HAJNA 23-24

♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
PAGE 23-24
***********************
Tunda suka shiga mota, take barci, har suka isa Abuja, kasancewar jikin da suka hau Sokoto Kaduna ya aje su, gidan shi ya nufa kai tsaye da ita, tada ita yayi, buɗe tayi tace “Umma dan Allah ki barni, a gajiye nake “, Qaseem yayi murmushi, a ranshi yace Allah sarki tana tunanin gida take, dan haka kawai ya ɗauke ta a hannun shi zuwa cikin gida, ma’aikatan shi na mamakin inda ya samo Hajna.
Ɗakin dake kusa da nashi ya aje ta, kwantar da ita yayi sannan ya ja ƙofar ɗakin, ɗakin shi ya shiga sa fara rage kayan jikin shi, wanka ya shiga ya fito, maimakon ya kira mai shirya shi ta shirya shi, sai ya saka kayan shi da kanshi, already asuba tayi dan haka sallah yayi dan ya riga yayi arwala a toilet, sallah yayi sannan ya dawo ya kwanta don a gajiye yake, murmushi yayi lokacin da ya tuna da Hajna, yanzu dama ce gare shi, zai samu abunda yake so, amma fa bazai aure ta ba, tunawa yayi da jibi zai je gurin yayar shi dake zaune garin Lagos, wadda yake cewa love, kasancewar ba musulma bace shiyasa be wani cika so yana zuwa gurin ta ba.
Da addu’a a bakin ta, ta tashi, ƙoƙarin buɗe idon ya take yi har ta samu ta sauke su a kan fankar ɗaki, da sauri ta tashi a firgice, tana mamakin ina take, da kallo take bin ɗakin yadda komai yaji, da alama mai gidan nan babban mai kuɗi ne, kallon ko ina take, sai yanzu ta tuna ta biyu Qaseem zuwa Abuja, to nan ina ne ma, tashi tayi ta shiga toilet, komai na toilet ɗin ya mata,kayan jikin ta cire, cikin bathtub ta shiga tare da sakar ma jikin ta ruwa, yadda ruwa ke sauka tana jin wani sanyi sai take jin son Qaseem yana ratsa gaɓoɓin jikin ta, she admit it, she really love Qaseem, ta shirya bada rayuwar ta akan soyayyar Qaseem.
NI KUWA NASMERH NACE ISKA NA WAHALAR DA MAI KARA.
Wanka tayi sannan ta fito, tayi matuƙar yin mamaki da ta buɗe wardrobe ɗin ɗakin taga kayan sawa, kuma na mata, ko da yake ba abun mamaki bane, saboda Qaseem womanizer ne shi, zaɓar wata riga tayi mara nauyi ta saka, sannan ta fesa turare kala-kala, sai yanzu take ganin irin kyan da Allah ya mata, asalin farin fatar ta ya fito, sannan pink lips ɗin ta ya bayyana, ƙugun ta ta kalla yadda ya zauna a jikin ta gashi ɗan ƙarami hakan ya ba shape ɗinta damar fitowa da kyau, shafa bakin ta tayi, dogon gashin kanta ta gyara, sannan ta tattara shi ta gefe ɗaya, wanda hakan yayi matuƙar ƙara mata kyau, murmushi tayi wanda ya fito da fararen haƙoran ta, wow masha Allah, masu karatu Hajna kyakkyawa ce ajin ƙarshe, tsayawa bayyana muku hakan ɓata lokaci ne, sallah tayi sannan ta fito zuwa parlor, lokacin ƙarfe 9:30.
A parlor ta same she kwance akan kujera, ɗaya daga cikin masu aikin shi na shafa mishi jiki da sunan tausa, idon ta suka ciko da hawaye lokacin da taga yadda yake wani lumshi ido, guri ta samu ta zauna nesa dasu, buɗe idon shi yayi yace“favorite one zoki mana”ya faɗa yana buɗe mata hannun shi, ba musu tazo, rungume ta yayi yace “kin tashi lafiya “, “Alhamdulillah” ta faɗa, murmushi ya sakar mata yace “ miye kike wani haɗe rai “, “hmmmm” kawai ta iya furtawa tana tashi daga jikin shi, ya fahimci saboda wannan yarinyar dake gaban shi take fushi, “favorite one, kin cika rigima waɗannan fa ƴan aiki na ne, ke kuma fa, ke tawa ce, su kuma kawai biyan su nake, banga abun fushi nan ba “ya faɗa, turo baki tayi tace “amma ai ba gaba na ya kamata kuyi wannan ba”, “to ai bansan zaki zo ba”ya faɗa, “amma ai kasan ina gidan nan”, kallon ta yake da mamaki yace “kina nufin bazan hole ba dan kina gidan nan, inaaa Hajna bazai yuyu ba, da halina kika ganni in kina iyawa ki zauna dani, idan kuma bazaki iya ba ban miki dole ba ki haɗa kayan ki ki koma”, shiru tayi tana bin shi da kallo, tabbas in dai kai kake son namiji ka bani, murmushi tayi duk da abun ya mata ciwo amma sai ta ɓoye, tashi tayi ta bar gurin, ɗayan parlorn ta shiga in da ta tadda sauran matan su haɗu, kowa da cup wanda ita bata san menene ba, “sannun ku”ta faɗa tare da zaunawa, gaisawa suka yi, trisha ta mata tayi kunun gyaɗa wanda dama shine abunda suka fiye sha, murmushi tayi tace musu ta gode, kwanciya tayi kan ɗayar kujerar, rufe idon ta tayi, maganar da Qaseem ya mata ke yawo a cikin ƙwaƙwalwar ta, hawaye suka zubo mata, saurin sharewa tayi, tana kwance har suka watse daga parlor saura ita da trisha kawai suka rage, “ke sister boss ce” Trisha ta faɗa, Hajna tace “a’a ni matar da zai aura ce”, Trisha tace “aure, shine yace miki zai aure ki “, Hajna ta girgiza kai alamar a’a, Trisha tace “in dai boss ne kina da aiki tabbas, dan marriage is not his card”, Trisha ta ƙara da “i have been working here for almost 15 years tun ina yarinya, mata da yawa sun zo sun zauna da Qaseem, kuma duka da sunan waɗanda zai aura, amma basu san Qaseem is very smart ba, shi be yadda da aure ba, rayuwar shi be yadda akwai aure ba “, da ta fahimce Trisha da kyau, tace “kina nufin duk abunda zan yi bazai aure ni ba”, Trisha tace “idan ƙaddarar ki ce ki aure shi za kiyi amma ni bana miki fatan ki aure shi, dan bazai fasa halin shi ba”, Hajna tace “amma me yasa kike faɗa min”, Trisha tace “na faɗa miki ne saboda nasan Qaseem, kuma mutum ne da baya gajiya da mace in dai karuwa ce, kuma kin bani tausayi ne, dan tunda na ganki nasan kina cikin damuwa saboda na bar Qaseem da Easter a parlor, nasan duk mai son shi zata ji haushi, kuma kece kawai musulma a cikin yaran da Qaseem ke mu’amala da su”, Hajna tace “kina nufin baya harka da musulmai? “, Trisha tace “ai shima ɗin be wani jima da karɓar musulunci ba, bazai wuce shekara biyu ba, kuma yayar shi na nan, har yanzu bata musulunta ba, ita ce ma ta kawo ni nan”, Hajna tace ya sunan ki? “, Trisha tace “, Trisha David Cameron, kefa ya sunan ki”, “Hajna Ibrahim Shinkafi “ta faɗa cikin murmushi, “wow nice name, Hajna! Nice to meet you” Trisha ta faɗa, Hajna tace “ thank you “, nan suka dinga labarin Qaseem, har take faɗa mata jibi Qaseem zai je gurin yayar shi, wanda duk bayan wata ɗaya yake zuwa, Hajna kuwa duk abunda Trisha ta faɗa mata yana shiga, a cikin labarin ta fahimci abubuwa da yawa da Qaseem yake so, da waɗanda baya so, Trisha ta yiwa Hajna alƙawarin ciwa idan Qaseem yayi tafiya zata taya ta gyara jikin ta kafin ya dawo,kuma zata koya mata yadda ake karairaya, da dai sauran su.
Anan zan dasa aya…………..
Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️????????????????????????????????????????????????????????????????