Uncategorized

HAJNA 2-4


♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️


Mallakin :- Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

*Bismillahir Rahmanir Raheem* 


PAGE 3-4

****************

Washe gari da safe wanka Hajna tayi, cikin shirinta na Islamiya, Hijabin daga saman shi ya yage dan haka sai da ta sa allura da zare ta ɗinke sannan ta fito, a zauren gidan su ta samu Baffa, gaida shi tayi sannan ya mata nasiha kamar yadda ya saba sannan ta wuce makaranta, a hanya ta haɗu da Umma ta je samo musu abunda zasu sa a baki. Gaida ta tayi sannan tace “Umma ko da na tashi ban ganki ba, ina kika je “, “Hajna naje samo kuɗi ne, da ƙyar aka ara min ɗari biyar”

Umma ta faɗa tana kwance haɓar zanin ta, nuna Hajna tayi, murmushin ƙarfin hali tayi sannan tace “Umma ai da ba kiyi haka ba”, “Hajna ina zan yadda yunwa ta kashe ki, zuwa zanyi na siyo mana dawa ko ta ɗari biyu ce, na siyo mana garin kuka na ɗari, sai na sayi magi da icce da sauran kuɗin, na yi mana tuwo muci, ko ya abinci yake ai yafi babu”, “to shikenan Umma ni zan wuce “Hajna ta faɗa tana wuce.


   A ɓangaren Fahna kuwa tun kiran farko ta dawo gida, saboda ta san Babanta shi yake tashin ta da asuba, Inna kuwa tunda Fahna ta fita tasa aka kira mata wata yarinya ta kwanta a gadon Fahna, da mahaifin ta ya dawo sai tace mishi ai tayi barci ciwon kai take yi, shi kuma be kawo komai aranshi ba, yanzu ma da asuba shi ne ya tashe ta, da miƙa ta tashi kamar me barci, tana cikin sallah Inna ta shigo ta same ta, bayan ta gama ne ta nunawa Inna kuɗin, ai kuwa suka ɓoye kuɗin,da safiya ta waye Baba da kan shi ya tasa ƙeyar Fahna gaba har makaranta.



Shigowar Hajna kenan ta hango Fahna zaune a gindin wata bishiya, ƙarasawa tayi gurin ta, Fahna tace “Kalar manya har kin ƙaraso kenan”, Hajna tace “haka dai kika ce ƴan matan duniya “, Fahna tace “wallahi ni Hajna kina bani mamaki, wallahi da kinsan yadda kika dace da irin harkar nan duk da bakiyi ba”, hararar wasa Hajna ta mata tace “ke ni ba wannan ba yunwa nake ji banci komai ba tun shekaran jiya”, Fahna tace“ baga irin ta nan ba, nace miki kizo ki fara bin maza kin ƙi”, “haba Fahna ni fa kinsan iskanci na be kai nan ba, ni ban iya baɗala irin taki ba, kuma bayan haka ma kinsan ni da shegen tsoro, kuma Baffa zai iya kashe ni duk ranar da ya samu labari”, Fahna tace “nima ɗin ai Baba zai iya kashe ni, amma nake yi, minene a ciki, ni wallahi ba zan mutu da talauci ba”, Hajna tace “ke kika ji zaki iya ni ba zan iya kasada da mutunci na ba”, Fahna tace “ai ke komai mutunci ke kika sani “, Hajna tace “naji dai, ke ma Allah ya shirye ki”.


    Haka suka cinye lokacin karatun su a waje suna surutu, a hanya Fahna ke gayawa Hajna kuɗin da ta samu yanzu, dubu goma taba Hajna, murmushi Hajna tayi tace“ nagode “, gidan su Fahna suka fara shiga, Inna ta dafa musu tuwon shinkafa da miyar kuɓewa suka ci sannan Inna ta zubawa Hajna a wani kwano tace “gashi Hajna ki kaiwa mahaifiyar ki”, Fahna ta rakata har gida, Umma na ta godiya taji daɗi sosai, ɗakin Hajna suka shige, da wani kallo Fahna ke bin ɗakin, “Hajna wannan ba rayuwa bace, me kika rasa a jikin ki da namiji zai ƙi, kawai kiba maza haɗin kai ki biya buƙatar ki, yanzu kalli ɗakin ki, dubi kayan jikin ki, ki kalli cikin kwali kike aje kayan ki, duba kiga takalmin ki ma duk sun tsufa”, Hajna tace “to se me Fahna haka Allah ke son ganina “, Fahna tace “ba wani har da son ranki kike a haka, amma rayuwa ta baki dama, kuma Umma macece da ba ruwanta da tarbiyar yaranta, bata takura miki zaki iya yin duk abunda kike so” Hajna tace “to shi Baffa fa ina zan kai shi, kinga Fahna ki bar maganar nan kawai ke ba zaki taɓa ganewa ba “, Fahna tace “to shikenan kanki kika yiwa bani ba”, daga nan kuma sai suka canza fira akan wani da yake son Hajna  “ke Hajna inda ma yana da kuɗi minene ciki dan kin kula shi “, Hajna tace “nifa ba wai maganar kuɗi a gabana ba, ni kwata-kwata be min ba”, dariya suka sa, Fahna tace “wani ƙolo da shi ko kaya yasa basa masa kyau”, “ashe ke ma kin lura “Hajna ta faɗa, haka suka dinga gulmar gayen nan har aka yi ƙarfe 9:00 sannan Fahna ta wuce gida.


Ƙarfe 12:30 na dare, Hajna na kwance har yanzu bata yi barci ba, abunda Fahna ta faɗa mata ɗazu shi yake mata yawo akai, tabbas tana da duk abunda maza suke so, amma bazata iya ba, a haka har barci ya ɗauke ta. 


   ABUJA…….. 


  Kwance yake akan kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, da alama wayar da yakw yi ta mishi daɗi, kallo na ƙarewa gidan ya haɗu, iya haɗuwa, zagaya ko ina na gidan nake yi saboda naga wayar tashi ba mai ƙarewa bace gashi bana ma jin me yake cewa, mamaki fal raina lokacin dana fahimci ba kowa a gidan sai masu aiki ƴan mata guda biyar, masu karatu idan kuka gansu zaku rantse ba ma’aikata bane uniform ɗinsu zai nuna miki su ma’aikata ne, wata riga ce mai wutsiya gefe da gefe ajikin su, a bayan ko wacce an rubuta aikin ta, (cooker, cleaner, washer, dresser, da kuma gardener) abin ya matuƙar bani mamaki dana ga rigar su kamar kayan barci, kowa aikin gaban shi yake. 


   Dawowa nayi parlor inda nasamu ya gama waya, fuskar shi na ƙarewa kallo bashi da makusa, dan kyakkyawa ne fiye da tunanin ku, sajen fuskar shi ya kwanta sosai, latsa wani abu yayi ba’a yi minti uku ba sai ga cooker ta shigo ɗauke da abinci, ita tayi feeding ɗinshi da kanta sannan ta bashi lemu yasha ta bashi ruwa sai ta wuce, ni kuwa nace wanene wannan mutumin mai ji ji da kai. 


   Wayar shi naji tayi ƙara sakw ɗauka yayi daga ɗaya ɓangaren naji ance “Qaseem kana ina shugaba na neman mu “tashi yayi da sauri ya shiga ɗaki, wanka yayi sannan dannan wani abu sai ga dresser ta shigo, ita ta taimaka mishi ya shirya ta fita, ohhh ni ina ganin ikon Allah namiji da suna ummi ????. 


Masu karatu nasan zaku so sanin wanene wannan ɗan faɗin ran ????kusance damu dan jin yadda zata kasance. 



I love u so much my fans, muna godiya da comment ɗinku tabbas kun nuna mana so ????❤️❤️❤️


Haɗin guiwar QUEEN NASMERH & RABIATUL ADAWIYYA. 


ALQALAMI YAFI TAKOBI. 


????????️ *ZAMWA* ????️????

( _Zamfara writters_ )



https://www.facebook.com/Zamfara-Writers-Association-zamwa-110643447448245/


  COMMENTS PLSS????????❤️❤️????????????????.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button