sukayi parking
Ƙofar motar aka buɗe musu wani mutun ne sanye cikin bakaƙen suit da gilasin sa baƙi ya bude musu tare da cewa "welcome" a cikin muryar nan tasa kamar a shaƙe shi
maryam ce ta ansa da fara'ar ta ita kuwa khadija fitsari ne kawai be zubar mata, kai duba tayi taga farfajiyar cike take da maza tiƙa tiƙa duk sanye cikin bakƙaƙen kaan da glass ɗin abtsaye ƙiƙam kamar an dasa su
wawuro maryam tayi "mun shiga uku maryam gidan yankan kai aka kawo mu" itama maryam ɗin da jikin ta ya fara sanyi ganin waɗannan ƙattin yasa itama yin shiru
“dis way pls” ya faɗa tare da nuna musu hanyar da zasu bi da hannu sa, bin shi sukayi a baya duk jikin su yayi sanyi
sunyi tafiya ta kai ta kusan minti goma kafin su ƙaraso wata ƙofa daga ganin ta ƙofar falo ce, door bell ya danna aka buɗe masa,
“they r here” ya faɗa tare da juyawa, matar da ta karɓe su me ɗan fara’a ce ba kamar mazan ba
“do come in pls” tace musu haka suka shigo jiki yayi sanyi, tsayawa sukayi suna ƙarewa ƙayataccen falon kallo
“pls wait here let me call madan”
“ok” suka ansa a tare
ina kwance ina game ɗina rebecca ta shigo
“madam u have guest”
“guest kuma tell them am sleeping” na faɗa na cigaba da game ɗina, ni wacece a gidan na da zanyi guest, ko kuma waye ma nawa yasan inda nake da za a ne mi, ƙila baƙin aliyu ne yace a kawo su in yi entertaining ɗin su ko a wane matsayin oho, ci gaba nayi da game ɗina hankali kwance
ko da ta fita taje ta sanar musu sai jikin su yayi sanyi, anya yayar da suka sani ce, maryam ce tayi karfin halin cewar
“go and tell her, her sisters from lagos maryam and khadija are here to see her” tsayawa tayi tana ƙare musu kallo tana tunanin taje ko kar taje
riƙe hannunta khadija tayi
“pls pls pls and pls i take God beg u call her 4 us” ganin iɗin roƙon da suke mata ne ya sa ta tausaya musu
“ok lemme go again but if she say she will not come out now u will have to wait oooh” ok suka bata ansa
ina kwance ni nama manta da wata rebecca ta zo
“madam”
“ooooooo….. Wat again”
“they say i should tell u dat ur sisters from lagos morya and kadija are here”
jin an anbaci sunan ƙannena yasani sakkowa daga gadon aguje nayi falon ban dai gaskata abinda tace ba amma ai ance gani ya kori ji
sune kuwa atsaye ƙiƙam, a guje naje na rungume su ina kuka ashe zanga ɗan uwana, suma rungume nin suka yi muks ci gaba da kukan mu, sai da muka yi mai isar mu sannan muka nutsa
“ku zo muje ɗakina” na faɗa ina jan hannayen su
“rebecca Kawo musu kayan su ɗakina, na faɗa ina yin gaba da hannun ƙanne na
“ya akayi kuka san inda nake”na tambaye su
“mijinki mana, shi yace mu zo”
“mijina kuma waye kuma mijina” na tambayesu, tsayawa sukayi suna kallon juna
a lkcn ne rebecca ta shigo musu da kayan nasu,
“ina linda tayi”na tambaye ta
“bata dawo daga kasuwa ba”
“ok haɗo musu ɗan abin sawa abaki”
ko da ta fita ƙara matsowa nayi kusa da khadija
“waye mijin nawa, yaushe aka ɗaura min aure” tsayawa sukai suna kallon juna
“yaya da gaske baki san kina da aure ba” gyaɗa musu kai kawai nayi don wannan lamarin ya girmi tunani na, ina da aure to me yasa miji bai taɓa zuwa inda nake ba
"to me gidan nan yaya aliyu" kamar in gwaɓe wa maryam baki wai wani yya aliyu, harara na bita da shi na kuma fuskantar khadija don ita a lamarin ta ba ta waasa
“Allah yaya me gidan nan ne mijiki, ke da tun zaman da kike yi a gidan baki san zaman aure kike ba” kaina ne ya kuma juyewa
“yaushe aka ɗaura min auren ban sani ba”
“kusan wata bakwai ke nan ko maryam”
neman maryam mukayi muka rasa ashe ita tuni tayi cikin closet ɗina
“yanzu yaya duk wannan kayan naki ne” muka jiyo muryar ta, kamar inje in rufe ta duka hka nake ji don haushi, wai ina da aure da kuma aliyu duk yaushe hakan ta faru na kuma tambayar kaina
ƙara dawo da hankali nayi ga khadijar wadda itama hankalinta yana kan kayan da maryam ta fito da su daga closet ɗin tana nunawa
“yanzu khadija wa ya ɗaura min ba tare da sani na ba”
“baba ne ” ta faɗa a taƙaice
hawaye kawai naji yana zubar min ashe baba sai da ni yayi shi yasa bai taɓa nema na ba, wayar khadija ce tayi ƙara ko da ta ɗauka baban ne
“eee gata” kawai naji tace ta miƙo min wayar
kunne na na kai wayar inda muryar babana ta daki dodon kunne na, yaushe rabon da inji muryarsa har na manta, a mutunce muka gaisa sannan ya dinga bani labarin irin hidindimun da mijina yake mas harda ceqa ɗan al barka ne ki bishi sau da ƙafa kin ji, to kawai nake cewa
“ga maman taku” ta karɓa muka gaisa ita ma ɗin dai ce min takeyi wai inyi masa godiyar hidimar da yakeyi da su, ko da muka gama khadija ce ta karɓa sukayi magana da ɗanta sannan sukayi sallama, wannan shine fa ake cewa ga ƙoshi ga kwanan yunwa
[7:43PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :18????
Naji daɗin zuwan ƙannena gidana inda duk abinda ban sani ba sai da suka sanar dani, na sha mamaki sosai, shima aliyun ya samun daman sake wa da ni son ransa, ba yadda na iya haka na dinga sakar masa jiki a gaban su amma da mun keɓe sai zancen ya canza, ya kan yi haƙuri da ni yace bazai yi rushing ɗina ba
kwanan su khadija shida suka fara shirye2 tafiya, muna zaune a tsakiyar ɗakina munbaje muna hira, su kuma suna haɗa kayan su,duk abinda da suka gani nawa sukace suna soo basu nake, sun haɗa kayan su tsab sai shirin tafiya
“yaya bazamu zaga gari ba kafin mu tafi tun da muka zo muna gidan nan bamu fita ba”inji maryam
Tsuru tsuru nayi nayi don gaskiya naga dacewar ace sun zaga ɗin amma rashin sanin hanyar da zan bi in faɗawa aliyu yasa ni na basar
“ai kuwa maji daɗi idan mun zaga muma muce mun zo birnin tarayya” khadija ta faɗa
“to shikenan ku bari idan aliyu ya dawo da daddare sai in faɗa masa
ko da ya dawo da daddare naje part ɗin sa na same ya fito daga wanka daga sai towel a ɗaure a jikinsa duk sai kunya ta kamani, gashin kan nan nasa sai ɗigar da ruwa yakeyi inda yake ɗiga a faffaɗan qirinsa,
“bari inje inka shirya na dawo” na faɗa ina juyawa
“no ba komai shigo kawai ai kasya kawai zan sa” Tsayawa nayi ƙiƙam ni ban shiga ba ni kuma ban fita ba, har sai da yazo ya jawo ya zaunar da ni akan cinyarsa
“ma kike so” ya tambaye ni, kasa magana nayi kaina na ƙasa ina wasa da ɗan zoben azirfar da ke hannu na
“kin zo ne kawai ki ganni”ya tambaya yana murmushi,girgiza masa kai nayi
“oooh akwai wani abu da kikesoo ne” na gyaɗa kaina
“ok ina jinki”
“dama su khadija sukace sunaso kafin su tafi su zaga gari, shine nace bariin faɗa ma kozamu samuaron mota”
“duk motocin da ke gidan nan ai naki ne, ki zaɓi duk wan da kuke son fitaaciki ta sai driver ya kai ku kinji” gyaɗa masa kai nayi alamar naji
“ga atm card ɗina nan daga nan ki kai su shopping don karsu koa gida ba tsaraba ko” ɗagowa nayi na kalleshi da fra’a ta kamar yasan abinda ke zuciyata