HALIN GIRMA 30

” Haka ne!” Tace tana gid’a kanta. Mikewa yayi cikin salo na burgewa, ya dan rankwafa yace
” Na barki lafiya!”
” Nagode!” Tace tana danne zuciyar ta, bayan sa tabi da kallo har ya fice gaba daya,
“Ahhhh!” Tayi kara tana jifa da trow pillow din dake kusa da ita,kamar ta shako shi haka taji, gashi kamar masifa yasan duk wani shirin ta, ta rasa yadda zatayi dashi ya zame mata tamkar kadangaren bakin tulu! Ya kuma zame mata ciwon ido, da za’a bata makami ace ta kashe mutum daya toh tabbas shi zata kashe, bata son ko ganin wulgawar sa.
Laila ce ta shigo, ta tarar da ita cikin halin da take ciki na bacin rai, bin ta tayi da kallo har ta dauki jakar ta, ta bud’e ta dauki ATM cards din Kilishin, ta juya zata bar dakin.
“Laila!” Tsayawa tayi ta juyo
“Ina zaki? Me kuma zakiyi da Atm dina?”
“Haba Mah, tunda har na dauka ai amfani zan dashi.”
” Shine ba zaki iya fada min ba?”
” Da ma fa na saba dauka kuma bana fad’a miki, why now?” Sai ta juya ta cigaba da tafiyar ta
” Zan dawo dashi wani payment kawai zan.” Sai data kai karshen kofar sannan ta fad’a, ta saka kai tayi ficewar ta, kwafa Kilishin tayi ba tare da ta sake cewa komai ba.
****Bayan fitar sa ne tana zaune da waya a hannun ta suna chatting sama-sama da Ya Maryam,rabin hankalin ta na kan Tv sai tana duba sakon lokaci zuwa lokaci, ta kira Abba bata same shi ba, kila ko ya fita ko kuma baya kusa da wayar. Kara wayarta tayi a tunanin ta Abban ne, sai taga number Ya Maryam ce, dauka tayi tana tashi zaune
“Ina ta magana a whatspp kin sauka, yanzu aka kira ni a gida Aunty Bilki ta haihu!”
” Dan Allah!”
” Wallahi yanzun nan kuwa ta haihu.”
” Masha ALLAH, me aka samu?”
” Ina ma na tsaya tambaya? Murna ta saka ni kiranki, kinga al’amarin Allah, bayan ta cire rai, dama ba’a cire rai da rahmar Allah.”
” Wallahi, kai Masha ALLAH, nayi murna sosai Allah ya bata lafiyar shayarwa.”
” Amin ya Allah, zuwa kano ya kamaki.”
” Gaskiya, dama yau zamu bar nan din, amma Abuja zamu wuce daga nan zamu dawo Kanon.”
” Ah shikenan ma, ki kirata toh kafin nan, bari na kira Amira itama na fesa mata.”
” Owk ki tura min number ta, Inaga kamar bani da ita yanzu.”
” Ok tam, zan ajiye miki a WhatsApp.”
” Yawwa.”
Ajiye wayar tayi farin ciki na kamata, after all a karshe dai itama ta samu nata babyn, shekara ashirin da aure amma bata taba ko batan wata ba, sai yanzu Allah yayi, dama dai sunji kishin kishin din ciki ne da ita musamamn da bata zo bikin da akayi ba, sai mutane suka kara tabbatar da zargin su, boye labarin sukayi sun fi so kawai aji haihuwa daga sama. Duk da bata da yawan magana amma tana masifar son kananan yara, musamman jarirai zuwa 4years haka, ko magana sukayi sai taji dadi, shiyasa take son kaninta Marwan ba kuma tajin komai idan Mama ta sakata aikin sa.
Daukar number aunty bilkin tayi, ta kirata tayi mata murna sosai, suna wayar kiran Abba ya shigo, ta katse na Aunty Bilkin ta daga nasa suka gaisa, anan yake fad’a mata labarin haihuwar ta nuna kamar bata sani ba tayi farin ciki sosai, bayan sun gama wayar ne ta kira Mamma take fad’a mata zuwan su, amma bata san ko a yau din zasu iso ba ko sai gobe dai, murna tana jiyo su Amaan ta wayar kamar zasu shigo ciki saboda karadin su.
***Tana idar da sallar la’asar sai gashi ya shigo, ba kayan da ya fita dasu bane a jikin sa, wasu ne daban da sukayi mata kama da sababbin da ba’a taba sakasu ba, gaishe shi tayi a ladabce tana daga kan sallayar, ya amsa yana zama, yanayin sa ya nuna a gajiye yake, sai ta tashi ta ninke sallayar ta ajiye ta nufi kitchen ta dauko masa ruwa da soft drink, akan tray ta doro ta dawo falon ta ajiye masa tana rissinawa, saurin tayata yayi yana hadawa da hannun ta da tray din, sukayi dariya a tare ta zauna a gefen sa tana zuba masa ruwan. Karba yayi yasha, sosai saboda tunda ya fita be saka komai a cikin sa ba, gashi sam baya jin yunwa so yake kawai su tafi.
“Ga abinci akan dinning ko na kawo maka nan?”
“Waye yayi?”
“Nice.”
“Owk zanci, amma ki zubo min a plate ba da yawa ba, sai ki taimaka min da fruit please,.”
“Ok.” Ta mike bayan ta karbi cup din ruwan ta ajiye, taje ta zubo masa abincin ta kawo ta koma ta yanko fruits din ta kawo, yana kwance ya mike kafafunsa, har sai data zauna a gaban abincin sannan ya sakko yana saka spoon din a gaban sa ya soma cin abincin hankalin sa a kwance, sosai yaci dan beyi tunanin zai ci kamar haka ba, sannan ya sha fruits din kadan, bayan ya gama yace
“Thank you…Abincin yayi dadi.”
Blushing tayi cikin jin dadin yabon da yayi mata, ta hau tattare kayan zata kwashe ya rik’e mata hannu
“Ki barshi yaran chan zasu gyara idan mun tafi.”
“Ai ba wahala, bari na kwashe kawai.”
Sakin hannun nata yayi, ta dauki tray daya, cikin takun da bata san tana dashi ba, ta shiga takawa zuwa kitchen din, kallon ta yake har ta kule kafin ya dawo hayyacin sa, yana kallo ya sake dawowa ta kwashe sauran ya sake bin steps din nata da kalllo, ba zai iya hakura ba, musamamn idan ciki ya dauka, ga kuma abunka da sabon angon da be san ya isa ba, tashi yayi har da dan saurin sa, ya sameta a kitchen din tana tattare dattin plates din, sam bata ji shigowar sa ba, sai ji tayi an rungume ta, ta baya. Ta juyo a dan tsorace kafin kamshin turaren sa ya mamaye ilahirin kitchen din.
Manne bayan su yayi waje daya, ya dora kansa saman gadon bayanta, ya shiga goga mata bayanta da kan nasa.
“Ba… Bari… Na karasa gyara kayan.”
“Barshi, ai dama ba aikinnki bane, ga aikin lada me yawa.”
Ya sake chusa kansa sosai, tsam ta dauke hannun ta, sanda taji hannun sa na yawo a daidai tsakiyar cikin ta, yana shafawa har zuwa kasan rigar ta, rik’e jikin kitchen cabinet din tayi dan ji tayi kamar zata fadi, Allah yaso ta dafe wajen. Daga ta yayi sama chak, ya wuce falon zuwa bedroom dinsu, ya dire ta yana mata murmushin mugunta, a matukar tsorace take dashi amma kuma ba zata hanashi ba, dan ba zai taba bata damar da zata hanashin, yabi ya kanainayeta da salon kaunar shi me tsayawa a makoshi!
Sai da suka bata lokaci sosai, dan har wani dan guntun bacci yayi bayan nan, da k’yar ta tashe shi yayi wanka ya shirya, suka fita a mota zuwa wajen Ammi, daga nan suka fice daga masarautar da magribar fari!
***
Tun bayan fitar sa bata tashi daga wajen da take ba, sai da taji yunwa na neman kai ta k’asa, ta tashi ta jawo ledar da ya bari ta cinye ragowar,tasha ruwa ta kwanta a wajen.
Har wajen takwas na dare Hajiyan bata dawo ba, turo dakin akayi, ta dago tana kallon sa, tashi tayi zaune da sauri tana kare jikin ta, murmushi yayi ya zauna a kusa da ita, ya ciro wayar sa a aljihu ya rik’e a hannun sa yace
“Zan kira miki Mama,dan ta kira tana son magana dake nace mata wayarki ce ta lalace, idan kika kuskura kika fad’a mata wani abu sai ranki ya baci.”
Banzan kallo tayi masa, ta warci wayar lokacin da taji tana ringing, bata jira Maman tayi magana ba ai tana jin ta daga ta rushe da kuka,
“Lafiya Zeenat, wannan kukan fa?” Tace a kidime tana saka handsfree dan Habib yaji shima
“Mama dan Allah kice wa Abba yayi hakuri na tuba, dan Allah!”
” Ki nutsu ki fad’a min abinda yake faruwa, menene?”
” Bana son auren nan Mama, dan Allah kizo ki tafi dani wallahi zan mutu!”