Uncategorized

HEEDAYAH 3

 

3…..

Heedayah ta fi minti biyar a tsaye tana Shesshekar kuka, jin bbu alamar xai dawo ta fara tafiya a hankali tana yi ma kanta jagora da hannuwanta biyu, da tayi tafiya kadan sai ta tsaya, ihun da taji aka yi wajen ya sa ta tsaya a mugun tsorace, ji tayi kamar an hankadata da katon abu ta fadi kasa, tun tana jin surutun jama’an wajen sama sama har ta daina ji kwata kwata. A hankali Heedayah ta bude ido tana

laluba inda take kwance, muryar namiji taji a gefenta yana cewa “Alhamdulillah she is back (Ta farfado….)” Ya kamo hannunta yana mata sannu murmushi dauke fuskarsa, kanta da yyi mata nauyi kawai take gyadawa tana kokarin mikewa xaune, ya komar da ita ya kwantar yace “A’a bari likita ya xo ya duba ki, bari in kirasa, ina xuwa ynxu” ita dai kai kawai take gyadawa, ba a dau lkci ba sai ga mutumin ya dawo da likita, directly Heedayah ke kallon fuskar likitan, ya sakar mata lallausan murmushi wanda bata san ma yana yi ba, likitan ya xaunar da ita ya dafa goshinta yace “Ya jikin baby girl?” Kifta ido ta shiga yi tace “Where am I? (Ina ne nan?)” Yana murmurshi yace “Hospital dear, fatan dai babu inda yake maki ciwo” kanta ta nuna masa, yace “Xai daina in sha Allah, xa a baki magani yanxu” shi dai wanda ya kirawo likitan kallonsu kawai yake, A hankali tace “Xan yi fitsari” likitan ya saukar da ita kasa, yana nuna mata kofar bandaki, hannunsa ta kama, yace “Xa ki iya dear, walk gently now (Kiyi tafiya a hankali….)” kin motsawa tayi, sai kuma a hankali tace “I can’t see (Bana gani)” da mamaki likitan da Mutumin da ya kawo ta asibitin ke kallonta, likitan yace “Why? is the eyes paining you? Idanuwan suna maki ciwo ne” Ta girgixa masa kai yace “Toh yi tafiyar ki da kanki” ta rike hannunsa gam kamar xata yi kuka tace “Ae ni bana ganin hanyan” sosai hankalin likitan ya tashi, haka zalika Mutumin dake Ward din da ya mike shima yana kallonta, don gaba daya tunaninsu a lkcn ta dalilin accident din ne vision dinta ya samu matsala, Banda innalillahi wa Inna ilaihi raji’un bbu abinda Mutumin ke furtawa yana kallon Heedayah. Likitoci sun fi biyar a kan Heedayah, all trying to figure out where the problem is, ko wannensu na kokarin gano inda matsalar take amma abu ya ci tura, ita dai sai bin duk inda ta ji motsi take da manyan idanuwanta, duk da ba ganinsu take ba, daga karshe dai aka ba Mutumin da ya kawota shawara kawai ya kai ta asibitin ido, ba karamin tashi hankalin wannan mutumin yyi ba, haka dai ya biya bill din asibitin ya dau Heedayah xuwa asibitin ido dake nan cikin garin kano. Dai dai lkcn da suka shiga haraban asibitin motar optician din dake duba Heedayah tun da aka haifeta har kawo lkcn da aka yi referring dinsu india kuma na fita daga asibitin. Mutumin dake rike da hannun Heedayah bayan ya sauketa daga motar ya duka dai dai fuskarta cike da damuwa yace “Daga yaushe kike daina gani Little girl? What was the last thing u saw? Meye abu na karshe da kika gani?” Tayi shiru sai kuma tace “Nima ban sani ba” Damuwa ne sosai fuskarsa, yace “Toh daga ina kike jiya da magariba kuma ina xa ki? Where are ur parents? Ina iyayen ki” Shiru tayi, staring at him kamar tana ganinsa, nan ya shiga tantaman ganin da tace bata yi, ganin yanda take masa kallon cikin ido ya kai yatsunsa har kusa da idonta yaga bata rufe ba har sai da ya taba lashes dinta, kikkifta idon ta shiga yi, yace “ki min magana, Where are ur parent? Ina iyayenki” Ta girgixa kai tace “I don’t know, (Nima ban sani ba)” da mamaki yace “Baki san inda iyayenki suke ba, ina xa ki jiya?” Ta fashe da kuka tace “Nima ban sani ba, kawai an saka ni a mota aka wuce da ni, sai na ji an sake hawa da ni bicycle kuma ynxu ban san inda aka kawo ni aka ajiye ni ba” rasa abun cewa yyi yana kallonta, can dai yace “Ya sunan garin ku?” Tace “Abuja” ya xaro ido ganin dai a garin kano suke ynxu, yace “Ya sunan baban ki?” Tace “Abba” yace “Abba??? Mamarki fa?” Cikin rawar murya tace “Ammi” Innalillahi ya dinga nanatawa a ransa, sai kuma yace “Abuja ya sunan anguwan ku?” Tace “Abuja ne” mikewa yyi just as confused as she is, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna goma na safe, yana rike da hannunta yana mata jagora suka shiga asibitin, Ba su suka fito ba sai kusan Azhar after series of Diagnosis da ya tabbatar da she was born with the blindness, a haka aka haifeta, kuma tana stage din operation din karshe kenan wanda xa ayi mata idan ba ayi nasara ba she will remain blind till the end (Xata xauna a makauniyar ta har karshe…) Alhaji Ahmad na rike da hannun Heedayah xuwa gun motarsa a haraban asibitin, bai ta6a shiga rudani irin na ranan ba, to ina xai kai wannan yar baiwar Allahn, kara kallonta yyi yaga bata wuce autarsa Rabi’ah ba, yanxu ina xai samo iyayenta ko wani wanda ya santa??? Yanke shawarar kai ta police station kawai yayi, yasan su xa su san yanda xa su yi da ita, driving kawai yake absentmindedly ya ji Heedayah tace “Abba, yunwa nake ji” ya d’an kalleta yana ci gaba da tukinsa yace “Me xa ki ci?” Tace “Shayi da bredi da kwai” sake kallonta yyi sannan ya dauke kai, Mintuna kadan ya rage ya isa nearest Police station, sbda yunwan da tace tana ji ya dau wata hanyar daban xuwa wani restaurant, abinda ta ce take so ya sa a kawo mata, ya tabbatar shayin ba xafi sosai sannan ya bude mata bread din da kwai ya mika mata, ganin yanda take ta lalube lalube kar ta kwa6ar da shayin ya mike ya koma kusa da ita, feeding dinta yayi har ta ce ta koshi, Banda kallonta bbu abinda yake yi cike da tausayinta, Bai taba ganin irin haka shi dai ba, yar karamar yarinya da makanta, tace “Abba…” Ya shafa kanta yace “Daughter” murmushinta me kyau tayi tace “Thank you” Bai ce komai ba, Amma naxari me iri iri yake yi a ransa, bayan few seconds ya kalleta yace “Ya sunanki?” Tace “Heedayah” Ya lumshe ido ya bude yace “Heedayah baki san anguwan ku a Abuja ba? Ki tuna da kyau ki gaya min daughter” Tace “Abuja ne gidanmu” ya girgixa kai ya mike yace “Tashi” tashi tayi ya kama hannunta kasancewar ya biya bill din suka fita xuwa gun motarsa, bayan sun bar Restaurant din, ya dau hanyar police station, Yana rike da ita suka shiga ciki, Bai bata lkci ba bayan yayi report ya bar Heedayah tare da su don yana da meeting da xai shiga karfe daya kuma a ranan yake son barin garin kano, sai dai har ya isa inda xa shi hankalinsa ya ki kwanciya, gaba daya ya rasa sukuni…. Washegari karfe takwas a police station yayi ma Alhaji Ahmad to be sure an samu iyayen Heedayah duk da yasan da kyar hakan ya faru a rana daya kawai, Bayan sun gaisa da policemen dake wajen suka sanar masa an kai ta orphanage for the meantime, shiru yyi na few seconds kafin yace “Shikenan, nagode….” Wani police officer yace “We will try our best in sha Allah, an kuma riga da an fara broadcasting tun jiya, so hopefully she will get back to her parent soon, (xa mu yi bakin kokarin mu na ganin ta koma ga iyayenta)” Alhaji Ahmad yace “Allah ya sa hakan” Sallama yyi masu ya bar station din. Ammi dake xaune saman gado a dakin asibiti da take ta kai hannunta xuwa na Mahaifin Heedayah dake xaune gefenta sai dai yyi nisa tunanin da yake, juyawa yyi ya kalleta, hawayen da ke gefen idonta ya gangaro cikin sanyin murya tace “Muhammad pls let nothing happen to my daughter, plss nothing shud happen to Heedayah, (Kada wani abu ya sami Heedayah) ku dawo min da yarinya ta” Uncontrollably ta fara kuka, tun xuwansu asibiti kwana biyu kenan sai yau tayi magana, Alhaji Muhd ya na rike da hannunta trying his best to be strong yace “Nothing dear, I mean nothing will happen to our daughter, (Babu abinda xai sameta) in sha Allah, zata dawo garemu soon da izinin Allah, hukuma na bakin kokarinsu, ki kwantar da hankali don Allah” Kuka kawai take bata ce komai ba, she looks so weak, ya sake hannunta ya fita don kiran likita. Da yammacin ranan Alhaji Ahmad ya gama shirin komawa kaduna, sai da ya bar gida sannan yyi deciding kafin ya tafi ya fara xuwa orphanage da yan sandan suka ce masa an kai Heedayah, Bai yi wani wahalan shiga gidan marayun ba bayan ya nuna Identity dinsa, ya dinga bin yaran dake wasa a waje da kallo, lkci daya idonsa ya sauka kan Heedayah dake rakube can gefe ita kadai staring into space, hannunta rike da ledan biscuit, kallonta ya dinga yi kafin ya nufeta ya duka kusa da ita har sannan bai daina kallonta ba hawaye ne cike manyan idanuwanta, lkci daya ya ji jikinsa yyi sanyi sosai, ya dafa goshinta yace “Heedayah” Hannunsa ta kama kamar tana jiransa a lkcn, sai ta fashe da kuka tace “Abba” Ya jawota jikinsa yace “Why are you crying? (me yasa kike kuka” Cikin rawar murya tace “Suna min dariya bana gani, wata ta karbe min biscuit guda daya, Abba ka kai ni gida gun Ammina….” Bai ce komai ba, can ya mike yana rike da ita yace “Toh daina kuka” goge idonta tayi, yana rike da ita still ya tafi office din shugaban wajen, bayan sun gaisa yace “What are  the process before adoption of a child in here? (meye matakan bi kafin daukan yaro a gidan marayu)” Tana kallonsa tace “It’s a very long process mister, (Matakan suna da yawa gaskiya” yace “Alright…. I will be back in some minutes time (Xan dawo nan da wani lkci)” kuka Heedayah ta dinga yi sosai da ta gane tafiya xai kara yi ya bar ta, haka nan ya bar ta gun masu kula da marayun wajen ya wuce, police station ya koma. Asp ya ajiye pen din hannunsa yana kallon Alhaji Ahmad yace “So you mean kana son tafiya da ita har lkcn da Allah xai sa a samu iyayenta” Alhaji Ahmad yace “Yes exactly sir” Asp yace “Sai dai kasan da cewar you didn’t adopt her, duk lkcn da iyayenta suka bayyana xa a mayar masu da ita” Alhaji Ahmad yace “In sha Allah, Ni ma nafi son haka, and as I have said sbda health issues dinta yasa xan tafi da ita, she won’t cope in the orphanage, i will be dropping all necessary information kamar yanda ka bukata duk da ni ba bako bane a gun ka, idan ma baka san ni yanda ya kamata ba, na tabbata kasan Yayana ai” Murmushi Asp yyi yace “Sure, I am not doubting you Barrister, Allah ya taya ka riko har kafin Allah ya bayyanar da mahaifanta” Alhaji Ahmad yace “In sha Allah, nagode sosai for understanding me” Wani short note Asp din yyi a takarda yayi stamping sannan ya kira wani police officer ya koma orphanage din tare da Alhaji Ahmad don dauko Heedayah. Har sannan Heedayah na xaune inda Alhaji Ahmad ya bar ta tare da daya daga mai kula da su, sai dai mai kula da su din bata gun, ita kadai ce xaune gwanin ban tausayi, har sannan ta ki cin biscuit din, Bbu 6ata lkci aka basa ita ya bar orphanage din bayan ya sallami police officer din, he can see how happy Heedayah was bayan sun shiga mota, ganin tana ta kokarin bude biscuit din hannunta ya amsa ya bude mata ya mika mata, tace “Abba xaka maida ni gun Ammina da Abbana?” Ya shafa kanta yace “In sha Allah daughter” tayi murmushi sosai tana cin biscuit din hannunta, seat belt ya sa mata, yana kallon agogo dake nuna masa biyar saura yan Mintuna, ya gama addu’o’in da xai yi sannan ya dau hanyar fita kano xuwa garin kaduna…..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button