4...... Har suka shigo cikin garin kd wajajen karfe tara na dare bacci Heedayah take, slowly yake driving bayan ya shigo anguwar da gidansa yake, anguwar so silent ga fitilu ta ko ina da ya haska anguwar kamar da rana, bakin wani gate ya ja ya tsaya yyi horn, wanda hakan ya farkar da Heedayah, laluba motar ta shiga yi tace "Abba...." yana kallonta yace "I am here..." Bata kuma cewa komai ba dama kawai so take ta tabbatar bai bar ta bane, ya d'an yi murmushi ya ja motar xuwa cikin babban compound dake dauke da gida ginin duplex bayan Mai gadi ya bude masa gate da sauri, parking yyi a space din da aka tanadar domin parking a compound din, wani matashi ne da baxai wuce 28 ba ya fito daga cikin babban building din gidan, ya nufo parking space din, Alhaji Ahmad ya kashe motar ya bude ya fito, Matashin ya d'an risinar da kansa yace "Sannu da hanya Abba" Alhaji Ahmad yace "Yauwa sannu, but ka damu ka kirani tun jiya da kake min sannu da hanya ynxu??" Yana fadin haka ya wuce sa ya xaga daya side din motar, da ido dogon Matashin ya bi sa bai ce komai ba, Alhaji Ahmad ya bude door din side din da Heedayah take, ya kamo hannunta ya sakko da ita daga cikin motar, Matashin ya d'an koma baya yana kallonsu a bit surprised, Alhaji Ahmad yace "Ka fiddo min laptop dina bayan motar, they are some other things ma ka taho da su ciki" Yana fadin haka ya nufi entrance din shiga gidan yana rike da Heedayah, Matashin ya bude motar ya dauko abinda yace masa sannan ya bi bayansu, Alhaji Ahmad na shiga parlor Rabi'ah da Khadija suka taso da gudu don rungume sa, sai dai ganin Heedayah da yake rike da duk suka tsaya basu karasa gun nasa ba, Khadija tace "Who is she Dad?" Yana kokarin cire takalminsa yace "Sabuwar 'yar uwar ku" kallon juna Khadija suka yi da Rabi'ah, ya karasa parlon ya xaunar da Heedayah kan kujera sai dai ta ki sakin hannunsa kmr xata yi kuka tace "Abba kar ka bar ni don Allah" Yace "Noo baxan bar ki ba, we are home yanxu" Yana fadin hka ya kalli Khadijah yace "Ina Mumyn ku?" Khadijah ta d'an cinno baki tace "Upstairs" ya daga Heedayah ya wuce sama da ita, Khadija da Rabi'ah suka juya suna kallon yayansu dake tsaye bakin kofa yana kallon ikon Allah shi ma, da sauri suka nufesa a tare suka ce "Ya Shuraim who is she? Wacece ita" Ko kallonsu bai yi ba, ya nufi part din Abbansu don ajiye masa system dinsa dake hannunsa. Alhaji Ahmad ya bude kofar parlon Mai dakinsa still holding Heedayah's hand, dai dai fitowar ta daga bedroom dinta, ya xaunar da Heedayah saman kujera kafin yace komai tana kare ma Heedayah kallo daga sama har kasa tace "Waye wannan kuma Barrister?" Yace "sannu da hanya ya kamata ki fara min sannan tambayoyin ki su biyo baya" a takaice tace "Toh sannu da hanya, wacce yarinyar ce wannan ka shigo min da ita har parlor?" Sai a sannan ya daga kai ya kalli matar tasa yace "Bakuwa ce" Ta d'an yatsina fuska tace "Bakuwa kuma? Daga ina? Kuma ina xa a kai ta?" Yace "Eh bakuwa.... Daga kano, kuma nan xata xauna in sha Allahu rabbi" Da mugun mamaki tace "Yar wacece ita din?" Yace "Baiwar Allah ce..." A kufule tace "Plss be straight barrister, ina ka samo yarinya? Kowa ma bawan Allah ne ai" Barrister yace "Gashi nan na gaya maki, what else did you want to know, me kuma kike son sani" kamar jiran tambayar take ta mayar masa da amsa da sauri tace "Manufar xuwanta gidan nan, sannan mun hada wani dangantaka ne da ita??" Ya gyara xama yace "Manufar xuwanta gidan nan shine don ta xauna da mu na wani d'an lkci, dangantakar mu kuma kawai shine kasancewar ta 'yar uwar mu musulma" Kallonsa ta dinga yi, surprised, Furious, and mad at the same time.... Blankly tace "I don't get you Abban Shuraim, ban gane abinda kke nufi ba, a ina kasamo wannan yarinyar??" Ya mike yace "Her parents are missing, so we need to look after her kafin Allah ya bayyanar da iyayenta, all that aside, she is blind Hajiya Maryam, makauniya ce...." Yana fadin haka ya fita daga parlon..... Hajiya Maryam da ta bi sa da kallon mamaki lkci daya tace "Tabdijam!!! Toh sannu Humanitarian, Do-gooder.... sai kuma nace maka gidana orphanage ne (Gidan marayu) ko kuma police station?? to wllh ka saurareni da kyau, yarinyar nan dai baxa ta xauna gidan nan ba, me muka hada da ita daga ganin yarinya a titi ka kinkimota ka kawo mana gida wai iyayenta sun 6ata kamar wasu gyada, Anya ma Barrister kasan me kake yi kuwa, yanda duniyar nan bbu gaskiya kwata kwata kowa ya xama mugu ya xama abun tsoro ka dauko mana yarinya ka kawo gida?? A'a wllh ba gidana ba, ka dauketa ka kai ta police station ko kuma ka kai ta gidan marayu" tana fadin haka ta wuce dakinta rai 6ace don daukan wayar ta, Heedayah dai na xaune sai kallon direction din da masifar ke tashi take yi, gaba daya a tsorace take, lkci daya hawaye ya kawo manyan idanuwanta.... Bayan minti biyar Hajiya Maryam ta fito dakinta tana kallon Heedayah tana huci ta daka mata tsawa tace "Ke maza tashi ki fita ki ban waje kar in illata ki...." Mikewa Heedayah tayi da sauri ta fashe da kuka tana laluben hanya tace "Abba where are you" muryarsa ta ji yace "I am here...." Har ya karaso cikin parlon kallon Hajiya Maryam yake, calmly yace "Wannan ya xama na karshe a gidan nan, kar ki sake yi mata tsawa, nace a gidan nan Heedayah xata tsaya har sai an samo iyayenta, I mean my words" bude baki tayi tana kallonsa da farko, sai kuma tayi wani murmushi me sauti tana tafe hannu tace "Toh sannu Humanitarian, idan ni ban kai inyi magana ka ji ba nasan baxa a rasa wa enda xa su yi maka ka ji ba, look Ahmad it's not as if i am being wicked, ni ba muguwa bace Allah ya ga xuciyata kawai xamanta ne damu bna so don hankalina bai kwanta da hakan ba, to wai ma akan me xata xauna da mu, kai da kke lawyer ai ya ci ace ka fi ni sanin me duniya ke ciki, to idan ba akwai wani boyayyen lamari a kasa ba daga xuwa meeting kano sai ka dawo da yarinya wai ka tsince ta a titi bbu iyaye, Kar ka manta idan kai lawyer ne to ni kuma matar lawyer ce...." Ya dakatar da ita yace "Wallahil Azeem Maryam wannan yarinya a hanya na hadu da ita kamar ynda na fada maki, mota ce ta bigeta muka yi asibiti da ita, I was there har ta farfado.... Let just stop all this, Maryam put Rabi'ah or Khadijah in her shoes plss" a mugun fusace tace "Allah ya kiyaye, I can't imagine my children in her shoes, why will I? Kar ma ka gaya min haka, Ni dai abinda na sani shine hankalina bai kwanta ba kuma baxai ma ta6a kwanciya da yarinyar nan ba, wa ya sani ma ko aljana ce da gashi haka??" Bai kuma ce mata komai ba ya kama hannun Heedayah dake kuka a hankali ya fita parlon da ita xuwa downstairs.... Hajiya Maryam ta kasa zaune a parlon nata sai xagaye take, bude kofar aka yi Shuraim ya shigo da sallama can kasa, Hajiya Maryam ta kallesa da sauri tace "Shuraim kana ganin mahaifinku koh? Me yake nufi da kawo mana yarinya gida ba dangin Iya balle na Baba, ya san yar wacece ko ma shegiya ce bai sani ba kawai ya kawo mana ita gida, wllh something is fishy, kuma in dai yarinyar nan xata xauna gidan nan sai dai mu bar masa gidan shi da ita gaskiya, don mu ba gantalallu bane, wai kuma makauniya ce kai ka ji fa???" Tun fara maganar ta sai a sannan Shuraim ya kalleta da sauri jin wai makauniya ce, Tayi mitsi mitsi da ido tace "Wllh haka yace Makauniya ce bata gani, kuma naga alamar hakan, she is blind, oh innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, me ya samu Barrister ni Maryam... Anya kuwa yana right senses dinsa??" Shuraim dai bai ce komai ba ya juya xai fita, a mugun fusace tace "Toh malam ba shiru xaka yi ba ka wani juya sumui sumui xaka wuce, xuwa xaka yi ka samesa tunda yana jin maganar ka, ka lallabasa ya fitar mana da yarinyar ya kai ta police station, bbu ruwana da gayyar tsiya, yarinyar nan baxata kwana gidan nan yau ba..." Shuraim na fita ya nufi Part din mahaifinsa, ya bude kofar parlon da sallama, Heedayah ce kawai xaune kasan carpet dake parlon ga cup din fresh milk a hannunta, jin an bude kofa ta dakatar da shan madaran da take yi tana waige waige, bai kalli direction dinta ba ya nufi dakin Abbansa, sallama yyi bayan ya amsa masa ya shiga, xaune ya samesa gefen gadonsa, ya karasa ya xauna nan kasa gabansa yana kallonsa yace "Ya hanya Abba?" Abba ya kallesa yace "Alhmdllh..." Shuraim ya d'an shafa kansa yace "Abba, akan wannan yarinyar....." Sai kuma yyi shiru, Abba yace "Yes, what about her? Ina jin ka" Shuraim yace "Is she suppose to be here?" Abba yace "Of course, ai nan din gidana ne ba na wani ba, so why won't she be here?? Me kuwa xai hana xamanta a nan tunda na amince da hakan?" Shuraim ya girgixa kai alamar ya rasa abinda xai ce, Abba yace "Yes gidana ne, ba naka ba, balle na Mahaifiyar ka" Shuraim yace "But Abba hakan ba dai dai bane, bbu abinda muka hada da ita, ba mu san ta ba, we don't even..." Dakatar da shi Abba yyi so pissed off yace "Get out my frnd, who are you to question my orders? And don't u even have human conscience? Xaka so kanwarka ta tagayyara a rayuwa?" Mikewa Shuraim yyi yace "I am sorry" daga haka ya nufi kofa ya fita, satan kallon Heedayah yyi, lkci daya ya wani hade rai ya fice daga parlon.