DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

 ko da na kai hannu na zan karɓa sai ya ɗauke abinsa 

“ai ba kyauta zan baki ba, sai kin biya” yafaɗa, ƙwalalo ido nayi don bansanda me zan biya ba
“karki damu kiss kawai zakiyi min card ɗin ya zama naki” ya faɗa rasa yaddi zanyi nayi,

Rufe idona nayi nakai lips ɗina saman kanshi amma to my surprise ashe akan lips ɗin sa na sauka, it was great, bani card ɗin yayi
“ayi siyayya lfy, kema kina iya zaɓar kayan mu na nan naga baki da su ko” gyaɗa masa kai nayi
“ok a siyo masu kyau don aji daɗin kwalliya da su” ya faɗa yana kashe min ido ɗaya ????

 Ko dana koma na faɗawa su maryam fitar mu kashegari ba ƙaramar murna suka yi

Kashegari ƙarfe 11:30 na safe muka fita, mun zaga gari sosai babu wanda na sani don haka yawo kawai muka dingayi parks sannan muka je wni restuarant muka ci abinci daga nan muka wuce shop rite, da farko ƙin sakin jiki sukayi sai da suka ga ina kwasar wa su mama da baba kaya sannan suma suka ɗaɗɗauka

 sai yamma lis sannan muka dawo tare da kaya niƙi niƙi ni ban ma san ko nawa muka kashe ba amma nasan mun yi ɓarna ni kaina kayan da na siyawa kaina ba kaɗan bane 



 da daddare naje maiyar masa da card ɗin sa sai yace in riƙe kawi a hannuna, gidiya nayi maisosai sannan na koma ɗaki na 




   kashegari sai 12:00 sannan su maryam suka tafi kamar in bisu amma ba hali haka na haƙura na dawo, ko da na tashi kwanciya sai duk kewar su ta kamani na kira su daya bayan ɗaya muka sha hirar mu sannan na iya bacci 


************

 Tsakanina da aliyu kuwa mun koma ƴar gidan jiya, don yanzu ko ya zo inda nake haɗe rai nake yi ni har yanzu banga dalilin da zai sa ya aure ni ba ba tare da izini na ba,


 Ina zaune naga missed call ɗin maryam wai khadija ta haihu nai mamaki yau watan su guda da sati biyu da komawa amma ta haihu sam cikin ta ba alamar ya tsufa na faɗa araina, tashi nayi tsam na kama hanyar part ɗin aliyu don ina son ayi  sunan da ni 


 yana kwance yana kallon ceiling ɗin ɗakin nasa na shiga da sallamata daga gani yayi nisa a tunanin nasa don ko jin sallamar tawa baiyi ba sai da na ɗan taɓa shi, sannan ya juyo ya ƙura min ido kamar yana neman wani bayani a fuskata

“kamar kinsan tunanin ki nakeyi yanzu, zo ki kwanta kusa da ni” ya faɗa yana me matsa min wuri

 ban musa ba na kwanta kamar yadda ya umarta rungume ni yayi tare da yin ajiyar zuciya, nakan jiyo bugun zuciyar sa sosai kamar zata fasa ƙirjin nasa ta fito, mun ɗan jima a haka sannan ya ɗan sassauta min ruƙon 

“kina buƙatar wani abun ne” ya tambaya, har na buɗe bakina zan yi magana sai wani abun ya faɗo min wato ni bana zuwa pary ɗinsa sai buƙatata ta taso, kunya ce ta kamani na kasa magana
“sweetheart just tell me ko menene”
“dama khadija ce ta haihu” na faɗa da ƙyar
“maa shaa Allah, yaushe”
” ɗazu an sami namiji”
“maa shaa Allah, Allah ya raya kina son zuwa suna ne” gyaɗa masa kai nayi

 "wannan ba komai bane muma tazo ta ziyarce mu dole ne kije, amma bakya ganin kema kafin ki tafi muma mu gwada ƙila ki tafi da ɗan abinki a nan" ya faɗa yana shafa min marata

“bana sallah”
“ohh ba komai ai akwai ƴar dabarar da mata suke yi idan basa sallah kin iya” shiru nayi masa don wannan zancen ya girme ni

ganin nayi shiru yasa shi fara wasa da jikina, ni a ganina bani da abinda zan bashi don haka me zai sa in zauna ina ɓata masa lkc don haka sai na tashi na yi ficewata ina jinsa yana ƙwala min kira amma ban kula shi ba

[7:43PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

   Page :19????


 Shirye shirye tafiya nekeyi ba kama hannu yaro, aliyu ya kaini shopping na kayan jariri da mai me jego muka yo musu siyayya sosai, inda wani less ya ɗauki hankalina na siyo mana shi mu uku don muyi anko, na kai ɗinkunan, na so tahowa da islam amma aliyu yace amaida ita gida don gaskiya iyayen sun mana kara, kuma haka ne gaskiya sunyi kara, haka inaji ina gani muka rabu da islam bayan shaƙuwar da muka ɗanyi 


 sai da da khadija tayi kwna huɗu sannan na kama hanyar lagos tare da aliyu a private plane ɗin sa, ko da muka je a hotel ɗin da yake suka muka, sai da muka kwana ɗaya sannan muka je gidan me jego don yi mata barka, sun yi mamakin gani na sosai

Inda duk inda nabi sai an bini da ido har mamakin mutane nayi wai nice yau na zama abar kallon su,

Ranar suna yaro yaci sunan baban mu abubakar wanda zamu dinga ce masa sadiq, an sha shagalin suna sosai, tun da aliyu ya ajiye ni ban kuma neman sa ba ta ina zan neme sa bayan banni da numbersa, hidimata kawai nake yi har nayi sati biyu da zuwa ba wanda yake takura min balle a tambayi yaushe zan koma

   **********
     *abuja*

yana zaune a ofice ɗinsa yau kusan kwanan sa biyar kenan kullum sai ya wuni da ciwon mara wata ran ma har hana shi bacci yake yi, na yau na fi na kullum don yau hatta zuciyarsa wani irin bugu take yi kamar zata faso ƙirjin sa

 ya kamata in koma china a ƙara duba min zuciyar nan tawa ya kuma faɗa, zazzaɓi ne ya rufe shi wanda hakan ne ya sa shi kashe ac ɗin da ke office ɗin tare da ƙudundune kansa akan couch ɗin da ke ɗakin daga nan bai san inda kanshi yake ba kuma again 


 Farkawa yayi ya ganshi a gadon asibiti, tare da ƙarun ruwa a hannun sa, ko da yayi yunƙurin tashi sai ya kasa duk jikin sa ciwo yake masa gashi har yanzu zuciyar tasa batai masa yadda yake so ba, ƙara kwanciya yayi ya zubawa ceiling ɗin ɗakin ido wasu hawaye suna zuba da idanun sa,


turo ƙofar yaji anyi tare da sallama , tj ne ya shigo da kaya a hannun sa ya nemi wuri ya ajiye su, rufe idon sa aliyun yayi kamar yana bacci

“har yanzu baka tashi ba” ya faɗa, komawa yayi kan kujera ya zauna yana mamakin ya baiga zainab ba, ɗauko wayarsa yayi don ya kirata yaji lfy bata zo ba mijinta a kwance a asibiti, nasan halin ta tsab ƙila wani abinne ya hana ta zuwa


  *lagos*

 ina kwance a ɗakin khadija muna hira da maryam da me jegon, waya ta tayi ringin sunan tj nagani don haka nai saurin ɗauka ina murmushi

“nayi fushi sai yanzu ka iya kirana ka ce min ƴata taje gida ko” na faɗa
“yi haƙuri yayata wallahi na ɗauka salmar ta kira ki ne” ya faɗa, ba haka na saba jin muryar tj ba idan muna waya, magana zanji yana yi kamar zai tsaga min kunne amma yau naji shi a sanyi sa don haka sai na sha jinin jikina

“lafiya ko tj naji ka kamar akwai wani abin”
“kina ina yanzu” ya tambaye ni
“ina lagos ƙanwata ce ta haihu nazo suna, amma in shaa Allah na kusa dawo wa”
“baki son mijinki ba lfy ba, gashi akwance a asibiti” jin an anbaci asibiti yasa ni tashi zaune ba shiri

“me ya same shi lfy lau muka rabu da shi”
“tun jiya da yamma aka tsince a asibiti a sume aka garzayo da shi asibiti” shiru nayi, na rasa abinda zan faɗa, dama bashida lfy ne be faɗa min ba na faɗa araina

“ban sani ba amma bari kaga yanzu zan haɗa kaya na inyi airport, Allah yasa in samu flight”
“in kinsamu sai ki kira ni sai in samu driver ɗin da zai ɗauko ki daga airport ɗin in kin iso”
“ok”

 sallama mukayi inda sai da muka gama sannan na fahinci gabaɗaya hankalin su yana kaina

“lfy yaya, me ya faru waye ba lfy” duk suka jejo min tambaya
“aliyu ne akwance a asibiti ba lfy”
“subhanallahi”

“tafiya zanyi yanzu Allah ysa in samu jirgi”
“muje in raka ki airport ɗin”inji maryam

   minyi sallama da khadija sannan muka kama hanyar sai da naje gida don haɗa kayana nan muke sanar da mama ita ma tace da ita za a je airport ɗin ni dai sauri kawai nake yi, ƙanina ne ya kaimu wanda yake bin maryam ɗan wajen mama, don haka na dinga azalzalar sa ya yi sauri



ko da mukaje airport ɗin na barau da kwaso min kayana ni kuma na tafi counter ko Allah zaisa in samu, luckily 4 me kuwa akqai jirgin da zashi abj a lkcn boarding ma yake yi don haka na biya

“madam babu commercial sit sun ƙare” ta faɗa haushi ne ya kamani yanzu take cemin flight ɗin yana boarding yanzu kuma sits sun ƙare,
“sai dai in kina iya biyan vip” ta faɗa ayangance, harara na daka mata
“ke ni ko kusa da pilot ɗinne saka ni” na faɗa mata ai kuwa nan da nan ta ciri kuɗin su a atm card ɗin dana bata ta cike min na karɓa nayi gaba abina

Naje wajen su mama na karɓi kayana mukayi sallama sannan na kama hanyar hawa jirgi ku sai ku ɗauka vip ɗin wani abin arziki ne mtss nai tsaki babu wani banban ci kawai dai kujerun sunfi ɗan girma ne da kuma ɗan space tsakanin su

 tj na kira na faɗa masa na taso yai mamakin samun jirgin da nayi da wuri hakasannan yace min kafin in ƙaraso zan tadda driver na jiranamu kai sallama na kashe wayata sai fatan Allah ya sauke mu lfy


  *************
 *abuja*


mun sauka lfy inda na tarar da driver yana jirana, na shiga muka kama hanyar asibitin, ko da na shiga ɗakin  yana zaune akan gadon da bowl na abinci a gabansa, yai mamakin ganina inda naga ya juya ya doka wa tj harara daga gani yayi warning ɗinsa na kar ya gaya min, shi kuma tj ɗin sai yayi kamar bai gani ba, ya rame sosai sai fari da yayi fayau haka



ƙarasawa nayi kusa da shi ina yi masa sannu tare da zama akan gadon na ɗauko bowl ɗin ind naci karo da farfesun kayan ciki, fara bashi nayi, da farko kamar bazai karɓa ba amma da yaga na tsire shi ido kuma naƙi sauke hannu na sai ya bude bakin sa ya karɓa, cokali buyi yayi naji yace 

“wasshh Allah na” tare da dafe ƙirjinsa
“sannu” muka haɗa baki nida tj
“ƙirjin ne again bari inje in kira likitan yazo ya kuma duba ka” tj ya faɗa yana fita, na ci gaba da bashi farfesun kaɗan ya kuma karɓa yace ya ishe shi, ajiye wa nayi na ɗauko hanky na ɗan gyara masa bakin sa sannan na ɗauki bowl ɗin don in mayar inda hakan yai dai dai da shigowar dr. ɗin da tj

“sannu ya jikin” dr ya faɗa yana buɗe file ɗin da ya shigo da shi
“ina ne yake ma ciwo” ƙirjin shi ya nuna dai dai in da zuciyarsa take
“sannu ai na baka pain reliever amma ina ƙara tuna maka ana sallamar ka kaje a ƙara duba maka zuciyar nan taka, cikin ya hdaina ciwo”
“zan je in shaa Alla ya daina”
“ok shiike nan ba wani matsala da ka ɗan ƙara warware wa sai a sallame ka” Inji dr
“ok dr mun gode” muka haɗa baki

ko da dr ɗin ya fita sai tj ya ƙara matsawa kusa da aliyu
“ɗan uwa me yake damun zuciyar taka” ya tambaye shi, nima abinda nake son ji kenan don haka sai na mai da hankalina akan aliyun inji me zai ce, ɗagowa yayi muka haɗa ido wanda hakan ne ya sani sauke nawa idon ƙasa
“ba komai kar ka samu damuwa, zuciyar tawa ce wani lkcn sai ta dinga bugawa fiye da yadda ya kamata”
“tun yaushe” ya kuma jeho masa da tambayar

dafe ƙirjin nashin da yayi ne tare da kiran sunan Allah yasa tj ɗin daina masa tambayoyin da yake masa
“tj ɗan kwantar da ni in huta na gaji da zaman, ita ma ka kaita gida ko ta samu ta ɗan huta tunda daga tafiya take”

   ni da kaina naje na kwantar da shi sannan nace wa tj ka tafi kawai zan cigaba da kula da shi, kallo na aliyun yayi baice komai ya lumshe idon sa sai bacci, gyara masa kwanciyar nayi sannan na koma gefe na zauna tj yayi mana sallama shima ya tafi ni kuma na hau tunani na


kar dai ace ni na sawa mutumin nan ciwon zuciya, kai yama za ayi ace ni na sa masa yaushe muka haɗun da zan sa masa wani ciwo, to wai  me yasa a zuciyar sa haka har ya kamu da ciwo kana da kuɗi me zai dame ka na faɗa arai na nai ta wasuwasi na har nima baccin ya kwashe ni ban  daina tunanin me yake damun aliyu ba

[7:43PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

 By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

???? nasibi writers association????
we shine with the smile of our readers so keep smiling ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺

 Page :20????



   Kwanan mu 15 a asibitin sannan a ka sallame mu ya samu sauƙi sosai kuma zuciyar tasa ta daina masa ciwon, amma duk da haka likita yai masa tunin na cewar ya koma ya kuma ganin likitan sa, inda sai daga baya ya faɗa mana cewar shekarun baya ne yayi fama da ciwon inda yake ganin likita a china,



 a irin jinyar da nake yi na fahinci cewar tsabar sha'awr da tayi wa aliyu yawa ce ta haddasa masa ciwon cikin wanda shine ummul aba'isin tada ciwon zuciyar tashi, rasa abinda zance nayi da dr ɗin yayi min bayani lkcn da naje office dinshi karɓo takardar sallama, na kuma kuɗiri niyya a raina in shaa Allah in dan tanine Mijina bazai kuma ciwon zuciya ba, babu yadda banyi ba mu saba da shi tun a asibitin amma ƙiri ƙiri yaƙi sai ko ya tsiri baccin ƙarya har na gasken ya tadda shi ko kuma dai ya ɗauki qur'ani ya tsiri karatu




     Ko da muka koma gida direct ɓangarensa muka nufa sai da naga ya kimtsa yai wanka ya sha magani ya kwanta sannan nima na wuce part ɗina don inɗan kimtsa

a gare na tadda da shi kamar da mutun nasan ta wannan ɓangaren bani da matsala ɗan watsa ruwa nayi ajikina sannan na shiga yau so nakeyi inyi wa mijina abinci da kaina

  Tuwon semo na tuƙa masa da miyar egusi wacce na soya egusi ɗin da ƙwai yadda egusi ɗin zai duddunƙuƙe sannan ya kakkama ragowar kayan da ke cikin miyar, sai farfaesun catfish, sai zoɓo naji ance zoɓo ma magani ne


tun da nazo gidan ban taɓa ganin anyi mana abincin mu na gargajiya ba sai na bature, don haka yau na canza salon da kaina, ko dana gama wanka nafaɗa inda sai da na shafe kusan minti talatin dani da yi masu yimin kwalliya don in fito fes da ni 


  wata yellow strapless riga na ɗauko wacce iyakacin ta rabin cinya na saka, bata hannu, sai zip a bayan ta, ta kamani sosai tai min ɗam kamar dama jikina aka gwada aka yi rigar, suma sai yaba min suke yi yadda nayi, a zuciyata nace balle kuma shi wanda akayi domin sa



   a back yard garden ɗin mu nasa suka jera min abincin sannan na shiga don inga ko ya tashi, yana zaune akan sallaya daga gani ya idar da sallah ne, samun wuri nayi na zauna kusa da shi har ya idar muka shafa tare

“ka zo muje kaci abincin ka” na faɗa ayangance
“ok ganin nan zuwa bari in ninke sallayar na” karɓar sallayar nayi na fara ninkewa

ko dana juyo zan masa magana sai na tsince shi yana kallona, kau da kansa yayi tare da yin gyaran murya

“muje ko” ya faɗa, noƙe kafaɗa ta nayi tare da zunɓuro baki
“ni dai sai ka ɗauke ni” na faɗa ashagwaɓe, murmushi yayi tare da kauda fuskar sa gefe
“in banda abinki kina ganin banni da lfy kice in ɗauke ki”
“to zaka ɗauke ni knka warke” na faɗa tare da matsawa kusa da shi har ƙirjina na shafen sa, murmushin ya kuma yi
“muje muci abinci yunwa nake ji”

hannun shi naja muka ƙarasa garden yai mamakin yadda nasa aka tsara wajen yai kyau sosai har kasa shiru yayi sai daya tanka
“welcome back party na haɗa maka” na faɗa masa a cikin kunnen sa wanda sai danayi ɗage sannan na faɗa, ɗan janye jikinsa ya ɗanyi daga nawa sannan ya samu wuri ya zauna, ko dana zuba mai abinci nan ma naga mamaki tab fuskar sa amma baice komai ba

    malmala biyu yaci sannan ya sha zoɓo sosai, kana ya gode wa Allah

“daga ji yau ba abincin cook na ci ba” ya faɗa da fara’a a fuskar sa
“girkin matar ka” na maida masa da martani
“gaskiya yai daɗi kin cancanci kyauta, yaushe rabon da cin abincin gargajiya mai daɗin wannan tun hjy na da rai” jikina ne yayi sanyi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Leave a Reply

Back to top button