Uncategorized

HAJNA 1

 ♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️


Mallakin:- Queen Nasmerh ; Marubuciyar & Rabiatul Adawiyya; Marubuciyar 


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*Bsmillahir Rahmanir Raheem*

PAGE 1-2

*******

Shigowa ta Ajiyawa kenan, wata unguwa ce da ke garin shinkafi, kallon unguwar nayi da kyau, da alama ba masu kuɗi a unguwar duk talakawa ne sai ɗai-ɗaiku zaka gani da rufin asirin Allah, wani gida na gani, ginin gidan ya tsufa, ko fenti babu, shiga nayi inda naga wata doguwar hanya da zata sada ni da cikin gidan, ko ina na gidan an share shi, kuma komai na aje inda ya dace, duk da talakawa ne hakan be hana su gyara gidan su ba. 

   Wani tsoho nagani sanye da jallabiya fara ta koɗe sosai, zaune yake akan wata tabarma, daga gefe kuma wata tsohuwa ce zaune sanye da zani daban, riga daban, “Hajna! “Umma ta faɗa,  tana kiran Hajna dake cikin wani ɗaki, wanda ni banyi tunanin mutum zai iya zama gurin ba, rufin ɗakin ma na kara ne, sannan da alama ko ruwan sama aka yi ruwa zasu iya kaiwa gurin.

   Zuwa tayi ta durƙusa gaban su,“ ina wuni Baffa ” ta faɗa tana gaida tsohon da ke zaune, ɗagowa yayi yace “lafiya ƙalau”, Umma tace “dama Baffan ki ne ke tambayar me ya hanaki zuwa makaranta “, sosa kanta ta shiga yi kamar wata mara gaskiya, duniya ta tsani zuwa islamiya, wata ƙarya ta faɗo mata, “ummm Baffa dama malamin mu ne……” bata samu damar ƙarasawa saboda Baffa ya dakatar da ita “Hajna kiji tsoron Allah, yanzu na haɗu da malamin ku yace min lafiyar shi ƙalau, yau kwananki huɗu baki je makaranta ba, kullum sai kice Malamin ku bashi da lafiya”, shuru tayi dan yanzu bata da ta cewa, Umma tace “kayi haƙuri wataƙila ko bata son zuwa ne”, Baffa da mamaki ya gama cika shi yace “ke fa na lura baki damu da tarbiyar yarinyar nan ba “, Umma tace “Allah ya baka haƙuri” tashi tayi ta shige ɗayan ɗakin.


   Faɗa yayi wa Hajna sosai dan Baffa mutum ne da yake da tsaurarren ra’ayi, bayan ya gama mata faɗa ne, ta tashi ta ɗauki bokiti ta fita zuwa ɗibar ruwa.


   A ɗayan ɓangaren kuwa wani gidan ne kusa da gidan su Hajna, wata yarinya ce kwance akan wata katifa ƴar ƙarama, waya take yi “yau ina zamu haɗu, wallahi ina mugun kewar ka” ta faɗa tana ƙara gyara kwanciyar ta, daga ɗayan ɓangaren aka ce “ wallahi nima baby nayi missing ɗin lallausar fatar ki “, “ta yayi amma sai ka biya”, yarinyar ta faɗa, kallo na ƙare mata, fara ce amma da alama farin bana Allah bane, ina ganin ta haɗa dana bleaching,  “kut, dubu ɗari?, wallahi sunyi kaɗan ” ta faɗa, “haba Fahna ki tausaya min kina gani fa wata ya kora ba’a biya mu albashi ba”, shiru tayi kamar bata jin shi, “kinji baby “, nan ma shiru bata amsa ba, “ Baby Fahna, na ƙara, zan baki dubu ɗari uku, amma zaki kwana fa”, juya ido tayi kamar yana ganin ta tace “ a’a dubu ɗari huɗu, idan ba haka ba malam sai anjima “, “ a’a baby na yadda” murmushi ta saki tace “to shikenan mu haɗu a  maryam hotel ” kashe wayar tayi.

 

     Ɗakin inna ta shiga zaune take tayi tagumi, zuwa tayi ta zauna tace “inna Alhaji Musa yana so mu haɗu yau, kuma wai kwana zan mishi” kallon ta inna tayi a gwatsine tace “ a nawa? ” “dubu ɗari huɗu” Fahna ta faɗa, jin an faɗi dubu ɗari huɗu inna ta washe baki tace “to shikenan, kije zan san yadda zanyi da baban ki “, tashi tayi ta shirya cikin wata atamfa mai kyau wanda Alhaji Musa ya ɗinka mata, gyalen ta ta saka cikin jaka, sannan ta rataya, sannan ta kawo hijabi dogo ta saka, fitar ta waje kenan ta haɗu da Hajna ta ɗauko bokiti da ruwa a cikin, alama ya nuna daga gurin ɗibar ruwa take, “ke kalar manya “Fahna ta faɗa, Hajna tace “ƴan matan duniya sai ina?” Fahna tace “gurin samo naira “, Hajna tace “Allah ya shirya min ke”, “yo ke Hajna ina zan yadda talauci ya kashe ni, wannan kasadar sai ku ai “, murmushi Hajna tayi tace“a dawo lafiya” , shigewa tayi cikin gida tana mamakin irin wannan rayuwar ta Fahna.


     Tashar mota Fahna ta shiga zuwa Maryam Hotel dake gusau, kiran Alhaji Musa tayi, ya faɗa mata ɗakin da ya kama, guri ta samu ta cire hijabin ta sannan ta yafa gyale, ɗakin shi ta wuce kai tsaye, Kwance yake daga shi sai gajeren wando, tun daga ƙofar ɗaki Fahna ta fara rage kayan jikin ta, dan Fahna in dai karuwanci ne ta shahara, wani girgiza jikin ta take yi tana ƙarawa, na take Alhaji yaji desire shi ta tashi, jawo ta yayi ta faɗa jikin sa, ƙoƙarin raba ta da rigar nonon ta yake yi, yana wani lumshe ido, saurin barin ɗakin nayi.


   Ɓangaren Hajna kuwa kwance take akan katifa tana tunanin rayuwa, yau ko Abinci bata samu ta sa a baki ba, dan ko ruwa ba’a ɗaura a gidan su ba, rufe idon ta tayi lokacin da taji cikin ta na ƙugi alamar yunwa, hawaye ne suka zubo mata, tana zaune taji Baffa ya dawo ranshi a ɓace, fitowar Hajna ya ƙara sa shi jin ba daɗi, tabbas shi zai iya jurar yunwa amma Hajna shekarar ta nawa?, duka-duka shekarar ta 19, ya zata yi da yunwa.

     Umma ce ta fito, “Baffan Hajna ka dawo?, “Eh wallahi, amma yanzu ma ban samo komai ba “, Umma tace “to Allah ya mana mafita, kowa ya sha ruwa, ai marece yayi, gobe Allah zai mana mafita”, Hajna kuwa juyawa tayi Zuwa ɗakin ta, ta kwanta, dan an riga anyi isha, rufe  ido tayi, ta furta “yaushe wannan yanayin zai wuce “, zuciyar ta tace ba rana Hajna sai kinyi aure wataƙila, Hajna shiru tayi tace wa zai aure ni, a wannan zamanin, masu kuɗi sai masu kuɗi, talaka ma sai talaka ɗan uwan shi kawai da talauci zan mutu.


  A ɓangaren Fahna kuwa Alhaji yayi aiki, duk ya jijjiga ta, dan duk sha’awar da yake ji sai da ya sauke ta akan Fahna, ita kuwa banda daɗi ba abunda take ji.



Masu karatu ina fatan zaku fahimci labarin mu, saboda zai zo muku a hanyar da bakuyi tunani ba, fatan mu ku yi amfani da darasin da labarin zai koyar. ????????



    Haɗin guiwar mu ce.


QUEEN NASMERH & RABI’ATUL ADAWIYYA


ALQALAMI YAFI TAKOBI


????????️ *ZAMWA* ????️????

( _Zamfara writters_ )



COMMENTS ƊINKU NA DA MATUƘAR MAHIMMANCI, HAKAN ZAI ƊAURA MU A HANYA. ????????????.


Comments please ????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button