WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 7

 

????WATA TAFIYAR????       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

????????????????????????????????

*????✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????✨*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“????`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~????????~~~~~~~

PAID BOOK

                  Free Page    

               07

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa Umar Zenith Bank, 

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

 Ganin ana gab da kiran sallah Magrib  ne yasa kawai ya wuce masallaci,bai samu shigowa cikin gida ba sai bayan sallar Isha’i,kai tsaye shiyan Nanne ya shiga da sallama,lokacin ita ma tana zaune saman dadduma tana jan Carbi,niman wuri yayi ya zauna shima yana yin nashi da hannu,sai da ta kammala ta yi addu’a sannan suka shafa tare, 

Tasowa ya yi daga inda yake,ya dawo kusa da ita ya zauna”Nanne ina wuni”

“Lafiya klau ɗan nan”

“Ya ƙarfin jiki”

“Alhamdulillah” daganan shiru ya yi yana jujjuya maganar,dan ya kasa ta yanda yai faɗa mata, kamar daga sama ya ji ta ce “kana tunanin ta yanda zaka sanar da ni ka bada Auren ƴarka ne? Lokaci ɗaya ya ji gaban shi ya faɗi,to waya faɗa mata, ko kuma a ina taji,dago kan shi dake duke ya yi yana kallon yanayin ta,abin da ya ƙara bashi mamaki shine rashin ganin damuwa a fuskar ta kamar yanda ya yi tsammani,cigaba da magana ta yi “kana mamakin ta yanda aka yi na sani ne? To hakan ba abin mamaki ba ne idan ka yi la’akari da yanayin matan gidan nan” Ɗan shiru ta yi,sannan ta ci gaba da cewa”abin da ka yi dai-dai ne ɗannan,naji daɗi sosai domin hakan da ka yi ya tabbatar min da ko ba na raye Asma’u ba zata yi kukan rashin dangi ba,na tabbatar da zaka riƙe min ita amana,ina Alfahari da kai Mudansir ako da yaushe,kuma na gode da kake tayani rike amanar ƙanwar ka,na gode Allah ya muku Albarka”

Hannun ta ya rike,yana mai jin hawaye na cika ma shi ido”Nanne ki daina gode min akan Asma’u,domin ita din jinina ce,kuma ina Alfahari da hakan,duk abun da nasan zanma ya’yan da na haifa to zanma Asma’u fiye da hakan,Nanne na gode da kika fahimce ni,na kuma gode akan kwarin gwiwar da kike ƙaramin a koda yaushe a kan Asma’u,kuma insha Allah sai mun yi Alfahari da wannan Auren ba ma mu kadai ba Nanne har ta waɗanda basu zata ba,sai abun yazo masu a ba zata,ina mai fatan hakan”

Hawayen ta ta share,tana mai tausayin rayuwar yarinyar,Allah sarki yarinya karama tana fuskantar jarabawa haka,ita dai fatanta Allah yasa nan gaba komai zai zo yazo mata da sauƙi,domin haka kawai jikin ta ke bata kamar akwai wani abu kuma da zai tunkaro su,ita dai fatan shine yazo da sauki,Allah ya gani ta matukar kaunar Asma’u haka kuma tana tausayin ta,tana kuma yi mata fatan alheri,kullum addu’ar ta shine in suna da rabon ƙara haɗuwa da juna Allah ya haɗa su,yasa yanda ta miƙa mata ita dunƙule cikin zani,yasa ita kuma a ranar ta kama hannunta ta haɗa da na Asma’u tana mai murmushi tana kallon fuskar ta,ta ce ga Amanar da kika ba ni,a yau gashi na damka maki abin ki cikin aminci,tana fatan wannan lokacin ya kasance tana raye. 

“yaushe suka tsara za a gudanar da komai? 

” Nan da wata daya Nanne ”

“To me su Ɗan Nanne suka ce”

kasa bata amsa ya yi,dan haka kai kawai ya dukar,dan ba zai iya sanar da ita cewa sun kwashe kudin sun wuce dashi ba. 

Ganin haka yasa kawai ta yi murmushi,domin kaf yaranta ba wanda ba ta san halin shi ba “karka damu akwai ajiyar da nake da shi,duk da bai da yawa sosai,amma na tabbatar zai taimaka maka ta wani wurin,sannan ina fata ka faɗa masu suje su gaisa da ƴan uwan Babanta”

“Eh Nanne,na faɗa  masu,sannan zuwa gobe in na dawo aiki zanje da kaina sai mu kara tattaunawa”

“To Allah ya kai mu”

Da Amin ya amsa, daganan sallama ya mata ya fita. 

Da kallon tausayin ɗan nata ta bi shi,tana mai   tunanin irin yanda Matar shi, dazu tazo tana ta mata hauka akai, akan me yasa be bada auren yarsu ba sai wannan mahaukaciyar gidan,”in Allah ya yarda Asma’u sai kowa ya sha inuwarki, da yardar Allah “.

     Zaune suke a falon gidan shi suna bashi labarin abin daya faru,sosai suke dariya mutanin”ni wallahi Yaya Ahmad na ɗauka zamu samu matsala da mutanen amma sai na lura makwadaitan kuɗi ne”

Murmushi yayi yana juyawa a kan kujera”ai haka dama muke so, domin irin su sunfi daɗin harka”cawar uncle Ahmad. 

Haris ne yace “uncle  me yasa kuka sa bikin har tsayin wata ɗaya,ni gaskiya da sati biyu kuka saka, dan wallahi na matsu na bar ƙasar nan”

Uncle Tahir ne ya kwashe da dariya “kai dai Haris faɗi gaskiya”

“Allah uncle ji nake garin ga ya ishe ni”

Uncle Ahmad ne ya katse su”gobe saiku shirya ku je ku gaida dangin Baban ta, kai kuma Haris sai kaje ku ga juna da yarinyar ”

Da sauri ya zaro ido”uncle! Ni zanje ganin mahaukaciya! Salon ta zo ta shake ni,bayan kuma kasan yanda nake tsoron Mahaukata! Gaskiya A’a ni ba zan je ba,kawai dai ku bari idan an daura auren na ganta daga nisa”

Duk yanda suka so su daure kasawa suka yi,dan uncle Nasir tsabar dariya sai da ya fado daga kan kujera.

Da kyar uncle Ahmad ya ɗaure yace”kai yanzun haka za ayi auren kana tsoron Amarya? 

“Wa yaga Ango me tsuron Amarya” Cewar uncle Tahir yana ƙara fashewa da dariya. 

Ganin yanda suka sashi gaba da dariya yasa ran shi ɓaci,dan haka tsaki ya ja, ya tashi zai bar masu wurin, da sauri uncle Ahmad ya dakatar da shi”haba magaji yi haƙuri zo ka zauna”

Bata fuska yayi”a gaskiya na sauke wannan tsarin,a fasa auren ba na so”ai jin abin da yace yasa da sauri suka bar dariyar da suke har suna haɗa baki wurin cewa”What”

“Eh a fasa ba na yi,dan ba zan iya tsayawa da mahaukaciya ba” Ya karasa faɗa yana kauda kai gefe. 

“Haba mana magaji ya zaka mana haka,bayan Aski ya na gab da zuwa gaban goshi, pls  kar muyi haka da kai” Uncle Nasir ya faɗa yana wani marairaice murya. 

“Ni dai ba zan tsaya da ita ba,gata wata ƴar ƙauye da ita”

Uncle Ahmad ne yace”to da kake wannan zancen waye yace ka tsaya da ita ko ka zauna da ita, kawai dai sau daya ne zaka dinga zuwa wurin ta a sati, kaga kenan sau uku zaka wurin ta,, in yaso sai mu dinga aika mata da kudi da kyauta,kaga kenan iyayenta ba zasu zarge komai ba,tunda su makwadaita ne”

Uncle Nasir ne ya amshi zancen”kuma ba ganin ta zakayi ba,dan da an yi Auren ta kammala mana aikin da zata mana ba shi kenan ba,kai kuma sai dai kawai ka tafi duk ƙasar da kake so,kuma ka aure matar da kake so, amma ka tausaya mana ace tsayin shekara uku muna jira,sai yanzun kuma da muka fara hangan nasara sai kace ka fasa,kasani fa wannan abun ba mu kaɗai bane har da kai Haris,domin yanzun ne lokacin mu,kuma lokacin samun nasaran ka a kanshi na har abada, domin na tabbatar idan har wannan abin ya kammala yanda ya kamata,,to ka masa zarra ke nan kuma ba zai taba kamo ka ba,sai dai ya  tabbata a yanda yake”

Wani irin lallausar murmushi ya yi,shi sam wani lokaci mantawa yake dashi,

to ya zaiyi a lokacin da ya ganta a matsayin matar shi, gaskiya zai su ganin yanda zai yi,Allah sarki wannan shi ake kira taron zaka zani Makaɗi gidan Mabushi,an haɗu da an dace,tuna hakan yasa ya fashe da dariya”gaskiya ka faɗa uncle,zuwa anjima zanje muga juna da yarinyar “yana kaiwa nan ya juya ya fita, yana mai ci gaba da dariya. 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button