HEEDAYAH 5

Jin budewar gate ya sa Alhaji Ahmad ya mike ya isa jikin tagar dakinsa yana kallon compound din gidan don ganin wanda xai fita, motar yayansa ne ya shigo compound din, ya bi motar da kallo har yyi parking, sannan ya girgixa kai ya koma ya xauna… Ba a dau lkci ba kuma wayarsa ya fara ring, ya duba ganin yayan nasa ke kiransa ya mike ya fita dakin, kwance ya ga Heedayah ta fara bacci nan kasa, ya
d’aga ta ya kwantar kan kujera sannan ya fita, direct main parlor ya wuce, ya tadda wansa Alhaji Umar zaune saman kujera ga Hajiya Maryam xaune parlon ta sha kunu kai kace bata ta6a dariya ba, xaunawa yyi ya gaida Yayan nasa, Alhaji Umar ya amsa yana kallon Hajiya Maryam yace “Me ke faruwa Maryam” Ta kwantar da murya tace “kana ji Alhaji, Ko awa daya ba ayi ba da dawowan barrister daga kano, amma sai me??” Nan ta kwashe komai ta tsara masa, tana matsar kwalla tace “Saninta muka yi Alhaji? Ko me muka hada da wannan yarinyar? Mun san me yasa iyayen suka jefar da ita da har shi xai daukota, to gaskiya naga abun ba wanda hankali xai dauka bane shi sa na kira ka don kayi intervene don gaskiya I don’t know what came over Barrister, ban san me ya samesa ba, kawai muna xaman xaman mu ya ja mana magana….” Alhaji Umar na kallon kanin nasa yace “Barrister wace yarinya ce wannan ka dauko ka kawo cikin gidan ka?” Alhaji Ahmad ya jinginar da kansa da kujera yace “Doctor nasan da kai ka ga yarinyar nn xaka yi fiye da abinda nayi ma… Sincerely I mean no harm to my family, taimako kawai nayi sbda Allah, and I thought they will also welcome the idea, na xata xa su so taimakon da nayi….” da sauri Hajiya Maryam ta katse sa tace “To family dinka basa son taimakon nan gaskiya, ur idea isn’t welcome, kawai ka maida ta inda ka ganta, idan kuma xuciyar ka baxai yarda ka maida ta ba to ka kai ta gidan marayu…” Wani kallo ya jefa mata yace “Baki isa ki bani order a gidana ba Maryam, I did what I know is right, you are not in the place to kick away my decision, nace baki isa ba” Alhaji Umar na kallonsa yace “Hold on bawan Allah, bana son hayaniya, ka saurareni….” Alhaji Ahmad yace “Dr if you are in anyway doubting me ka kira abokin ka Asp Usman, he will explain everything to you, Babu abinda xai boye maka, shi ma ya bani go ahead din tahowa da yarinyar when I request doing so, ban taho da yarinyar nan ba sai da izini da sa hannun Asp….” Mikewa Alhaji Umar yyi bayan shirun wani lkci yace “Ynxu ina yarinyar take?” Barrister ya mike yace “Mu je ka ganta tana sama parlona” Bin bayansu Hajiya Maryam ma tayi xuwa part din mai gidan nata da sauri, kallon Heedayah dake bacci Alhaji Umar ya dinga yi kafin yace “She so little” Alhaji Ahmad ya bude hannunsa yace “Of course she is” hannu Alhaji Umar ya kai goshinta ta bude ido da sauri ta kamo hannun tace “Abba…” Ya d’an yi jim sai kuma yace “How are you?” Shiru tayi tana kokarin mikewa ya dagata ta xauna, Hajiya Maryam sai kyabe baki take fuska a murtuke tana kauda kai, Alhaji Umar ya girgixa kai ya sauke ajiyar xuciya yace “This is serious… abinda xai faru ynxu shine ke Maryam kiyi hakuri ta kwana xuwa gobe xa a san ynda xa ayi in sha Allah, they will be a meeting tomorrow at my resident idan Allah ya kai mu” shi dai Barrister bai ce komai ba, Hajiya Maryam tace “Allah ya kai mu, amma wllh baxan rike yarinyar nan ba Kun ji rantsuwar musulmi sai dai duk abinda xai faru ya faru” daga haka ta fice daga parlon duk suka bi ta da ido. Karfe goma Barrister Ahmad ya fita parlonsa xuwa parlon Hajiya Maryam, kallo take ita da Rabi’ah da Khadijah a parlon nata, Khadijah tace “Toh Mumy me yasa bai kai ta orphanage ba??” Hajiya Maryam ta kyabe baki tace “Neman suna mana, ke ko bayan lawyer gashi Humanitarian din da ya laka ma kansa, to wllh ba dai wannan gidan ba, dai dai nake da su dukka….” Rabi’ah tace “And kuma yace makauniya ce fa” Hajiya Maryam ta dau apple din gabanta tace “Ko kurma ce sai ya fitar da ita gidan nan, ban gama wahala da nawa yaran ba baxai kwaso min wata can ba, ba dangin iya balle na baba, shi dai ya cika fitina ne kawai” Khadijah tace “Ni dai idan yace nan xata xauna gwara in koma gidan Aunty Fatima, I can’t stay in the same roof with her, what if muguwa ce” Hajiya qMaryam tace “Sai dai shi da ita su bar mana gidan….” Shigowan Abban yasa tayi shiru, Yana kallonsu gaba daya yace “Bani da abinci a gidan nan yau kenan?” Hajiya Maryam tace “Ohh na xata you are full ai da naga kafi concentrating kan yar tsintuwa, ban san kana tare da yunwa ba, Rabi’ah go and serve him downstairs” kallonta kawai yake kafin ya gyada kai ya juya ya fita parlon, a hankali Khadijah tace “Abba is just acting strange, dubi fa ko kula mu bai yi ba tunda ya dawo…” Hajiya Maryam tace “Atoh ina xai kula ku ga makauniya ya saka a gaba Khadija” Rabi’ah ta tashi ta fita don kai ma Abban nata abinci parlonsa, Yana xaune parlon yyi nisa tunanin da yake, ta ajiye abincin tace “Abba ga abincin” yace “Baxan ci ba, ki dibar ma yarinyar nan kawai ki fita da sauran” ta kalli Heedayah dake kwance fararen idonta a bude, ta d’an hade rai ta bude abincin ta diba kadan ta daura nama daya, kallonta kawai Abban nata yake yi yace “Add the meat” Ta kara daura wani naman sannan ta mike ta fita da sauran abincin. Mikewa yyi ya tafi gun Heedayah yace “kina Jin yunwa ko?” Ta gyada masa kai, ya kama hannunta ya dau plate din abincin ya fita, main parlor ya koma, ya shiga wani d’an corridor ya kwankwasa daya daga kofofi biyun dake wajen, wata matashiya da baxata haura talatin da biyar ba ta bude kofar, ganinsa ta durkusa da sauri tace “Sannu da dawowa Alhaji, ina yini” yace “Lfya lau, ga wannan yarinyar ki kula da ita, ki bata abincin nan, sannan ki taimaka mata tayi wanka ki mata shimfida ta kwanta, tana da matsalar ido” Matar ta kama hannunta da sauri tace “To in sha Allahu Alhaji” daga haka ya juya ya bar wajen bayan yyi mata sai da safe. Washegari da ya kasance lahadi bacci yan gidan suka dinga yi har karfe takwas, Hajiya Maryam ta sakko parlor wajajen tara don ganin ko Saudat ta gama shirya breakfast, Kitchen ta sameta tana juye ruwan Lipton dake ta kamshi a flask, alamar dai ta gama komai shi kadai ya rage, Heedayah na xaune daga kusa da kofa hannunta rike da cup din shayi da Saude ta hada mata ga plate din kwai da dankali da plantain, Hajiya Maryam ta wani xaro ido tace “Saudat me xan gani haka? Wa ya saki wannan aikin, a ina kika ga yarinyar? Ko a ina kika santa?” Da sauri Saudat ta xube kasa tana gaisheta tace “Hajiya… Alhaji ne ya kawo min ita jiya da daddare yace in kula….” Tsawa tayi mata da karfi tace “Toh wllh a bakin aikin ki, da ya kawo maki ita baki iya xuwa ki sameni ba? Kawai sai ki yanke hukunci sbda ke ke ajiye da kanki? To wllh kin gama min aiki a gidan nan yau, yanxun nan xa ki kama gabanki” Hakuri Saude ta dinga bata a tsorace tana cewa “Hajiya wllh Alhaji ne ya kawo min ita kiyi hakuri ki rufa min asiri, ni ban san komai ba” Hajiya Maryam tace “Ni dai nace kinyi na aikin ki wllh, maxa tattara yanaki yanaki” daga haka ta juya ta fice daga kitchen din tana huci. Karfe goma Alhaji Ahmad ya dau Heedayah suka fita xuwa parking space, Hajiya Maryam dake xaune ta bi sa da kallon mamaki sannan ta kalli Shuraim dake operating laptop a parlon tace “Ka gani ko Shuraim, gaskiya abun nan ya fara bani tsoro, wannan abu ba na hankali bane… Something is wrong somewhere, what is wrong with your father” Shi dai kallonta kawai yake bai ce komai ba, wayarsa ya fara ring ya dauka ganin Abbansa ne ya kai kunne, Daga daya bangaren Abba yace “Ka gaya ma babarka karfe sha daya ne meeting din don Dr ya kirani xai yi tafiya” Shuraim yace “Toh Abba” Daga haka ya katse wayar, Yana kallon mahaifiyarsa yace “Abba yace Baffa xai yi tafiya, so da wuri xa ayi meeting din” mikewa Hajiya Maryam tayi tace “Toh ai a shirye nake sai ka kira kanninka duk mu duguma xuwa gidan, wato baxai iya gaya min ba sai dai ya bada sako a bani, to duk muje ayi ta ta kare yanxu” Babban gida ne sosai don har ya fi na Barrister Ahmad girma, Shuraim yyi parking a parking lot din gidan, Mumy ta fito ta nufi hanyar shiga gidan, direct dakin Hajiya Amina Uwar gidan Alhaji Umar ta nufa, bayan sun gaisa Hajiya Amina tace “Daxun nan Alhaji ke ce min akwai meeting wai kuna hanya, ni dai nace to Allah ya sa lafiya” Mumy tace “Ina fa lafiya, wllh ba lafiya….” Tsaf ta kwashe ma Hajiya Amina abinda ke faruwa ta sanar mata, Hajiya Amina ta buda ido sosai tace “Iko sai Allah, to meye ma’anar hakan da Barrister yyi??” Mumy tace “Ni nasan masa, ni dai wllh wllh kinji rantsuwar musulmi koh?? To yarinyar nan baxata xauna tare da ni ba, ba ruwana…. Haka kawai ban san hawa ba ban san sauka ba yanda duniyar nan ta lalace…” Hajiya Amina tace “Toh ai dama bbu wannan xancen, taya xaki rike yar da ba a san tushenta ba, kada ki kuskura wllh, Wai kuma makauniya kamar dai a wasan kwaikwayon hausa…” Mumy tace “Ke ki bari kawai, nasan karshe Dr yace a barta gidan nan….” Da sauri Hajiya Amina ta katse ta tace “Wajen wa??? Haba wannan ai labari ne, bbu wanda xai soma wannan gangancin…” Dariya Mumy tayi tace “Toh ba sai abokiyar xaman ki ta riketa ba” Hajiya Amina tayi tsaki tace “Ai sai dai ta kai ta gidansu amma wllh bbu wajen xaman yarinyar nan a gidan nan” Mumy tace “Atoh, taimakon da idan kayi ma yanxu yake xame maka jaraba” Mikewa tayi tace “Bari in je in gaida tsohuwar can…” Hajiya Amina tace “Tana can kuwa yau bbu mutunci ta tashi….” Mumy tayi dariya tace “Ni dai Allah ya dube xuciyata ya rabani alakakai…” Hajiya Amina tace “Wa?? Ai xance komawa gidan ki take yanxu” Mumy tace “Tabdi, xaman mu baxai yiwu ba, wnn karan karara xan fito inyi magana” daga haka ta fita dakin. Da sallama Mumy ta bude kofar wani daki ta shiga ciki, babba daki ne sosai bbu abinda bbu a ciki irin dai na tsoffi, Shuraim na xaune kusa da wata tsohuwa da tayi tsit lkci daya ganin shigowan Mumy, Mumy na murmushin yake ta xauna kasa tace “Sannu Kaka….” Tsohuwar na gyara daurin dankwalinta tace “Sannu…” Mumy tace “An tashi lafiya kaka” kaka tace “eh toh lafiyar kenan, amma kin gan ni nan?? Wllh tun safe bbu karen da ya leko ni a gidan nan har shi Umarun, hana rantsuwa dai ya shigo da Asuba ya gama xamansa a can na kusan minti talatin ya fita, wllh Maryam gidanki ya fiye min nan sau goma, gwara ke da yunwa kawai kike bari na….” Mumy ta hadiya abu da kyar ta sunkuyar da kanta, Kaka tace “Kinga wannan bakar matar Amina?? Ni dai ina ga da kyar ta wanye lafiya, ni dai ki tafi da ni gidanki” Da sauri Mumy tace “Ai hakuri ake yi a ko ina kaka, ko ina hakuri ake ba wai wani abu ba, kawai ayi ta hakuri tunda Doctor ya fi son yana ganinki kusa da shi, kuma ma hakan ya fi wllh, yanxu ma meeting muka xo yi bbu lafiya” Da sauri kaka tace “Me ya faru kuma?” Mumy ta gyara xama tana tabe baki, nan ta tsara ma Kaka duk yanda aka yi daga daren jiya har xuwa safiyan yanxu har da kari, Kaka da ta gwalo ido tana kallonta tace “Ba lafiya, shi Ahmadun yace bbu wanda ya isa ya saka shi ya kuma hanashi?” Mumy tace “Toh nima dai ban gane kan lamarin ba, abun dai gashi kamar almara” Kaka tace “Toh ina yar makauniyar take yanxu?” Mumy tace “Tun sassafe ya fice da ita ko bi ta kanmu bai yi ba…..”