Uncategorized

HALIN GIRMA 30

 Halin Girma      30

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

******* ★

A durkushe ya ganta tana kuka ta rik’e kanta, saurin durkusawa yayi a gabanta yana janye hannun nata

“Menene?”

“Miciji!” 

Tayi maganar tana nuna masa wajen, saurin kalla yayi amma be ga komai ba, ya yunkura zai tashi ta kankame shi sosai tana fashewa da kuka. Hannun ta ya kama zuwa wajen switch din falon, ya kunna haske ya bayyana a ilahirin falon, wurwurga idonsa ya dinga yi a gaba dayan falon amma be ga komai ba, 

“Aina kika ganshi?”

“Adaidai nan zai shiga dakin chan!”

“Tsaya .” Ya tsaida ita yana sake dubawa amma babu komai. Riketa yayi ya kaita daki, tayi saurin rikeshi ganin zai fita

” Dan Allah karka fita ka barni.”

” Kinaji? Calm down babu abinda zai faru, yanzu zan dawo.”.

Sakin sa tayi, ya fita ya taso securities din a gaba, suka zo suka hau bincika falon da ko ina na part din,ciki ya koma ya sameta ta kudundune a saman gadon still jikinta be bar rawar da yake ba, tana addu’a kasa kasa, daga gani kasan ta tsorata sosai dan bata taba ganin shi haka a zahiri ba. Jawota yayi jikin sa, ya mannata da kirjinsa yana shafa mata baya kad’an kad’an.

” Babu abinda zai faru kinji? Ki kwantar da hankalin ki.”

Da kai ta amsa masa, zuwa lokacin ta fara dawowa nutsuwar ta, sai wani uban juyi da taji cikin ta nayi,ta dora hannun ta a saman cikin yana yatsine fuska, kallon hannun nata yayi, ya dauki nasa ya dora a saman nata yana tayata shafa cikin, 

“Ciwo?”

“Eh.”

“Sannu zai daina, bari na dubo ko sun gama dubawar.” 

Ya kwantar da ita ya fita, a tsaye ya same su rik’e da abu me kama da maciji, matsawa yayi yana dubawa cikin son karin bayani

“Macijin roba ne ranka ya dade!”

“Roba?” Yace cikin yanayin mamaki

“Me ya kawo shi nan? Me yasa bamu ganshi ba tun da rana sai yanzu…”

“Waye da waye suka shigo part din nan?” Ya fad’a yana daure fuskarsa tamau. Rantse rantse suka hau yi, kowa na son kare kansa, wata uwar tsawa ya daka musu, duk suka nutsu suka kame suna masu saukar da kansu k’asa 

“Kwana daya tal na baku, ku gano wanda ya shigo part din nan har ya ajiye wannan shirmen, koma waye sai ya fuskanci hukunci me tsanani!”

” Yes sir!”

Har ya juya sai kuma ya tsaya.

” Get ready, we are leaving tomorrow in the afternoon!”

” Yes sir!” 

Suka kara hada baki wajen fad’a sannan ya juya ya bar su a wajen da sassarfa. Dayan dakin ya shiga, ya hau bincike wasu kaya da sauri da sauri, ba zai yarda a taba masa ita ba, idan har ba zasu iya tsayawa iya kansa kawai ba, toh zai yi abinda zai girgiza su matuka. Ya dan dau lokaci a dakin, sai da ya tuna ya barta ita kadai ya kuma san tsoro take ji, sannan ya koma da sauri, ya tarar bacci ya dauke ta, ta takure waje daya tana fitar da numfashi kad’an kad’an. AC din dakin ya rage, zuwa low ya dawo ya gyara mata kwanciyar, ya kura mata ido yana jin son ta na kara ruruwa a zuciyar sa, ba zai bari banzar al’adar gidan su ta taba ta ba, zai yi duk abinda zai yaga ya kareta da dukkan karfin da yake dashi.

   Da asubah ya tashe ta, sukayi sallah a dakin, sannan ya fita ya shigo mata da micijin robar yana mata dariya

“Matsoraciya, nina fa na shigo dashi jiya by mistake, abun wasan yaran chan ne suka bani, ashe sai na yar dashi ban ma lura ba.”

Shiru tayi tana kokarin daidaita maganganun nasa da abinda ta gani, idan har ba gizo idon ta yayi mata ba, toh tabbas tafiya ta ganshi yana yi, har ya kai kofar dakin kafin ta daina ganin sa.

“Common!” Yace yana son dauke tunanin ta

“Babu komai fa I promise you.”

“Amma na ganshi fa yana motsi!”

“Imagination ne kawai nothing else, karki damu ki kwantar da hankalin ki.”

Shiru tayi tana kallon sa, yanayin sa yayi mata kama da na wanda yake so ya dauke hankalin ta, amma idan ba haka ba babu yadda za’a yi taga abu yana tafiya da idonta ya zama imagination kuma, hore mata idon yayi yana jawo ta jikinsa

“Karki yi ta tunani kinji? Anjima zamu wuce ma, Abuja zamu fara zuwa na gaida Mummy, daga nan muyi tafiyar mu gidan mu mu sha soyayyar mu.”

“Da gaske?”

“Da gaske mana, are you happy?”

“Naji dadi sosai, bari na fara hada kaya na, da wuri zamu tafi ko? Ko sai da yamma.”

“Yamma!”

Komawa tayi ta zauna tana jin kamar yamman ya mata tsayi

“Zanga Aji ne, sannan bana son kowa yasan mun tafi sai Ammi kawai, shiyasa ba zamu dauki yaran chan ba, i mean ma’aikatan gidan, akwai screening da za’a yi musu kafin su biyo mu.”

” Owk Allah ya kaimu.”

” Amin my beautiful wife.”

Murmushi tayi, ya dauko musu al’qurani me girma suka shiga karantawa, ya dinga admiring muryarta da yadda take bawa kowanne harafi hakkin sa, cikin nutsuwa da fitar da tajweed a duk in da ya dace. Sai da rana ta fito, sannan sukayi wanka, suka shirya a tare suka fita don karyawa, bud’e warmers din yayi, ya kakkala sannan ya saka aka kwashe masa su daga wajen, ya aika part din Ammi aka karbo musu breakfast din, taso ya barta tayi amma ya hanata, ya kuma ki gaya mata dalilin da ya saka shi sawa a kwashe abincin da aka girka a part din, bata ce komai ba, ta barshi a zuwan kawai zata ji koma menene daga baya, dan ta lura yadda ya boye masa kanta kafin aure akwai abubuwa da yawa da yake boyewa a yanzu ma, duk da haka ba zata zarge shi ba, zata bashi lokaci sosai ta kara fahimtar shi, jikinta na bata akwai wani abu da shi kadai ya sani, sai ko Aji da take ganin kusancin su yafi na kowa hatta mahaifiyar sa da mahaifin sa.

  Bayan sun gama breakfast din ne ya fita, cikin shigar kayan sojoji da suke masifar yi masa kyau, cikin rakiyar yaransa ya nufi part din Kilishi, wanda tun kafin ya karasa sakon zuwa nasa ya ishe mata, tana zaune ta gama karyawa, tashi tayi da sauri ranta na baci, tasan zuwan sa babu abinda yake jawo mata sai bacin rai. Daki ta shiga ta chanja kaya, ta zauna tana jiran sanarwar isowar sa. Tana jin sanda ya shigo, dan har falon ta na ciki ya shigo, ya zauna fuskar sa fes dauke da farin ciki, idonsa na kan kofar da zata fito, ya dan dauki lokaci a zaune har ya fara tunanin ko ba zata fito ba, agogon hannun sa ya kalla, ya daga kai ya kalli na jikin bangon dakin, a tare suke tafiya dakiya daya, sauke idon sa yayi yana murza agogon nasa, takun tafiya yaji, yaki d’agowa amma yasan itace,sai da ta zauna sannan ya dago yana dubanta, yayi murmushi cikin salon girmamawa yace

“Barka da gida ranki ya dade.”

“Barka dai, ya iyali?”

“Lafiya kalou kalou, kamar yadda kike fata a kowanne lokaci.”

Yak’e tayi, tasan magana ya fad’a mata, dan ya saba gasa mata ita dama, murmushi ya sake yi yana lankwasa hannayen sa baya

” Haka ake so ai, sai a sake kula sosai.”

” In Sha Allah, za’a kula kulawa me kyau, duk wani me sharri Allah zai maida masa kansa ma, saboda addu’a itace makamin mumini, kuma matakin duk wata nasara.”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button