HEEDAYAH 11

min da xancen da ya saka ni cikin damuwa kwarai, I don’t know I am really confuse junaid….” Yana kallonta sosai yace “Me ya faru Mami?” Ta kuma
yin shiru, bayan few seconds taga bbu wani amfanin boye boye kuma, nan ta sanar ma d’an nata intention din Barrister Ahmad a kanta, junaid bai iya
ya ce komai ba na kusan second talatin, can dai yyi gathering courage ba tare da ya kalleta ba yace “Toh, idan hankalin ki ya kwanta da hakan Mami,
Allah ya sa shine mafi alkhairi a gare mu baki daya” kallonsa kawai take bata ce komai ba, ya mike yace “Na xo daukan system dina ne” daga haka ya
wuce sama ta bi sa da ido, dakin Farida ya bude, ya ga Heedayah kwance edge din gadon tana bacci, riga ne da wando jikinta kamar dai ‘yar turawa,
he wondered if she is neva tired of sleeping, karasawa cikin dakin yyi walking slowly ya isa kusa da gadon yana kallonta, a hankali ya mayar da ita
tsakiyar gadon ya gyara mata dogon gashinta dake rufe idonta, jin an bude kofar dakin ya mike tsaye da sauri, kafin Mami tace komai yace “A gefen
gadon na sameta….” Mami ta gyada masa kai kawai, ya juya ya fita dakin…. Da daddare Barrister ya tafi gidan Yayansa, bayan sun gaisa da kaka
yace “Na je can gida na tarar Maryam ta kwashe yara sun bar gidan Baaba” Kaka tace “Kila ganin gida taje….” Shiru yyi yana kallon mahaifiyar
tasa, kaka tace “Toh ina dama xata je idan ba ganin gida ba, ai ta kwan biyu bata je ba, kaga kai kuma kafin ta dawo sai amaryarka tayi kokari ta
tare xuwa nan da ranan juma’ah tunda yau talata, wannan makeken bangaren da nake sauka sai ka sa a gyara ma amaryar ayi fenti da komai da komai
kawai, ita kuma Maryam ban ce ka kirata ba balle kace xaka mata fada, uwarta taje gani….” shigowar Baffa ya sa Kaka tayi gum, ta sauya xancenta.
Ranan juma’ah aka daura auren Barrister Ahmad da Barrister Rahinah, though they did it in a confidential way, bbu wani gayya, duk abubuwan nan dake
faruwa Hajiya Maryam na can ta lula xuwa gidan wata childhood frnd dinta a Zaria tare da su Rabi’ah wai kar barrister ya biyota gidan kanwar
mamarta, ita a dole sai ta basa wahala, Shuraim kadai take kira don samun update, sai dai me? Shi ma bai san da auren ba sai a ranan juma’ar, shi
ma kuma da asuba Abban nasa ya sanar masa a masallaci da suka hadu, he was so shock ya ma kasa cewa Abban nasa komai, haka nan Abba ya wuce ya bar
sa wajen a tsaye, ita kanta Hajiya Amina mum din su Sudais ranan ta ji xancen daurin auren daga bakin Baffa da safe, nan tayi ta kiran Hajiya
Maryam amma wayarta a kashe, bata fasa kira ba har sai da aka daura wnn aure amma bata samu Mumy ba….. Washegarin ranan da ya kasance Saturday
Mami xata koma can gidan Barrister Ahmad, shopping suka tafi tare da Heedayah, Farida da First daughter dinta Amira dake aure a Abuja, su dai sun
yi farin ciki da auren mahaifiyar tasu kilan hakan ya rage mata damuwa sosai, don duk sun san barrister Ahmad, A cikin mota Amira tace “Kinga yanxu
Mami sai ki bar ni mu tafi da Farida sai ta dinga xuwa maki hutu kawai ko” Mami dake ta tunanin makomar autar tata tun bayan da aka daura aure don
bata ta6a jin tafiya da ita gidan barrister ba, baxai ma yiwu bane, ta kalli Amira tace “Alright dear” Amira na dariya tace “Kinga cikin ruwan
sanyi kin bani ita” Babban shopping mall Mami tayi parking suka fita, Amira na rike da hannun Heedayah suka shiga ciki gaba daya, shopping sosai
Mami tayi, yaranta na taya ta, Mami da ta lura Heedayah ta gaji da jan ta da ake ta yi, duk ta yi wani laushi, kana ganinta kasan ko kadan bata
sa6a da wahala ba koma wani iri, Mami tayi murmushi ta samu kujera nan kusa da counter ta xaunar da ita sannan ta koma gun yaranta, a kan idon wani
mutumi dake tsaye shelf din turare yana diba, ya cire glasses dinsa yana kallon Heedayah sannan ya kalli Mami da ta sha corner xuwa gun su
Amira….