NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 43 – 44

*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
             _(ya dace ya gyara kansa)_
                 *_Bilyn Abdull ce????????_*

                   *_[43➖44]_*
………….Zaman amsa wayar yayi d’an kwallin Jiddah a hannunsa, yanda yake amsa wayar zaisa ka tabbatar shi da malam ne, kusan
mintuna uku kafin suyi sallama ya ajiye wayar saman gado yamik’e yana fad’in “Baba na gaisheku ke da auntynki”.
      “Muna amsawa, yana lafiya shima?”.
       “Lafiya lau yake”. ‘Yay maganar yana warware d’an kwalin’.
       Duk yanda yaga Maimunatu nayi haka ya lankwasa d’an kwalin kafin ya d’ora akan Jiddah, itadai saima ta hangame baki, dan da farko dukta d’auka wasa yakeyi. Kasa daurewa yayi.
      tace, “Kawo Zan iya d’aurawa fa”.
        “Yarinya kin makaro kuma ai, kedai tsaya kawai”.
     Babu yanda ta iya dole ta tsaya tana kallon ikon ALLAH itakam. Aiko sai gashi ya d’aura mata, sai dai yanda yay d’aurin dolene kayi dariya, saikace irin tsofaffin yarabawannan Wanda suka k’ware a iya d’aura gwagwgwaro. Hakanne yasaka jiddah saka dariya batareda ta shirya ba, shima dai abin yabashi dariya dan haka ya d’an dara yana fad’in “Wannan bai yiba kawo a sake”.
       “Nidai Na gode, bara kawai Na d’aura Wanda Na iya”.
       “Haba hajiyata, d’aurin nan dai duk wanda ya gansa dolene yabani Aword akansa, kinga kuwa yanda kika wani had’u”.
      Jiddah ta rufe fuskarta da hannu tana dariya, sosai rayuwarsa take birgeta, shi mutumne mai sauk’in kai, kuma haka yakamata kowanne miji ya kasance da iyalinsa kodan shima ya samu farin ciki, MANZON ALLAH har y’ar tsere yanayi da iyalinsa saboda susami farin ciki, amma banda mazanmu Na hausawa, wani zakiga yanata dariya da fara’a a waje, amma da zarar yashigo gida saiya hau kumbura fuska tamkar fulawar da aka kwa6a danyin burodi. Hakan kuma yana k’untata iyalansa sosai, kwata-kwata mazanmu basa koyi da ilimantarwar da addininmu yay mana akan rayuwar aure, kowa tasa yake tsarawa, alhalin kafin ya kawoki gidansa lalla6aki yake da soyayya tamkar kwai a cokali……….
      “Tunanin mi kikeyine Jiddah?……”
      Firgigit tadawo hankalinta saboda ta6atan da yay, ta sauke ajiyar zuciya tana fad’in “Babu komai”.
          “Okay, to tashi muje ki gaida auntynki ko”.
     Kanta ta jinjina masa, sannan cikin marairaicewa tad’an kallesa ta janye idonta, “Dan ALLAH na saka hijjab? Wlhy bazan iya zuwa gabanta a hakaba”.
     Murmushi yad’anyi, “Uhm saka, amma fa yau kad’ai”.
      “Nagode”.

Tunda suka fito take kallon tsakar gidan, bawani k’ato baneba, gashi nan dai d’an cif dashi, rayuwa dai ta duniya ya wadatar dasu Alhmdllh, dan bazasu dai takuraba koda ansamu yara a nan gaba, tunda suka iso k’ofar d’akin Maimuna gabanta ke fad’uwa, haka kawai sai takejin tsoro-tsoro, dan bata mance had’uwarta da Hajia Deluwa ba.
      Shine ya fara shiga bayan yayi sallama Maimuna dake zaune ta amsa masa, murmushi yamata kafin yay mata alamar tare yake da bak’uwa.
      Maimuna data fahimci shida Jiddah ne saita mik’e ta nufo inda yake, hannu ya bud’e mata alamar tazo, kansa tayo gadan-gadan, saida tazo dab dashi saita waske tanufi k’ofa.
    Baki bud’e yabita da kallo, tajiyo tamasa gwalo kafin ta bud’e labulen tana fad’in “Amarya shigo mana”.
      Kan Jiddah a k’asa tad’anyi murmushi kafin tashigo da sallama, Maimuna ta amsa tana kama hannunta suka ida shiga cikin falon.
      Aliyu dake zaune yad’ago yad’an kallesu, ganin kan Jiddah a k’asa yake saiya harari maimunatu. Yanzuma murmushi tad’an masa, kansa ya nuna wai shi?. Saita girgiza kanta alamar A’a.
     Itadai Jiddah batasan mi sukeyiba, data zaunama saitacema Maimunatu “Aunty ina kwana?”.
      Zama kusa da ita Maimunatu tayi tana amsawa fuskarta d’auke da murmushi, “Lafiya lau Amarya, ina fatan kin tashi lafiya? Ya kuma bak’unta?”.
     “lafiya lau aunty”.
 “To masha ALLAH Amarya, yanzu dai ga abinci, oga bismillah”.
       Aliyu dake kallonsu yad’anyi murmushi, yayinda acan k’asan ransa yake ambata ”Matar kwarai rabin addini, duk Wanda yasamu yagama dacewa”.
       A filait d’aya Maimun ta zuba musu soyayyar doya, sannan ta had’ama kowa tea.
     Har Oga da Uwargida suka fara ci Jiddah takasa, sai juya cokali take a cikin shayin, Maimuna ce tayi magana ganin Jiddah bataci ko sau d’ayaba.
      “Amarya kobak’ya sonshi a canja mikine?”.
     Da sauri Jiddah tace, “A’a aunty”.
       “To dan ALLAH kici, nanfa gidankine, mukuma y’an uwankine, babu batun bak’unta a tsakaninmu kinji”.
       “kai Jiddah ta kuma gyad’a mata”.
     Aliyu dai najinsu baice komaiba.
       Da k’yar dai Jiddah tasamu tad’anci kad’an, shima dan Maimunatu tana magana ne idan taga tayi shiru, ahaka suka kammala, Maimuna tafara tattare kayan, hakanne ya saka Jiddah mik’ewa ta tayata, saida suka kimtsa wajen sannan suka dawo suka zauna.
        Zama Aliyu ya gyara tareda dai-daita kansa yakoma fuskar babu wasa, hakanne yasakasu suma duk suka nutsu wajen maida hankali a garesa.
      Yay maida idonsa a Kansu “Assalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wa barakatuhu”.
      Atare suka amsa masa.
     “Alhamdulillahi, godiya ta tabbata ga ubangijin talikai daya taramu anan wajen matsayin Abu d’aya, wannan ikonsane kuma hakan rubutaccene agareshi tunkan musan zamuzo duniya, shine mai tsara yanda yaso, yakuma tabbata ga Wanda yaso. Da farko Jiddah muna miki barka da zuwa cikinmu, muna kuma miki fatan alkairin samunki kamar yanda muke k’yautata miki zato, kamar yanda na shaida miki tun farko ina zaune da matata lafiya, kuma tanamin dukkan abinda Na buk’ata, idan kinga sa6ani a tsakaninmu saina tsakanin harshe da hak’ori, k’yawawan halayenta yake k’ara girmama k’aunarta a raina kullu yaumin, insha ALLAH indai kika kwantar da hankalinki nasan zaman lafiya zai cigaba da girmama a gidanan. Maimunatu ga Jiddah nan, Y’ar uwarki kuma k’anwa a gareki, kamar yanda Na fad’a miki ina k’yautata zato a gareta, domin mutuniyar kirkice da kowa ke yabon k’yawawan halayyarta, kamar yanda nake k’aunarki a zuciyata itama inajin k’aunarta, yarinyace mai tarbiyya da sanin yakamata, insha ALLAH ina fatan bazaku samu matsalaba koda anan gaba. Nasihar dazan mana gaba d’aya amatsayinmu na iyali shine hak’uri, hak’uri jagorane, kuma katangane ga kowanne bawa, sannan kuma mutuncine ga cikar kamalar d’an Adam, duk inda akace maka wane yanada yawan hak’uri, to lallai zaka sameshi nagartaccen mutumne shi abin son koyi ga kowa, babu wata nasara dake tabbata saida hak’uri, idan babu hak’uri ko ibadar da mukema bazamu jureba, dukanku Na yarda da tarbiyyarku, ina kuma k’yautata zaton samun farin ciki a gareku, ayanzu banida wani makusancin daya kaiku, dan kafin kowa yasan matsalata kune zaku fara sani, hakama a tsakaninku, kunfi kowa kusanci da juna, dan kafin Abu ya sameku wani yataso daga danginku kunma kankushi, so babu kusancin da yakai wannan muhummanci kuwa a tsakaninmu, ina rok’inku amatsayinku Na masu ilimin addini, kunsan dokar ALLAH da abinda MANZONSA ya koyar damu, to ina fatan zamu gina rayuwarmu akan wanan tsarin, dan bai k’yautu ga d’iyan musulmai ba ace yana koyi da wani Abu Na yahudanci, dukkan mai kwaikwayon wani Abu daya fita daga tsarin koyarwar MANZON ALLAH da sahabbansa, to lallai za’a tasheshi da Wanda yake kwaikwayo aranar tashin alk’iyama, to duk abinda zamuyi yakamata mubishi a bisa tsarin addinin islama saimuga mun samu kammu cikin aminci da kwanciyar hankali. Lallai shi kishi gaskiyane, duk kuma macen dazaka ajiye bata kishinkama wannan ba Sanka takeba, to amma muringa tunawa ba kishin matan yanzu ne kishiba, dan wani kishin banda tsantsar jahilci babu komai a cikinsa, kishi mai cike da tsafta shine rige-rige wajen k’yautatama miji tamkar yanda matan msnzon ALLAH suka gunadar da nasu, tananne zakuga miji ya karkata ga son wata, dan ita zuciya Na son mai k’yautata Mata, sannan tanak’in mai munana Mata, harga ALLAH inajin sonku da k’aunarku a raina ku duka, wadda zatafi zama a zuciyata kuma yana a gareku, dan wadda ta kwantarmin da hankali da bani kulawa itace da wannan nasarar, abinda zaisa muji sassaucin kishin juna kuwa shine tsoron ALLAH da danne zukatanmu, mu d’auki rayuwar tak’aitacciya mai yankewa babu shawara, muringa tuna zafin d’aukar rai da kwanciyar kabari da tsayuwar hisabi, duk Wanda ya munanama d’aya acikinmu koda da hararane wlhy sai ALLAH ya tambayesa, dan haka saimu kiyaye, ba shakkan ganin idona zakuyiba, kuji tsoron Wanda ya haliccemu baki d’aya, sannan Ku tayani da addu’ar samun damar yin adalci a tsakinku, dan ina tsoron ranar da za’ace gani natashi cikin mutane masu shanyayyen jiki saboda rashin adalci a tsakanin iyalina. Daga k’arshe ina kuma rok’onmu dan ALLAH muji tsoron ubangiji adukkan abinda zamu aikata a wannan zaman, karmu zama cikin masu shiryama juna makirci ko jifan juna da sharri koda Na maganane, karmu biyema duk Wanda zai kawo 6atanci a zamantakewarmu, koda kuwa acikin makusantanmu ne, karmu biyema sharrin zuciya ta sak’a mana abinda zamu dawo muna Dana sani, muringa tinawa a kowanne motsinmu akwai mala’iku dake biye damu rik’e da alk’alaminsu, kuma Ubangijin al’arshi yana jinmu yana ganinmu, ALLAH yay muku albarka yabamu zaman lafiya da kwanciyar hankali Na har abadan”.
        Kowacce ta amsa da amin, zukatansu duk sai suka kuma raunana dayin sanyi, aganinsu minene abin zafafawa akan wannan gajeruwar rayuwar da bakada tabbacin kaiwa safiya…….
       Aliyu ya katse musu tunani da fad’in “Maimunatu mizakice?”.
      ‘Dan murmushi tayi na k’arfin hali tana had’iye hawayenta da suka cika mata ido, “Duk abinda Zan fad’a Yaya ka fad’eshi, sai dai nace ALLAH yabamu zaman lafiya da hak’urin jure yau da gobe, dan itace mai wahalar, insha ALLAHU zaka samemu fiyema da yanda kake tunani, kamar yanda kafad’a hak’uri shine jigon komai Na rayuwa, ALLAH ya bamu mai amfani, yakuma baka k’arfin gwiwar adalci agaremu, dukda Alhmdllh kakai ayaba maka, dan nidai Zan iya bugar k’irji ako ina nace mijinmu adaline, ya banbanta da maza da yawa dakan wulak’anta matansu aduk lokacin da zasu k’ara aure, sannan kuma bakaimin romon bakaba nacewa k’addarace ta sakaka k’arawa badan kasoba, kafito kanka tsaye kasanarmin sonta kakeyi shiyyasa zaka aurota, kaga hakan dakayi ka k’ara Mata kima da daraja a idona, sannan baka tozartaniba yanda Zan kalli k’ara aurenka a matsayin gazawata ba, kabi dukkan sharud’a da matakan da kowanne musulmi adalin magidanci yakamata ace ya d’ora gidansa akai, dan maza da yawa suke gur6ata zaman lafiyar gidansu tunkan aure da bayan shugowar amarya, harga ALLAH ina k’aunar y’ar uwata a matsayinta Na musulma kuma Mace, abinda zai k’ara sakamin ita arai kuma shine zamantakewarmu cikin aminci babu cutar da juna ko k’untatawa, ALLAH yabamu zaman lafiya yakuma k’ara mana tsoronsa koda gujema azabar wuta”.
     Amin, jiddah da malam suka fad’a. Sannan ya d’ora da fad’in “ALLAH yaymiki albarka, yakuma k’ara muku k’arfin gwiwa bisa k’yak’yk’yawar niyyarki”.
     Nanma Jiddah ta amsa da amin.
    Ya maida kallonsa ga Jiddah itama, “Jiddah fa mizakice?”.
        Kai Jiddah ta girgiza, cikin sanyinta tace, “Duk abinda yadace kun fad’a, fatana ALLAH yabamu k’warin zukatan aikatawa da hak’uri, sannan nima harga ALLAH Aunty tashiga raina saboda k’yak’yk’yawan halinta da awannan zamanin yay k’aranci ga mata, akanyi dogon bincike kafin asamu mace irinta, wadda miji zai k’ara aure sannan ta kar6i matar da hannu biyu dakuma zuciyar musulinci, nagode sosai aunty, halayyarki na gari da ya sanarmin tunkan shigowata gidannan tabbas nagansu a yanzu a gareki, ALLAH yabani ikon koyi da nagartarki”.
      Murmushi Aliyu yayi sannan ya amsa da amin. “To Alhamdullahi matana nagodema ALLAH Na gode muku, sai maganar kwana, Yaya kuke ganin za’ayi?”.
      Itadai Jiddah k’asa tayi da kanta, dan a ganin wanan ba huruminta baneba yanzun.
     Maimunatu tayi murmushi tareda d’an kallonsa ta kauda idonta. “Nidai a 6angarena banida matsala, akan kwana hud’un a marya Na k’ara muku shida, wannan shine gift d’ina agareku na aure, sannan aganina kwana bibbiyu Alhamdllh, amma k’anwata ya kika gani?”.
     Shiru Jiddah tayi tana sunkuyar dakai.
     “Kiyi magana k’anwata, dan kema kinada hak’in fad’ar ra’ayinki”.
       “duk yanda kikace yayi”.
      Maimuna zata sake magana Aliyu ya dakatar da ita, “Yanda kika fad’ad’in yayi, sannan kuma maganar kwana shida da kika k’ara mana mun amshi uku kawai, mun gode”.
       “Kayi hak’uri babu jayayya a tsakaninmu, idan kukak’i amsa sainaga kamar kun rainane”.
    Harara yad’an zabga Mata sannan yace, “To mungode”.
     Itadai Jiddah Uffan batace dasuba.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button