Uncategorized

HABIBI DA’IMAN 201-220 END

 *page 200-205*

..”Eh tapiya khadijah amma ki kwantar da hankalinki keda pretty zaku zauna kafin mu dawo ai ba Matsala ko? Nauyayyar ajiyar zuciya ta safke jin cewa pretty zata dawo gidanta su zauna kafin su sudawo yasa hankalinta ya kwanta, d’aga mashi  kai tayi alamar ba damuwa

 Bayan kwana biyu da faruwar hakan suka shirya suka tafi shida Rafeeq dasauran abokanan aikinsu dazasuyi tafiyar tare, sannan pretty ta dawo gidan khadijah,  sai dad’i takejI haka sukayi zamansu cikin jin dad’i..

 

Kwance take saman cinyarshi tana karanta wani novel mai suna …kawarta ce sanadi

 

Samra kenan ayayin da Muhsin yake waya da abokin nashi yana cewa ” gaskiya J nidai a tawa shawarar kada kace idan ta tashi haihuwa sai kunje wata k’asa, in banda abinka kai da kake Abuja meye na tafiya wani wuri? Ai akwai hospitals masu kyau”…daga can b’angaren banji abinda  yace ba sai ji nayi Muhsin yace

 

“OK yanzu saura sati daya kadawo kenan?..

 

 “Toh ba damuwa zataji a gaida

Rafeeq”

 

 

 

 

Hanging up din call din yayi sannan ya shafa kan Samra da tayi nisa a karatunta yace “Jiddan na gaidaki..ina amsawa Ashe basu nan?

 

 

 

 

“Eh ya akayi kika Sani?..nima da mukayi waya da Islam ne take gaya Mani don ita gida ta koma wai bata iya kwana ita kadai a gida”

 

 

 

 

Tashi Muhsin yayi da niyyar fita yace “toh kinga laifinta ko ke zaki iya kwana ke kadai ne” zumbura baki tafara yi shikuma yayi saurin ficewa don kada ta shiriritar dashi zuwa massallaci

 

 

 

***

 

 

*3 months ago*

 

 Alhamdulillah komai yana tafiya Normal a yayinda b’angaren jiddan da khadijah har yanzu tana fama da laulayin cikin domin kuwa yana wahalar da’ita dukda yafita watannin kwaikwai amma hakan baisa ya sararamata ba

 

 

 

 

 

Fitowarta kenan daga bedroom ta nufi inda Jiddan yake zaune tare da katon cikinta kamar kace haihuwa yau ko gobe saboda wani irin girma da cikin  yayi duk bai wuce wata shidda ba

 

 

 

 

Zama tayi sannan ta bude mashi tafin hannunshi ta saka mashi wasu beat’s guda ukku tana k’ok’arin yin magana  saurin cewa yayi

 

 

 

 

“Eyye bincike kikayi Mani ko hrtcon? Girgiza kai tayi tace “a,a wallahi kawai nima bansan yadda akayi naje wurin ba kawai dai ina mamakin yadd har yanzu suna nan”

 

 

 

 

“Toh naji ina D’an hannun yake?hannunta dake boye a bayanta ta fiddo tare da mik’a mashi, yace “oh da b’oyewa zakiyi ko? Bayan Ke ki ka bani..”a,ah nifa da ajewa zanyi idan na haihu insa ma baby koh” ta k’arashe maganar cikin sigar shagwab’a

 

 

 

 

Da Sauri ya kamo hannunta ya saka mata yana cewa “toh gashi jeki aje tunda baby khady zakisa mawa don ita kad’aice zan iya bari asamawa

 

 

 

 

Tashi tayi dakyar  ta tafi don adanawa tana cewa “yayana da alama idan na haihu zaka daina ji dani”… biyota yayi yana cewa “wane ni indaina ji dake princess ai bari ma in gwada maki yadda nakeji dake…daga haka suka ida shigewa dakin _(nace uhmm komi zasuyi da wannan tukeken cikin ???? dake gabanta_ )

 

 

 

 

Bayan sati d’aya da faruwar haka suna zaune yayin da khadijah tayi pillow da cinyarshi shikuma yana shafa kanta, saidai kuma da alamar damuwa a fuskarshi Wanda ko khadijah bata ankare ba saboda TV take kallo

 

 

 

 

Cikin muryar dake tabbatar da damuwarshi yace “khadijah.. Juyowa tayi da sauri takalleshi saboda yadda sautin muryarshi ya daki dodon kunnanta, sannan yaci gaba da cewa “naso ace kin yarda munje anduba abin da zaki haifa dukda ina tunanin lokaci baiyi ba gashi yanzu zamuyi babbar tafiya Wanda sai mun share 3 months bamu dawo…cikin murya mai kama da ta kuka ta katseshi tana cewa

 

 

 

 

“Rabin raina kana nufin wani wuri kuma zaku?share mata hawayen ya farayi don lokacin har sun fara zuba yace “pls khadijah nima abin yana damuna saboda nasan baninan zaki haihu harji nake kamar na aje aiki saboda ke saidai kuma me zan baki kici idan na’aje  aikina?

Shiyasa nake son kiyi hak’uri ai matar soja itama soja ce koh? Haka yak’arashe maganar cikin k’arfafa mata gwiwa

 

 

 

Da Haka dai ya samu ya lallasheta tare dayi mata alkwarin zai kaita wajen  Momy  ta zauna sannan idan ya dawo za’a basu Hutu sosai saboda aikin da zasuyi babba ne

 

 

 

Bayan kwana ukku da faruwar haka Jiddan da khadijah suka rabu da juna, shi yatafi aikin da aka tura su itakuma ta koma gidansu Jiddan

 

 

 

 

Wanda lokacin da zai tafi suma ne kawai khadijah batayi ba, kai kace idan ya tafi bazai dawo ba *_(nace wannan kuma Allah ne masani_*)

 

 

 

 

 

Sannu a hankali tunda Jiddan ya tafi saida suka kwashe wata d’aya basuyi wayaba duk khadijah tabi ta damu, a b’angaren cikinta kuwa Momy na kula da’ita yadda yadace inda ta  cigaba da zuwa awo, shima Abba yana  bakin nashi k’ok’arin ganin bata cikin damuwa

 

 

 

 

 

Kwance take tana kallon katon cikinta da yayi mata nauyi, wani bangare na zuciyar ta na tunanin mijinta..

 

 

 

Kamar daga sama taji wayarta na ringing, dauka tayi tare da zaro ido ganin Jiddan ne ke kiranta, ai kuwa da sauri ta dauka don taji muryar habibin nata

 

 

 

“Yayana!..” Na,am khadijahtu ta ya kike? Lapiya lau shine ka manta dani ko ka kirani”

 

 

 

 

“Haba princess ya za’ayi na manta dake damar wayarce babu don inda muke ba service don baki San yadda nake kewarki ba keda baby ta” Dan murmushi tayi Wanda sai da ya jiyo ta tace “muma muna kewar ka sosai saboda Kaine ginshikin rayuwar mu” jindadin kalamata yasa ya lumshe idanun shi kafin yace

 

 

 

 

“Allah khadijatu ina missing dinki sosai duk da allurar da akayi mamu but kullum cikin sha’awarki nake don har na fara tunanin yadda zan jure har 2 months nan gaba”

 

 

 

 

Saida tayi kamar zatayi kuka cikin shagwaba tace “nifa cikina yayi kato dayawa..” Khadijah kada ki rikitani mana kina irin wannan shagwabar kuma ai katon ciki bazai hana abani ba, ni ban San yadda zanyi ba ma don lokacin da zan dawo nasan kin haihu ga….dariyar da take ne ya katse mashi maganar dayake, da haka dai sukaci gaba da hirarsu ta ma,aurata  cike da sha’awar juna

 

 

 

 

*After 2 months*

 

Zaune yake cikin mota Wanda kiris yarage su shiga Kaduna saidai idanuwanshi a lumshe suke kamar maijin bacci Wanda fuskarshi kad’ai zaka kalla kasan yana cikin farincikin dukda ramar da Yayi

 

 

 

 

Saboda damuwar dayake ciki narashin haihuwar khadijah gashi harta  wuce edd d’inta da kusan 3 weeks, wannan shine abinda ya haddasa damuwar captain J wanda yasashi rama

 

 

 

Tun kafin ya shiga cikin gidan hancinshi ya fara jiyo mashi k’amshin matarshi, lokacin da yayi arba da’ita kuwa ba’a magana saboda yadda farin ciki da tausayi yakamashi don duk yadda yake tunanin girman cikin ya wuce tunaninshi

 

 

 

Ko kunyar idonsu Momy baiji ba ya kama hannunta ya rik’e  yaki saki tunda ita ko tashi wuya yake mata don ma Momy nasata tana Dan takawa kullum da safe tana zagaya harabar gidan haka yak’arashi rashin ta ido yawuce d’aki domin yasakarma kanshi ruwa

 

 

 

Dare kuwa nayi ko kunya baiji ba yace ma Momy d’akinshi zata kwana, ba yadda ta iya dashi dole ta kyaleshi tare dayi mashi gargadin kada ya takurama

khadijar

 

 

 

K’iri-k’iri yau gashi ga khadijah kwance amma ya kasa biyan bukatarshi saboda wani irin tausayinta da yakeji, a hankali ya matsa kusa da’ita yashiga kissing d’inta duk Inda ya samu don wani irin kewarta yakeji, itama bata hanashi ba don tasan yadda yake buk’atarta,haka ya cigaba da wasanninshi da’ita har saida yaji yasamu natsuwa

 

 

 

 

A hankali takejin bayanta na ciwo har ya fara tsanani sai lokacin Jiddan ya lura da yadda take ya mutsa fuska

 

 

 

 

K’ok’arin tadata yayi, sannan ya saka rigarshi yana tambayar ta amma ta kasa bashi amsa, ganin ciwon nata kamar nakuda ce yasa ya kira Momy suka wuce asibiti bayan Sun d’auki katin da take awo dasauran kayan data had’a cikin wata k’aramar trolly na haihuwa

 

 

 

Bada b’ata lokaci ba aka wuce da’ita Labour room, bayan kamar 2 hours khadijah ta d’auka bata haihu ba haka yasa Jiddan ya kasa daurewa dole sai da aka barshi ya shiga Inda take kasancewar ita kad’ai ce cikin Labour room, rik’e hannunta yayi yana karanto mata addu’oi saidai ita bata masan yanayi ba don gaba d’aya tafita hayyacinta

 

 

 

 

Wani irin ciwo da azaba takeji nan take tafara nishi sai ga ga jariri ya fad’o yana ta tsala kuka itakuwa bata ma San inda kanta yake ba hakashima Jiddan baibi takan D’an ba gani khadijah na wani irin numfashi

 

 

 

 

Sai lokacin  likitan daya amshi haihuwar yagane yayan biyu ne ganin tana wata nakudar tadaban don koda akayi mata scanning Allah yaboye baiwarshi d’aya kawai suka gani basu ga d’ayanba

 

 

 

 

Da kyar ta bude bakinta tace “yayana ka yafe..Mani ..bazan iya ba I’m sorry…”plz khadijah kada kice haka zakiyi Mani kidaure zaki iya..”, wata dubarace tazo mashi sai ya saka mata yatsanshi guda cikin bakinta

 

 

 

 

Jitayi an saka mata wani Abu abaki hakan yasa tayi wani irin yunk’uri sai dai kuma kash jira take taga ta inda mala’ika zai bullo mata

 

Batayi aune taga wani irin duhu mai kama da inuwa yana lullube d’akin iyayin da bakinta keson karanta Kalmar shahada saidai data kama sai ta kasa idawa sakamako rashin sanin Inda kanta yake…

 

 

 

 

 

 

 

    _*Mrs Abdul Sule*_

[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: ????????????????????????

 *HABIBI DA’IMAN*

????????????????????????

 

 

 

*WRITTEN BY*

    *HALIMA MK*

 

 

DEDICATED TO SA’ADATU ALIYU KABUGA

 

 

*???? KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

 

 

_Ina matuk’ar ganin k’ok’arinki Zainab Yusif Kaita_  _(Zee kaita_)  _wurin ganin kin yad’a online Novel don haka wannan page d’in sadaukarwa ne gareki  kiyi yadda kikeso dashi halak malak Mk ta mallaka makishi_

 

 

 

 

*page 205-210*

 

 

Koda Jiddan yasa mata hannu cikin baki sai yaga ta yunkura kamar zatayi amai Wanda yayi sanadin fad’uwar d’ayan jaririn dama haka yake so saidai  kuma wani sabon tashin hankalin daya shiga wanda bai wuce naganin khadijah bata numfashi ba, da sauri ya fara jijigata yana kiran sunanta amma ina…

 

 

 

Kasancewar likitocin sun gane suma tayi yasa sukace ma jiddan yafita, amma fir yak’i fita saima birkice masu da yak’arayi duk yabi ya rud’asu don dole suka rabu dashi ganin in suka takura yafita kamar zai iya shiga wata matsalar yasa suka hak’ura suka gyaleshi

 

 

 

 

Saida sukayi nasarar farfad’owar ta sannan suka dank’ara mata allurar tsaida jini, shikuwa gogan naku sai lokacin ya samu natsuwa sannan yabi takan yaran da aka gama gyarawa aka mik’a su wajen Momy da Abba

 

 

 

Kallon yaran yake cike da so da kauna duk da yaci burin samun mace saboda har addu’a yake kan Allah yasa khadijah ta haifi mace amma Allah bainufaba, amma dukda ba macen bace bai hanashi jin kaunar yaran ba cikin zuciyarshi Wanda yakasa misalta son dayake masu da komi cikin zuciya da jinin jikinshi

 

 

 

Ganin khadijah na bacci yasa Momy ta mik’o mashi dabino, dama Wanda aka fara  haihuwa ne hannunshi tace “maza tauna kasa masu” ba musu ya amsa yasa musu tare dayin addu’a

 

 

 

Haka suka kasance cikin farin ciki Jiddan kuwa kasa bacci yayi daga ya lek’a yaran sai ya kalli khadijah sai ya koma yaci gaba da nafila yana godema Allah da irin wannan ni’ima dayayi masu, kafin safiya kuwa kowa yasan khadijah ta haihu sai farin ciki Ihsan keyi don tana mutuwar son yara

 

 

  A hankali ta bud’e idanuwanta bata sauke su kan kowa ba sai mijin nata da iyayen shi, bud’e baki tayi da niyyar tayi magana saidai Jiddan ya Rigata yana tambayarta ya takejin jikin, ita dai momyy tea ta shiga had’a ma khadijar, saida tasha tace ta koshi sannan aka mik’a mata yaran Jiddan na rik’e da d’aya don wata irin yunwa sukeji sai tsotsar hannu suke

 

 

 

Lokacin da ta rungume su ji tayi duk duniya ba abinda take k’auna sama da abinda ta haifa koda kuwa kowa zai k’isu, ba musu ta shiga shayar dasu dukda d’aurewa kawai take saboda akwai zafi idan suna tsotsa duk Jiddan na lura da’ita

 

 

 

 

Gaba d’aya khadijah d’akin Momy ta tare tana jego shikuwa jiddan kin komawa Abujah yayi tunda sun samu hutu gashi Momy ta kasa ta tsare kullum Sai dare yayi yake samun ganin matar tashi da babys gashi kullum idan ya tambayi khadijah koda sunan da takeso asa Sai tace duk Wanda yasa yayi dama tun tana da ciki yake tambayarta

 

 

 

Haka akaci gaba da zaman barka ranar suna na zagayowa yara sukaci sunan sulaiman da Jamilu Wanda hakan yayi mukar faranta ran khadijah kuma ba k’aramin mamaki tayi ba dama abinda yahanta fada don kada jiddan yaji kishi Sai gashi yasa da kanshi

 

 

 

 

Kwanan khadijah 27 da haihuwa jininta ya d’auke Wanda Juddan ya lura da haka don ya shigo nemanta ya ganta tana sallah lokacin cwt S ke kuka dayake haka suke kiransu cwt S da cwt J

 

 

 

 

Kamar kullum yau ma da dare ya shigo d’akin da take tare da kwantar da cwt J da yayi bacci sannan ya koma kusa da khadijah ya zauna tare da rik’e hanunta kafin yace

 “Andeejana yaushe zamu koma gida? D’ago manyan idanunta tayi ta zuba mashi su na D’an wani lokaci tana karantarshi, shima ita yake kallo kafin tace “amma kasan sai nayi arba’in koh?..”toh ai naga kina sallah yaufa”…”duk da haka kasan Momy

bazata bari ba

 

 

 

D/an yamutsa fuska yayi alamar ana ta kura mashi kafin yace “toh naji amma don Allah yau..sai kuma yayi shiru, kallonshi take alamar tanajinshi

 

 

 

Tashi yayi tsaye tare da janyo hannunta itama ta mik’e tsaye, k’ok’arin janta yake taja ta tsaya hakan yasashi juyawa yana kallonta, Dan dakewa tayi tace “ina zamuje ne? Don ita ta harbo jirginshi tun lokacin daya shigo tanazarceshi

 

 

 

K’ara had’e rai yayi yace “toh kina tunanin zan saida ki ne? Daga haka ya kara Jan hannunta sai takara turjewa tana turo baki

 

 

 

Juyowa yayi a D’an fusace sai kuma ya kwantar da murya cikin lallashi yace ” Haba khadijah d’akina fa zamu kisan me nakeso Haba..”toh ba Kaine kemin fad’a ba”

 

 

 

“Toh shikenan na daina yi hak’uri kizo muje kinji” zare hannunta tayi daga nashi ta fara cewa “gaskiya yayana Kayi hak’uri kofa arba’in banyi ba sannan idan Momy tagani fad’a zatayi taga kamar nice na biye ma… Cikin fad’a ya katseta don wannan karon khadijah takaishi k’arshe bayajin zai iya danne fushin shi

 

 

 

 

“toh shikenan khadijah kada ki biye Mani Nida nake mijinki kinsan dai yadda laluri na yake yau kusan 4 months rabona dake amma ke baki damuba baki tausayina kamar yadda nake maki baki son abinda nakeso kamar yadda nake son naki koda kuwa zan cutu amma bari kiji in gaya maki baki isa kisani aikata zina ba idan hakuri na ya k’are zan karo aure don biyan buk’ata ta”

 

 

 

Daga haka ya fice daga d’akin cikin tsananin bakin ciki da abunda tayi mashi don bata San yadda yake bacci ba kullum shiyasa tayi mashi haka

 

 

 

 

Tsaye tayi inda ya barta tana kuka babban tashin hakalinta bai wuce yada yayi fushi da’ita ba don bai taba yi mata haka ba har yana ikirarin k’ara aure Wanda bata jin zata iya sharing d’inshi da wata don haka da sauri tabi bayansa

 

 

 

Yana zuwa d’akinshi yayi ma k’ofar key sannan ya duke yanajin dacin yadda khadijah tasa yayi mata fad’a yau dole ya nemi mafi… Tunaninshi ne ya katse jin tana buga k’ofar tana kuka tare da kiran sunanshi, tabbas bai iya yi mata dogon fushi da jure jin kukanta don yasan bata saba ba shiyasa take kuka sosai

 

 

 

Bud’e mata k’ofar yayi bata jira komai ba ta rungumeshi tana kuka duk sai yaji ya daina jin haushinta tausayinta ya kamashi itakuwa bottoms d’in rigar shi ta shiga cirewa tana shafa mashi lallausan gashi dake kwance saman kirjinshi har a lokacin bata daina kukan datake ba, d’aukarta kawai yayi ya D’ora saman gado yana cewa “pls daina kuka banso kinji” shiru tayi tare da had’e bakinsu tana kissing d’inshi tuni jiddan ya manta inda yake, nan take ta fara aika mashi da abubuwan da tasan yafiso daga gareta, shikuwa har wasu hawaye yake fiddawa yana mata surutai itama tana biye mashi, daga haka Na jawo masu k’ofar Na tafi gudun kar inzama mai ganin kwammm

 

 

 

 

Bayan kamar 30 minutes jiddan ya D’an samu natsuwa sai kallonta kawai yake, a hankali tace “yayana yaranmu fa su kad’ai ne Kayi hak’uri da wannan kaji Na koma wajensu”, d’aga mata kai yayi cike da gamsuwa yace “ba komai tashi  kije amma pls kullum ki dinga bani 30 minutes kinji d’aga mashi kai tayi alamar ta yarda sannan ta kama hanya

 

 

 

Hartaje bakin k’ofa sai kuma tajoyo tare da cewa “da gaske aure zaka k’ara? Tasowa yayi ya rugumeta don har kwalla ta cika mata ido yace” sorry fushi ne kawai kinsan ke kad’ai zan aura DA’IMAN don haka kada ki damu daga haka yasamu tayi shiru sannan ta koma wajen yaran

 

 

 

Hamdala tayi ganin Momy har lokacin tana wajen Abba, toilet ta shiga tayi wanka saida ta fito sannan Momy ta shigo don tayi mata saida safe sannan ta jaddada mata ta daina tafiya toilet tana barinsu su kadai a d’aki ta dunga kiran Afrah ta zauna da su

 

 

 

Tunda ga ranar kullum khadijah sai taba mijinta 30 minutes Wanda har yanzu Momy bata Sani ba gashi tana faman gyara ta amma Jiddan na mirjewa kullum ba Wanda yasani

 

 

 

Saida ana saura 3 days su koma sannan Momy ta lura da hakan shiyasa tasa Jiddan ya tattara ya koma Abuja acewar ta yaje yasa a gyara gidan kafin zuwan khadijah shikuwa ganin ta gane gashi saura 3 days yasa ya tafi don kada ya bata mata rai

 

 

 

Haka khadijah tasha gyara har ta gaji bayan 3 days ta koma tare da wata dattijuwa da zata tayata raino mausuna baba Ayyo

 

 

 

Bayan komawar khadijah rayuwa ta kasance mai dad’i da farinciki a garesu Wanda suka shiga nuna ma juna sabuwar soyayyah kamar basu taba shiga wani tashin hankali ba _rayuwa kenan_

 

 

 

 

*AFTER 5 YEARS*

        ????????????

 

Abubuwa da yawa sun faru acikin wannan lokacin ciki kuwa harda K’arin auran Usman mijin Ashanty Wanda iyayenshi ne suka bashi wata yar uwarshi mai suna Nafisa tunda ita Ashanty bata haihuwa sanadiyar magungunan hana d’aukar haihuwa da tasha a baya, Alhamdulillah suna zaman lafiya don nafisar ta haihu kuma suna zaman lafiya dukda tasan baxata tab’a kama k’afar Ashanty ba a zuciyar Usman

 

 

 

A b’angaren Seema ta haihu har sau biyu Rayyan sai Ridwan, Samra twince ta haifa itama Dinah da Daleelah, Islam d’anta d’aya tahir

 

 

 

Al amarin Ihsan da Rafeeq kuwa har yanzu Allah bai basu ba dukda suje Asibiti an tabbatar da lafiyar su kuma ko yaushe zasu iya samun haihuwa sai dai hakan bai daina sa Ihsan damuwa ba don ma Rafeeq bai barinta don shi mutum ne mai raha bakoda yashe ake ganin damuwarshi ba

 

 

 

 

 

     *_Mrs Abdul Sule_*

[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: ????????????????????????

 *HABIBI DA’IMAN*

????????????????????????

 

 

 

 

 *WRITTEN BY*

      *HALIMA MK*

 

 

 

 

 

DEDICATED TO SA’DATU ALIYU KABUGA

 

 

 

 

*???? KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

 

 

 

 

*page 210-215*

 

 

 

Bazata wuce shekaru 33 ba amma kai kace yar 25-26 ce, zaune take tana shayar da wani yaro da bazai wuce shekara 1 ba aduniya

 

 

Jitayi an rugumo ta ta baya hakan yasa ta juya tana kallonshi, shima ita yake kallo da murmushi saman fuskarshi, d’an zumbura baki tayi tace “kai yayana cwt J fa na kallon mu” d’aga kanshi yayi ya kalli yaron da gaba d’aya hankalinshi ba Kansu yake ba saboda cartoon d’in da yake kallo

 

 

 

Sakinta yayi yakoma gefanta ya zauna tare da amsar zaid da ke hannunta Wanda tuni yayi bacci sannan yace “wai bazaku tashi Ku shirya ba lokaci na tafiya fa…” Nifa nan yayana shirye nake shi waccan da kake gani tun d’azu nasa mashi kaya amma yaki sa takalmin shi ko irin murnar yawon da yara keyi baiyi wani irin murdadden haline da shi

 

 

Dariya jiddan yayi da har sai da zaid ya motsa sannan yace “gaskiya ki daina  yi ma takwarana haka da cwt S ne baki cewa komai don yanzu ma nasan shi kike jira amma,…jiyayi an rufe mashi ido daga baya hakan yasashi yin shiru yana murmushi don yasan kowaye kafin yace “lalle my boy ya tashi lafiya tunda..sakin idon nashi yayi yace ” daddy, Momy good morning” murmushi khadijah tayi tace gud morning my son ya naga baka shirya ba ina Aunty taka?…uhm mun shirya fa nine kwai bansa kaya ba shine tace nazo naga kayan da J zaisa asamani irinsu “wanan karon jiddan ne yayi magana yace

 

 

“Toh ka gansu koh toh je kasanya kace mata kuyi Sauri Ku muke jira kaji my son d’aga kanshi yayi alamar toh sannan ya kama hanya, har ya isa bakin k’ofa kuma sai ya juyo ya kalli D’an uwanshi yace ” J ko magana bakayi Mani ba fa” ko kallon inda cwtS yake baiyi ba kamar badashi ake magana ba sanin halinshi ne yasa S tafiya batare da ya k’ara cewa komai ba

 

 

 

Tashi khadijah tayi cikin fushi taje ta kashe TV d’in sannan tace “kanajin D’an uwanka na maka magana amma koh tanka shi bakayi ba toh tashi ka wuce kasa takalmin ka mu tafi, zuburo baki yayi tayi saurin cewa Allah zan mangareka in baka tashi ba hakan yasa cwt J tashi ya nufi d’akinsu shikuwa jiddan kallonta kawai yake yadda ta dage tana masifa kafin yace

 

 

 

“Allah khadijah ki daina yi ma yaron nan masifa yanzu da D’an uwan nashi na nan da sun had’e maki kai” batace komai ba sai tab’e baki da tayi ta nufi hanyar d’akinta don ta ida shiryawa don tasan halin ya’yan nata ga kama da suke sosai sai dai shi S hakuri gareshi shiyasa Ihsan ke sonshi gabad’aya ma gidanta yake kwana

 

 

 

Akasin cwt J da sai yaga dama zai maka magana haka idan bai sanka ba toh ko zaka mutu bazai maka magana ba

 

 

 

Zaune take  a d’akin cwt S tunda ya tafi take nan wurin gabad’aya ta lula duniyar tunani

 

 

 

Rungume hannuwanshi suke a kirji yana kallonta don bata san dawanzuwarshi a wurin ba yana kallonta, a hankali ya taka har zuwa inda take bai jira komai ba ya rungume ta hakan yasa ta dawo cikin hakalinta

 

 

 

Ajiyar zuciya ta sauke yace “haba pretty meyasa haka ni nagama kwanan kinyi kiba kodai nayi ajiya anan ne?tare da shafo cikinta, ita kuwa murmushi tayi don tasan tsokanar ta yake don bata wuce 3 days da gama al’adarta ba

 

 

 

Maganar shice ta katse mata tunani yace “yadai ko babyn ne? D’an yamutsa fuska tayi tace “uhm my Rafeeq zuciyana ke tashi apple nake son ci” ai da sauri ya tashi yana cewa bari na kawo maki kinji karki wahala, ita kuwa dariya ta hauyi don haka sukeyi pretending kamar tana da ciki shi kuma yayi ta lallaba ta kamar da gaske

 

 

 

 

Tana nan sai ga cwt S ya dawo b’ata lokaci suka shirya sai Kaduna domin gudanar da shagalin bikin Aslam da za’a fara gobe

     

            *****

 

 

Zaune take ayayin da kwallah suka cika idonta babu Wanda take tunawa sai Laila, jitayi an dafata suna had’a ido ta fashe da kuka yace “don Allah Aisha ki daina kuka ko wani abun akayi maki? Girgiza kanta tayi tace a’a yace “toh ya akayi?..”kada kayi tunanin ina kukane saboda rashin haihuwa hasalima godiya nake ma Allah da ya mallaka Mani miji irinka saidai duk sadda zan tuna rayuwa ta ta baya dole nayi kuka musanman Laila da shekararta 5 cikin kasa jiddan d’in da ta mutu kanshi yananan ya zama wani Abu yak’ara samun girma da kud’i da Y’aya  ba kamar yadda ta Sani ba”

 

 

 

 

“Addua ya kamata ki dinga yi mata kinji? Don ba,a fidda ran rahama ga musulmi” daga kanta tayi sannan suka ci gaba da hirar su ta masoya

 

 

 

 

Kwanaki 3 suka share a kd ana shagalin biki sannan suka dawo gida Wanda duk wannan hidimar da ake Ihsan bata lafiya saboda malaria da ta kamata saidai tanajin sauki saboda magani da take sha

 

 

 

 

Bayan dawowarsu ne Rafeeq ya matsa  mata dole suje sukaje asibiti ganin zazzab’in da yatafi sai yadawo don shi bai yadda ba ace mutum baya lafiya amma kullum sai k’ara hawa take kamar ansama pulawa yis  don har wani Dan tumbi ta aje

 

 

 

 

Zaune suke a gaban likitan suna jiran jin abinda zaice, batare da wani shakku ba ya d’ago yana kallon Rafeeq kafin yace “ya akai kasan tanada ciki ka bari ciwo ya kamata kuma bakuzo asibiti da wuri ba”

 

 

 

Da mamaki Rafeeq da Ihsan suke kallonshi,

“Ciki kuma! Shine abinda Rafeeq ya maimaita kafin likitan ya tabbatar mashi da ciki kuwa har na 4 months, shidai Rafeeq bai daina mamaki ba kafin yace “but doctor duka batafi 1 week da gama mesturation d’inta ba and than babu wata alama ko laulayi daya nuna mana hakan

 

 

 

Murmushi likitan yayi sannan ya d’ora da cewa “tabbas akwai mata irin wadanan saidai basu da yawa wata kila idan cikin yakai wata shidda ta bari sannan ya kalli Ihsan yace madam ina fata baki matse cikin dai ko?

 

 

D’aga mashi kai kawai ta iya don tanajin abin kamar a mafarki,  da haka likitan ya sallamesu tare da rubuta masu magani sannan ya shawarce su da su rink’a zuwa asibiti akai akai

 

 

 

Haka suka koma gida cikin farinciki da godiya ga Allah sannan suka hau sheda ma mutane Wanda kowa saida yayi mamaki

 

 

Haka ihsan taci gaba da rainon cikinta har ya kai wata Tara lokacin nan cwt S sai murna yake Auntyn shi zata Haifa mashi baby mai kyau don har zama yake ya danna mata kafarta idan tayi kumburi, haka zalika ko laulayi batayi sadai kumburin kafa shima sai da cikin ya tsufa

 

 

Tsaye take a kicin tana motsa girki Rafeeq na gefanta yana mata magiyar ta tafi ta zauna shiyayi don bai son abinda zai wahalar da’ita, haka itama ta dage akan exercise ne takeyi

 

 

 

Ji tayi wani irin fitsari ya matseta hakan yasa ta sakar mashi girkin sannan ta  nufi toilet

 

 

 

Saidai tana tsugunawa taga tayi jage jage ga kan jariri har ya leko

 

Ihu ta saka saboda tsabar firgita da tayi ai da sauri Rafeeq ya shigo toilet d’in bayan yakashe gas d’in

 

 

 

Ganin yanayin da take ciki yasa ya d’auketa sai asibiti tare da cwt S da sai kuka yake ganin Auntyn shi za’a kai bata lafiya

 

 

 

Suna isa aka karb’eta don har kan da yafito sai lokacin Rafeeq ya kira jiddan ya sanar dasu sannan yace suje d’akin Ihsan su taho da kayan haihuwa

 

 

Haka kuwa akayi ko 10 minutes basu k’ara ba suka iso Wanda yayi dai-dai da haihuwar Ihsan Wanda saida aka fara mik’o masu jaririyar sannan suka shiga ganin Ihsan d’in

 

 

 

 

Shidai jiddan kallon jaririyar yake kawai ga wani irin kyau tun kafin kammaninta su fito baka iya tantance dawa take kama amma masu karatu kuyi imagining kyan d’iyar Rafeeq da Ihsan don gaba d’aya baka iya gane daga wane b’angare tafi kama balarabiya ko bafullatana

 

 

 

 Ihsan bata sha wuya wajen haihuwa ba haka kuma bata koma gida wanka ba har ranar suna tazo d’iya taci sunan…

 

 

 

 

 

 

 

      *_Mrs Abdul Sule_*

[1/17, 10:49 AM] Halima Mk: ????????????????????????

 *HABIBI DA’IMAN*

 

 

 

 

*WRITTEN BY*

   *HALIMA MK*

 

 

 

DEDICATED TO SA’DATU ALIYU KABUGA

 

 

 

*???? KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

 

 

 

 

 

 

???? ???? ???? ???? ???? ???? ????

 

 

 

 

 

Ba k’aramar bajinta da kuma surprise d’in jiddan Rafeeq yayi ba domin kuwa d’iya taci sunan khadijah za’a dunga kiranta da kadra

 

 

 

 

Ba k’aramin farinciki sukayi ba mussaman jiddan shidai yana so ace cikin yayansu ansamu khadijah shikuwa cwt S har rigima yake sai an Goya mashi ita banda uban tafiyar da baya shiga harkar kowa kamar ba yaro ba don idan cwt J nayin wani abun har tsoro yake ba khadijah gashi da k’ok’ari a makaranta don har yafi S

 

           ****

 

 

Bayan shekara ukku da faruwar haka Ihsan bata k’ara haihuwa ba khadijah kuwa ta haifi Khalid Wanda take goyo yanzu

 

 

 

Rayuwa ta zama mai sauk’i a garesu don kuwa yanzu ba yan kananan kud’i su  jiddan keda suba shiyasa suke jin dad’insu

 

 

 

Sulaiman ne yayi sallama hannunshi rik’e dana kadra an sanya mata kaya pink sai wata white d’in Teddy da ke hannunta da ta cire hular kanta tasa ma Teddy d’in ita kuma tabar gashin sai rito yake tsakiyar bayanta

 

 

 

Tana shiga ta haye saman cinyar jiddan tana dariya yace “ah babyn daddy ya akayi ne? Cikin maganar ta da bata kware ba tace” Mami ce chace mujo muyi waca da chiwit ce jatayi bacci” dariya jiddan yayi kafin yayi magana yaji cwt J yace “Allah daddy yarinyar nan na b’ata Mani rai tayi ta bata Mani suna” daga haka ya wuce d’akinsu shi har yayi #zuciya, ita kuwa sakin baki khadijah tayi ta bishi da kallo aranta tana cewa wannan wane irin yarone ni dije

 

 

 

Tunaninta ne ya katse jin cwt S na cewa “my kadra kinga ran J ya baci zo muje ki bashi hak’uri kinji” harararshi khadijah tayi tace “toh bata zuwa ai banga abinda akayi mashi ba”

 

 

 

Diddira k’afa yafarayi yana cewa “pls Momy ki bari mana kinga yanzu yana iya kuka fa…bud’a baki tayi daniyar yin magana jiddan yai saurin cewa toh kutafi Allah yayi maku Albarka

 

 

 

 

Jan hannun kadra sulaiman yayi suka nufi wurin J, aikuwa suna zuwa suka tarar da shi sai fushi yake shi kadai

 

 

 

Dafashi S yayi yace “haba bro kayi hakuri meye nafushi bayan kasan ba laifinta bane bata iya fad’i bane ba”, koda kadra taga haka itama sai ta dafashi tace” blo kayi hakuli kaji” abinma dariya yaso yaba cwt J hakan yasa ya saki ranshi yana dariya yana cewa “wai ita yarinyar nan duk abinda taga kayi shi take kwakwayo fa” daga haka yabar fushi kafin su jawo game d’insu su fara bugawa

 

 

 

 

Bayan shigewar su S d’aki Jiddan ya jawota a jikinshi yana cewa “habibty ki daina damuwa da halin yaran can haka Allah ya halicce su idan kika tukura masu kina iya ganin su samu wata matsala baki ganin ko ciwo d’aya yayi sai guda yayi haka kuma basu San bacin ran junansu”

 

 

 

D’aga kanta tayi alamar ta gamsu kafin ya manna mata kiss a wuya yana cewa “khadijah bazan daina gaya maki ina sonki ba kin isheni rayuwa, ni don Allah nake sonki inso mu kasance tare har abadan”..

 

“Nima HABIBI… Huhhh DA’IMAN ina sonka ina tare da kai bazan… Game bakinsu da jiddan yayi shiya hanata idawa itama sai ta shiga yi mashi martani

 

Saida suka gaji don Kansu sannan suka bari saidai basu daina kallon juna ba Wanda hakan yazama sabo a garesu domin aikawa junan su sak’onin da kalaman bakinsu suka kasa furtawa

 

 

 

Kukan da Khalid ya farayi ne Wanda har yake neman tashin zaid dake bacci shine yasa suka dawo daga duniyar da suka tafi

 

 

 

Tashi jiddan yayi ya d’aukoshi suka shiga yi mashi wasa tare yana dariya……………

 

 

 

Alhamdulillah anan na kawo karshen wanan litafin nawa mai suna HABIBI DA’IMAN inda nayi kuskure Allah ya gafarta Mani yasa mu karu da abin dake ciki

     

       ****************

 

*_Mu kasance masu yarda da kaddara a duk lokacin da tazo mana, basai kayi ma Allah laifi ba zai jarabe kaba don ya gwada imaninka sai yayi ta kaddaro maka abubuwa cikin rayuwarka  kuma ba don baya sonka ba yayi hakan ba_*

 

 

*_hak’uri a duk halin da ka tsinci kanka yana kaika ga babban rabo, don haka ka godema Allah a duk halin da kake ciki domin kafi wani, wani kuma yafika_*

 

 

 

*_d’aukar mummunar dabi’a akan rashin hak’uri cikin halin da ka tsinci kanka na jawo maka masifa a cikin rayuwa kamar yadda Jiddan ya d’auki d’abi’ar shan giya amma sai laila ta hanashi zaman lafiya_*

 

 

*_Duk girman laifinka idan ka tuba Allah na yafe maka sannan ya baka abinda bakayi tunanin samunshi ba idan yaso kuma ya jarebeka_* *(Ashanty*)

 

 

 

 

*_Ko kun San soyayyar gaskiya bata tsufa kamar yadda mutane ke ganin a kwai lokacin da soyyayya ke k’arewa, masoyin gaskiya yana sonka a duk yadda kake ba kuma zai taba gudunka ba saboda tausayi shine ginshin alakarku_*

 

 

 

*_Madallah da iyayen da basu sa ma rayuwar gidan auran yayan su ido, suna d’aukar kaddara a duk yadda tazo masu_*

 

 

 

*_D’a namiji baya kad’an musamman idan ya nuna yanason auren saboda rashin yin hakan na iya jawo b’anna da dama kamar haka:- rashin natsuwar matashi a koda yaushe don haka bazai maida hankali akan harkokinsa ba, shaye-shaye, zina da dangoginta, d’aukar munanar dabi’a saboda yana ganin an tauyeshi da sauransu_*

 

 

 

 

*_Wata soyayyar idan ka rabata bakasan mazai faru ba gara a dunga sanin abinda ya dace ayi_*

 

 

*_Babban kuskurene kice zaki bar gidan iyayenki saboda auren dole, haka kuma yana da had’ari, ka uzura ma d’anka sai ya auri Wanda baiso hakan na iya jawo matsaloli da Dama, wata rana zaka ciza  lebe tabbas idan ka kori yarka daga gida saboda tayi maka wani laifi_*

 

 

 

*_Mu kula, mu lura, mu gane rayuwar yar kad’ance idan kayi hak’uri wata rana sai labari babu abinda yafi dad’i ga ‘ya mace in banda ta samu miji na gari_*

 

 

 

 

      _It’s lucky to marry ur first love_

 

 

 

*_Bazan mance namijin k’ok’arinku gareni ba_*

*Halimatu Kangiwa (Aunty haliloss)*

*Aisha Ali Garkuwa*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

             

 

 

 

            *_Mrs Abdul Sule_*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button