HAJNA 5-6

♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️
Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
PAGE 5-6
***************’
Office ya nufa inda oga ke kiran sa, a ƙofar shiga meeting ɗin ya haɗu da Farween, kallon wulaƙanci yake ma Farween dan a duniya ba wanda ya tsana irin Farween, a ran Farween murmushi kawai yayi yace Qaseem kenan Allah ya maka magani, to masu karatu kunji dai wannan sarkin faɗin ran sunan shi Qaseem.
A meeting hall ɗin suka zauna inda kowa yayi shiru yana jiran abunda za’a ce, kallon kallo ake yi tsakanin Qaseem da Farween, jin gyaran muryar ogan su ne yasa suka maida hankalin su, bayani yayi akan cigaban da za’a kawo a company ɗin da kuma ƙarin salary ma kowane ma’aikaci.
Meeting ɗin yayi kyau sosai, kamar dai ɗazu a ƙofar fita hall ɗin yayi karo da Farween, wani jawo shi yayi yace “kai wani irin mutum ne, taya zaka na bibiya ta, nasha faɗa maka ni ko hanya bana fatan ta haɗani da kai “, murmushi Farween yayi ma kashe zuciyar maƙiyi sannan yace “ni bani da lokacin kula sakarai irin ka, idan baka son ganina ka kashe ni mana”, maganar da Farween yayi tayi matuƙar ɓatawa Qaseem rai, amma sai ya haɗe rai ya wuce da kallo Farween ya bi bayan Qaseem, cikin kallo irin na natsane ka, shi kanshi ya tsane Qaseem saboda mugun halin shi.
Kai tsaye gida Qaseem ya wuce, already anyi magrib, wanka yayi sannan ya ɗauro arwala ya zo yayi sallah, parlor ya dawo ya zauna, yana kallo, har yanzu ma’aikata na kai-kawo a gidan, kowa sai aiki yake yi.
**********
AJIYAWA
Kwance take akan katifar ta, kasancewar daren jiya anyi ruwa duk sun jiƙata, dan karan ta aka rufe samman ɗakin ta bazai hana ruwa kaiwa ba, zazzaɓi ya rufe ta, Umma na gani zaune daga gefen ta tana jiƙa mata maganin gargajiya, bayan ta gama ne ta bata sannan tace “Hajna bari naje na ɗebo miki yanɗori, a dafa miki, insha Allah zazzaɓin ki zai sauka”, gaɗa kai tayi dan bazata iya yin magana ba.
Fita Umma tayi, bayan gidan su naga ta zagaya gurin daji ne, ɗibar yanɗori tayi sannan ta koma cikin gida, tukunya ta ɗaura a wuta sannan ta dafa maganin, Hajna na kwance a ɗaki Umma ta shigo da maganin ta bata, sauran tuwon jiya Umma ta ɗauko ta miƙa mata “karɓi maza ki cinye, yanzu zazzaɓi zai sauka bari na je na gyara ɗaki na duk ruwa sun ɓata shi.
Ɗakin ta tashiga, masu karatu kar ku so kuga ɗakin su Umma ashe ɗakin Hajna Aljannar duniya ce akan na su umma, duk saman gurin ya hude, ɗakin duk ruwa sun ɓata shi, idon Umma ya cika da hawaye tace “ya Allah ka mana sassauci ” gyara ɗakin tayi sannan ta gyara ɗakin Hajna, lokacin barci mai nauyi ya ɗauki Hajna.
Bata farka ba sai da aka yi sallar azahar, wanka tayi sannan tayi sallah, tana saune a tsakar gidan su Baffa ya dawo da leda a hannun shi, ya miƙawa Umma sannan yayi wa Hajna ya jiki, abinci Umma ta ɗaura, suka dawo suna fira, Hajna kam shiru tayi dan bata magana in dai su Baffa na magana.
Suna zaune Umma ta zuba musu abinci suna ci, Fahna ta shigo, zaunawa tayi ta gaida Baffa, “Lafiya ƙalau Fahna ina iro”, cewa da mahaifin ta wanda ya kasance babban aminin Baffa, “yana gida “Fahna ta faɗa, Baffa yace “to ki gaida shi”, “insha Allah “Fahna ta faɗa tana kama hannun Hajna suka shige ɗaki, da kallo Hajna ke bin ta, “wai minene kika wani jawo ni ɗaki” Hajna ta faɗa tana haɗe rai, Fahna tace “nifa wuya ta dake kenan ba’a miki abun arziki “, Hajna tace “wane abun arziki, ke kina da maganar da ta wuce ta maza ne”, Fahna ta ɓata rai tace “to ai hanyar da ake yin kuɗi kenan, Hajna sai in baki son gaskiya amma kinsan dole sai an bi maza za’a yi kuɗi “Hajna tace “ke kike ganin haka ni ban gani ba, kuma hanyar arziki zata zo ta inda banyi tsammani ba, kar ki sake min maganar nan”, Fahna tace “ni bazan gaji da jan ra’ayin ki ba, tabbas watarana zaki fahimta”, Hajna yi tayi kamar bata ji me Fahna ke cewa ba, ganin Hajna bata karɓi zancen ta ba yasa suka canza labari.
A ɓangaren Qaseem kuwa bayan yayi sallar isha ɗaki ya wuce ya latsa wayar shi, da misakin ƙarfe 9:30 na dare naga ya danna wani abu cikin minti 5 sai ma’aikatan nan nashi su biyar sun shigo, kallon su nake yi a raina nace su kuma waɗannan me ya kawo su nan cikin dare, kallon su naga yana yi, lokaci ɗaya naga ya nuna mutum biyu daga cikin su, sauran suka fita, biyun suka tsaya, kallon su yake yi daga tsakiyar gado, a hankali suka fara takowa har gaban shi, ɗaya tayi gefen hannun shi na dama ɗayar kuma tayi hagu, hannayen su suka ɗaura akan hannun shi a hankali suna mishi tafiyar tsutsa a jiki, wani ihu yake saki na daɗi, su kuma suna cigaba da yi, zaren dake gefen rigar su ya warware, ai kuwa rigar su ta faɗi, asalin surar jikin su ta bayyana, da hannun shi ɗaya yake kama boobs ɗinsu yana murzawa, suma ɗin sun rikice sai wani faɗa mishi suke yi a jiki yana rufe ido, dana ga abun ba irin na mu bane ba shiri na ja ƙofar ɗakin na gudu dan ido na basu iya ɗaukar wannan abun.????????
A ɓangaren Hajna kuwa fira suke da Fahna “Hajna kinsan me Alhaji musa so yake na kwana biyu gurin shi “, Hajna tace “me zaki mishi”, “biyan buƙata mana”Fahna ta faɗa, Hajna tace “to ya zaki yi da Baba, kinsan kamar Baffa yake “Fahna tace “yo Inna zata ce mishi naje gusau kwana biyu zanyi ma ƙanwar ta”, shiru Hajna tayi tace “to ke baki jin tsoro “, “tsoron me zanji Hajna, bariki fa akwai riba, ga daɗi ga kuma kuɗi” Fahna ta faɗa, Hajna tace “ni ai bazan iya ba “, Fahna tace “baki dai so ba”, Hajna tace“ naji mu bar zance, Allah ya tsare hanya “, nan suka taɓa hira da zata tafi Fahna tace “muje waje ki rakani ƙofar gida sai muyi hoto”, ba tare da Hajna ta kawo komai ba suka fita suka dinga ɗaukar hoto a waje, har sai da baban Fahna ya zo wucewa, kasancewar yafi Baffa tsanani ya dinga musu faɗa wai ba tarbiya bace suna hoto a waje, gaida Baba Hajna tayi sannan ta koma cikin gida, ita Fahna gida ta shiga ta soma gyara kayan ta, inna tayi wa Baba maganar zuwan Fahna ziyara, da kamar bazai yadda ba dan ranshi ya bashi wannan tafiyar tsiya ce, amma inna ta sa kuka abunki da mata, dole ya haƙura ya bar Fahna ta tafi, a cewar sa kwana uku kawai ya yadda tayi kuma shi da kanshi zai je ɗauko ta, Fahna kuwa ba ƙaramin daɗi taji ba dan dama Alhaji musa Abuja zai je da ita da ta isa gusai, tana da kwana biyu tare da shi, a daɗin ta ????????????????????????idan suka dawo zata gidan aunty kareema sai Baffa ya ɗauke ta, amma inna tace mishi a’a ita a dole kwana biyar zata yi, dole ya yadda dan shi mutum ne da baya son yawan rigima.
Haɗin guiwar : Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya.
ALQALAMI YAFI TAKOBI
????????️ *ZAMWA* ????️????
( _Zamfara writters_ )
https://www.facebook.com/Zamfara-Writers-Association-zamwa-110643447448245/
SHARE
AND COMMENTS PLSSSS ????❤️