Uncategorized

HEEDAYAH 13

fito duk ta yamutsa xanin gadon” daga haka ta juya ta koma ciki, Junaid ya ajiye ledan hannunsa ya koma inda Heedayah take tace “Me yasa ba ki cin 

abincin?” Kamar jira take ta fashe da kuka a hankali tace “Ni ban iya ci ba” xaro ido yyi yana kallon tuwo da assorted miyar veg din gabanta, yace 

“To me xa ki ci?” Tace “I want to take tea” ya kara wara ido, bude kofar parlon aka yi ya juya, wani dogon matashi ne just his mate ya shigo 

parlon, sanye yake da 3 qtr da polo, Shuraim ya karasa cikin parlon waving at him without much interest yyi xaman sa kan kujera, kaka ta leko don 

ganin waye, tana ganin Shuraim ta hade rai sosai tace “Dawowa kayi ka kashe mu lkcn mu bai yi ba ko ya aka yi??” Dauke idonsa yyi daga kallonta ya 

fiddo wayarsa ya maida dubansa kai, kaka tace “To idan ma mun mutu bayan ka tafi Junaidu na shaida, ehe” daga haka ta koma ciki, ba a dau wani lkci 

ba sai ga ta tafito tana washe baki tace “Sannu Junaidu bari in kawo maka abincin na ka” Junaid yayi murmushi yace “To ngd” a gabansa ta jera masa 

abincin, shi dai bai ce komai ba duk da a koshe yake, xata wuce ta gaban Shuraim kamar ana forcing dinsa yace “Ina yini” tayi kamar bata ji sa ba, 

sai ga ta ta dawo tace “Toh ka ci abincin mana Junaidu” Junaid na murmushi yace “Toh” sauka yyi ya bude warmer din ya ga shinkafa ce da lafiyayyen 

Miya da ya ji nama, sai ga wani bowl da aka yanyanka kayan ganye, kallon Heedayah yyi da plate din tuwon gabanta, sannan ya kalli kaka dake kokarin 

share bakin kofar ta, matsawa yyi kusa da Heedayah murya can kasa yace “Xa ki ci shinkafa?” Da sauri ta gyada masa kai, Ta gefen ido Shuraim ke 

kallonsu, Junaid ya dau plate ya diba shinkafar da Miya da nama, ya dauke tuwon da ta fara kacalcalawa ya ajiye mata shinkafar, a kan idon kaka da 

ta saki tsintsiyar hannunta ta mike da sauri tace “La la la kar ka bata, gantalalliya ce wai bata iya cin tuwo ba, to uwar me xa a bata, ko gidan 

Amadun da ya tsinto ta ma ai ana tuwo balle nan, mu ba wasu masu kudi bane da xata ce bata cin tuwo har da hawayenta, shinkafar kuma iya cikinka 

nayi nima tuwon na ci, idan aka ce xa a biyeta ai sai ta lalace Allah ya tambayemu….” Heedayah dai sai xare ido take kamar xata yi kuka ta dafe 

plate din shinkafar don kar ma a dauke, Junaid yace “Kaka ni na fi son tuwon ne shi yasa” Kaka ta saki baki tace “Allah?” Yana murmushi yace “Ehh” 

ta tabe baki tace “Toh Allah ya raba bawa da wahala don ko na wahala gun neman shinkafar nan da miya, to ai sai ka ci tuwon ita kuma sai ta karata 

da shinkafar duk da ni dai ban bata ba, kaji min yarinya dai da mugun hali” tuni Heedayah ta fara cin shinkafar, idan akwai abinda junaid ya fi 

tsana rayuwarsa tuwo, sai kallon tuwon yake yana tunanin ta wani side din xai fara ci, da cokali ya debi tuwon ya kai baki yana ci da kyar, mikewa 

Shuraim yyi ya maida wayarsa aljihu ya nufi kofa ya bi ta gefen kaka ya fita, kaka ta mike tace “Ka dai ga ko? Mugun hali har tsiro sai da yyi a 

jikinsa, tirrr Amadu dai bai yi sa’a ba ya haifi jaraban duniya kawai, to ba gwara min Sudess ba ni dai” sake bin kofar Junaid yyi da kallo don ya 

dai ga Shuraim na kama da Abba amma bai yi tunanin son dinsa bane. Hajiya Maryam ce xaune parlonta kai kace rasuwa aka yi mata, duk ta fita 

hayyacinta, idon nan nata duk a kumbure ga su Hajiya Sadiya, Hajiya kyauta, har da Hajiya Amina da dai kawayenta gaba daya sun kusa 7 sai Yan 

uwanta uku, Hajiya Zaliha tace “Ban da ma dodewar tunani da kwakwalwa ke har kya dau shawarar wannan tsohuwar da shekara da shekara kuna dauki ba 

dadi da ita, to duk gari kowa cewa yake ita ce ma karfin auren barristern, ita ta matso da auren ma aka yi da wuri wuri” Mumy ta fashe da 

matsanancin kukan takaici amma ta kasa cewa komai, Hajiya safara’u tace “Toh Kuma meyasa duk tsawon lkcn nan kika ki kunna waya fisabilillahi” 

cikin rawar murya Mumy tace “Ita ta sa in kashe wayar wai sai na basa wahala kafin ya gano inda nake da yara, kuma kusan kullum sai mun yi waya da 

ita, tayi ta shirga ni wai Ahmad na nan duk ya daga hankali ana ta nemana gari gari, har rahotu ya kai ma yan sanda, ko abincin kirki baya ci, da 

mun gama wayar kuma sai ta ce in kashe da sauri” Mutanen parlon suka kwashe da dariya ciki har da Hajiya Amina, Mumy ta hade rai tana bin su da 

kallo, Hajiya Sadiya na kyakyatawa tace “Ban ta6a ganin makiran tsohuwa irin matan nan ba, gaskiya ta sha ki da yawa, lkci daya ta rama duk 

abubuwan da kika dinga mata tana xaune gidan nan” Mumy ta mike tace “To bari ku ji wani abu, ba don ba ni da abinda xan iya yi bane kan tsinannen 

auren da barrister yyi ya sa nake kuka ko hankalina ya tashi, A’a kuka nake saboda takaicin da yarintata ba a min kishiya ba sai yanxu, kuka nake 

sbda boasting da na dinga yi cikin mutane Barrister baxai ta6a min kishiya ba, kuka nake sbda makircin da annamimiyar tsohuwar nan ta hada min, ita 

kuma wnn mata da tayi kuskuren auren mijina ina jiran shigowarta gidan nan, wllh sai ta gwammace bata ta6a sanin Barrister ba, ita kuma wnn yarinya 

da aka min kishiya ta dalilinta….” Wani murmushi Mumy tayi tace “Da farko xamanta gidan nan kirgagge ne, sannan kafin ta tafi sai na tabbatar da 

shaida xata bar gidan wanda har girmanta baxata manta ba, sannan a makantan ta xata tsaya har karshen rayuwarta, wllh wllh bana wani jin kishiyar 

da aka min kamar yanda nake jin yarinyar nan a rai na, ita ce sillar rugujewar duk wani farin ciki nawa….” Hajiya kyauta tace “Toh nan dai da 

kwana biyu xa su tare da uwar rikon tata, ke dai gashi kin samu an sauya maki komai na bangaren ki kamar ke ce amaryar, amma ni tunda nake ban taba 

ganin irin haka ba, anya ba aljana barrister ya kwaso ba me son ta tarwatsa maki gida, gashi ma tana kan yin haka tunda ta sa an rangada maki 

kishiya yar boko yar gayu” Mumy tace “Za mu ga wanda xai tarwatsa wani ni da ita, na fa ce maku ynxu ni ba ma da kishiyar xan goga ba….”

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button