HAJNA 11-12

♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
PAGE 11-12
******************************
Tashar mota suka isa, motar Shinkafi suka shiga, gaban Fahna ke duka, dum dum, tasan yau bata da me ceton ta sai Allah, Baba ma be ce komai ba.
A ɓangaren Hajna kuwa sharar tsakar gida take yi, yayin da Umma ke wankin kayan ta, bayan ta gama sharewa ne ta kama wankin da mama keyi, tare suka ɗauraye kayan “Umma ki bari haka, ni zan shanya”Hajna ta faɗa, komawa Umma tayi ta samu guri ta zauna, kallon Hajna take, a ranta tana tausayin ƴarta.
Mama na tsakar gida zaune lokacin da Fahna da Baba suka shigo, ganin fuskar Baba ta sauya ba kamar yadda ta saba gani ba yasa gaban ta faɗuwa, dakewa tayi tace “Baban Fahna kun dawo “, “eh ya” faɗa tare da shigewa ɗaki,Mama kallon Fahna tayi tace “me ya faru “, Fahna zatayi magana kenan Baba ya fito daga ɗakin sa da wata ƙatuwar dorina, dukan ta ya fara yi tana ihu, kamar ranta zai fita, masu karatu tun ina ƙirga dukan da Baba ya ma Fahna har na kai na daina ƙirgawa, Mama ce ta dakatar da shi ta hanyar riƙe dorinar, “haba ya zaka sami yarinya kana duka kamar Allah ya aiko ka, kuma ba wanda ya min baya ni “, kallo Fahna yayi da jikin ta yayi ja abunka da farar fata yace “ina kika je”, Fahna da take jin zata iya komai akan rayuwar da take yi kuma ita ba mai hanata tace “Abuja naje “, “gurin me?”, baba ya sake tambaya, “gurin karuwanci! Ta faɗa da gadara, Baba ji yayi an caka mishi wani mashi a zuciyar sa, dan be taɓa tunanin abun ya kai haka ba, danne zuciyar shi yayi yana jin kamar zata fashe, jiri ya fara gani, ba tare da ya ankara ba ya faɗi ƙasa, ihu Mama ta sa, wanda har maƙota ana jiyo ta, tana faɗin “Baban Fahna ka tashi “, jini yake zubar mishi ta hanci da baki, Fahna kuwa ko a jikin ta, Baffa ne ya iso ƙofar gidan dan dama sun a aje da Baba idan ya dawo daga gona yazo ya same shi su fita neman aiki, jin kuka Mama da abinda take faɗa ya sashi shiga cikin gidan ba shiri, kwance ya samu Baba, da sauri Baffa ya ƙaraso “Malam Habu me ya same ka? “, Baffa ya tambaya, cikin jini Baba yake faɗa mishi abunda ya faru, sannan ya ƙara da bazai taɓa yafe mata ba, duniya zata koyar da ita darasi, Baffa yace “Malam Habu banso kayi wannan furucin ba”, tari ya ƙara turniƙe shi, ɗaukar shi sukayi zuwa wata ƙaramar asibiti, suna zuwa likita ya shaida musu ai Baba baya da rai, sanadiyyar bugawar da zuciyar shi tayi ta fashe, dafe kai Baffa yayi a hankali yana furta “inalillahi wa inna ilaihir raju’un “, Mama kuwa zubewa tayi ƙasa tana kuka, da ƙyar Baffa ya samu ta tashi suka koma da gawar gida.
Hajna na zaune duk ta gaji, labarin mutuwar Baba ya zo mata, kuka ta fara yi, dan Baba kamar uba yake a gare ta, Umma tace “Hajna ke kina kuka to ita Fahna wa zai lallashe ta, ki tashi ki wanke fuskar ki kije ki lallashe ta “, tashi tayi, kamar yadda Umma ta umarce ta haka tayi, zaune ta samu mutane duk an cika gidan, ɗakin Fahna ta nufa, a ɗaki ta same ta tana waya, sai dariya take yi, Hajna murza idon ta tayi dan ta kasa yadda da abunda idon ta ke nuna mata, amma duk da haka abunda ta gani shi take sake gani, jiki ba ƙwari ta matso kusa da Fahna tace “Fahna lafiyan ki dai? “, “eh mana lafiya na ƙalau me kika gani” Fahna ta faɗa tana kashe wayar ta, girgiza kai Hajna tayi tace “amma baki san mi ke faruwa ba ko “, murmushi Fahna tayi tace “baba ya rasu ko, to sai me in baba ya mutu, ai ni ina da raina “, Hajna tace “amma ko cikin marasa hankali ke kinfi kowa “, kallon ta Fahna tayi tace “saboda ni Baba ya rasu”, Hajna ta zare ido cike da tsoro tace “kuma hankalin ki kwance? “, nan Fahna ta bata labarin abunda ya faru, dafe kai Hajna tayi tace“amma baki kyauta ba”, Fahna tace “a gurin ki kenan “, Hajna tace “yanzu dai ba wannan ba, tashi zaki yi mu fita waje gurin zaman amsa gaisuwa kar mutane su gano wani abu”, ɗaukar hijab Fahna tayi tare da jan shi ya rufe mata fuska, Hajna ta kamata suka fito.
Guri suka samu suka zauna, da aka buƙaci iyalan mamaci da suje suyi bankwana da shi, Hajna tayi wa Fahna magana a kunne “Fahna tashi kije”, ce mata tayi “nifa babu inda zani, mutumin da yace bazai yafe min ba har abada “, Hajna ce tayi ƙarfin hali tace “Fahna bazata iya ganin gawar shi ba, tana jin ciwon rashin shi”, kowa a gurin ƙara tausaya mata yayi, wata tace “wayyo Allah sarki, abunka da ɗa da mahaifi, gashi itace ƴar shi ta farko dole taji ba daɗi”, wata tace “yarinya Allah ya baki ikon haƙuri “Hajna ce ke ƙarfin halin amsa musu da ameen.
Bayan sati biyu da rasuwar Baba, Fahna ta haɗa kayan ta, ta bar garin, wanda a garin ba wanda yasan abunda ya faru, Baffa kawai yasan asalin gaskiyar sai Hajna da Umma, kuma kowa yayi shiru da bakin shi, yanzu ma da zata tafi Mama cewa tayi gurin ƙanwar ta zata Kareema, Hajna kawai ta san gaskiyar.
Kamar kullum yau suna zaune wajen makaranta, Fahna tace “kinsan gobe zan wuce gusau, kuma gashi kullum sai na miki maganar Alhaji Qaseem baki cewa komai “, murmushi Hajna tayi dan duk lokacin da Fahna ta ambaci sunan Qaseem ji take yi kamar an mata kyautar kujerar makka, “Fahna idan nace miki bani son Alhaji Qaseem nayi ƙarya tun daga ranar da kika nuna min hoton shi ko barci bana iya yi saboda tunanin shi “, Fahna tace “Alhamdulillahi an zo gurin, to yanzu minene matsalar?”, Hajna tace “Baffa! “, “wai ke kullum maganar ki Baffa, in dai kin amince ki bar min komai hannu na”, shiru Hajna tayi na wani lokaci sannan tace“ a’a Fahna, wannan shawarar tare za muyi ta”, Fahna tace “gobe da safe zan wuce gusau, idan muka yi magana da Qaseem duk yadda aka yi zaki ji”.
Love you all fans ❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Haɗin guiwar : Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️
????????️ *ZAMWA* ????️????
( _Zamfara writters_ )
https://www.facebook.com/Zamfara-Writers-Association-zamwa-110643447448245/
Comments plsss. ????????????????