HEEDAYAH 11

Tun da Hajiya Maryam suka dawo gida da kawayenta take kuka kamar ranta xai fita, ji take kamar ta bude ido taga cewar duk mafarki take, ya xa ayi
Barrister ya mata kishiya bata mutu ba?? Hajiya kyauta tace “Ke Maryam bari ki ji in gaya maki, idan xaki share hawayen ki ki san nayi ki share,
don 6ata lkcn ki kawai kike, wllh wannan kukan baxai fisshe ki ba, wajen nan dai da baki son xuwa dolen ki nan xa aje da ke yau a san nayi, don wnn
mata ni dai da kamar wuya mijin ki ya fasa aurenta duk haukan ki kuwa, na farko in dai kyau ne baxa ki nuna mata komai ba, ke diplomar ma da ya
kika kare? Ita kuwa lawyer ce fa me xaman kanta, kinga kenan ta kure karatu, ga shi da gani dai kin san ba cikin wahala take ba tana da kudin ta,
ke dake buga buga ki raruma gun miji fa?? ni wllh ba karamin kwarjini matar ta min ba ma, da ba ku fito ba dama ni wucewata xan yi kar ta sa a
daure mu kamar yanda tace” Hajiya Maryam ta katse ta a fusace tace “Ni fa da ku ke gani nan babu abinda ya isa kai ni gun malami a duniyar nan, ku
dai ku bar ni inyi ta kai na kawai idan baxa ku bani shawara ba, ni kadai raina na ishi kowa, wllh karuwar nan baxata shigo min gida a matsayin
kishiya ba, muna nan da ku kuma xa ku ce na fada, ita kuma wnn makauniyar dama sai dai ta kara shiga duniya wani ya tsince ta a wani garin amma ba
mijina ba….” Tana kai wa nan ta mike ta dau gyalenta tana share idonta, Hajiya Sadiya tayi wani dariya tana kallon kyauta tace “Bar ta, xata dawo
ta same mu ne ai” Ficewa Hajiya Maryam tayi daga dakin rike da makullin motar ta….. Direct gidan Dr Umar ta nufa, yau dai ko shiga bangaren matan
gidan bata yi ba ta nufi gun kaka, da sallama ta bude kofar parlon kaka dake uwar daka ta fito da sauri tana cewa “huuu Ko waye don Allah ya share
kafarsa ga tsumma na ajiye bakin kofa, wllh kazamai ne matan gidan ko sharan kirki basa yi a makeken parlon nan nasu sai a tattako a xo a yasar min
a nawa parlon….” Hajiya Maryam ta dinga goge kafarta a tsummar kamar an aikota, kaka tace “Aa Maryam daga ina haka da sassafe kuma” Ta karasa
cikin parlon ta xauna kasa cikin sanyin murya tace “Daga gida kaka, ina kwana” Kaka ta xauna tace “Lafiya dai naga idonki a kukkumbure ko Balaraba
ce ta rasu??” Ta fashe da matsanancin kuka tace “Ba lafiya ba wllh kaka….” Kaka tace “Ikon Allah me ke faruwa Kuma? Ni dai jiya Amadu ya shigo
min da rana wai ya xo gaisheni a nan kuma yake ce min wai aure xai kara har ya samu matar yar kaduna ce, ni dai nace masa ba ruwana, ana xaune
lafiya fitina ya shigo ciki, to daga haka ni bai ce min ga abinda ke faruwa a gidansa ba….” Cikin kuka sosai Mumy tace “Abinda ya kawo ni kenan
ma kaka, wai aure fa xai kara….” Kaka ta saki salati tana tafe hannu tace “Ohh ni na ga abinda ya isheni ni Rahamar ubangiji, me Amadu ke nema a
duniya da xai kara aure ana xaune qlau, ni dai yana gaya min ce mashi nayi ba ruwana, don bn san kan xancen ba….” Mumy ta share idonta tace “Idan
ma sbda wnn baiwar Allahn ce ya kawota kawai xan riketa na amince” iyakar wnn furucin da Mumy tayi bakinta, don kuwa ta sha alwashin ko an fasa
auren aka kawo mata Heedayah sai ta sake lulawa da ita wani duniyar daban, duniyar ma na kauye, can xata sa aje a wurgar da ita don ma kada
mistakenly wani me rufin asiri ya dauketa har ya taimaka mata, a yanxu dai duniya bbu wanda taji tana tsana kamar wnn yar yarinyar, har ta mance
rabon ta xubda hawaye ta shiga tashin hankali da xai hanata bacci sai a dalilin Heedayah, Kaka tace “Aa ni ya kawo min ita ma nan kawai xan riketa,
kar a ja maki kaffara kina xaman xamanki, dama bbu me min wanke wanke da shara tsigalallun yaran nan duk ba kulasu nake ba ta kaina nake” Mumy tace
“Makauniya ce fa kaka” kaka tace “To makafi basa wanke wanke da shara aka ce maki Maryam, ai dai naga ba kuturwa bace, sai in kada mata kumfar in
sa mata ruwan dauraya in ajiye mata kwanukan in xaunar da ita ta wanke min su tass” Mumy tace “Aa kaka wahala kawai xata baki, ni din dai xan
riketa, ai d’a na kowa ne” Kaka tace “Atoh dai, ki kwantar da hankalin ki kawai, bbu wani xancen kara aure in dai da raina tunda xaki riketa, to
idan ba toxarci Amadu ke son mana ba meye kuma karin aure ana xaune kalau, wannan ne kuma bai haifu ba gaskiya don baxan yrda ba” Mumy taji
hankalinta ya d’an kwanta, tana share idonta tace “Toh shkkn kaka nagode” Kaka tace “Haba godiyar me kuma, ai yi ma kai ne, yanxu shawarar da xan
baki a nan shine ki dau kayan ki kala daya ko biyu ki tafi gidanku, idan ba haka kika yi ba Amadu baxai dawo hankalinsa ba, ki tafi da fitsararrun
‘ya yan nan naki ki bar masa gidan ba kowa sae kujerunsa da tv, nan xaki ga ya shiga taitayinsa wllh, kaddai ki gaya ma wnn dunkum din d’an naki
kudurin ki don wllh hana ki xai yi ya cuce ki, ki bar masu gidan shi da ubansa kawai” Mumy da ke kallon kaka tana jinjina shawarar ta a ranta, tayi
murmushi tace “Gaskiya ne kaka, hakan xan yi in sha Allahu ina komawa kuwa” Kaka tace “Atoh maxa tashi ki tafi tun yanxu ki hada hada kayan, ai mu
xamaninmu haka muke yi, idan miji ya musguna maka ka hada kayanka ka bar masa gidan sa, xo ki ga yanda hankalinsa xai tashi kuwa….” Mumy ta mike
tace “Toh sai anjima kaka, nagode sosai, Allah ya kara girma, sai mun yi waya” daga haka ta fita, kaka ta bi ta da kallo har ta rufe kofa sannan ta
ta6e baki ta juya ta koma cikin dakinta tana cewa “To ai idan Amadu ya fasa auren nan ma ni sai naji dalili wllh, da kaina xan kai sadakin auren,
huuu wai ba kunya ba tsoron Allah matar da ke bari na da yunwa me saka min nama tsoka daya ce wannan fa jama’ah, Ehh lallai duniya ya lalace…..”
Da yammacin ranan Abba ya tafi gidan Barrister Rahinah don sake tabbatar da abinda ta gaya masa a waya da safe, nan ta nuna masa she is serious, ko
da wasa bata sanar masa cewar Hajiya Maryam ta xo gidanta ba, yana murmushi yace “Toh nagode Rahinah, in sha Allah gobe xa mu je can gun kawun
ki…” Mami tace “Allah ya kai mu….” Basu wani jima ba ta koma cikin gida don tace masa girki take, shi kuma ya wuce. Mumy na komawa gida dama ta
hada kayanta ynda Kaka tace mata, ta hada har da na su Khadijah da Rabi’ah ta bar gidan, makarantar su ta fara biyawa ta sanar masu inda xasu
sameta idan an tashi sannan ta wuce gidan kanwar Mahaifiyarta dake nan kaduna. Mami ce xaune study area dinta tana kallon files din gabanta, gaba
daya mood dinta isn’t okay, ta kasa gane ko she is making the right decision marrying barrister, har xuciyarta tana son taimakon Heedayah amma ba
irin taimakon da xai kai ta ga aure ba at this stage, ta jinginar da kanta da kujera tana tunanin ta ina xata fara sanar ma yaranta wannan xance me
girma, amma kuma ai idan bata Aure Barrister ba ta 6ar matarsa ta ci bulus kenan, ta shigo har gida ta yi mata cin mutunci sannan ta bar ta haka
nan, muryar junaid taji yace “Mami aiki kike?” Ta daga kai da sauri ta kallesa don bata ji shigowansa ba ma, ta mayar da glass din da ta sakko
idonta tace “Sure, ka shigo kenan” yace “Nayi sallama naji shiru” ya ja kujera ya xauna yace “Mami this two days naga kamar kina da damuwa, meye
matsalar ki gaya min” shiru tayi kuma bata daga kai ta kallesa ba, yace “Talk to me Mami” ta sauke ajiyar xuciya tace “Junaid barrister ne ya xo