HEEDAYAH 10

ta bude kofar parlonsa ganin wuta a kashe ta gane ya kwanta, ta lallaba ta nufi daki tana tafiya a hankali, tana shiga duk da wutan a kashe yake
tasan yyi bacci ta tafi inda tasan yana ajiye wayarsa ta dauka ta fita daga dakin, bangarenta ta koma ta bude wayar ta shiga call log dinsa, Number
da aka yi saving da Great barrister taga last call dinsa, nan ta duba taga yana yawan kiran number, msg ta shiga tayi scrolling har xuwa farko,
hankalin ta ya fara kwanciya ganin kawai text ne da ya shafi aiki, a hankali ta fara gwalo ido bayan tayi nisa ganin salon message din ya fara
sauyawa har ta kai karshe, xufa ne ya karyo mata ta ajiye wayar ta rasa tunanin da xata yi, can ta dau wayarta ta kwashe number tas sannan tayi
dialing, sae da ya kusa katsewa aka daga, daga daya bangaren Mami tayi sallama, shiru Hajiya Maryam tayi xuciyar ta na bugawa jin muryar mace,
kawai ta katse ji tayi kamar ta daura hannu a ka tayi ta ihu, ta xauna gefen gado tana furta innalillahi, kallon wayarta tayi, sae kuma ta shiga
call log tayi dialing wani lamba, yana fara ring aka dauka, Ta hadiye abu da kyar tace “Sadiya wllh da gaske Barrister neman aure yake, Ashe da
gaske yake wllh, gashi ynxu na bincike wayarsa kaff har na samu lambar warce yake nema da aure, na shiga ukuna Sadiya, da yarinta ta ba a min
kishiya ba sai yanxu a kan wata shegiyar yar tsintuwa makauniya….” Ta fashe da matsanancin kuka tace “In dai Alhaji yyi auren nan ai tawa ta
kare, dariya xa ayi min a gari ki bani shawara don Allah kawata, wllh dariya makiyana xa su min” Hajiya Sadiya dake saurarenta baki bude tace “Aure
fa kika ce Maryam?? Ke sai ki yrda ki barsa yyi auren? Toh ynxu dai ae sai ki wanke kafarki mu tafi inda kike ikirarin bbu abinda xai kai ki”
Hajiya Maryam tace “Ina???” Hajiya Sadiya ta kyalkyale da dariya tace “Wa enda kike raina taimakonsu mana….” A fusace Hajiya Maryam tace “Allah
shi kiyaye, tun da can da kuruciyata ban ta6a xuwa ba sai ynxu a kan yar yarinyar da na haifa?? Yar cikina? Ni nan da kike gani na ishi kowa wllh,
Kuma muna nan dake auren nan baxae ta6a yiwuwa ba ni nasan me xan yi, ke dai kawai ki xo gobe don Allah, sae da safe” daga haka ta katse wayar, ta
kusa awa daya xaune kafin ta iya tashi ta mayar masa da wayarsa ta dawo dakinta, daren ranan bata yi baccin kirki ba, Wai ita barrister xai ma
kishiya sbda taki rike makauniya??? Tayi kwafa ta juya tana jiran dai gari ya waye. Mami na xaune tana ma Heedayah gyaran dogon gashinta dake ta
kyalli, yau ma dai bata je aikin ba don har lkcn bata samu wanda xai kulan mata da Heedayah ba, Farida kuwa na boko daga safe har 6, wayarta ne ya
fara ring ta dauka ta kai kunne, sallama aka yi mata daga daya bangaren ta amsa, Hajiya Maryam dake xaune dakinta da Hajiya Sadiya da wata kawarsu
Hajiya kyauta tace “Don Allah da barrister nake magana” Mami tace “Yes, wacece ke magana?” Hajiya Maryam ta gyara xama tace “Toh Barrister wata yar
matsala ce wllh ta taso mana muna neman lawyer, shine wani abokin aikina ya bani lambar ki, yyi assuring dina you can help…” Mami tace “Allah
sarki sai dai na dau hutu baxan yi aiki ba cikin satin nan gaba daya” Hajiya Maryam ta gwalo ido tace “Don Allah ki taimaka barrister, ya gaya min
irin kirkin ki da taimakon ki, ke kadai xaki iya rufa mana asiri kan lamarin nan, don Allah barrister ki dubi girman Allah ki sauraremu, wllh muna
cikin tashin hankali sosai” Mami tace “Kar ki damu malama xan hada ki da wani barrister, he is also good xama ki ji dadin nasa aikin fiye da nawa,
I can send you his number now” da sauri Hajiya Sadiya tayi ma Hajiya Maryam alamar tace mata to ta turo… Hajiya Maryam tace “Toh ngd Barrister,
Allah ya saka, ina jiran lambar” Mami tace “Kar ki damu, let me send you” daga hka ta katse wayar, cikin few seconds ta tura ma Hajiya Maryam
number Barrister Ahmad, Hajiya Maryam da ta ji kmr xuciyarta ya fashe cikin tashin hankali tace “Na shiga uku, kun ga lambar mijina ta turo min dai
koh???” Hajiya Sadiya tace “Toh sake kiranta” hannu na rawa ta sake kira, Hajiya Sadiya ta amshe wayar tace “Ki dubi girman Allah Barrister ki bamu
lkcn ki ki saurari matsalar mu, an ce mana ke ce maganin kukan mu, wllh ko nawa kika bukata xa mu biyaki domin Allah ki taimake mu…” Da mamaki
Mami tace “Wnn barristern da na tura maki numbersa ya ma fini iya aiki, xae saurare ku fiye da ynda ni xan saurare ku” da kyar da kyar suka shawo
kan Mami kan ta amshi case dinsu, Mami ta girgixa kai tace “Gaskiya baxan fita gidana ba ynxu, sae dai ko ke ki xo ki sameni” Hajiya Maryam tace
“Wnn ae ba matsala bane, bari in taho ynxu ma, Allah ya kara girma da daukaka Barrister, ki turo min address din plss” Mami tace “Ameen, xan tura
maki ynxu” daga hka ta katse wayar, ta tura address din nata, Hajiya Maryam tayi wani murmushi ta mike ta dau mayafi da Makullin mota jikinta har
wani 6ari yake tace “Ku mu je” fita duk suka yi suka bar gidan a motarta. Gane gidan Hajiya Rahinah bai masu wahala ba, suka yi parking a waje
bayan sun sanar ma Mai gadi Hajiya Rahinah suke nema kuma ta san da xuwansu ya bar su suka shiga cikin gidan. Har entrance din shiga gidan suka
nufa suka tsaya, Hajiya Sadiya ta danna bell, Mami da ta saka Heedayah gaba tana mata tambayoyin ynda aka yi har ta fito gida…. exactly labarin
da Heedayah ta bada a station ta sake ba Mami, ta kare da cewa sai taji ana tafiya da ita a bicycle kawai sai ya wuce ya bar ta bai kai ta gun
Amminta ba kuma, tana fadin haka ta fara hawaye, Mami dake ta naxarin d’an labarin ta gane daga all indication kidnapping yarinyar aka yi sai kuma
Allah ya kubutar da ita, mikewa tayi jin an sake danna bell for the third time ta nufi kofa ta bude tana kallonsu Hajiya Maryam, Hajiya Maryam ta
kirkiro murmushi tace “Sannu fatan ke ce barristern?” Mami tace “Oh, okay ga kujeru can bari in fito yanxu, ku jirani a can” Hajiya Maryam ta saka
kai ta raba ta gefenta ta shiga ciki, tace “A’a xai fi daga cikin dai barrister, tonon asiri ai ba dadi” sauran ma duk suka shige ta gefenta,
kallonsu Mami tayi da d’an mamaki, Hajiya Maryam ta isa tsakiyar parlon tana kallon Heedayah da wani expression, sauran kawayenta ma duk suka tsaya
kusa da ita suna kallon Heedayar, Kasancewar Mami lawyerr yasa lkci daya ta gane abinda ya kawo matan nn gidanta ba abinda suka ce bane, Hajiya
Maryam tace “Toh kinyi tsaye bakin kofa ae sai ki karaso ki ji case din mu koh barrister?” Heedayah dake xaune saman kujera da apple a hannunta ta
mike da sauri don in dai ta ta6a jin murya to baya ta6a bacewa a sense of hearing dinta, ko da kuwa an dau lkci sosai sai ta gane muryar duk inda
taji, Mami ta karaso parlon tace “Bana bukatar jin case din ku, domin bana hulda da Yan tasha, ku kai case din ku wani wurin, and ku fitar min a
gida immediately now….” Hajiya Maryam tayi wani dariyar rainin hankali tace “Koh?? To sai ki fitar da mu ta karfi Mai gida, bari ki ji….. ba
barrister ba, ko judge ce ke na xo ne in yankar maki lafiyayyen wani ki fita hanyar mijina Barrister Ahmad, shi ba gantalalle bane irin ki, kin
gama xaga duniya kinyi yawon karuwancinki shine xaki wani makale masa ya aure ki sbda baki da tunani ko? To wllh kin yi kadan, mijina ba sa’an