Uncategorized

HABIBI DA’IMAN 1-20

 *HALIMA* *Mk*

         

*Dedicated* *to* *sa’adatu* *Aliyu* *kabuga*

 

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION.

 

Bismillahir Rahmanur Rahim.

 

Godiya ga Allah daya bani ikon fara rubuta wannan littafi mai suna *Habibi da’iman*.

 

Ina rok’on Allah yabani ikon gabashi lafiya,Allah yasa kuma,mu Amfana da Abinda keciki.

 

Wannan k’irk’iranran labarine,banyishi Dan wani ko wataba,duk Wanda yayi dai-dai da labarin rayuwar shi,Akasi Aka samu.

 

Muje zuwa????????????????????????????????

 

 

 

*page 1-5*

 

 

“Ganinan fa,Yaya khadija kujirani,mayafina kawai zan saka”

 

 

 

 

Wadda aka kira da Yaya Khadija ce taja tsaki,taja wani troly bag,dake kusa da ita,tare da cewa”wallahi zanyi tafiyata,matsalar mutun ya had’a tafiya daku kenan,aita b’ata lokaci”

 

 

 

Mamansu dake gefe,ta girgiza kai”kedai Khadija idan tafiya ta kama Kaduna zaki,baki kwantar da hankalinki,sai kinga anje”

 

 

 

Dariya tayi tare da cewa” wallahi Mama na k’agara inje inga Aminina”

 

 

 

Ihsan”To muje nagama shirya wa”

 

 

 

Khadija ta juya ta kalli Mahaifiyarta dake zaune Tace”Mama zamu tafi”

 

 

 

“To Khadija Allah ya tsare Hanya,Allah ya kaiku lafiya,Ku gaida Mani Y’ar Uwata,kuma ku kula da kanku”

 

 

 

“To Mama insha Allahu,kuma zamu gaida maki ita”

 

 

 

Suna maganar suna fita zaure,a k’ofa gida suka ga Mahaifinsu Zaune,durk’usawa sukayi,tare dayi mashi bankwana,yasa masu Albarka dakuma fatan su isa lafiya.

 

 

   

Adai-daita sahu suka shiga,suka nufi tasha domin hawa motar Kaduna,ba b’ata lokaci kuwa suka samu Mota.

 

 

A cikin mota,ta d’auko wayarta,Nokia ta danna kira,bajimawa ta fara magana.

 

“Hello Yaya jiddan,ya kake,gamunan mun taho”

 

Daga d’ayan b’angaran hace”to Yar’Uwa Allah ya tsare Harna k’agara kizo”

 

 

“Wallahi nikaina na k’agara,to amma muna Hanya ai”

 

 

“Badamuwa Allah yakawoku,lafiya”

 

Nan suka d’anyi fira,sannan sukayi bankwana.

 

 

       *********

 

Suna isa Kaduna,ko Abinci bata tsaya ciba,tashi tayi zata tafi.

 

 

Aunty Fa’iza Tace”to ina kuma zaki?”

 

Tayi dariya tare da cewa,”zanje gidansu yaya Jiddan”

 

Aunty Fa’iza ta kalleta Tara dakai mata harara”daga Ajiye jikka sai gidansu Yaya Jiddan”

 

“Nidai Aunty…”

 

“Oyoyo My k’anwa,you are wel come” Jiddan ne ya shigo gidan yana maganar.

 

 

Khadija ta wangale baki tana dariya”oyoyo,Wallahi yansu nake shirin tafiya”

 

Aunty Fa’iza Tace”cewa zakiyi yanzu tsayuwar dakike tafiya zakiyi”

 

Suduka sukasa dariya,Jiddan ya durk’usa ya gaida Aunty Fa’iza tare da cewa”Mama ina yini,ya bak’i?”

Jiddan yana kiran Aunty Fa’iza da Mama kasan cewarta,mahaifiyar Abokinshi.

 

 

Suna gama gaisawa da ita yajuya wajan Khadija”to Aminiya ta,sai muzauna muyi fira,Dan wata biyu kenan bamu had’uba”

 

 

Zama tayi kan kujera,tagaidashi,nan suka shiga firar shak’ur da sukayi.

 

Nan nasaki baki,ina kallonsu,labarinsu kawai suke daka gansu kasan sun shak’u da juna.

 

 

Khadija Tace”wallahi Yaya jiddan Nak’agara in gama skul nan zan dawo da zama”

 

 

Jiddan yayi murmushin jin dad’i yace”aikam Dana cigaba da farin ciki”

 

 

Saudat (wato d’iyar Aunty Fa’iza tace” tab aikam da shikenan,muyita zama muna fira,kin dawo nan kenan”.

 

 

Aunty Fa’iza tana gefe tana jinsu,tace”lallai yaran nan,bakuda Hankali,daga gama makaranta shikenan sai kidawo nan,ba kuma Maganar Aure”

 

Dam gaban Jiddan ya fad’i,jin Amsa maganar Aure,sannan kuma tabbas maganar Aunty Fa’iza haka take.

 

Yakalleta yace”hakane kuma Mama,dasun yi Candy sai Aure”

 

Aunty Fa’iza race”eh mana mi akejira”

 

 

Khadija ta turo baki,”Ku wallahi Aunty yanzu bakuda magana sai Aure”.

 

 

 

Jiddan ya kalleta,”kinga daga lokacin shikenan,mun rabu kina gidan mijinki”.

 

 

“Tab ai wallahi,shima mijin saidai yayi Hak’uri,dan bazan fasa zuwa hutu nanba”

 

 

Dariya sukasa suduka Jiddan hada hawaye”kinga shikenan,ba abinda ya dameni,saidai kawai inzo in gaida Mama in tafiya ta”

 

 

Aunty Fa’iza tace”kajishi,kamar da gaake,Wanda inba Khadija tazo gidannan ba,sai inyi sati biyu banganshiba”.

 

 

 

Nan dai sukayita fira,har aka fara kiran sallar Magrib,kowa ya tashi shikuwa Jiddan Massallaci ya nufa.

 

 

         ********

 

Bayan sallar isha’i Jiddan yadawo,nan dai suka zauna sunata fira,tare Khadija ta zuba musu Abinci,haka suke cin Abinci ko yaushe atare indai Khadija tazo.

 

Suna cikin cin Abinci,Saudat ta kallesu “waini ba’acin Abincin dani”

 

Khadija ta harareta,”wannan na gabanki kiyi yaya dashi?”

 

Dariya Sukayi Jiddan yace”barta shishshigi ne kawai”

 

“Assalamu Alaikum”,Muhsin ne ya shigo tare da sallama.

 

Khadija ta d’ago” sannu da zuwa Yaya Muhsin”

 

Kallanta kawai yayi,tare da cewa”sannu da zuwa”

 

Saudat ta munsileta tare da cewa “gayanan yazo….”

 

Muhsin ne ya kalleta cikin d’aure fuska alamar ba wasa”Ke mi kike cemata?”

 

 

*kubiyoni taku har kullum*????

 

                *Mrs* *Abdul* *Sule*

[1/17, 10:46 AM] Halima Mk: ???????????????????????????? *HABIBI* *DA’IMAN*

 

 

 

 

*WRITED* *BY* *HALIMA* *Mk*

 

 

 

*DEDICATED* *SA’ADATU* *ALIYU* *KABUGA*

 

 

 

*DABAZARMU* *WRITERS* *ASSOCIATION*

 

              *page* *6* *~* *10*

 

 

 

 Karaf!! Khadijah tace “yaya muhsin wai yau mike damunka? ko irin oyoyo d’in nan bakayi mani ba”

 

Baice mata komi ba sai wata harara da yayi ma Jiddan tare da wuce wa ciki

 

Khadijah tace ” yaya Jiddan kaine ka b’ata ma ya muhsin rai ko?

 

Jiddan yace “shareshi kawai dan nayi mashi dariya dazu shine yake fushi, amma zamu shirya”  duk wannan abinda ke  faruwa bai fasa ba khadijah abinci a baki ba. Anty Fa’iza kuwa kallon su kawai take.

 

            *********

A yaune su khadijah keta shirye shiiryen koma wa katsina kasancewar hutun su yak’are,  Jiddan na gefe rike da trolley d’in khadijah ya k’ura mata ido

 

Kallanshi tayi tace “kallon fa” yace “uhmmm ina tunanin idan kika tafi kika barni zanyi rashinki cikin zuciya ta!  Tare da dafe satin zuciyarshi.

 

Murmushin jin dad’i tayi tare dayin fari da idanuwanta tace” kaima ya Jiddan nace kadawo katsina ba”

 

Lips d’inshi na k’asa ya ciza yace “kada kidamu na kusa dawowa”

 

Juyawa tayi ta nufi cikin mota tare dayi mashi waving hannunta, bayan tashiga motar ne yazo daidai inda take yace “khadijah”  tace “Na’am”  yace “i love you”  tayi Murmushi tace “i love you too”  tare da kashe mai ido daya. Batare da b’ata lokaci ba driver dazai kaisu yaja motar suka wuce.

 

 

Isarsu k’ofar gidan, ihsan ta bud’e k’ofar motar ta ruga da gudu cikin gida tana cewa “Mama where are you? i’m back”  shuru tayi ganin ya Suleman shida Mama suna magana, da gudu tak’arasa inda yake tana cewa “oyoyo ya ss yaushe ka dawo” Murmushi yayi yace pretty tun shekaran jiya nadawo amma banganki ba” ihsan tace “kaduna mukaje nida yaya khadijah ” ina tsara bata” tace “ya nida bansan kadawo ba”  “to yanzu kinsani”

 

Khadijah ce ta shigo tare dayin sallama hakan yasa suka yi shuru.

 

Durk’usawa tayi tace “Mama mundawo”   “to sannunku, ya kuka barosu Hajiya Fa’iza? Lafiya lau cewar khadijah, tare da Juyawa ya ss ina wuni”  amsawa yayi Batare da ya kalleta ba.

 

Kallon Mama yayi yace “sai anjima zandawo, har yaje bakin k’ofa ya juyo yace ma khadijah kidafa man indomie” sannan yatafi

 

Gunguni tafarayi shifa ya ss ya cika sa aiki daga dawowa na” Mama ta kalleta tace “uhmmm kanku akeji”

 

 

  Ya ss Asalin sunanshi Suleman Shehu Matazu, wanda abokansa suke mashi lak’abi da ss matazu, sun kasance Neighbors d’in su khadijah ne wanda suke da kyaukyawar alak’a, suleman shine babba a gidansu sai younger sisters d’inshi twince ne samra da seema.

 

Yanzu haka yana karatunshi a k’asar KSA inda yake karantar medicine. Mahaifinshi ba Maxauni bane yana fita k’asashen waje dan gudanar da kasuwancin shi. Sai Mahaifiyarsu wanda suke kira da Ummi.

 

Suleman bazai wuce shekara 25 ba, Farine dogo wanda yake da manyan idanuwa da dogon hanci da kagansa zaka gane kyakyawan bahaushe ne wanda d’abi’arsa take cike da miskilanci, hakan ne yasa ‘yan mata ke sonsa ga kud’i suna Ratsashi.

 

Yanzu ma hutu yadawo, kasancewar idan yadawo bayasan cin abincin kowa sai Umminshi da khadijah. Gashi ba wani shiri suke da khadijah ba ita batason mutum mai jida kai. Shikuma yana gudun raina

 

Kasan cewar khadijah kad’aice idan ta dafa mashi abinci yake jin dad’inshi shiyasa some times yake tunkararta. Ita kuma take ganin ya cika takura.

 

 

 

 

 

 

 

               Mrs Abdul Sule

[1/17, 10:46 AM] Halima Mk: ????????????????????????????????

 

*HABIBI* *DA’IMAN*

 

 

 

       *WRITED* *BY* *HALIMA* *Mk*

 

 

*DEDICATED* *SA’ADATU* *ALIYU* *KABUGA*

 

 

 

*DABAZARMU* *WRITERS* *ASSOCIATION*

 

 

           *PAGE* *11* *~* *15*

 

 

 

 

Misalin k’arfe 8:30 na dare, ss ne ya shigo gidan su khadijah a lokacin tana kitchen tana dafa mai indomie, hakan yasa ya nufi kitchen d’in ya tsaya ta bayan ta batare da tasa niba sai aikin ta takeyi, shikuwa tsaye yayi yana kallonta,

 

 

Sanye take da wani pencil d’in wando da black d’in riga da takusa kaimata gwiwa, sai bak’ak’en toms da tasa ga gashinta da ta d’aureshi ta tubke a tsakiyar kanta sai rito yake a bayanta.

 

 

Jiyowa tayi da nufin ta d’auko plate, kawai sai ganinshi tayi,yayi sanadiyar tsorata ta har ta tafi zata fad’i saurin riko hannunta yayi sundauki kusan 1minute a haka suna kallon juna.

 

Zumburo baki tayi “gaskiya kaifa yaya”

 

“Au damma kin samu antaimaka maki”

 

 

Daidai lokacin ta gama juye mashi indomie d’in cikin plate ta mik’a mashi, kallon rainin hankali yayi mata yace “sai ki kawo mani palour, batare da ya k’ara kallonta ba”

 

 

Hakan yasa tabishi da abinci tare da d’auko mashi ruwa cikin fridge

 

Aje mashi tayi a gabanshi, sannan ta wuce d’aki.

 

 

 

              ********** 

 

Haka rayuwa ta cigaba tsakanin Jiddan da khadijah shak’uwa, soyayya da tausayin juna yana k’ara ratsa jinin jikansu.

 

 

Wanda yanzu khadijah nada shekara 16, suna ta shirye shiryen yin graduation d’insu.

 

 

Saidai wani abunda ke damun khadijah cikin ranta, bai wuce yadda har yanzu Jiddan bai fara karatunshi ba.

 

 

Kusan yanzu shekara shi ukku da gama secondary school d’inshi, A yanzu yana shekara ta 19.

 

Amma yana zaune a gida sanadiyar iyayen shi sun fison yaje yayi degree d’inshi direct.

 

Shi kuma yana ta samun matsalar jamb. To yanzu gashi khadijah zata gama makarantar ta, shima a wannan shekarar zai sake zana jamb

 

 

               *********

 

 

Allah mai iko maiba bawa abinda yaso, a lokacin da yaso, kamar had’in baki Jiddan da khadijah sunci jarabawa.

 

Ayayin da sukayi applying umar musa yar’aduwa katsina (umyuk)

 

 

Inda shi Jiddan zai karanci Geography, ita kuma khadijah zata karanci English, saudat kuma chemistry.

 

 

   Yanzu Rayuwa tayi wa khadijah da Jiddan dad’i kasan cewar kullum suna tare a school, hakan ne yasa ake masu lak’abi da inkaga zarah kaga wata.

 

 

 

Haka suka cigaba da gudanar da rayuwar karatunsu.

 

Har suka kai 200 level. Kowa mamakin yadda soyayyar Jiddan da khadijah take, domin kuwa makarantar babu wanda bai san suba shiyasa suke birge mutane da yawa.

 

 

Amma duk da hakan kusan kullum sai sunyi fad’a da juna, saboda ko kad’an Jiddan baison yaga khadijah tana magana da wani, itama haka, to amma wani abun kamawa yake, saidai fad’an ba yayin nisa suke shiryawa.

 

 

Kamar kullum yau ma sungama leacture d’insu zasu tafi gida, domin saudat tun d’azu ta wuce gida.

 

 

Zaune suke ita da Jiddan suna fira ya kalleta yace  “khadijatu”  yadda yakira sunan tane yasa ta tattara hankalinta gaba d’aya akansa, yace “rufe idonki”

 

Sai ta rufe batare da tace mashi komi ba, d’an yatsanta na ukku  yakama yasa mata wani d’an k’aramin zoben azurfa tare da manna mata kiss ahannun, hakan yasa ta bud’e idonta tana kallon shi cikin shaukin so da kauna.

 

 

Kallonta yayi yace “khadijatu this my promise, pls don’t leave me, ina sonki fiye da kaina idan narasaki bansan yadda zanyi ba, inasonki har gaba da Abadan!!!!!

 

 

Baikai ga k’arasawa ba ta rufe mai baki sakamakon hawaye da tagani a idonshi.

 

 

“i love you yayana”

 

Wani zoben ya dauko yabata tasa mashi suna dariya. Sannan suka wuce gida

 

 

 

 

 

                Mrs Abdul Sule

[1/17, 10:46 AM] Halima Mk: ????????????????????????

*HABIBI* *DA’IMAN*

 

 

 

*WRITED* *BY* *HALIMA* *Mk*

 

 

 

*DEDICATED* *TO* *SA’ADATU* *ALIYU* *KABUGA*

 

 

 

 *DABAZARMU* *WRITERS* *ASSOCIATION*

 

            *page* *16* *~* *20*

 

 

 

Isarta k’ofar gidan taga saudat na zence da saurayinta inspect kabeer, hakan yasa suka gaisa ta wuce cikin gidan.

 

 

Bayan taci abinci ne suna fira da Mama, ya ss ya shigo tare dayin sallama, hakan yasa khadijah ta shige d’aki.

 

Shi kuma ya zauna tare da gaida Mama yana tambayar ta ina ihsan? Tace “taje islamiyya, ya karatun naka?

 

Yace” karatu ai mungama lafiya, daddy ma yace in shirya nan da two weeks zan fara zuwa wurin aiki “

 

Mama tace”masha Allah sauran aure?

 

Gaskiya Mama ni bantashi aure yanzu ba, duka i’m 28 years fa”

 

To aishine cikar kamalar mutum, yanzu kaga saudat nan da shekara daya za’ai bikin ta, lokacin takai 300 level”

 

To Mama Allah yayi mana jagora”sanna ya wuce gida.

 

Duk wannan firar da sukeyi khadijah tana jinsu, duk jikinta yayi sanyi especialy da taga ansama saudat rana.

 

 

  Washe gari da taje makaranta ne k’awayenta mimie da Rabi’atu, suka fuskanci kamar khadijah tana cikin damuwa gashi tak’i gaya masu, kuma Jiddan yana leactures ballanta su gaya mashi.

 

Hakan yasa suka tafi wurin saudat, suna zuwa suka tarar da saudat da k’awarta Asiya suna fira kasancewar basu da leactures time d’in.

 

Bayan sun gaisa ne suke tambayar ta miya samu khadijah? don yau da alama tana da damuwa,

 

Saudat tace “nima bansa niba tun jiya naganta haka, may be ita da mutumin nata ne”

 

Asiya tayi Karaf tace “damani saudat ina son in tambayeki wai miye sirrin khadijah da Jiddan ne? 

 

Don soyayyarsu da shak’uwarsu, sun dad’e suna birge ni, musamman yadda suke ba junan su kulawa.

 

Saudat ta kad’a kanta tare da yin Murmushi tace

 

“nima bana jin idan aka raba Jiddan da khadijah zasu iya Rayuwa, saboda soyayyarsu ta samo asali ne tun muna yara,

 

A lokacin nan khadijah tana zuwa hutu gidan mu a kaduna, kasancewar Mamanta da Mama na ya da k’anwa ne, gashi tsakanina da khadijah 7 month ne.

 

Su kuma su Jiddan neighbors d’in mu ne a kaduna, kuma Jiddan da yayana Muhsin abokaine.

 

 

Tun khadijah na shekara 5 take zuwa  gidan mu hutu, shiyasa muka tashi kusan komai namu iri d’aya.

 

Lokacin ne Jiddan idan ana fad’a da khadijah sai ya dunga bata gaskiya, gashi kuma bata jin magana, shiyasa da tayi laifi sai ta ruga wurin shi”

 

Saudat taja numfashi tace “a wannan lokacin ba wanda ya kawo komai a ranshi, kuma suma basu kawo komai a ransu ba,

Sai lokacin da Jiddan ya kai 15 years ne ya fahimci son khadijah yake, hakan yasa ya fara taka tsantsan da ita, baya yadda tana shige mashi kamar da.

 

A hankali ya fara fahimtar da ita menene so daga nan salon shak’uwarsu ya canza suka k’ara kaunar junansu, dan haka soyayyar Jiddan da khadijah daga Allah ne

 

Domin Jiddan yana son khadijah kamar ya had’eta ta, kuma duka iyayenmu sun sani.

 

Kuma Nima na shaida Jiddan nason khadijah ba dan kyanta ba, ita ma haka,  sai don Allah”

 

Mahaifiyar Jiddan tana son khadijah kamar ita ta haifeta, kasancewar Jiddan ne babba d’a na miji agidansu, yana da yayarshi maisuna jiddah sai kannenshi Aslam da islam, sai Afrah da Afnan.

 

  Saudat tace to kunji labarin Jiddan da khadijah, Asiya tace tab “aiko dole su shak’u da juna”

 

Mimie ce tace “kutashi muje capteria muci abinci don ni yunwa nake ji”

 

Rabi’atu tace “to acici” daga nan suka wuce capteria.

 

 

           *********      

 

Khadijah Usman Abdallah shine cikaken sunanta, mahaifinta bafullatanin rugar gyaza ne dake karkashin hukumar kankiya.

 

Mahaifiyar ta kuwa yar gire ce dake jihar yalo hakan yasa sukayi gadon kyau.

 

Allah ya azurta su da ‘yaya ukku, safwan shine babba, wanda yake karatun shi a kano, sai khadijah, sannan auta ihsan, dake primary 3.

 

 

Khadijah ta kasance ba fara bace, amma tafi chocolate Haske, zaka kirata fara domin haskenta mai yellow ne kuma ita ba ramamma bace. Gashin ta kuwa har gadon bayanta, hancinta ba wani mai tsawo bane sosai bakinta ma d’an ma daidai ci ne, amma tana da manya idanuwa da Gashin gira kamar balaraba.

               Wannan kenan 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button