Uncategorized

HEEDAYAH 12

ta duka xata daga Heedayah, Kaka tayi saurin cewa “Kai ku ji mata ba yini ku ka kawota ta min ba dama, kinsan ynda muke da ita ne? D’a na fa ya 

tsinto ta tana galantoyi a titi” Mami ta mike tace “To shkkn mama, sae anjima” kaka tace “Ko anjima da daddare ba sai ki xo ki tafi da ita ba” Abba 

tuni ya fita, Mami tayi ma kaka sallama ita ma ta fita. Kaka na kallon Heedayah da jikinta yyi sanyi jin an tafi an barta tace “To sun baki abincin 

ma kuwa, don naga Amadu har wani rawa kansa yake shi a dole yyi amarya” Heedayah ta gyada mata kai kawai, kaka ta mike tace “Ni dai ba ruwana don 

ba barinsu Allah xai yi ba idan suka bar ki da yunwa” cup ta dauko a inda take jera su ta dawo ta bude flask ta debi ruwan xafi, shayi me kauri 

sosai ta hada a cup din ta bude bread ta dau slice biyu ta daura a plate ta debo dambun nama da tsoka uku na nama ta watsa kan plate din ta ajiye 

ma Heedayah a gabanta tace “gashi nan maxa ki cinye ki bani kwanuka na, duk cikin ki ya hade da bayanki kice min kin koshi” tana fadin haka ta mike 

ta koma daki tana cewa “Haka matar ta xo tsiya tsiya ba komai, kamar ta baxata kawo d’an lemonta ko ma dai turare ba tace gashi kaka” tabe baki 

tayi ta ci gaba da linkin da take. Heedayah dae na xaune da shayi a gabanta don ba yunwa take ji ba, ita din ba wata me cin abinci bace sosai, bude 

kofar parlon aka yi a hankali, Sudais ya shigo, direct inda ya hango turarensa da kaka ta dauke jiya ya nufa don dama abinda ya kawo sa kenan, ya 

duka xai dauka kenan ya ga Heedayah dake xaune, mikewa yyi tsaye yana kallonta sannan ya nufeta ya duka gabanta, she looks so sad, shi dai ya kasa 

yarda da abinda Shuraim yace masa wai fararen idon nan nata basa gani, hannu ya kai har kusa da idon ya ga bata motsa ba, ya sauke hannunsa a 

hankali, murya can kasa yace “How are you?” Juyawa tayi da sauri jin murya kusa da ita, Amma kuma tayi shiru tayi tana kallonsa directly in the 

eye, yace “How are you?” a hankali tace “Fine” yace “To ki sha shayin ki….” Tace “Na koshi” hannu ya sa aljihunsa ya fiddo chocolate biyu ya kamo 

hannunta yace “Toh ga chocolate ki sha, ko in bude maki?” Ta gyada masa kai, ya bude guda daya ya saka mata a hannunta, xai yi magana sae ga kaka 

ta fito, tana ganinsa tace “Ni dai wllh ba ruwana idan baki na ya bi ka Aliyu, nace kar ka sake xuwa min nan xan ja Allah ya isa, Kuma wllh na ja a 

raina tun ranan” Yace “Tunda ke ba Baffa bace kuma ba Umma bace me xai dameni, Allah ya isan ki iyakarsa lebenki” ko kadan bata ma san me yake cewa 

ba, don bude baki tayi kawai tana kallon shayin gaban Heedayah, can tace “Naga ikon Allah, Ke baki sha shayin bne har ynxu kika bar shi a 

walakance?” Heedayah ta marairaice tace “Na koshi” kaka tace “Amma ke dai muguwa ce, kina kallo ina hada shayi duk na yi barna da madarata da 

banvita kiyi shiru ki kyaleni sbda mugunta??” Sudais yace “To da idon ki taga kina hada shayin ta maki shiru kaka” Kaka tace “Ba ruwana da wnn, 

ance maka haka Allah ya bar su, duk suna sane da komai ke faruwa a inda suke, kawai tayi niyyar walakanta ni ne, amma tana sane lkcn da nake kada 

shayin” Sudais ya dau cup din shayin yace “Toh bari in Shan…..” Kaka tace “Haram…. Ban baka ba har xuciyata, Amadu ne ya siyo min kayan shayin 

ba Umaru ba” dariya yyi yace “Toh shi din ba Abbana bne, Kuma ae dama abincin Haram dadi ne da shi” kaka ta fashe da kuka ta nemi kujera ta xauna, 

sai da ya shanye shayin ya ajiye mata cup yyi ficewarsa….. Hajiya Hauwa ce ta kawo abincin rana bayan azahar, Heedayah na xaune kan darduman da 

Kaka ta shimfida mata wai tayi sllh, Hajiya Hauwa da suke ce ma Aunty a gidan, ta gaida kaka tace “Ga abinci kaka” kaka tace “Toh yau dai kun bar 

yunwar ta gigitani gaskiya, Amma bbu komai Allah yyi albarka, amma fa ni dai nasa yar nan tayi sllh bn san ko ba musulma bace” dariya sosai Aunty 

tayi tace “Musulma ce mana kaka” kaka tace “Atohh naga dae ta iya alwalar…” Aunty tayi murmushi tana kallon Heedayah ta isa kusa da ita ta kai 

hannu kanta tace “Bari in kawo maki naki abincin kin ji daughter?” Heedayah ta gyada mata kai kawai, Aunty ta juya ta fita, sae ga ta ta dawo da 

plate din shinkafa da miya da salad a gefe sae neman kaza ta ajiye gaban Heedayah tace “Ki jira ya huce sae ki ci, kaka xata baki ruwa idan kika 

ci” daga haka ta fita, kaka na kallon Heedayah tace “To me kika yi ma iyayen naki suka sallama ma duniya ke d’a na ya kwaso ki?” Heedayah dai bata 

ce komai ba don Hausan ya mata girma, kaka ta tabe baki tace “Toh, Allah shi yasan dai dai, mu dai gashi mun kwaso ki bbu dangin iya balle na 

Baaba, muna neman lada wajen Allah” Bayan la’asar Kaka ta kwashe Yan wanke wankenta ta bude wani kofa da xae fitar da ita bayan gidan, inda aka yi 

mata pamponta ta kada kumfa ta ajiye ruwan dauraya ta dawo ta daga Heedayah dake bacci tace “Taso ke ma a dinga cin amfanin ki ba wai ki ci ki sha 

kiyi kashi kiyi ta bacci ba, tun xuwan ki kike bacci” a haka ta kai ta bakin tap ta xaunar da ita kan kujeran tsugunno dake wajen tace “Maxa kiyi 

ta lalubawa kina daukan kwanukan kina wankewa ga ruwa a gefen ki, mace kike gidan wani kuma xa ki” daga haka kaka ta wuce ciki ta bar ta, tunda 

Heedayah take bata ta6a wanke wanke ba, bata ma san meye shi ba, hka ta dinga daukan kwanukan tana tsoma su cikin ruwa tana fitarwa, har taji bbu 

wani nan kuwa duk suna gefe daya a ajiye, mikewa tayi pink wandon jikinta da ya wuce gwiwarta a jike jagab, kofa taji an bude a tunaninta kaka ce 

tace “Na gama” duk a tsorace take hannunta rike da plate biyu da cup daya, Shuraim ne tsaye bakin kofar alamar shigowansa kenan gidan a tunaninsa 

kaka ce backyard din, hannu Heedayah ta sa tana laluba wajen xata wuce ta ci tuntube da kujeran da ta tashi daga kai, cikin few seconds komai ya 

faru, duk da effort din Shuraim kuma jikinsa ta fada hakan bai hanata buge kneels dinta a kasa ba, shirun da Shuraim ya ji tayi ya sa yyi saurin 

daga kanta yana kallon fuskarta, sae a sannan ta wara ido ta fasa wani ihu da ya raxana shi, lkci daya ta kankamesa tana cewa wayyo kafanaa, kaka 

ta saki flask din ruwan xafin hannunta ta taho a guje tana cewa “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, yar mutane ta mutu a gidana, na shiga uku na 

banu, me xance ma Amadu” Shuraim ya kalli kafan nata yana kokarin dagata ta rirrikesa cikin kuka tana cewa “Wayyo a kai ni wajen Abba, wayyo Abba 

ya xo….” kin fitowa kaka tayi ta dinga lekowa jikinta na rawa, Shuraim ya hade rai, ganin Heedayah ta ki tsayawa yace “Baxa ki tsaya ba sae na 

mare ki?” Kuka sosai take yi tace “Baxan iya ba kafan yana min ciwo…” Daukarta yyi ya shiga parlon kaka da ita ya kwantar da ita saman kujera 

yana kallon kafar, cikin rawar murya Kaka tace “Kaddai karyewa kafar yyi Ali?” Ta gefen ido Shuraim ya kalleta kafin ya mike yace “Ni na sani…” 

Kofa ya nufa zai fita ta cafkosa ta fashe da kuka tace “Don Allah ka rufa min asiri ka duba mata kafar tun da kai ma likita ne, Kar Amadu ya 

kullaceni, wllh sai in iya tattara kayana in gudu ba ruwana da bacin ran Amadu, ya takarkare ya tsinto yarinya kuma ace a gidana ta karye….” 

Heedayah dai sai kuka take tana kiran Abba, kaka ta xauna kasa ta saki matsanancin kuka tace “Ka ji algungumar wai Abba ko??” Shuraim ya hade rai 

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button