Uncategorized

HAJNA 31-32

 ♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️


Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya




QUEEN NASMERH’S WATTPAD ACCOUNT 


Show me love and follow 

https://www.wattpad.com/user/AsmaunanaLawalliman?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍




*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* 

*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*

*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*


*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*


Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.



*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PENBismillahir Rahmanir Raheem*

PAGE 31-32

*************************

Wannan shafi naku ne Hajna fans ????????????????????????????????????????, tabbas kuna nuna min soyayya, kuna ƙarfafa min guiwa da comment ɗin ku, saboda haka na sadaukar da shi gare ku, love you all muah????????????????


*****************———–❤️❤️————**’*************************


Washe gari da safe Hajna tashi tayi wanka ta shirya cikin wando da riga, wanda yayi matuƙar fito da asalin kyan ta, a parlor ta sami su Trisha suna kallon wani series film double kara a novelaE, zaunawa tayi suka yi kallon tare, magana taji Trisha nayi da Juliet wato mai wa Qaseem wanki da guga “Juliet kinsa yanzu zamu fita kasuwa “, Juliet tace “ohk to shikenan bari nayi wanka, sai mu fita”, Trisha ta juyo ta kalli Hajna tace “Hajna za ki bi mu, ko zaki ga gari “, murmushi Hajna tayi tace “eh Trisha, dama ina so na fita”, a tare suka fita bayan Juliet ta fito, sai aka bar Favor, Easter da kuma Adaku, taxi suka tara ta kai su har kasuwa suka biya mai taxi ɗin sannan suka fara zagaye, wasu kayan gyaran jiki suke ta siye, sannan suka dawo gida, Hajna dai ba abun da ta siya, suna dawowa ta faɗa toilet wanka ta sake yi sannan ta fito ɗakin, tana cikin sa kaya Trisha ta shigo ɗauke da wani cup a hannun ta, miƙa mata tayi tace “oya Hajna sha wannan”, da kallo Hajna ta bita, “nace kisha, bana son tambaya ” karɓa Hajna tayi, yadds Trisha tace haka tayi ta ɗaga kai ta shanye shi tas, Trisha tace “good of u, kinga kafin Qaseem ya dawo kin tsima, ki jira na dare kuma”, murmushi Hajna tayi tace “kina nufin wannan tsimi ne? “, “eh shine, sannan daga yau zaki riƙa shan kayan bata, da kayan gyaran jiki, kafin Qaseem ya dawo”, shiru Hajna tayi kafin tace “haka zai sa ya so ni? “, Trisha tace “haka bazai sa Qaseem ya so ki ba, kar ki manta so a zuciya yake ba jiki ba, Qaseem zai so ki ne kawai idan zuciyoyin ku sun haɗu, amma for now ki yi wannan, wataƙila kisamu sauƙi, saboda ko ba komai zaku kasance tare”, sosai Hajna taji daɗin maganar ta, godiya ta mata, sannan Trisha ta bar ɗakin.



        Fahna bata ƙaraso Abuja ba sai bayan la’asar, a parlor ta sami Hajna zaune, gaisawa Hajna tayi da saurayin da Fahna tazo da shi, sannan aka kai shi masaukin baƙi, abincin shi ma can aka sa Adaku ta kai mishi, Fahna kuwa ɗakin Hajna ta fara zuwa, wanka tayi sannan ta zauna, tun da ta fito wanka ta lura da irin kallon da Hajna ke mata, “ke wai kallon me kike min” Fahna ta tambaya, Hajna tace “naga kinyi ƙiba, kin ƙara kyau, minene sirrin, kin zama wata irin babba “, murmushi Fahna tayi tace “wani guy na haɗu dashi, ina gaya miki kuɗin shi nake ci, yanzu haka na siye gida”, Hajna tace “shi kuma wancan fa? “, “satin da ya wuce muka haɗu da shi, har ya siya min mota da waya” Fahna ta faɗa, Hajna ta zare ido tace “Fahna kin yi nisa fa “, Fahna tace “ke ba wani nisa, ni maganar Qaseem nake so muyi”, nan Hajna ta sake faɗa mata abunda yake mata, Fahna tace “namiji fa, muddum ya ɗaukoki ya kawo gidan sa, to ki bashi jikin ki kawai”, Hajna tace “to ai baya nema na”, Fahna tace “to ke mikike da bazaki neme shi ba “, Hajna tace “Qaseem fa ya wuce tunanin ki”, Fahna tace “waɗannan shegun kayan da kike sawa suna rufe miki jiki ki daina, Hajna kina da shape, kinfi duk matan da Qaseem ya aje gidan kyau, diri da komai, amma sun fiki fitar da jikin su waje, taya zai kula ki, ki samu kaya ƙanana kina sawa “, Hajna tace “to in be kulani bafa”, Fahna tace “duk taurin kansa, in ya jiki a jikin sa rikicewa zai yi, sannan ki riƙa shan kayan gyaran jiki, sannan ki siye wani magani na nan kina matsawa a jikin ki, zai dawo dake sabuwa kullum, ki gane kawai”, Hajna kuwa wani sanyi taji a ranta, dan gani take kamar ta samu Qaseem ta gama.



     A cikin kwana huɗu Hajna ta ƙara kyau, asalin surar ta, ta bayyana, Fahna sai ɗirka mata magani take, ga na Trisha, kullum sai Fahna ta fita da Hajna yawan zaga gari, inda idon Hajna ya buɗe sosai, yanzu ta ƙara sakewa da garin Abuja, Fahna kuwa sheƙe ayar ta, take yi, duk namijin da ya tari gaban ta, matuƙar yana da kuɗi to zata afka masa ba wasa, kwana biyar Fahna tayi suka koma ita da gayen ta, idan ta ɗaura Hajna akan turba kala-kala na karuwanci, Trisha ta ɗaura daga inda aka tsaya.


YAU DAI NACE BARI NAJE SHINKAFI


Umma na gani zaune tayi tagumi, sallama Baffa yake yi amma ina bata ma jin shi tayi nisa da tunani, zaunawa yayi ya ɗan taɓa ta, firgigit ta dawo daga duniyar tunani, “wai minene, ina ta sallama amma ko ki amsa ni, tunanin me kike? “Baffa ya faɗa, kallo shi tayi, idon ta cike da hawaye tace “tunanin me zanyi inba na Hajna ba, yarinyar nan bamu san halin da take ciki ba”, Baffa da takaici ya kama yace “idon ki zai tsiyaye dan kuka in dai Hajna ce “, Umma tace “amma kasan be kamata kana faɗan haka ba ko”, “to mikike so nace? “Baffa ya tambaya, “ kasani sarai yarinyar ba haka take ba, amma ko uzuri ka gagara mata”, tashi yayi yace “wani uzuri zan mata, me na mata da zaki ce na ƙi mata uzuru, ita ta zaɓi ta bar mu, ta zaɓi shawarar ƙawa akan shawarar da nake bata, me sheda ce kullum sai na yiwa yarinyar nan nasiha, to yanzu ta tafi so kike naje har in da take na ɗauko ta? “, shiru Umma tayi dan a wannan fannin tasan Baffa keda gaskiya, a ranta tace Allah ya dawo mana dake gida, Allah yasa ki dawo gida a lokacin da muke raye.


     A ɓangaren Qaseem kuwa hutawa yake a Lagos hankalin shi kwance, kullum yana gurin party da ƴam mata ya taɓa wannan ya taɓa wannan, har sati ya cika, inda yau yake shirin komawa, dan shi, kan shi ya matsu yaga Hajna.



Anan zan dasa aya……………. ✍️????


Shin ya zata kasance tsakanin Hajna da Qaseem.


Ku kasance dani Queen Nasmerh dan ɗauko muku rahoto.



Godiya ta musamman gare ku masoyan mu.


Haɗin guiwar:Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya.



ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????????️ *ZAMWA* ????️????

( _Zamfara writers _ )

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button