HABIBI DA’IMAN 181-200

*page 180-185*
_inaba makarantan littafin nan hak’uri najin shuru kwana biyu wani babban uziri yahanayi yi Wanda nake buk’atar addu’o’ehku Allah ya shige mana gaba kan halin danake ciki, yanzun ma zakuji shuru har saina ga abinda Allah yayi, dafatan zaku k’arbi uzurina_
*K’*arar birkin da mai motar ya taka tun kafin ya isa wajen Khadijah shi yayi sanadin juyowar ta duk da ya samu ya tsaya tun kafin ya banketa wanda space kadan ya rage tsakanin shi da’ita
Ganin motar dake k’ok’arin banke ta shine al’amarin da ya girgiza kwalluwar ta da duk wani Abu dake aiki a ciki, tuni ta zube sume a wurin sanadin tuna irin had’arin da tayi a yayin fitowar ta daga asibiti don ta tabbatar da mutuwar SS
Allah sarki HABIBI DA’IMAN har wani tsinkewa yakeji jinin shi nayi baya son abin da zai dunga wahalar da Khadijah, shi kanshi bazai iya misilta irin yadda k’aunarta ke gudana a cikin jinin jikinshi ba
Da Sauri ya iso wajen, har kyarma yake ya rungume ta a jikinshi yana jijigata, kuka yafarayi kamar ba namiji ba yana kiran sunan tah da k’arfi
Bai tsaya bin takan su Adnan ba ya d’auketa sai asibiti, suma bayanshi sukabi bayan Adnan yace ma mai motar ya tafi ba komai
Yana zuwa aka karb’eta, saida sukayi nasarar farfadowar ta sannan suka dank’ara mata allurar bacci saboda sumbatun da ta farayi
Kafin wani lokaci kowa ya hallara a asibitin, likitan da ya duba Khadijah yayi masu bayanin ba wani problem kawai don ta tuna komai na rayuwar ta ne amma zata tashi normal don haka da ta farka zasu sallame ta
Da misalin k’arfe 7:15pm a yayin da kowa ke haramar tasowa daga masallaci Khadijah ta farka da surutai a bakinta wanda yayi dai-dai da dawowar Jiddan daga masallaci
Tun kafin ya shiga yake jin surutun ta hakan yasa yayi saurin shiga, saidai kuma yana zuwa bakin k’ofa ya tsaya saboda jin abin da take cewa
Kuka take tana cewa Mama yanzu Yaya SS ya mutu kenan da gaske Kuna nufin kuce narasa cikinshi dake jikina, wayyo Allah ka jikan mijina ka kai rahama a k’abarinsa saida nace mashi banason zuwanshi Kano ba amma ya tafi…. To gashi abinda jikina kebani ya afku
Shigowar Likitan baisa ta daina surutan datake ba, duba ta yayi sannan ya bata hak’uri kafin ya tambayi Mama ina mijinta hakan yasa Khadijah ta tuna da Jiddan kawai sai wasu sabbin hawayen suka shiga k’ara zubo mata saboda kaunarshi gareta da ta tuna
Ta tabbatar ba zata taba samun masoyi kamar Jiddan ba mussaman ita data hango girman kaunarta cikin kwayar idonshi wanda bako wane namiji bane zaiyi abin da Jiddan yayi akan bazawara ba Mai kuma curin kwakwalwa ba
Tana sane Yaya SS zai iya hak’ura da’ita depending da situation d’in da ake ciki amma tana da yakinin Jiddan ba zai iya barinta ba no matter how d situation is
Don ko lokacin da tana gidan Yaya SS tana yawan tuna Jiddan saboda zuciyarta na bugawa tare da tashi, kawai dai tana kukan rabuwa da Yaya SS saboda ya kyautata mata a zamantakewar su kuma shi bai tab’a nuna yana kishi da Jiddan ba don ko zoben dake hanunta yasan na Jiddan ne
Tunanin ta ne ya katse jin likitan naba safwan sallamar ta ita kuma Mama harta fara sallah don lokaci har ya tafi
Kallon ta safwan yayi yace “toh tashi kiyi sallolin dake kanki sai mu tafi ko? Ba musu ta fara k’ok’arin tashi saidai da kyar ta tashi har safwan na rik’eta sannan ta wuce donyin alwalla tai sallah
Al’amarin Jiddan koda ya gama jin abin da khadijah ta fada sannan yaji doctor nacewa ina mijinta kawai sai ya fita ba tare da kowa ya ganshi ba
Zuwa yayi jikin motar shi ya jikingina yana tunanin irin soyayyar da ya gwada ma Khadijah tun tana k’arama amma cikin wani dan k’aramin lokaci wani yayi awon gaba da’ita, ya ta tabbatar da Sulaiman yana Raye ba abin da zai hana Khadijah taki zabarshi _(nace anya jiddan?)_
Tana gama duka sallolinta suka fara haramar tafiya don Dama ita suke jira
Jitayi bata iya d’aurewa shiyasa ta fidda kunya tace ma Mama “ina Yaya Jiddan? “Nima ban San Yaya akayi bai dawo ba daga tafiya masallaci” safwan yace “nasan wani babban abune ya tsareshi kawai mu tafi gida na mashi ma waya yabiyo mu” ita dai Khadijah bata iya cewa komai ba har suka ga abinda suke suka fita
Jiyayi ciwonshi na Neman tashi, abunda rabon da ya tashi har ya manta, d’aga kanshi yayi yaga had’ari ne sosai a garin wanda da Gani zai zubda ruwa sosai, shiga cikin mota yayi ya zauna saboda iskar da ta fara yawa, yana tuna sadda suna makaranta idan suna zaune da Khadijah aka fara ruwan sama shiga take ciki tayi ta rawa k’arshe shima sai ta jawoshi cikin ruwan hankali ta zai kwanta…
Tunanin shine ya katse saboda hango su da yayi sun fito amma sai suka tsaya alamun magana suke, shiyasa shima ya fita da niyyar yaje wurin su
Mama ce tace “anya safwan mun tafi cikin hadarin nan? ” toh mama in banda abinki idan bamu tafi ba tsayawa zamuyi sai ruwan ya safko wanda bamu San ranar tsayawar shi ba ga dare nayi” shikenan mama tace sannan suka nufi wajen mota
Back seat Mama ta zauna shima safwan ya shiga mazaunin driver sai Khadijah da har ta bude kofa zata shiga sai kuma ta juya saboda bugun zuciyar ta da take jin ya k’aru kuma tanajin kamar Jiddan na kusa da ita
Karaf idanun su suka had’u dana juna, hakanan taji ta kasa d’auke idonta a kanshi shima haka, safwan da sai magana yake mata saboda taki shigowa jin tayi banza dashi yasa ya duba abin da take kallo sai yaga Ashe Jiddan ne, rufe k’ofar yayi yaja motar ya batta nan tsaye, sai da ya isa inda Jiddan yake yace “Dama kai muke jira toh sai gaka ka taho da’ita” d’aga mashi kai kawai Jiddan ya iya yi don hankalin shi nakan Dijee…????
A hankali ta fara takawa saboda yadda zuciyar ta ke fizgarta zuwa wajen wanda bata da kamarshi wanda yayi ma rayuwar ta rumfa tako ina, wanda duk girman laifi zata iya yafe mashi don ko da taji cewa Jiddan ne ya banketa wanda yayi sanadiyar zubewar cikinta bata k’ara maganar ba
Shikuwa Jiddan kwayar idonta yake kallo so yake ya gano idan akwai sauran soyayyar shi ko kuma babu SS ne kawai aranta..
Baifi taku ukku ya rage tsakanin su ba, ruwan sama ya kufce kamar da bakin kwarya, tsaye Khadijah tayi don ta kasa motsa koda k’afarta sai Jiddan ne ya ida takowa inda take tare da jawo ta zuwa jikinshi
Sun d’auki kusan 2minutes suna kallon juna ga ruwan saman dake dukan su amma in banda kallon juna ba abin da suke
D’aukarta yayi yasa cikin motar sannan shima ya shiga, bai zarce ko ina ba sai hotel d’in da ya kama, har yanzu babu wanda yace komai kowa da abinda zuciyar shi take sak’a mashi
D’aukar ta yayi kamar wata jaririya, yasa k’afarshi ya rufe k’ofar ya nufi cikin hotel d’in da’ita, saida ya shiga daki sannan ya direta saman gado
shiga toilet yayi ya had’a ruwan dumi sannan yafito, baice mata komai ba ya hau cire mata kaya itama bata hanashi ba, saidai badan k’aramin tada mashi hankali surar jikinta yayi ba
Sharewa yayi ya kaita cikin ruwan ya aje sannan shima ya shiga har yanzu ba wanda yace komai cikin su
Sun d’auki kusan 10 minutes sannan Jiddan yasaka bath rope ita kuma ya nadeta cikin towel, saida sukayi alwalla sannan suka fito, dayake akwai kayanta a dakin saboda jiya nan ta kwana, shiyasa ta d’auko hijab d’inta shikuma yajasu sallah kasancewar har yanzu ruwa ake sosai
Knocking d’in da akayi ne yasa Jiddan tashi yaje ya bud’e Dama yasan room service ne ya kawo abinci, amsa yayi yazo gurin Khadijah ya zauna
Ruwan Lipton mai zafi ya fara bata shima ya shiga sha sai da suka gama sannan suka hau cin abincin
Suna gamawa yajata saman gado suka kwanta tare da rungume ta tsam a jikinshi
Sun Dad’e shiru ba wanda yace komai, karo na farko Jiddan yace “I luv u..” Nima yayana bani da kamar ka” sai da ya goga hancinshi saman fuskarta sannan Yace “har SS?…”eh har shi mana” ajiyar zuciya ya sauke sannan yace “toh me yasa kikayi ta kuka kamar nine na mutu? D’an murmushi tayi don ta gane kishi ne ke d’awainiya da Jiddan tace “saboda a zaman mu ya kyautata Mani sannan bai tab’a nuna yana jin haushinka ba, amma ba hakan na nufin d’aya kuke ba shi masoyi na ne amma na wucin gadi kai kuwa na har gaba da abada ne shiyasa wasu lokotan zakaji ina kiranka da HABIBI DA’IMAN ma,ana MASOYINA HAR ABADA
K’ara rugumeta Jiddan yayi tare da manna mata kiss yana cewa “wlh ina son ki sosai Khadijah yadda ni kaina ban iya misiltawa Allah ya bammu tare, da haka dai har bacci yayi awon gaba da su
Su Mama ina isa gida suka ci karo da baba zaije asibitin, ganin su kad’ai ne batare da khadijah ba yasa shi tambayar ina suka barota Mama ke mashi bayanin tana wurin mijinta d’aga haka baice komai ba ya shiga gida don shima yasan suna bukatar lokaci, a wani bangaren na zuciyar shi yana tausaya masu saboda yadda sukaga jarabawar rayuwa su duka.
_Mrs Abdul Sule_
[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: ????????????????????????
*HABIBI DA’IMAN*
*WRITTEN BY*
*HALIMA MK*
DEDICATED TO SA’ADATU ALIYU KABUGA
_Amarya shalele,Amarya bakya laifi ko kinkashe d’an masu gida_ _*Aisha Aliyu kabuga*_ _Allah yabada zaman lfy Allah yasa next year muzo musha bikin suna wannan shafin naki ne ke kad’ai kisha shagalinki amarsu ta ango_
*page 186-190*
Zaune take tayi shiru batace komai ba yayin da jirginsu yayi nisa cikin sararin gajimare, abubuwa biyu ne suke addabar zuciyarta, na farko kunyar Ammi da takeji kasancewar basu tab’a had’uwa ba sai da biki yazo gashi seat d’inta tare yake dana Ammi,yayinda Rafeeq shikuma yana wajen Abbu sai Rafeeqa dake zaune ita da wata Mata
Dukda kunyar Ammi da Ihsan keji bai hana tunaninta tafiya wajen halin da yar uwar ta take ciki shiyasa ta k’osa su isa Egypt tayi waya da’ita
Kamar an tsikareta ta tuna data manta wayarta gida saboda abubuwan da sukayi mata yawa sai yanzu ta tuna, Ammi dake lura da ita tace
“‘yata ya akayi ne? Sadda kanta tayi tana kallon yatsun hannunta da yasha lalle tace “waya ta na tuna da na Manta ban d’auko ba” tak’are maganar cike da girmama, D’an murmushi Ammi tayi irin nasu na manya tace “kada ki damu idan munje sai a siyo maki wata” d’aga kanta tayi tace “toh Ammi nagode”
Ayayin da Ammi take yaba hankalin Ihsan cikin zuciyarta dukda kasancewarta yarinya shiyasa take godema Allah da yaba d’anta irin matar da take fata yasamu gashi tafito gidan tarbiya ga kuma natsuwa data fuskanchi yarinyar nada ita, bugu da k’ari gata kyakyawa don har tafi khadijah kyau duk da tsanani kamarsu don ita Ihsan tana da beauty point Sab’ani khadijah da bata dashi, shiyasa most of people kece mata pretty
Suna isa sai ga Yusuf mijin Rafeeqa yazo d’aukar su, shima balarabe ne dayake yana da wani aiki a gabanshi shiyasa bai samu zuwa bikin Rafeeq ba
Shaddad D’an Rafeeqa da bazai wuce shekara goma ba ya rugo wurinsu yana farin cikin ganinsu dayake ba’a tafi da shi ba saboda makaranta saida ya gama tsalenshi na murna ganin mum d’inshi da granma gakuma uncle d’inshi da sabuwar aunty daya yakawo masu sannan suka shiga mota suka nufi gida
A cikin motar ne yake tambayar Ammi wannan ce sabuwar Aunty d’inshi matar uncle Rafeeq, Ammi ta amsa mashi dukda bai iya Hausa ba cikin larabci yake maganar bai hana Ihsan fahimtar wasu kalaman nashi ba tunda ba laifi ana koya masu a islamiya
Zuwansu gida keda wuya kowa ya kama bacci saboda gajiyar da suka kwaso, gashi dama saukar dare sukayi ma k’asar, gashi washe gari za’a fara shagalin da Ammi ta Shirya masu na murnar biki
Da misalin k’arfe 8:00am na Egypt Wanda yayi dai dai da 7:00am na Nigeria, Ammi ce ta shigo d’akin da Ihsan ta kwana don ta duba ko ta tashi, saurin gaida ta tayi kafin Ammin tayi magana sai da tayi murmushi sannan ta amsa tare da cewa “toh kiyi sauri ki shiga toilet kiyi wanka ga break d’inki can ga kuma kayan da zakisa nan bisa gado don har mutane sunfara taruwa” amsa mata Ihsan tayi cikin ladabi sannan ta shiga toilet
Saida ta gama yin breakfast sannan ta d’auko kayan da Ammi tace tasa, mamaki ne ya kusa kasheta saboda yanayin kayan baxata iya sakasu tafita cikin mutane ba duk da rigar lafiyarta lau hannun ne aka tsaga kamar wata tantabara amma siket din duk a tsatsage yake har wurin cinya, shigowar Rafeeqa ne yasa tayi saurin juyawa
Dafa kafad’ar Ihsan tayi tace “sister dama nasan kina nan kin kasa saka kayan shiyasa nazo ince maki kada ki samu damuwa babu na mijin dake shigowa ko ango sai idan da dalili zaki ganshi, da wannan zacen na Rafeeqa ne yasa tasamu kwarin gwiwar saka kayan duk da tanajin kunya sannan ta Dora alkebba data gani had’e da kayan
Haka akayi shagali tare da al’adu irin na larabawan misra (cairo) ita dai Ihsan taga yadda akai ta dura mata karanfani dayi mata wanka da ruwan madara sannan aka koma b’angaren kamshi, sai kusan k’arfe 11:00am aka gama sannan tasa wata doguwar Riga mai hula ta zauna a d’aki ayayin da mutane keta kai kawo cikin gidan
Rafeeq ne ya shigo cikin parlour ya tambayi Ammi yana son ganin Ihsan don ya bata waya ta gaisa da yar uwarta, sai lokacin Ammi ta tuna daba waya hanunta shiyasa ta yarda Rafeeq ya shiga d’akin da take tare da gaya mashi ya kama ta ya siyo mata waya itama idan mutane sun lafa ta kira su Mama taji ya jikin khadijar
Sallamar da Rafeeq yayi ita ta katse mata tunanin gida da take, zama yayi dab da’ita sannan yace “pretty ya kike? Lafiya lau ina kwana? D’an murmushi yayi sannan ya amsa tare da cewa “dama zuwa nayi mu gaisa inji mikeke buk’ata” shiru tayi sai kuma tace “ina son gaisawa da mutanen gida…toh yanzu wa kikeso a kira Mama ko khadijah? Sai ta d’ago ta kalleshi sannan tace “a fara kiran Mama sannan ya khadijah” yace “uhm autar Mama kenan ai yanzu kin zama tawa” ita dai batace komai ba don a tsorace take, ganin su kad’ai ne a d’akin
***
Ranar da ta haska window d’in d’akin har ta samu ratsowa ta gefen labulan ta dira har bisa gadon baccin su, haskenta ne zai tabbatar maka da baza’a wuce k’arfe 10:00am ba amma har yanzu baccin su suke cikin kwanciyar hankali don ko sallar asuba yau tare sukayi saboda sun so su makara kasancewar sun Tara bacci mai yawan gaske a idanunsu
Jiddan ne yafara bud’e idonshi bai sauke su ko ina ba sai kan fuskar khadijah dake dab da shi tana baccinta, lumshe idonshi yayi ya bud’e yana k’arema fuskarta kallo, gaba d’aya tun ranar da ya ganta anyi mata Kunshi lokacin da yace ta dauko mayafi ta Ruga yaga ta canza sosai amma sai yau ya kara lura da canzawar tata duk da gyaran da tasha amma yana jin canji Dan gane da ita ga kyau da take karawa don hatta kirjinta yanzu a cike yake…
Motsin da tayi ne ya ankarar da shi zata tashi shiyasa yayi saurin rufe idonshi kamar mai bacci
Kamar yadda yayi itama haka ta zuba mashi ido tanajin kaunarshi da tausayinshi na ratsata, jikinshi ta kalla taga yadda duk ya murde sai ta tuna lokacin da suna makaranta ba haka yake ba amma yanzu duk ya canza saboda yawan exercise… “Kallon fa? Da sauri ta kalleshi sannan ta tabe baki kamar zatai kuka tace “dama ba bacci kake ba kana kallona” rugumo ta yayi yana cewa “haba hot milk ni asuwa in kalleki” mutsu mutsu ta farayi sai kuma ta tsinci kanta da son jin kamshin jikinshi shiyasa ta shiga tusa kanta shikuwa hakan da take mashi na Neman jawo mashi abin da yakeson,dama ya d’aga mata sai ta ida warwarewa sannan yakoma bakin aiki ya d’aura daga inda yatsaya
D’ago kanta yayi yace menene? Kwanta bari in shiga wanka, bare baki tayi da niyyar d’ankara mashi kuka sai kuma wayar shi ta d’auki ringing
Yana dubawa yaga MY R ne sai da ya kada kai tare da yin murmushi sannan ya d’auka ita kuwa khadijah tuni takoma jikinshi ta lafe
“A’a aboki kace Mani kun tsufa Egypt…”toh handsome ina zaka sani tunda jiya soyayya tasa ka manta damu” gashin khadijah ya shafa sannan yace “Allah ban San wulakanci kasan indai batun kyau ne kafini” karaf Rafeeq yace “haka kuma matata tafi taka sai dai matsala daya daka fini zama smart” yatsina fuska Jiddan yayi yace “zan baka time nasan d’okin amarcine ke damunka yanzu ina pretty take mu gaisa inji dai baka yi mata komai ba ko?….”ah ni su Yaya manya gata nan so take Ku gaisa don tabar wayar ta nan gida”
Amsa tayi tare dayin sallama, sai da suka gama gaisawa sannan yasa ma khadijah wayar a kunne sai lokacin ya lura Wai bacci take, mamaki ya kama shi amma sai ya share ya tada ta ta gaisa da Ihsan sannan ta koma
Tashi yayi yaje ya siyo masu abinci ya dawo har lokacin bacci take hakan yasa ya tada ta, da kyar ya samu taci abincin kad’an ta kuma cigaba da baccin
A b’angaren su Ihsan da Rafeeq tana gama wayar ta tashi da niyyar tafiya yayi saurin rik’o hanunta, a tsorace ta waigo tana kallon shi yace “pls bamuyi fira bafa..a hankali tace ” toh ka sakeni sai muyi firar” sakinta yayi amma kafin kace kabo ta ruga da gudu, mai Rafeeq zai idan ba dariya yana cewa duk yawonki saina sha zumar yarinya kin gama guje gujenki kizo hannu tare da barin d’akin
***
Waya yake da wani abokin aikinsu da za’a d’aura aurenshi gobe dayake kano yake shine yake sanar da shi Rafeeq yana Egypt don haka bazai samu zuwa ba,
Daga can b’angaren Usman yace ” haba ba damuwa dama Mujaheed yace yana nan tahowa yau toh kai sai yaushe?.. “Dama tunda karfe 2:00pm za’a d’aura auren shiyasa Nace gobe da safe zan taho…bai ida wayar ba ya kashe saboda jin khadijah ta tashi tana kyara amai
Rik’eta yayi harta gama sannan ya gyara wajen duk jikinshi kyarma yake saboda yadda yaga tana amai ga jikin ta ya d’auki zafi dama ba tun yauba yake lura da yadda ta canza ba
Saida ya samu ta d’ansha ruwan tea kad’an sannan ya shiryata don zuwa Asibitin Allah bamu lafiya dayake mai asibitin abokin uncle d’inshi ne don yana son aduba mashi ita nan take
A gurguje ya tafi da ita asibitin kuma kamar yadda yaso haka ya samu aka duba ta batare da b’ata lokaci ba
Zaune suke shi da khadijah yayin da Dr Yusuf ke gabansu, shidai Jiddan ya k’osa yaji mai xaice…mik’o mashi takadar Dr yusuf yayi ita ta katse mashi tunani, sannan yace….
*_Mrs Abdule Sule_*
[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: ????????????????????????
*HABIBI DA’IMAN*
*WRITTEN BY*
*HALIMA MK*
DEDICATED TO SA’ADATU ALIYU KABUGA
*page 176-180*
*Y*au saura 3 days a fara biki, amare sunsha kyau har sun gaji, Khadijah kuwa har wani yellow yellow fatarta keyi ga kirjinta da yak’ara cika yayi fam, saidai tun ranar da sukazo har yanzu Jiddan baisamu ya ganta ba
Don kullum idan yaje gidan sai ace batanan shi kuma bazai iya tambayar Mama inda ta tafi ba haka zaigama ‘yan kewaye kewayenshi yatafi batare da yaga ta inda zata fito ba yakuma kasa tambayar koda Ihsan inda taje ba
Ita kuwa khadijah tana sane take guje mashi don tasan cewa zaiyi ta bishi masaukinshi al halin ga ‘yan uwa tana Gani harda wad’anda ta Dad’e bata Gani ba kuma ai akwai kunya aga tabi miji hotel shiyasa ta kashe wayarta don ma karya dameta da magiya
Zaune suke palourn ba kowa daga mai k’unshi saimai gyaran jiki tare da su Ihsan sai khadija dake zaune gefe don ita an gama mata na k’afarta har ta wanke yanzu ma na hannun da akayi take jira ya bushe
Seema da ake cikin yi mata kunshi tace “Allah Yaya Khadijah bakiga yadda Jan k’ushin nan yayi maki kyau ba” tace “kedai Seemah ko zagina kike? Sai ga Iman tafito daga kitchen tace “toh uwar kuri an yabeki madadin ki gode kin tsaya kina wata magana gaskiya Jiddan na fama dake” tak’arshe maganar tana dariya
“Wallahi ba wani fama kedaice za’ace kina fama da mijinki tunda har yau bamu taba gaisawa ba kullum baya gari halinsu d’aya da mijin saudat” duk tana maganar ne cikin tsiwa shiyasa Iman tace
“Oh ni nashiga ukku da Khadijah sha kuruminki ranar d’aurin aure zaizo Ku gaisa ni kuma in huta da gori, zabura Khadijah tayi kamar wadda aka tsikara, Iman da har ta tsorata tace “lafiya?
“Allah wani irin fitinannen fitsari nakeji kamar yazubo mani wallahi ban iya rik’eshi” Iman tace “toh ai sai ki sakeshi a gaban k’annanki tunda baya rik’uwa”
Jiddan da yazo shigowa palourn yaji abin da khadija ke cewa sai ya tsaya yana sauraranta
Ihsan ce keyi ma Khadijah dariya, khadijah tayi saurin kallonta tace “ke ni tsararki ce shekara nawa na baki? Ihsan tace “yi hakuri 6 years kika ban..”toh gara ki shiga hankalinki”
Sai kuma ta tabe fuska tace “ya zanyi bari in tafi toilet d’in can baya in wanke don gaskiya ban iya rik’e fitsarin nan har lallen nan ya bushe” tashi tayi Iman na mata dariya sai, tashin ta keda wuya kallabinta ya fadi k’asa kallon Iman tayi
Tace” Iman don Allah d’auko ki d’aura mani” tace “haba yariya sai dai ki tafi haka” tsoki ta buga sannan takama hanyar fita
Shi kuwa jiddan yanajin inda zata tafi sai yaje wurin ya boye yana jiranta, tana zuwa ta durk’usa zata bud’e famfo saiji tayi an rik’e mata kugu tabaya, da sauri ta bud’e baki zatayi ihu yayi saurin rufe mata baki da hannunshi
Shiru tayi tana kallon shi, baice mata komai ba ya jata zuwa toilet d’in sannan ya tartare doguwar rigar jikinta
Tsaye tayi tana kallon miyake nufi, ganin kallon datake masa yasa ya d’aure fuska kamar bai tab’a dariya ba yace “tsuguna mana kiyi! Ba musu ta tsugunna tayi, tana ganin ya debo ruwa zai mata tsarki tai saurin rufe idonta aranta kuwa cewa take ai wannan iskanci ne ba tsarki ba….
Tunanin ta ne ya tsaya saboda jin yadda tsigar jikinta ke tashi, haka ta d’aure har ya gama suka fito, shima tsarkin da yayi mata ba k’aramin tada mashi hankali yayi ba d’aurewa kawai yayi
Saida ya tattara natsuwar shi sannan yace “Khadijah guduna kike ko? Tace “a’a” “toh ina kallabinki…”yana parlour”
“jeki d’auko mayafinki ki rakani idan munje kin wanke k’unshin acan” d’aga mashi kai kawai tayi, saida ta bari tayi nisa da inda yake sannan ta juyo tace
“Nizakayi ma wayau toh ba inda zan bika” sannan taruga da gudu cikin palourn, lips d’inshi ya d’an lasa yace “yariyar nan ta raina ni but zanyi maganin ta soon
Haka yaja mota ya tafi cikin fushi, washe gari ma da akayi kamu baije ba don fushi yake da Khadijah, itako harkar gabanta kawai take
The next day ya kama ranar dinner, zaune suke kowa ya shirya suna jiran azo d’aukar su ita dai Khadijah tayi shiru tana sauraron Iman dake ce masu Ihsan wai bayan aure idan kuka d’an saba da namiji yanaso wani lokacin mace ta nuna tana buk’atarshi amma a cikin kissa….
Motocin da suka fara zuwa ne yasa suka fita ita dai Khadijah ta manta da tayi ma Jiddan laifi
Suna zuwa kowa ya kama gaban shi suka bar khadijah nan tsaye a tunaninsu sunsan Jiddan ne zaizo d’aukarta, sai ware idanu take taga ta inda zata ga Jiddan amma bashi ba alamarshi har amare suka gama tafiya bata ganshi ba
Daga can baya ta hango shi zaune shi kad’ai cikin mota, murmushi tayi ta nufi wurinshi saidai yana ganin ta ya d’auke kai
Bud’e motar tayi ta shiga tace “sorry nabarka kana ta jira, bansan nan kayi parking ba” banza yayi mata baitanka mata ba, ganin yashare ta ne yasa ta tuno laifin ta wanda ita bata d’aukeshi da wani abuba balle haryayi fushi, kallonshi tayi cike da kissa tafara bashi hak’uri amma still yayi banza da’ita, har suka isa wurin da za’a gudanar da dinner d’in
Biki yayi biki mawak’a kowa sai baza basirarshi yake don ya kwashi rabonsa kamar daga sama zazzafan muryar mawak’in nan Nura M. Inuwa yafara kiran sunan Jiddan yana wasashi yana fad’in soja marmari daga nesa, hakan yasa Jiddan tashi ya nufi cikin taron yana b’arin kudi
Dandanan idon yan mata yayi kanshi, shi kuwa mai wakar sai wasashi yake tare da kiran sunan uwar gidanshi
Khadijah ko ganin yadda ‘yan matan wurin sukayi mashi ca sa ido yasa wani azabeben kishi ya gama cikata, tashi tayi taje cikin taron tare da rik’ e hannun Jiddan, gudan kuma ta Dora saman kafad’arshi
Ganin yadda take taka rawa jikinta na wani irin juyi duk sai shima yaji kishi ya dameshi, Jan hannunta yayi bai zame ko ina da’ita ba sai cikin mota
A back seat ya aje ta shima yaza gayo ya shiga, kamota yayi zai rungume tace “yayana lafiya bafa gida Muke ba” kwalla ce ta taru cikin idonshi yace “so kike in maki kuka sannan ki bani hakkina? Sati d’aya kenan rabona dake amma guduna kike, Ko kin manta annabi yace ko akan dabba ne miji ya….bata bari ya ida ba ta had’e bakinsu wuri guda
Har sassarfa Jiddan keyi saboda yadda yayi missing d’inta saida ta lallabeshi sannan ya kira d’aya daga cikin soldiers d’in dake wurin yayi driving d’insu donshi baida kuzarin driving
Suna zuwa hotel d’in ya shiga nuna mata yadda yayi missing d’inta, har sunyi nisa sai wayar shi tafara ringing don ita khadija tata na gida
D’auka yayi yaji Rafeeq wai su Ihsan ke Neman khadija shine ya kira yaji ko suna tare don basu ga lokacin da suka fita tare ba, amsa mashi Jiddan kawai ya iya yi don baya cikin hankalinshi sosai don ba k’aramin canza mashi Khadijah tayi ba ga kirjinta da ya k’ara cika
Washe gari jama’a suka shaida d’aurin auren Rafeeq da Ihsan, Samra da Muhsin, Seemah da Abdul Jabar, Mujaheed da Islam dukda amaryar Islam na Kaduna amma kawu yace a d’aura anan don a rage ma mutane wahala
Lokacin kai amare nayi aka kai Ihsan wajen Ammi don tace Egypt zasu wuce washe gari don akwai bikin da ta had’a can saboda ‘yan uwanta
Motarshi yayi parking a gaban gidan su Seemah sannan ya kalli Khadijah yace “kiyi sauri don Allah” toh tace dashi ta fara k’ok’arin bud’e k’ ofar saiga Iman, gaisawa tayi da Jiddan sannan take ce ma Khadijah tazo su gasa da Adnan gaya can tsaye dasu Seemah hakan yasa ta nufi inda suke
Seemah ce ke kuka sosai Adnan na lallashinta, cikin kuka ta fara cewa “dole inyi kuka wlh mutuwar Yaya SS ta dawo Mani sabuwa saboda yadda yaci burin ganin ranar nan…
Dai-dai lokacin khadijah ta iso, jin abinda Seemah ta ambaci SS yasa ta shiga tariyo kamanin mai sunan, bakin ta har kyarma yake tace “S..S..” Adnan da baisan da’ita a bayanshi ba saijin maganar ta yayi shiyasa ya juya
Shima tana ganin shi ta tuna inda tasanshi, ja da baya ta farayi har ta hau saman center din bata sani ba,
Ba abin da take furtawa sai “S..S..SS…S.S wata mota ce ta shigo layin batareda mai tukin ya kula da Khadijah ba ji kake……..
*_Mrs Abdul Sule_*
[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: ????????????????????????
*HABIBI DA’IMAN*
*WRITTEN BY*
*HALIMA MK*
DEDICATED TO SA’ADATU ALIYU KABUGA
*page 191-195*
“Uhm su Jiddan kenan an kusa zama manya…” Haba! Don Allah likita bokan turai kada kace Mani zargina dai-dai ne” d’aga kai Dr yayi sannan ya mik’o mashi takkada tare da cewa” a kallah cikin dake jikinta yayi sati biyar har yashiga na shidda don haka kada ka damu kanka akan laulayin datake da zaran cikin yayi kwari zata daina insha Allah, amma kafin nan bari na rubuta Makan maganin da zata dungasha insha Allah zasu taimakamata wurin kuzari da lafiyar abinda ke cikinta”
Shidai Jiddan gyad’a kai kawai yakeyi kamar k’adangare yana kallon khadijah data sadda kanta k’asa
Ita kuwa rayuwarta ta bayace ta dawo mata sabuwa saboda tunawa da tayi da wancan cikin nata da SS,wanda yaci burin idan ta haifi namiji zaisa sunan Jiddan saboda farin cikin ta… Tunanin ta ne yakatse jin Jiddan ya kama hannunta da niyyar su tafi
Har suka isa mota ba abin da tace, kafin kuwa su isa ???? d’in yayi mata tambaya takai goma ko tana son wani abu, amma batace komai ba
Suna zuwa ta shiga wanka shi kuma ya tafi sawo masu abinci, bayanta gama shirya wane ta zauna zaman jiran dawowarshi, Bai d’auki lokaci matsawo ba sai gashi ya dawo, zama yayi ya bud’e abincin da niyyar ciyar da’ita sai gani yayi tafara kakarin amai
Da sauri ya rik’eta ayayin da take mashi nuni da ya rufe abincin, bayan yarufe sannan ta samu natsuwa, kallonta yayi yace “baki ci? D’aga mashi kai tayi sannan tace “batason k’amshin miya ko kallonta ma batasoyin…”
“Toh yanzu mi kike son ci? d’aga kanta tayi sama alamar tunani sannan tace “danyan mango” yace haba khadijatu ai wannan ba abinci bane sai yayi maki illah” d’an shagwabewa tayi kamar zatayi kuka,take ya diririce yace “toh naji zan samo maki amma ki fad’i harda abinci kinji? Shuru tayi na wani lokaci sannan tace “toh shinkafa da mai sai gishiri kada asa magi da yaji”
Da tausayi ya kalleta jin irin abincin da zataci kuma ita nan shiyafi mata dadi, da sauri ya fita don samo mata abincin, ita kuwa tunanin shashshakar da Ihsan ta tab’a had’a mata lokacin da tana da cikin SS take kwad’ayinta yataso mata, wani miyau ta had’e sakamakon tasshin tafarnuwa data tuna Wanda ya lullub’e shashshakar da taji manja a wancan lokacin, amma ba yadda ta iya haka ta hak’ura don tasan zatayi ma Jiddan wuyar Samu,gashi bayadda zatayi ta had’ata a inda take
Wayar tace ta d’auki ringing saida ta k’ara a kunne sannan tace” my Iman kin kyauta ai …”haba khadijah nafaje gida akace kina gurin mijinki toh ko hotel d’in kikeso na biyo Ku? “Toh bani kikazo gani ba?..” Eh hakane amma ina tunanin notinki ya kwance ko”
Dariya khadijah tafarayi tana cewa “ni ba k’usa bace balle ace ina da noti saidai ke” a b’angaren Iman d’in itama dariyar tayi tace “Kinga ni kira nayi inyi maki congract shine kika tsareni da d’umi…” Uhm kedai bari Wallahi ina ma kan tunanin wancan cikin na ya SS”
“Sai hak’uri Allah bai hukunta jini SS zaitaka doron k’asa ba” nunfasawa tayi ta cigaba da cewa “wai kuwa ya kikaji lokacin da kika farfad’o na d’auka baki San anyi auren Ku da Jiddan ba…”
“a’a ko d’aya don wallahi dana farka da tunani rasuwar SS natashi saidai ina jin ance mijina sai naji komai yak’ara dawo Mani kamar a mafarki harda zuwan mu india duk ina sane wallahi”
Tun tana wayar Jiddan ya shigo in banda kallonta ba abinda yake, saida ta gama wayar sannan ta kalleshi tare dayin murmushi tace” sannu my dear kadawo? D’aga mata kai yayi ya aje abincin yana k’ok’arin bud’ewa don shi burinshi bai wuce taci abincin ba
Saida ya bari ta gama cin abincin sannan yace “kin k’oshi d’aga mashi kai tayi tana k’ok’arin kwanciya shima sai ya kwanta tare da shafa cikinta Wanda hakan yayi mata dad’i
Ganin tana lumshe idonta yasa yaci gaba dayi mata haka har bacci yayi awon gaba da’ita sannan ya tashi don had’a kayansu
Wanka yafara sannan ya had’a kayanta daban, nashi daban saboda gida zai barta, Inyadawo kano sai ya dawo su wuce Abuja saboda yanayin datake ciki
Lokacin data tashi taga abin da Jiddan yayi sai tahau tambayarshi ya akai yaware kayanta daban danashi batare zasu tafi ba, bai tunanin komai ba yagaya mata gida zai barta, aikuwa ta bud’e mashi shafin rigima harda kukanta, tun yana kwatanta mata har ya gaji ba yadda ya iya dole ya yarda zai tafi da’ita tunda baya son abin da zaisa mata damuwa.
A Daren ranar sukayi bankwana da kowa don har gidan Samra saida sukaje da gidan Iman sai a lokacin Iman ke gaya ma khadijah itama ciki gareta, sannan rabi’atu ta haihu, da wannan farin cikin sukayi sallama da juna
Washe gari tunda safe suka kama hanyar kano shiyasa k’arfe 10:00am tayi masu a kano
Hotel Jiddan yakama masu kasancewar kwana d’aya zasuyi, saida ya tabbattar da mutuniyar tashi taci abinci kafin ya shige wanka
Yana fitowa ya ganta saman gado bacci ya kwasheta da k’irin d’anyan mangwaron ta a hannu, d’an murmushi yayi duk da bayason tana sha amma yaya iya dole yakyaleta tunda yanayi ne yasata shanshi, agurguje ya shirya ya fita
Koda ya isa wajen abokin nashi Usman yafara mashi tsegumi wai yadade bai iso ba, saida Jiddan ya bari ya kai aya sannan yace “toh naji sarki mai Aisha bada kanka asare kaje gida kace ya fad’i,nima da hrtcorn d’inna nazo shiyasa kaga na Dade don Kasan…uhm”
“nasan me? cewar Usman, saida Jiddan ya k’ara shakar iska da kyau don yaji dad’in koro da bayani sannan yace “nakusa zama babafa…”kai captain banson k’arya fa!” kallon ukku saura kwata Jiddan yayi mashi kafin yace “na tab’a Maka k’arya ne? Ka bari anjima da’ita zamuzo dinner saika tambayeta tunda ni nazama mak’aryaci”
“rufaman asiri shegen gora ni rashin kunyata baikai nan ba”
“na’aza ka wuce nan tunda ni baka yarda dani ba, badamuwa in munzo sun gaisa taga Kuma amaryar, tunda yau dai Allah yayi Usman ya auri Aisha” dariya sukasa baki d’aya sannan sukaci gaba da yadda zasu tsara shirye-shiryensu har zuwa lokacin da aka D’aura Auren
Jiddan bai samu damar komawa wajen khadijah ba sai gabda la’asar, yana zuwa ya tadda ta tana karatun novel na Hausa na fitacciyar marubuciyar nan _zarah surbajo_ Wanda tauraruwarta ke haskawa a duniyar yanar gizo mai suna Ummu Aymana, duk sai yaji ta bashi tausayi don yasan kad’aici ma kadai ya isheta shiyasa baiso zuwa da’ita ba
Tana ganinshi ta tashi ta rungume shi, zaunar da’ita yayi bakin gado sannan yace “kad’aici ya isheki ko? Bata bashi amsa ba tahau ragemashi kayan jikinshi tana cewa ” yanzu kazo kayi wanka kafin lokacin sallah don nasan ka kwaso gajiya sosai” shidai kallonta yake yana murmushi saboda yadda yaga ta warware ta samu
sauk’i sosai
Aikuwa kamar yadda yayi niya Ana gama sallar la’asar yajata suka fita yawo harda siyayya yayi mata da wata purple din gown me kyau da zata saka anjima idan zasu dinner tunda shima purple din kaya zaisa, basu suka samu dawowa ba sai gabda magrib don haka jiddan ya wuce massallacin dake cikin hotel d’in bayan ya aje khadijah ta wuce room d’in dasuka Kama
***
Shikuwa Rafeeq bil hakk’i yakeson kebewa da pretty amma gudunshi takeyi haka kuma Ammi ta kasa ta tsare bata bari yana samun damar ke bewa da’ita, donshi harya farajin haushi shiyasa ya k’osa su koma Nigeria
Zaune suke a parlour shida Ammi yayin da Ihsan ke zaune gefe guda tana saurarsu duk da ba duka abinda suke cewa takeji ba amma su a zatonsu Bataji maisuke cewa ba
Duk zance bai wuce son abashi matarshi dayake ba, saida kyar ya samu Ammi ta tashi ta barshi da Ihsan, itama kuwa Ammi na fita tayi niyarfita
Saurin shangabanta yayi yace “haba ina zaki?tace “Ammi nakeson bi” zaro ido yayi yana kallonta saboda cikin harshen larabci tayi maganar
“Pretty dama kin iya larabci? Kice kinajin abinda Nace ma Ammi..girgiza kanta tayi tace “a,a ina dai gane kadan ” d’an murmushi yayi yace ” OK zamu dungayi tare har ki kware kafin ki Haifa Mani babies masu kama da…. Bai ida ba ta shammace shi ta ruga ba yadda ya iya dole ya hak’ura
***
Dinner tayi dinner,Amarya da Ango ansha kyau, inda fasihin mawak’in nan Ali jita yana ta suburbud’a masu jitarshi, su khadijah da jiddan suma sunsha kyau da sauran Wanda suka halarci Wurin liyafar kowa kagani sai wallai niya yake don kyau
Mamaki bai kama khadijah ba saida taga Amaryar Don tabbas bazata taba mantawa da fuskar Ashanty ba duk da sau d’aya ta tab’a ganinta a bisa tsautsayi, dasauri ta is a inda Ashanty take hakan yasa Jiddan yabita da sauri
Tun kafin khadijah ta iso Ashanty ta hangota itama sai tayi saurin isa inda take tare da rungumeta tace “khadijah!….” Aisha! Cewar khadijah da mamaki sukuwa Usman da Jiddan harma da Mujaheed dayake wurin kallonsu suke suna mamakin dama sun San juna?
Tunaninsu ne ya katse jin Ashanty na ambatar ina Laila? Ai dan danan fuskar Jiddan ta canza, kur ya kura ma khadijah ido Don sonjin wacece Ashanty Don duk yadda akai tana da alaka da Laila…..
_*Mrs Abdul Sule*_
[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: ????????????????????????
*HABIBI DA’IMAN*
*WRITTEN BY*
*HALIMA MK*
DEDICATED TO SA’ADATU ALIYU KABUGA
*page 196-200*
Juyowa khadijah tayi tana kallon Jiddan tana k’ara nazartar yanayin da yashiga daga ambatar sunan Laila da akayi, wani kallon tuhuma ya cigaba da aika mata nasan sanin ya akai tasan Ashanty da kuma miye alakarta da’ita, bata wani b’ata lokaci ba ta hau yi mashi bayanin yadda tasan Ashanty da kuma taimakon da tayi masu
Jikinshine yayi Sanyi da irin namijin k’ok’arin datayi naganin yakubuta daga sherrin Laila yana kuma godema Allah da yashiryar da’ita kafin lokaci ya k’ure mata, bakamar Laila da tayima duniya zuwan wohi ba, kallon b’angaren da Usman yake yayi yana k’ara jinjina mashi na jajircewa dayayi ga abinda yakeso, Don shi shaida ne akan irin son da Usman keyima Ashanty duk da kasancewar basu San juna ba da’ita
Kuka Ashanty ta fashe dashi jin cewar Laila tarasu, bayan ta nisa da kukan ne takama hannun khadijah tana cewa “khadijah kamar yadda kika sani sunana Aisha, Usman kuma d’an uwana ne, kasancewar mahaifin mu baya bari muyi karatu gaba da secondary yasa yake zab’a mana mijin aure domin duk yayye na mata haka yayi masu mazan ne kawai ke cigaba da karatunsu har inda suke son sutsaya, toh nima haka ta kasance a kaina sai dai ni gaba d’aya Allah baisaman son Usman araina ba,domin nafi kwad’aitar da incigaba da karatu ganin bazan iya auren shiba bama shiba kowa ne namiji yasa nagudu nabar gida da zumar na tafi karatu saina gama in dawo nasan lokacin zasu gane amfanin hakan…”
Nisawa tayi sannan taci gaba da cewa “Ashe abinda ban sani ba na tafka baban kuskure a rayuwata tunda ba kud’i gareni ba, haka naci gaba da rayuwa ta a garin Kaduna ba Wanda na sani har Allah ya had’ani da Laila wadda itama auren dole ne ya korota shine mukaje gidan wata magajiya karuwai, itace silar samu a hanyar bariki har takai da munzo munfi k’arfinta saboda da manyan Alhazai bariki muke harka.
In takaice maki labari daga baya ma sai muka tattara muka koma Abuja Don babu abinda bamuyi har Allah ya had’amu da Jiddan Wanda shine mutum na farko da ya fara gagarar mu duk dani bazai iya shaida fuskata ba kasancewar bamu tab’a had’uwa saboda wani sab’ani da muke samu, amma nasan fuskarshi tawa ce kawai baisani ba, har hakan ta kasance..
Lokacin da na dawo gida kuwa da kyar nasamu iyaye na suka yafe Mani sannan na fara Neman tuba wurin Allah haka dangina ma na nemi gafarar su kafin daga baya Usman ya dawo yace zai aureni Don har lokacin baiyi aure ba
Daga farko mahaifina yak’i amincewa nima haka don ina ganin ban cancanci ya aureni ba dukda kasancewar bani d’auke da wata cuta amma ai da kunya saida nagama yawon tazubar ace namiji kamili kamar Usman ace zai aureni amma ganin yadage yasa nayi istibira’i wata ukku, shine har Allah yanuna mana wannan lokacin toh kinji abinda yafaru bayan rabuwarmu
Kallon Jiddan khadijah tayi cike dajin tausayin Aisha sannan ta kalli Usman tana jinjina mashi kai alamar yayi k’ok’ari kafin Jiddan yace “shine Wanda nake gaya maki shima saboda soyayya yasa ya tafi soja” khadijah tace “dama akwai masu iyayin abin da kayi? Sai Ashanty ta bata amsa da cewa “gara ke aure kikayi amma nifa kedai Allah ya rufa asir….bata ida ba Usman ya kama hannunta yana cewa
“Kunga fa mutane sun taru wurin nan ya kama ta mubar zancan nan” jiddan yace “kaide ko sauri kake akai maka matarka ai da Rafeeq na nan da kasha tsiya “dariya Usman yayi yace “dad’in abunma kokai baibariba balle kayima wani tsiya”
Daga haka suka cigaba dayin abinda ya kawo su, anci an sha sannan ango da amarya suka wuce gidansu saidai muyi masu fatan alheri
A gajiye suka koma masaukinsu, don haka wanka kawai khadijah tayi ta kwanta shima yana gama yan danne dannenshi a waya yayi wankan sannan ya kwanta tare da rungumota
Tanajin yadda ya rungumeta tasan abinda zaiyi mata, tunanin gajiya da yadda take jin jikin ta take saidai tasan dole Jiddan ya nemeta don rabonshi da’ita kusan 4 days kenan
Juyo da’ita yayi yafara manna mata kiss ako ina nasak’on jikinta, k’ok’arin cire rigar baccin kawai yake saidai ganin bata mashi yadda yakeso yasa ya d’ago yana kallon cikin idonta da kyar yace
“kin..gaji..koh? Girgiza mashi kai tayi don badan k’aramin sonshi da tausayinshi takeji ba, rugumeshi tayi tana shafa mashi kai kamar yadda ta saba mashi Wanda hakan na mashi dad’i sannan tace “I luv u.. Ko amsa bai iya bata ba ya shiga k’ok’arin nema ma kanshi natsuwa a inda yafi daukar mashi hankali kafin ya fara tona mata asirin zuciyarshi da yadda sonta ya raunanata shekaru masu yawa bak’aramar k’ara tara mata gajiya yayi ba don Saida yaji tana neman yi mashi kuka yasa yasarara mata badan yagaji ba sai don tausayinta don baik’i ya kwana saman ruwan cikinta ba yana kwasar gara
Washe gari suka kama hanya sai Abuja Wanda ba abinda khadijah keyi cikin mota daya wuce bacci shidai Jiddan mamakin baccinta yake saboda bata d’aukar lokaci sai kaga ta bingire da bacci kamar wata jaririya don yanzu hours din da take tana bacci yafi yawa akan Wanda take farke ita dai haka nata cikin yazo dashi kenan ganin shi k’adai ke zancen zuciya yasa yak’ara maida hankalinshi kan driving tare da ambaton Allah abakinshi
Suna isa lokacin ta tashi daga bacci, Jiddan yake nuna mata gidan Rafeeq Wanda kana hagenshi daga nasu gidan sannan suka shiga gida
Sakin baki khadijah tayi da suka shiga tace” yayana waya gyara gidan? Rumgumo ta yayi ta baya tare da d’aura kanshi saman kafad’arta yace “tun kafin mutaho nakira maigadi yasa matarshi ta gyara don nafison da mun dawo ki bani…bai ida ba ta b’anb’are hannunshi dake saman kugunta da yunk’urin rugawa
Saurin rik’eta yayi yace “haba khadijah wannan ai wautace sai kija Mani asara, don Allah koda wasa kada kice zaki ruga kinji? Ita harga Allah mantawa take tana da ciki don haka tasaki yar dariya tare da cewa “toh aini mantawa nake fa” sugummar ta yayi kamar wata yarinya sai kad’a k’afafunta take, bazarce ko ina da’ita ba sai bedroom d’insu yana cewa
“Toh ai shiken bari kigani d’aukarki mazanyi princess” dariya ta kamayi tana cewa “ai kuwa yau har tawai nakeso kayi Mani.. Harda ma…..
Ban ida jin abinda suke cewa ba sakamakon banko k’ofar d’akin da sukayi ni kuma ban bisu ba saboda Biro ta da ta k’are sai na tafi sayen wata
***
A yaune su Rafeeq suka dawo don haka Jiddan bai samu zama ba tunda dagashi har Rafeeq din ranar Monday zasu koma aiki, yoh Alhamdulillah sun dawo saidai mu baro ma pretty da Rafeeq fili don shan amarci
A gajiye ya dawo gida, khadijah na ganinshi tazo ta rungume shi, kumatunta ya girgiza kamar yadda suka saba tun suna yara itama tayi mashi kafin su fara zuba soyyayar su yadda ya dace
Kwaci tashi asarar mai rai cikin khadijah har ya shiga wata ukku iyayin da take samun kulawa mai kyau daga wurin Jiddan
Dawowar shi kenan daga wajan aiki, sallama yayi khadijah ta amsa mashi batare da ta taso tayi mashi oyoyo ba kamar yadda ta saba saboda abinci da ta tusa gaba tanaci
Zuwa yayi ya tsugunna gabanta yace “an deejah na abinci akeci? Daga mashi kai tayi, shi kuma kallon abincin yake ba wani Abu bane illa taliya da manja
A hankali yace “idan iceprncess ta yarda zanje gidan Rafeeq naci abinci” don shi yagaji da cin komai jalof ace kwata kwata ba’a son ko kamshin miya
A b’angaren ta itama tausayinshi takeji don tasan dole ya gaji shiyasa tace “me zai hana idai ba za’ayi Mani tsarabar kamshinta ba”
Yar k’aramar dariya yayi sannan ya tashi yayi wanka ya wuce gidan Rafeeq
Koda yaje saida Rafeeq ya gama sharranceshi sannan suka gaisa tare da fara cin abincin tare
Hira suke sama-sama Jiddan yace “Rafeeq kasan wani Abu? ..a’a sai kad’i cewar Rafeeq sannan Jiddan yace so nake idan khadijah ta haihu insa sunanta” dariya Rafeeq yayi yace “toh kai wayace maka mace za’a haifa idan aka haifi namiji fa? “sai in bata zab’i idan namiji aka haifa, d’an k’aramin murmushi Rafeeq yayi yace “toh dame za’a rinka kiranta?kasan bazamu kirata da khadijah kai tsaye ba
Plate d’in daya gama cin abinci ya ture tare da gyara zaman shi saman cushion din sannan yace “wannan kuma naba abokina zabi”, da farin ciki Rafeeq ke cewa “ai kuwa naji dad’i kuma zan bata suna Wanda ya dace da ita Allah dai ya safki khadijah lafiya…” Ameen wai ina pretty take ne ? “Uhm wlh fushi take don na gaya mata batun tafiyar mu shine ake fushi, shiyasa kaganni zaune parlour ni kad’ai, saita d’an huce sannan in gaya mata yanayin aiki ne kasan ita ba sabawa tayi ba”
Mikewa Jiddan yayi yana cewa “kaga ni banma gaya ma khadijah ba gashi jibine..mstww ni wlh ban son tafiyar nan saboda yanayin da khadijah ke ciki akwai had’ari in barta ita kad’ai”
Tafiya suka farayi Rafeeq na d’an taka mashi yace “ai sai hak’uri amma ni da ka barta ita kad’ai tunda ga yar uwarta kusa a kulle gida daya mana basai su xauna wuri d’aya tare ba” gyada kai jiddan yayi alamar gamsuwa yace “hakan kuwa yayi sai a kulle nan ita pretty taje can ” da wannan shawarar sukayi sallama da juna sannan jiddan ya wuce gida
Yana zuwa ya tarar da ita ta gama cin wani abincin shima da manja, kusa da ita ya zauna sanan yace “wai khadijah baki gajiya da cin wannan abincin shifa na barki kinaci..” Toh yayana ya zanyi bakina ne ba dad’i”
“Toh khadijah kema dai ko nama bakici don Allah ki dinga ci kinji? D’an shiru tayi sannan tace “naji zan dinga ci amma nakan rago..”badamuwa zansa a dinga kawo maki duk bayan kwana biyu saboda an tura mu aiki zuwa Cameroon amma ba dadewa zamuyi ba don bazamu wuce two weeks ba”
Tun kafin ya gama maganar khadijah tayi sake da baki tanajin shi hakan yasa kwallah taruwa cikin idonta Baice komai ba sai don tunanin yadda zai tafi ya barta ita kadai bayan tana da laluri kuma tana buk’atar shi kusa da’ita.. Girgiza mata kai ya farayi alamun kada tayi mashi kuka
Itama kanta da girgiza tare da cewa “tafiya fa kace!…