HEEDAYAH 6

shi, me ta min da xan koreta banda abun ka sudais? Amadu yayi ta rikonta har Mahadi ya bayyana ma bbu abinda ya sha min kai ni dai….” Sudais ya
shafa kansa yace “Idan ya kai xuciyar ki ce masa xa kiyi kin amince ya riketa” A mugun fusace tace “To ya rike ta mana, ni ina ruwana, ai d’a na
kowa ne, amma gaskiya ka daina min rashin kunya xan hada ka da ubanka, kaf ka raina ni tamkar ynda uwar ka ta raina ni” ya d’an bude ido ya juya ya
nufi kofa xai fita Kaka tace “Allah yyi min tsari da kai ni dai katon banxa” Abba ya mike xai fita rike da Heedayah, Hajiya Maryam ta mike da sauri
tace “Wllh to ka nemi inda xaka kai ta ba gidana da na yarana ba…” Kaka ta bude baki tace “Naga bala’i, gidanki kuma Maryam?? Ta ina hakan ya
faru” Baffa yace “Wait Ahmad it’s better kasan inda yarinyar nan xata xauna, u can’t force her to hold the little girl, it’s not even possible,
tunda tace baxata riketa ba baxa ayi mata dole ba” Abba ya juya yana kallonsu gaba daya kafin yace komai Hajiya Hauwa tace “Babu damu Barrister, ka
kawo min ita ni xan riketa in sha Allah har iyayenta su bayyana, Allah ya shige mana gaba, yayi mana mai kyau…” da sauri kaka ta katseta tana
wurwurga ido tace “Ki riketa a wani gidan Kuluwa??? Kaji min mata ba tsoron Allah kamar gidanta, Haka kawai ba mu san ko mayya bace yarinya dare
daya ta karar damu a gidan a shiga uku xaki wani ce xaki riketa, shi dai Ahmadun da yaga xai iya ya tafi can ya karata, ni dai Allah ya rufa min
asiri ba shi kadai na haifa ba, in dai har ina gidan nan yarinyar nan baxata xauna ba, idan ko xata xauna sai dai a sallameni in tafi, bbu ruwana
da kwashe kwashe ta kaina nake” tana fadin haka ta juya masu baya kamar karamar yarinya, Baffa dai sai kallon D’an uwan nasa yake, Hajiya Maryam
kuwa sai hararansa take tana girgixa kafa tana wani murmushi irin ba shi da wata mafita kuma ai, ya gyada kai yana kallonta da kyau yace “Shikenan,
Xan auro warce xata rike ta a satin nan in sha Allah” Daga haka ya fice daga parlon rike da Heedayah, kasa motsi Hajiya Maryam tayi jin abinda yace
ta bi sa da kallo baki bude, Kaka tayi wani dariya tace “Atoh dai, tun ba yau ba dama nake cewa kayi aure ka ki, yanxu ai gashi xaka yi ba don
Allah ba, xaman ka da Maryam ko kaddara, gwara ka auro warce xata rike yar da amana don a ynxu kam yarinyar bata da maraba da marainiya, tsinanne
ne kadai xai ki taimakon ta….” Ta gefen ido Baffa ya kalli mahaifiyar tasa yyi saurin sunkuyar da kai.