Labarai

Malamin Coci Ya Bace Tare Da Mabiyan Sa Mutum 20 Bayan Yace Subi Bayan Sa

Sama da mako guda ba a san inda Fasto Kalibala Samuel da mabiya 20 daga cocinsa suke ba.

An ce Kalibala ya shawo kan ’yan cocinsa da su kulle gidajensu, su bi shi zuwa wani wuri da ba a sani ba, sannan su kashe wayoyinsu.

Tuni dai ofishin ‘yan sanda a Uganda ya fara neman mutanen da suka bace, tare da fatan mayar da mutanen da suka bata ga iyalansu legit.ng ta rawaito.

Sama da mako guda ke nan da Fasto Kalibala Samuel ya bace tare da mabiya sama da 20 daga cocinsa, cikinsu har da iyali mai mutane bakwai.

Dangane da bacewar, jami’an ‘yan sanda a yankin Mityana na kasar Uganda suna gudanar da bincike a kan halin da mutanen ke ciki.

Duk membobin sun kashe wayoyinsu

A cewar rundunar ‘yan sandan Uganda, ‘yan uwa bakwai din sun hada da Namuwaya Jesca, Ssekyewa Shakim mai shekaru 19, Nampeewo Shifrah mai shekaru 17, Muteesasira Muhammad mai shekaru 10, Ssenabulya Muhammed mai shekaru 8, Nakintu Angel mai shekaru 4 da Uwuzeeye Mable.

Bayanai sun nuna cewa Fasto da mabiyansa sun kulle gidajensu, sun bace kuma tuni suka kashe wayoyinsu.

“A halin yanzu muna bin diddigin bayanai, bayan daya daga cikin mabiyan, ta kulla hulda da daya daga cikin ‘ya’yanta, wanda ta bari a baya,” in ji sanarwar ‘yan sandan.

Abin da ya warware shi ne, nan take mutumin ya sake kashe wayar kafin ya bayyana inda take.

Za mu gano su, in ji ‘yan sandan Uganda

Rundunar ‘yan sandan ta yi Allah-wadai da matakin faston, inda ta kara da cewa abin takaici ne a gare shi ya yi amfani da hanyoyin da ba su dace ba wajen sarrafa mabiyansa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Irin wannan hali na da yuwuwar budewa ‘yan uwa da suka rasa ‘yan uwansu raunuka a lokacin da ake gudanar da bikin Kibwetere a Kanugu.”

Sai dai an tabbatar wa ‘yan uwa da ‘yan uwansu da suka bace cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don haka kada su karaya.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button