NOVELSUncategorized

KWARATA 41

???? —— 41

      Dariya Dikko yayi mai shiga zuciya yace tou miye ribarki idan kin tunamin asiri ? Ai asirina da naki a haɗe yake ki tona tunda ban riƙe miki baki ba , amma ki sani idan kin tonashi sai ki fara neman hanyar da zaki rufeshi saboda tabbas wata rana zaki zama ni , ni kuma zan zama ke , kije abunki amma duk abinda zaki kiyi na hankali da tunani , cikon kuɗi kuma da kike magana
bake ba da wani abu ya shiga tsakani dake nake ganin mutunciki da ƙimarki saboda kina da wani matsayi na musamma a rayuwata da zuciyata wanda ta dalilinshi kuma nake ɗaga miki ƙafa , duk abinda ya fita hannuna na gama dashi har abadan abada ,

      Kuma zuciyata ta faɗamin cewa ko kin tafi sai kin dawo bata taɓa faɗamin ƙarya akanki ba duk abinda ta faɗamin gaske ne , idan akacemin An mata ta mutu ina da yaƙini zuciyata tacemin a , a tou tabbas idan nazo zan ganki kina numfashi , sauka lafiya amma banda kukan dare dan ina buƙatar bacci a wannan lokacin kiyi kuka da safe kiyi da rana amma idan har kikayi kukan dare gani nan zan dawo ,

      Kallon budurwar yayi ya nuna mata da hannu ke koma mota muje , shiga tayi mota shi kuma ya biyo bayana , gabana yasha yace An mata karki zo kiyi abunda zai zama matsala a rayuwarmu , ki manta da abinda ya faru baya mu fuskanci sabuwar rayuwa ,

      Cikin kuka na kalleshi nace har ƙarshen numfashi na bana fatan na sake kasancewa dakai wallahi , kuma zuciyarka ta faɗa maka gaskiya tabbas zan dawo amma ɗaukar fansa zata dawo dani , 

      Murmushi yayi tare da cewa haba yarinya , Dikko ne fa ! Kin manta nine na koya miki ? Nine nayi kuma nine na fara baki idan daɗi kikaji ko zafi duk nine dai , ruwa idan da rabonka cikin sa ko ka zuba a kwando bai maka yoyo , ni ba abin farautarki bane zaki duk jarumtatai yana ganin ƙimar mafarauci a wancan karon suma kikayi , wannan karon ma haka zata sake faruwa dake ba suma ba har jinya sai kinyi , idan kin dawo ɗauka fansa zaki gane Dikko ba sa’ar wasanki bane domin saina baki azabar da sai kinyi fitsarin wahala bayan kin dawo daga duniyar suma , tsoro na zai shigeki a lokacin da kika kasance dani a shifimɗa ɗaya , idan kuma Dikko baya nan zakiyi kuka bacci ya gagareki gidan biki ko suna Dikko yana tare dake a zuciyarki domin zan zame miki garkuwa , da hannun damarshi ya daki na haggu yace wallahi jarumi ɗaya ake a ƙarni nine jarumin wannan lokaci , Dikko jarumin maza ne kuma ke da kanki zaki faɗa keje ki dawo ina nan ina jiranki ,

     Idan kuma soyayya ta dawo dake , ƙasa ya kalla yana nazari bayan wani lokaci ya kalloni yace tabbas zaki zo zuwa gareni kina roƙon na baki soyayya ta , nace wa ni ? Yace tabbas ranar zata zo , nuna kaina nayi tare daci gaba da cewa yi haƙuri Dikko ka manta da wannan wasan kwaikwayon naka har abadan duniya hakan bazai yuwu ba , murmushi yayi tare da taɓa daidai saitin zuciyarshi yace ina da tabbacin zaki soni kamar dai yadda na faɗa , ko kina da tabbacin cewa baza ki taɓa so na ba ? Nace Eh har abadan abada , murmushi yayi yace ƙarya kikeyi , nace da gaske nake , yace zaki gani nima nace zaka gani , girgiza kanshi yayi yace jeki abunki ,

        Ci gaba nayi da tafiya har yanzu yana tsaye a wurin dana barshi , motoci masu komawa katsina nayi ta ɗagawa hannu har Allah yasa na samu masu ragemin hanya shiga nayi na nufo katsina yayin da Dikko ya shiga suka kama hanyar abuja ,

     Budurwar Dikko kuma ga wayarta a hannuna , domin dana koma mota dama ba jaka na koma ɗaukowa ba waya na ɗauko abinda yasa na fito da jaka dan karsu zargi ni na sace kuma nasan idan sukayi gaba zasuyi tunanin wurin fitowa ta yada ita , Baba da Mama da kowa nata yana cikin waya…

     Tunda Dikko suka tafi yake kukan zuci daren jiya da An mata tasan irin matsalar daya fuskanta akanta da bata baɗa mishi ƙura ba , abinda ya faru tsakaninsu sirri ne babu wanda ya sani sai shi sai ita sai Allah , yana bata mutuntukar mutuncinta daya ɗauka amma yarinta ta hanata kusantowa gareshi !

      Abinda ya faru jiya , bayan Dikko ya faɗawa An mata yana santa tafiyarta kawai tayi ta barshi palo zaune kamar wani sakarai , bata daɗe da shiga ɗaki ba Dady yace yana nemanshi duk abinda yakeyi ya barshi yazo , shine ya tashi ya fita babban palo ya ɗauki makullin mota ya fita kuma a gaban idon Sultana yabar gidan…

Bayan yaje gida a palon Dady ya samu Al ‘ Ameen gurfane a gaban Dady , kallo ɗaya yayi mishi ya ɗauke kanshi tare da samun wuri shima ya zauna can nesa da Dady , bayan ya zauna ya gaishe da Dady ya ansa shima Al ‘ Ameen ya gaishe da Dikko , Dikko bai ansa gaisuwar ba , kallon Al ‘ Ameen Dady yace ya kira mishi Ummar ,

      Miƙewa Al ‘ Ameen yayi kafin ma ya fita daga palon Umar ya shigo saboda dama tuni an kirashi bai samu isowa da wuri bane , bayan kowa ya zauna Dady ya kalli Al ‘ Ameen yace ga Babana nan ka sake faɗar abinda ka faɗa , shiru Al ‘ Ameen yayi , Dady kuma ya kalli Umar bayan Al ‘ Ameen yaƙi magana yace Umar wace yarinya ce take zaune da Baba ?

      Da sauri Umar ya kalli Dikko amma shi basu yake kallo ba yana kallon wani wuri daban , cike da fargaba Umar yace wallahi Dady nidai ban sani ba , Dady yace tou aini Al ‘ Ameen yace min ya ajiye mace gidanshi na goroba road bayan ni nasan Babana baya huɗɗa mata shi yasa hankalina ya tashi , Umar sake kallon Dikko yayi amma har yanzu Dikko fuskar nan tashi dai kamar yadda take kullum kuma har yanzu baya kallonsu kawai dai yana saurarensu.

     Dady yace ƙarya zakamin ne ? Ya tambayi Umar , Umar yayi shiru , Dady yace ma Al ‘ Ameen yanzu ina yarinyar take ? Tana gidan har yanzu ? Al ‘ Ameen yayi shiru , gyara zama Dikko yayi yace tana gidan Dady , amma lokacin dana fito na barta tayi bacci ,  nayi kuskuren rashin sanar dakai amma da Allah kayi haƙuri nayi amfani da maganar ka ne da kace na zama mai kyautatawa duk wanda naga rayuwarshi tana buƙatar taimako ,

       Yarinya ce ƙarama shekarunta bazai wuce 18 ba kuma na baka labarinta kwanakin baya itace yarinyar da mukeyin faɗa tou yanzu mun daina faɗan ne , a tsawace Dady yace ɗiyar ɗan caca ? Karuwar Babana ? Cikin ladabi Dikko ya sauke kanshi ƙasa tare da rufe idanuwanshi , Dady yaci gaba da cewa duk ƙoƙarin kare martabar ka da nake maka ni zaka ɓatawa siyasa ka ɓatamin suna har cikin jahata ? Ni zaka zubarwa da mutunci ? Ka ɗauko karuwa ka ajiye a gidanka ka bar matarka kaje ka kwana da “yar iska mara tarbiya wacce tafi ƙarfin iyayenta itace wacce kake ganin kaine zaka gyara mata rayuwa ?

       Masifar da tasa iyayenta suka yada ita ba ƙarama bace kai shine kaje ka ɗauko ka dawo da ita rayuwarka kai sarkin imani da tsoron Allah ? Kana siyasa zaka ɓatawa kanka suna , ka zubar da mutuncinka a idon duniya ina amfanin mu’amula da karuwa ? Ko zaka dafa Al ‘ Qur’ani kayi rantsuwa kace baka neman yarinyar nan babu wanda zai yadda , da yarintar ka baka bi mata ba sai yanzu da shekaru suka fara hawanka ? Tou idan dan rashin lafiyar matar ka ne Momynka ta nemo maka auren ɗiyar yayarta shikenan na kashe maganar…

      Murmushi Dikko yayi tare da cewa gaskiya Dady ban tsara zama da mace 3 ba a rayuwata itama Sadiyar haƙuri nayi kawai na ansa amma ni gaskiya mata 3 sunmin yawa wannan karon bazan ansa ba kuyi haƙuri , ciki ɓacin rai Dady yace wallahi idan dai ina lumfashi a duniyar nan baza ka auri karuwa ba sakaran banza da baka san macen da ya kamata ka aura ba , shi aure daka ganshi yana buƙatar cancanta mutuntaka asali da nasabar mace , banda kake sakarai ka rasa wacce zaka so sai karuwa ? Karuwar kake tunanin zata zama uwar “ya “yan ka ? Ni wallahi ko jirgi zan siya bana buƙatar na hannu sai sabo shi yasa bazan iya auren zawara ba amma kai dan baka kishin kanka har kake tunanin auren karuwa , wallahi da kasan kanka ko mace baka nema ,na tsani wani yayi amfani da abu nayi amfani dashi saboda tsanar da nayi ma abun yasa bana sauka hotel , duk jahar daka gani babu inda banda gida babu ƙasar da ban mallaki gida ba dan na tsani wani ya shiga a wuri na shiga sakarai wawa dakai idan baka fita harkar yarinyar nan ba zaka haɗu da fushi na ,

          Dady kayi haƙuri kasan…. Tsawa Dady yayi masa yace nasan me ? Ko zaka mutu banajin komai Babana ,  Dikko zai sake magana Dady yace fita bana san ganinka , jiki a sanyaye Dikko ya miƙe ya fita , ɗakin mom inshi ya nufa itama faɗa ta mishi sosai domin Allah kaɗai yasan abinda Al ‘ Ameen ya faɗa akan Sultana ,

      Itama wata yayarshi da isowarta kenan nigeria tazo ganin Sadiya ta sako bakinta tayi ta ma Dikko faɗa tare da cewa kadaiji kunya wallahi kuma kayi asara ka rasa wacce zaka so sai ɗiyar ɗan caca , abun kunya duk nasabarka da mutunci gidanku kaje ka auro mana ɗiyar marasa asali , jiƙar matsafi ɗiyar ɗan caca karuwa tou ka faɗamin ita me zata haifa ? Kalli yadda tazo ji yadda take tata rayuwa wace irin tarbiya zata ba “ya “yanta ? Gaskiya Dikko ka bani kunya da ina alfahari dakai amma , Dikko ya tareta da cewa amma yanzu kin daina ko ? Tou kije kiyi ta daina warki kuma ki fitar da bakinki idan ba haka ba kuma duk abinda nayi miki ke kika jawa kanki ,

      Momy tace rufemin baki mara kunya ko itama halin karuwanci zaka nuna mata ? Dikko yace tou ta ƙara aibata ta kiga yanda zanyi da ita ! Wallahi saina zane mata jiki tas idan kuma tana ganin zaki hana na daketa ta fito waje wallahi saina bi ta kanta da mota na wuce , wani irin mari Momy taimishi dan tasan halin Dikko da kafiya idan dai yace zaiyi sai yayi idan kuma ya rantse akan abu ko za,a mutu baya kaffara saiya aikata wallahi ,

      Kallon Yayarshi yayi yace akanki aka mareni ko ? Jinjina kanshi yayi tare da miƙewa yace zan haɗu dake , tace ni ba’a kaina aka mareka ba akan karuwa dai , cikin ɓacin rai Dikko ya nufi wurinta Momy tace idan ka taɓata ban yafe maka ba shanyayye , dariya yayar tashi tayi tare da cewa aikin san karuwa koba asiri akwai bariki mai wahalar goguwa a zuciya , wallahi Dikko ka daiji kunya ɗiyar daka isa ka haifa ai ko baka haihu ba ka kalli ɗan abokinka , fita Dikko yayi daga ɗakin dan idan ya tsaya komai zai iya faruwa ,

      Wurin motarshi ya samu Umar , kuma Umar shine ya faɗawa Dikko cewa Al ‘ Ameen yazo ya faɗawa Dady komai kuma ya ɗora da cewa idanma aure mai gida zaiyi ga ɗiyar yayarshi , shine ya kawota gidansu Dikko kuma tayi sati tunda tazo Dikko bai taɓa ganinta ba sai yau , kuma Dady shine ta tursasa Dikko yaje asibiti ya ɗauketa ya tafi da ita ya ajiyeta kaduna , tunda tazo itace take kula da Sadiya , tana kyautatawa kowa na gidan , 

     Ita kuma Momy ta riga data yanke shawara kawai Dikko zai auri autar ɗiyar yayarta , kuma duk zagin da yarinyar nan tayiwa Sultana wallahi Dikko baiji ba , baisan sunayi ba dan hankalin shi baya wurinsu yana can ya tafi duniyar tunani , bige²nsu kawai yaji , amma wallahi baiji zage²nsu ba , Al ‘ Ameen shi yasan komai akan Sultana kuma shine ya bawa ɗiyar labari yace ta faɗawa Sultana tace Dikko ne ya bata labari , amma tayama Dikko zai fara wannan sakin layi ? Bayan bai haɗa Sultana da kowa ba ,

       A gajiye na iso anguwarmu tafiyata babu jimawa anguwar ta samu ci gaba sosai , tun daga farkon layin hannun da Dikko ya sissiye har zuwa gidan dawankashi an bugeshi anyi wani irin zuƙeƙen gini babu wani maƙoci daya raɓeshi baya tare da kowa sai gidajen dake kallon gidanshi , waje kawai aka gyara aka ciccina mishi fulawowi ciki kuma aka watsa dawakuna da wasu irin lafiyayun karnukan turawa masu kama da kuraye , an ƙawata gidan da wasu irin fitulu wanda idan dare yayi aka kunnasu haskensu zai gauraye ko ina da ko ina ,

      Gidanmu na shiga da sallama , Nana tana gani na ta tashi da gudu ta shige ɗaki , Babana na gani kwance saman tabarma yanajin magana na ya karkato da kanshi dakel ya kalleni ,

     Kowa ya tsaya yana kallona babu wanda ya ansa min sallamar da nayi , wurin Babana na nufa na durƙusa na kamo hannayenshi nace meke damunka ? Kallona yayi cike da tsantsar ƙauna sannan ya buɗe baki dakel idonshi ya cika da hawa yace shine kika tafi kika barni….? ????

Murmushi nayi tare da goge mishi hawayen nace ai gani na dawo ? Kana tunanin zan tafi na barka ne ? Bayan bana iya rayuwa saida kai ! Dare da rana safe da yamma yanayin farin ciki da damuwa halin yunwa ko ƙoshi babu kowa a zuciyata sai kai , farin ciki ya dawo rayuwar kunci da damuwa zata kama gabanta , 

       Har yanzu babu wanda yayi mana magana ga gida cike da jama’a yayin mutane suka fara janye “ya “yansu , matar Baba ƙarami ta kira “yarta gefe tace ki wuce ki tafi gida annoba ta dawo ,

      Wane yaro ne ya shigo gidan cikin farin ciki yana barka da dawo uwar ɗakinmu , ban kalleshi ba kuma ban saurareshi ba ina kallon yadda jama’a suke tsame “ya “yansu saboda zuwana , jinjina kai na nayi tare da cewa wane yaro a kawomin abinci da Allah , saida ya saramin caucau Allah dai ya kare miki sharri yayi maganar cikin muryar dabanci , nace Amin shi kuma ya fice…

      Fitar wane yaro nabi duk wanda ke gidan da kallo , sannan nace duk sannun ku ? Na dawo ya mai jiki ? Babu wanda ya bani ansa , murmushi nayi na zauna gefen Babana , ban gama zama ba Amisty ta shigo , fitowar Nana daga ɗaki shigowar wane yaro da kwanon abinci , Hafsa A ‘ i Saude Zalifa Karima sai kuma wata daban wacce nake tunanin itace suke zuwa gidanta wato Asma’u ,

      Murmushi nayi tare da miƙewa tsaye nace dama nasan ranar nan tana zuwa shi yasa na taho gida na dawo kuma a tafe nake da sabon salo na baya ba komai bane ba , ga Sultana ga Amisty ga kuma Hafsa ku kaɗai nake da damuwa daku sauran kuma banma sansu ba , ….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button