NAJEEB 41

Malamin ganin haka yasa gaba d’aya yaji NAJEEB din ya k’ara bashi tausayi Sosai, lallai an bar gini tun ran Zane, da yawa haka yanzu iyaye sukeyi basa bama yaransu ilimin addini saina boko, wanda wannan Abun ya zama ruwan dare, sudai burinsu y’ay’ansu suyi ilimin boko kawai na addini kuma ko oho, Allah yasa mu dace.
Da yawa masu kud’i suna d’auka kaman ba zasu mutu ba, gaba d’aya sunsa duniya a gaba, basa tuna mutuwa, sudai duniya kawai suka sa a gaba…..
Malamin ya kira Sunan NAJEEB da fad’in Allah mai yafiya ne ga bayinsa baya Kama bawa da laifin da bai sani ba, sannan koda mutum ya aikata Sabo, Indai harya tuba toh Allah zai yafe masa, a cikin…..
SURATU AL’IMRANA:
Wanda take karantar da cewa Allah yana karban addu’ar wanda ya kira shi da gaskiyar niyya, kuma yana keta al’adu Da wannan kira. Babu abin da yake da wuya ga Allah idan an kadaita shi da tsarkakewa daga shirka da abin da ya yi Kama da shirka.
Toh ka gani Allah yana yafe ko wani laifi amma banda shirka
Allah babu wani abin bautawa face shi, rayayye mai tsayuwa da Kome, Al’imran Aya ta (2)
Ya sassaukar da littafi a gareka da gaskiya, yana Mai gasgatawa ga abin da ke gaba gare shi, kuma Allah ya saukar da attaura Da linjila. Al’imran Aya ta (3)
A gabani, suna shiryar da mutane, kuma ya saukar da littattafai masu rarrabewa. Lalle ne wad’anda suka kafirta da ayoyin Allah suna da azaba Mai tsanani. Kuma Allah mabuwayi ne, ma’abucin azabar ramuwa. Al’imran Aya ta (4)
Lalle ne Allah babu wani abin da ke boyuwa gareshi a cikin k’asa, kuma babu a cikin sama. Al’imran Aya ta (5)
Malamin ya kalli NAJEEB yace kaga Allah yana Sonka da rahma tunda har ka farga ka gane, domin yau Idan mutum ya mutu bashi da wani hujja ko uzuri da mutun zai kawo wanda ya hanashi sanin uban gijinsa
Amma yanzu da yake Allah na Sonka da rahma gashi ka farga da wuri tun lokaci bai k’ure maka ba
An kawata wa mutane son sha’awoyi d’aga mata da d’iya, da dukiyoyi abubuwan Tarawa daga zinariya da azurfa da Dawaki kiwatattu da dabbobin ci da hatsi. Wannan shine dad’in rayuwar duniya. Kuma Allah a wurinsa kyakyawar makoma take. Al’imran Aya ta (14)
Kace : shin kuma, in gaya muku mafi alheri daga wannan? Akwai gidajen Aljanna a wurin Ubangiji saboda wadanda suka bishi da takawa, koguna suna gudana daga k’arkashinsu, suna madauwama a cikinsu, da matan aure tsarkakku, da yarda daga Allah kuma Allah mai gani ne ga bayinsa. Al’imran Aya ta (15)
Allah ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face shi, kuma mala’iku da ma’abuta ilimi sun shaida, yana tsaye da adalci babu abin bautawa face shi mabuwayi, mai hikima. Al’imran Aya ta (18)
Malamin ya kalli najeeb yace Allah mai gafara ne, sannan Allah mai adalci ne, yana yafiya Idan aka ro’ka, yana amsa kiran wanda ya kirashi….
Kace: Idan kun kasance kuna son Allah, toh ku bini, Allah ya so ku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Kuma Allah mai gafara ne mai jin k’ai. Al’imran Aya ta (31)
Toh kaji abunda wannan ayar take fad’a? Allah mai gafara ne, Najeeb Allah yana son Idan bawansa zai tuba yayi tuba ta tsakani da Allah wanda ya tuba kenan, bawai mutum yace Allah na tuba ba, sannan ya koma abunda yake aikatawa na sak’o ba, Allah baya son irin wannan tuban….
Najeeb yayi ajiyan zuciya tare da fad’in Malam gaba d’aya Ina son insan addini na, sannan ina son ka koyar dani kaman sabon wanda ya musulunta wanda bai San komai ba, ina son ka fad’amin duka hakkokin dake kaina, sannan mai addini yayi umarni da muyi da kuma wanda yayi hani dashi, wlh Malam yau kawai nima da kaina …… Maganan ibtisam ta fad’o mishi a cikin kunne Ina jin kunyar kiranka da sunan musulmai….. Wani hawaye Mai zafi yaji ya fito Mai, lallai dole tace haka, shima da kanshi abunda yaji yanzu kenan, gaba d’aya yana jin kunyar kiran kanshi da sunan musulmai….
Malam dinne ya katse mishi tunani tare da fad’in Alhmdlh tunda har zaka Fara koya, lallai mutane irinka suna da Sa’a a rayuwa, kwata kwata wata d’aya zanyi a America in koma saudiya, amma yanzu just kawai for you zanyi wata uku, domin nida kaina naji Ina burin ka koyi abubuwa da yawa, kuma insha Allah inka dage zaka San abubuwa da yawa, yanzu abu na Farko kasan miye addini?? Ya ake bauta ma Allah, abunda zamu Fara kenan…….
Tun daka ranan najeeb ya Fara d’aukan darasi wajan malamin, kuma malamin ya lura najeeb yana son karatun gashi yana saurin d’aukan abunda aka koya mishi, hatta sallah najeeb ya gane da ba dai dai yakeyi ba, domin kuwa a da kawai yana yine sunan muna musulmi.
Najeeb kullum yayi sallah yana ro’kan Allah akan ya bud’a Mai kwakwalwa, tare da neman gafaran Allah akan abunda ya aikata cikin rashin sani, sai dai abu d’aya dake ranshi yana fama da yawan sha’awa ga tunanin ibtisam ko a wani hali take yanzu oho, domin tunda yazo bai kuma zancen taba, ko yayi waya da iyayenshi baya magananta Suma basa masa zancan ta
Najeeb ya fad’ama Malam irin yawan sha’awan da yakeji, inda malamin yace ya dinga yin azumi
Hakan koh yakeyi yana azumi, lallai najeeb ya yadda addinin musulunci bai boye komai ba, a kullum yaje wajan malam sai yaji wani sabon Abu Wanda bai taba jiba, wasa wasu har yayi wata d’aya yana d’aukan darasi, najeeb yasan abubuwa da yawa, yasan yanda ake bada Zakka, yanda ake kula da hakkin iyali, yanda zai bauta ma Allah, abubuwan da Allah ya hana da Wanda Allah Ya halitta, a halin yanzu malamin yana koya mai ba’ki domin yace Idan ya iya zai iya karanta komai……
ABU ZARIA FEMALE HOSTEL
ibtisam gaba d’aya ta canza ta rame gashi sun Fara exam, abubuwa sun Mata yawa a Kai na Farko ga cewa har yanzu akwai aure tsakaninta da najeeb na biyu gashi ko kira babu balle yasan wani hali take, wani irin hawaye ne ya zubo mata a ido tare da fad’in inda kabir ta aura daba haka ba , da tasan yanzu yana can yana nuna Mata so, tare da caring, kai auren wanda baka so babu dad’i ko kad’an
Tashi tayi ta goge hawayen dake idonta inda ta fita waje ta zauna a wajan wata bishiya tana danna wayarta wanda kabir ya bata, kiran iPhone, kaman daka sama taji an rufe Mata ido, da sauri ta Fara k’okarin cire hannun a fuskanta, k’okarin cire hannun tayi tana fad’in Zarah na gane ki AI.
Dariya Zarah tayi tare da fad’in taya akai kika gane?
Ibtisam murmushi tayi tace kamshin turarenki mana
Zarah tayi dariya tare da fad’in kai yau paper din yau yaso ya caza min kwakwalwa Wlh, abun babu dad’i
Ibtisam tace Kai ni gaba d’aya ma Sai dai ince Allah yasa dai inga dakyau, domin wlh Zarah kwata kwata ban San mai nake rubutawa ba, ko karatu bana iyayi daka na Fara sai inji baya shiga, wlh abubuwa sun min yawa
Zarah tace ibtisam Nima na lura da hakan, tunani ne ya miki yawa zaki ce, ba abubuwa ba
Ibtisam tace Hmmm
Zarah taci gaba da fad’in ibtisam ya kamata ki yarda ki kuma amince kiyi hakuri kina son mijinki ki, ki yadda ku zauna komai ya wu……
Ibtisam wani mugun kallo ta watsa ma Zarah, tare da fad’in dan Allah ya isa haka malama, ni na ce miki Ina sonshi?? Ko ni nace miki ina bukatar zama dashi?? Zarah yanda d’an uwanki baya bukatar zama dani Toh nima haka bana bukatar zama dashi, ki duba saki d’aya ya rage mana amma yace ya sakeni, inda badan ina haila ba, toh da sakin ya saku, wlh Zarah na tabbata tunda harya iya k’arasa igiyar dake tsakanin mu a lokacin da badan haila ba da yanzu babu auren, tun daga lokacin na tabbatar baya son zama dani, na kuma tabbatar da tsanar da yakemin da gaske ne…… Sai kuma ta fashe da kuka
ita dai Zarah ido ta bita dashi
Ibtisam cikin kuka taci gaba da fad’in najeeb ya cuceni ya amsa budurcina ba tare da saninshi ba, burin ko wace mace takai budurci d’akin mijinta yanda zata samu girma da mutunci a wajan miji, haka naita lallaba kaina tare da taimakon Allah, na ri’ke kaina Amma najeeb yayi sex dani ya rabani da wannan budurcin ba tare da saninshi ba, a lokacin inma ni ba virgin bace bai sani ba, tunda bai San inda kanshi yake ba, yamin ciki yace ba nasa bane, harta kamashi nayi yana…… Sai kuka mai cin rai
Zarah shafa mata baya take alaman tayi hakuri tayi shuru tabar kuka
Ibtisam tace wlh Zarah tun ranan da Nayi yunkurin zubar da cikin nan, amma bai zube ba, daka ranan Nayi nadama, kuma sai Allah ya jarabceni da son cikin, domin tunawa da Nayi inda ya fita da nasha magani Nayi kissan Kai wannan shine dalilin da yasa naji jikina ya mutu, sai gashi washe garin ranan ganin halin da najeeb ya shiga Wanda yasa Nayi mugun tsorata na rasa cikin Wlh duk yanda najeeb yakai da bacin rai Ina tunanin Bai kaini ba, nasan dole yayi zargin nina zubar domin a jiya nayi k’okarin in zubar abun baiyi ba, sai gashi washe gari ya zube…..
Dan shuru tayi tana zubar da hawaye Mai zafi, sannan taci gaba da fad’in, inda kowa zai fad’i sanadin zubar da cikin zai gane cewa najeeb ne sila, tunda inda baisha alcohol ba, yaje ya saka kwalba shigan mishi ciki ba aida banji tsoro ba har cikin ya zube……
Zuwan kubra ne yasa ibtisam yin shuru da maganan da takeyi wanda yasa tayi saurin goge hawayen da takeyi.
Kubra zama tayi kusa dasu tana fad’in na shiga uku yau, kai ku tayani murna Allah ya soni da kunji labarin na mutu
Zarah tace maiya faru dake??
Tace Hmmm Kedai Bari…… Yau na had’u da dan iskan daya so d’aukan rayuwa ta, Kai Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, sai ta saki kuka tana fad’in yau na tsallake Rijiya da baya, ban taba jin ance yau anyi Tsafi da karuwa ba sai dai inji ance anyi Tsafi da kamilan mace, Ashe yanzu duniya ta canza da kowa ma yi akeyi
Sex yace zaiyi dani, na amince mukai na Farko ya shiga toilet saina dauki wayarsa domin tayi min kyau saiga sa’ko ana fad’in idan kayi sex din Farko da ita a…… Daka nan sa’kon ya datse, nan na bud’e sa’kon naci gaba da karantawa….. A na biyun saika saka Mata tsutsa domin dodon mu ya nuna yarinyar tana da baiwa sosai, yanzu haka inkun gama na biyun tsutsan ya fita nan take ka korata tun kafin ta mutu domin awa biyu zatayi indai tsutsar ya shigeta…….. Saita fashe da kuka tana fad’in Wlh ban gama karantawa ba na saki wayar tare da d’aukan jakata na gudu, ina hanya sai kirana yake mutumin daka karshe kashe wayan Nayi…..
Wlh ban taba jin tsoran Allah ba irin yanda naji tsoran in had’u dashi yau inya d’auki rayuwa ta, wlh gaba d’aya tsoran Allah ya kamani, in Naje Mai zance mishi??
Na farko nice na kai kaina da kaina, naje anyi zina dani, na mutu ba tare dana Tuba ba, wayyo Allah na na shiga uku……. Kuka take sosai tana fad’in Allah na tuba, wlh yau Nayi nadaman abunda nake aikatawa lallai duniya Abun tsoro ne, gaba d’aya har yanzu wlh a tsorace nake, gashi na Farko da yayi babu condom ni yanzu tsorana kar ace ya sakamin tsutsar tun a na farkon ba tare dana Sani ba, ko kuma ya samin wata cutar tunda Dan mafia ne…..
Ibtisam gaba d’aya jikinta har rawa yake saboda tsoro tare da tausayin kubra din
Zarah kam tace kubra tunda yanzu kin gane gaskiya, sai kiyi ta neman gafaran Allah tare dayin istigfari Allah zai yafe miki, domin Allah mai gafara ne ga bayinsa, Indai har mutum ya nemi gafara wajan Allah toh Allah zai yafe masa
Kubra tace zarah ina jin tsoran kar in mutu, wlh ji nake kaman ya samun tsutsan tun sex din Farko da mukayi, wlh Ina jin tsoran in mutu na shiga uku kuka take Sosai mai ban tausayi kallo d’aya zaka mata ka gane tana cikin firgici tare da tsoro
Ibtisam tace ki daina wannan kukan kubra, mutuwa hutu ce, karki manta duk Mai rai Mamaci ne, sannan Koba yanzu ba dole akwai ranan da zamu mutu, ga Allah muke kuma gareshi zamu koma, babu wani abun tsoro a cikin mutuwa, domin mutum zai koma wajan mahaliccin shi…..
Kubra cikin kuka tace nasan haka, amma ni ban aikata abunda zanso in had’u da ubangina ba…..
Ibtisam tace kar kice haka Allah cikin SURATUL AN’AM…..
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halitta sammai da k’asa kuma ya Sanya duffai da haske, sa’an nan kuma wad’anda suka kafirta da ubangijinsu suke karkacewa. SURATUL AN’AM Aya ta (1)
Shi ne wanda ya halitta ku daga laka, sa’an nan kuma ya yanka ajali, Alhali wani ajali ambatacce yana wurinsa, sa’an nan kuma ku kuna yin shakka. SURATUL AN’AM Aya ta (2)
Kuma shine Allah a cikin sammai, kuma a cikin k’asa, yana sanin asirinku da bayyanenku, kuma yana sanin abin da kuke yi na tsirfa. SURATUL AN’AM Aya ta (3)
Kubra duk abunda kikeyi Allah yana kallonki, na tabbata Allah yana sonki da rahma shine ya had’aki da wannan mutumin domin ki tuba, wlh kubra Allah yana son bayinsa, ki duba irin girman zunubin da muke aikatawa amma idan muka kirasa saiya amsa, idan muka ro’kesa gafara saiya yafe mana…..
Kubra rungume ibtisam tayi tana kuka, tare da fad’in hakane ibtisam Wlh na yarda Allah yana sona shi yasa ya ganar dani da sauri, wlh ko yanzu Allah ya d’auki rayuwa na tuba da duk abunda na aikata, kuma Wlh tuban gaskiya Nayi, in kuma inada rayuwa gaba, zan kasance mai bauta ma ubangijina tare dayin duk abunda yayi umarni inyi
Ibtisam tace Alhmdlh tare da fad’in
Wanda aka juyar dashi daga gare shi, a wannan Ranar, toh Lalle ne (Allah ) Ya yi masa rahama. Kuma wannan ne tsira bayyananniya. 16 SURATUL AN’AM
Idan Allah ya shafe ka da wata cuta, to babu Mai kuranyewa gare ta, face shi, kuma Idan ya shafe ka da wani Alheri, toh shine, a kan Kome, mai ikon yi . 17 SURATUL AN’AM
Kuma shi ne tankwasa a kan bayinsa, kuma shine mai hikima, masani. 18 SURATUL AN’AM
Toh Kinga ya Allah shine mai shiriya da bayinsa, Kinga da Farko kin fad’a halaka, amma yanzu Allah ya ganar dake
Zarah tace hakane, kubra ki k’ara godema Allah, idan kika duba duniya ba komai bane, babu jin dad’i a duniya, cikakkiyar ni’ima tana Aljanna
Kubra tace hakane, amma sai Ina jin tsoran kaman Allah bazai yafe min ba, ki duba nice bin maza lesbians duka Inayi……
Ibtisam tace karki k’ara fad’in haka ki duba girman laifin da shaidan yayi ma ubangiji, idan kika duba SURATUL A’araf….
Lalle ne hakika mun halitta ku, sa’an nan kuma mun suranta kuyi sujada ga Adam. Sai suka yi sujada face Iblis bai kasance daga masu yin sujadar ba. Aya ta 11 suratul A’araf
Ki duba irin laifin da Iblis yayi wanda Allah ya bashi umarni ya’ki bi, domin yana ganin shine mafifici domin an halicceshi da wuta, shi kuma Adam an halicceshi da laka
Kinga dai irin girman kan shaidan wanda yayi ma Allah amma daya nemi alfarma sai Allah yayi mishi inda yace ma Allah….
Yace kayi mini jinkiri zuwa ga Ranar da ake tayar da su. Suratul A’araf Aya ta 14
Allah yace lalle ne, kana daga wadanda aka yi wa jinkiri . Suratul a’araf Aya ta 15
Bayan Allah yayi masa jinkiri sai shedan yace ….
Yace to Ina Mai rantsuwa da halakarwar da kayi mini Lalle ne ina zaune musu tafarkinka madaidaici. Suratul A’araf Aya 16
Sa’an nan kuma, hakika Ina je musu daga gaba garesu, kuma daga baya gare su, kuma daga barin jihohin damansu da barin jihohin hagunsu: kuma ba za ka sami mafi yawansu masu godiya ba. Suratul A’araf aya 17
Kinji irin abunda Iblis yayi alwashin batar da al’uma inda Allah yake ce Mai…
Yace : ka fita daga gareta kana abin zargi korarre. Lalle ne wanda ya bika daga gare su, hakika za ni cika jahannama daga Gare ku, gaba d’aya. Suratul A’araf Aya ta 18
Kuka ibtisam ta saki tare da fad’in kinci irin laifin da Iblis ya aikata wanda inda zaiyi sujada ga Annabi Adam lallai Allah zai yafe masa
Toh haka Muma Idan mukai laifi kuma muka ro’ki gafara lallai Allah zai yafe mana……
Kuka yaci karfinta sannan taci gaba da fad’in wlh duk Wanda yabi turban shaidan lallai alkawarin Allah na jiransa, Indai harya mutu bai tuba ba, kubra da yawa yanzu idan mace bata irin rayuwar Banza kallonta ake bata Waye ba, wacce take iskanci ita ake ma kallon wacce ta Waye, Innalillahi’wa inna ilaihirajiun,
Wlh ya kamata muji tsoran Allah, mu tashi daga turban shaidan, babu Waye wa irin mace ta suturta jikinta sannan ta kame kanta, wannan itace Waye wa, bawai fitar da tsiraici ba, da rayuwar Banza ba, da yawa mutane sun amsa kiran shaidan wanda yayi nasara a kansu, sai yasa a kullum ake son bawa Ya nemi tsari daga tsaida na’a nanne
Kubra tace lallai yau na gane rayuwa na kuma k’ara yarda, duk abokin da bazai fad’a maka abunda Allah yace ba, tabbas ba Aboki bane, duk abokin da zai dinga kaika hanyar halaka ka guji wannan abokin, ibtisam wlh Nayi nadaman sanin mutane da yawa a rayuwa ta, wanda sune suka k’ara Sani cikin wannan banzar hanyar, wlh babu rayuwa Mai dad’i kaman bin abunda Allah yace, sannan Kak’i abunda yayi hani dashi …. Sannan yau kawai na gane babu mutunci ga mace face gidan aurenta, domin da yawa abunda yake cutan mu sai muce sai mun gama karatu za muyi aure, muna mantawa aure baya hana komai, yanzu na tabbata inda inada aure da yawa bazanyi wani abu ba, koda kuwa Ina son inyi, saboda koda banji tsoran Allah ba zan dinga jin tsoran kar wannan mijin nawa ya ganni ko a Kai mishi labari, amma da yake banda aure yin Abu nake iya son rai na, ban damu da kowa ba, tunda iyayena ba a nan suke ba…..
Ibtisam tace hakane, amma rashin aure bashi bane kesa mata yin iskanci a jami’a ba, abun tsoran Allah ne kawai, ki duba zarah ai gata bata da aure, zan iya cewa bata kula samari ma, Kinga ta kame kanta, akwai ma ire irenta Wanda suka kame kansu basa irin wannan rayuwar, saboda sun ri’ke addini kuma suna tsoran Allah, dan Sun San komai suka aikata in wani Bai gansu ba, toh Allah ya gansu, kuma shine mai sakayya, mai hukunta bawa dai dai da abunda ya aikata
Kubra tace hakane, mudai munbi rudin duniya, amma yanzu Alhmdlh Allah ya ganar dani, kuma indai har inada rai ban mutu ba, zan zama cikakkiyar musulma Mai bauta ma Allah, tare da kame kaina sannan inna samu miji inyi aure duk da nasan kona samu mijin in yaji ba budurwa bace ni, zansha wulakanci amma zanyi hakuri in jure, dama duk Wanda ya zabi hanyar sabon Allah zaiga ba dai dai ba a rayuwa
Ibtisam tace ku tashi mu shiga ciki
Tashi sukayi suka shiga ciki, inda ibtisam tace kubra ta kunna wayarta
Kubra tace wlh Ina jin tsoro Karya kira
Ibtisam tace karki damu ki kunna
Kunna wayar tayi Aiko tana kunnawa saiga kiran mutumin nan ya shigo tace kin gani koh??
Amsan wayar ibtisam tayi tare da dannawa tasa a speaker
Mutumin yace hello kubra
Ibtisam tayi mata alama da tayi magana
Kubra dakyar tace inaji…..
Yace har yanzu baki mutu ba…..
Ibtisam ta fusge wayar tare da fad’in bata mutu ba, kaine zaka mutu insha Allah…..
Kit wayar ta mutu alaman ya kashe wayar
Kubra kam babu abunda take sai kuka tare da fad’in Kun gani koh, kunji abunda yace koh?? Na shiga uku
Ibtisam tace miye haka kubra?? Bayan d’azu kika ce koda kin…..
Tun Kafin ibtisam ta k’arasa kubra tace hakane, nan ta Fara addu’a cikin ranta, da sauri ta bud’e data tare da shiga play store tayi downloading app na complete qur’an audio, nan ta saka ta Fara ji, ikon Allah uhm lallai babu wani sarki face Allah, shine sarki kuma Mai jin kai.
Allahu Akbar Allah mai rahma mai gafara ga bayinsa wanda suka tuba, mutum yayi ma Allah babban laifi sannan Idan ya nemi gafara Allah ya yafe masa….
Mai yasa mu muke ri’ke da y’an uwanmu musulmai?? Ya kamata Muma mu dinga yafiya, idan aka mana abu, idan ka yafe kaima sai Allah ya yafe maka
Kubra jin karatun al’qur’ani yasa gaba d’aya taji nutsuwa a tare da ita, duk wani firgici da takeji sai taji duk ta daina, ga wani tsoran Allah da taji yana k’ara shiganta, lallai maganin ko wace cuta da nasiba tana cikin al’qur’ani Mai girma
Kubra haka ta zauna a dakin su ibtisam har dare yayi inda tace itafa a nan zata dinga kwana, domin a d’akinsu babu na Allah ko wacce tayi nisa, tare da fad’in Tana zargin d’ayan ma ta shiga cult
Koda su Aisha suka shigo d’akin suka ji kubra ana jin karatun al’qur’ani, abun ya basu mamaki, hauwa kasa hakuri tayi tace yau duk yanda akayi Kinji wa’azi a wani wajan wanda ya ratsaki kikai tuban mazuru….
Dariya Aisha ta saki tare da kallon kubra tace Nima fah Abun yaban mamaki, bandai fad’a bane kawai, wai kubra yau kodai kin had’u da wani sabon guy USTAZ ne yayi miki wa’azi
2gnovel
4medicals
Smidris
Kubra tace uhm, ban had’u da USTAZ ba sai dai na had’u da Wanda yayi niyan zama ajalina nan ta basu labari
Dariya suka saki tara da fad’in Wlh wannan k’arya ne
Kubra jin haka tayi banza dasu tare dayi musu fatan shiriya domin ita yanzu Allah ya ganar da ita gaskiya kuma ta gane
AISHA ta kalli Zarah tace nidai dan uwanki nake so, inda zai aureni dana daina harkan banzan nan…..
Ibtisam jin wani abu tayi ya tsaya mata a wuya da taji abunda Aisha ke fad’i……..
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());